Breaking News

HAUSA NOBLE'S

13. GANGAR JIKINSA NA AURA P13 NA JAMILA UMAR
TANKO(JUT) Ta sake sa randawowa makaranta idan
hutunsu ya kare kasancewar taji haisam ya yaba da
sakamakontadon haka zai sake yi mata siyayyar
makaranta dabiyan kudin makaranta da aka ce duk term
akebiya kuma dubunnan nerori. bayan kowacce tayishiru da
kukan da dayawa suke yi sai haisam yace''duk kunyi kokari
kasancewar 'yan ajin babu marar kokari yace kowacce tazo
ta karshe anan ajin ne ab.c. Ko d ita zata zo musu ta wajen
goma sha waniabu, kunga kowacce tayi kokari karku damu.
Yadauko wata katuwar leda a gefensa ya ce dai dai suringa
tasowa suna karba.Biscuit nemai dadi ya rarraba musu
kowacce daliba ta samutun daa kan rauda har eneka
eddiward kowacce tafara murnar tayi kokari. Da haisam
yaga duk sunware yana musu wasa da dariya sai yace'' ina
si na shaida muku daga yau ko kuma ince daga dagagobe
ranar hutu idan na tafi hutunnan shikenan natafi kenan.
Gaban kowacce ya yanke ya fadi. Bamugane ka tafi ba
kenan uncle haisam '' su duka sukatambaya . Haisam yayi
murmushi yace ''kun san nicopper ne. Nazo ne yin bautar
kasa wannan makarantar(N.Y.S.C)KUMA yanxu lokaci yayi
damuka kare don haka idan na tafi hutun nan bazandawo
makarantar nan ba. Ina muku fatan alherikuma shawara
nake baku akan kowacce ta dagetayi karatu banda wasa ''
kowacce jikinta yayi sanyifuskarsu alamar basu ji dadin
wannan batu na class master dinsu ba . Suna son haisam
saboda kula dasoyayya da yake nuna musu wasa da dariya
akoda yaushe sai wasu dayawa daga cikinsu sukarushe da
kuka. Babu kamar rauda, nusaiba dahannah, ai kuma gara
rauda da nusaiba akanhannah wani sabon tashin hankali ya
rufta mata fiye dana dazu. Haisam zai bar makarantar nan
itakuma ina zata dosa ?''.Haisam ma wani tsananin bakin
ciki ne yamamaye a zuciyarsa yana tsananin son yan
ajinsa.Baya so ya tafi ya barsu yana tausayinsukasancewar
yan yara babu kuma wani malami komanyan daliban da
zasu zauna suna basushawarwari kamar hannah, wa zai
kula da hannah? A bar zancen kudin makaranta da siyayya
(provision )ita kanta tana bukatar a kula da ita dakara
karfafa mata gwiwa wajen idan ta tafi hutugida ta dawo
makaranta. Koda a gida an ce baza tadawo ba tasa kuka
har sai an dawo da ita. Ga wasuabubuwa da suka yi mata
nauyi a aji ma'ana bata ganewa sai shi haisam da kansa
yake nunnunamata har sai ta gane. Allah sarki hannah ya
fada azuciyarsa ji yake kamar ya rushe da kuka
dantsananin bakin cikin rabuwa da dalibansa. Ammaya
daure ya dinga lallashinsu, idan wadannnansuka yi shiru sai
wadansu su rushe da kuka. Haisam har ya gaji da lallashi
yace su tashi su tafidakunansu sai gobe zasu hadu a wajen
assemblyhutu, suka nufi dakunansu kowacce na
sharbehawaye. Haisam kuma ya nufi gidansa dake
staffqurters yana mai matukar jin ba dadi a ransa.
Kowayayi shiru ya daina kuka amma banda hannah.
Nusaiba da rauda suka dinga lallashinta amma takidainawa
taki cin abinci sai tayi kamar tayi shiru tadaina sai ta tuna ta
rushe da kuka. Haka ta yini curtana kuka. Rauda tace waini
hannah kukan nan dakike yi kinfi kowa son yaya haisam
ne ? Ni fa munfikusa da shi babana abokin babansa ne.
Kuma yayana auwal abokinsa ne. Haka kuma yata
ywadaya uba daya ramla budurwarsa ce koma
nacematarsa ce don har ansa musu raba, sanda
mukeamerica yan gidansu a gidanmu suke sauka insunje
kuma da muka dawo nan kasar saboda yayahaisam ma aka
kawoni makarantar nan tunda yana malami yace da abbana
makarantar akwai karatu.To harni na hakura na daina kuka
ke ba za kihakura ba kamar kinfi kowa sonsa. Ya ce dai
kekanwarsa ce kuma ni a sanina 'yan uwansa duk akano
suke na sansu kuma amma ni ban sanki ba.Kuma duk yan
uwansa babu masu kama dake ke kamar balaraniya kike ko
buzuwa ce ni ban saniba'' nusaiba tace'' haba rauda meye
haka in ba yaruwarsa bace zai fada ne ? Hannah ta sake
rushewada kuka. Daman abunda rauda take yi mata
yaisheta. Tunda aka kawo ta malam haisam yacekanwarsa
ce taga rauda tana kishi da ita. Wai ya za ayi ace hannah
kanwar yaya haisam ce bayan itakadai ce kanwarsa a
makarantar. washe gari da sassafe dalibai suka shirya
kayansutsaf na tafiya gida suka saka kayan makaranatar
(uniform)suka dunguma babban dakin taro (hall)don yin
assembly hutu. Hannah nusaiba sukakinkimo jakunkunan
kayansu na sakawa sukakuma rarrataya jakar litattafansu a
baya. Akwatinsu kuwa da katifu da bokitai a wani daki ake
lufgawaa rufe. Ba.a tafiya dasy gida. A bakin hall din
sukaajiye jakunkunan sannan suka shiga cikin hall dindan
yin assembly. Kallo daya haisam yayi wahannah yasan
tasha kuka kuma tana cikin tashinhankali . Principal ta
sanarwa dalibai cewa an basu hutun kwana arba'in da
biyu. Don haka ranar dakwana arba'in da biyi ta cika
kowacce daliba kadata kara ko kwana daya. Idan ta kara to
za.a koratagida. Baza a karbeta ba. Sannan tayi musu
nasihohiakan idan suka je gida su dinga taya iyayensu
aikibanda yawo a gari gidan kawaye balle kuma masu
samari. Mataimakin principal ma ya tofa albarkacinbakinsa.
Ya jawa daliban kunne akan su zamamasu da.a da ladabi
da biyayya a duk inda suke.