MIJIN MARAINIYA PART 1
MIJIN MARAINIYA PART 1
.
Na Fadeela Lamido
Bismillahir rahmanir rahim
Zaune take a dan ma tsakaicin gidan su tana ta faman
share hawaye wata dattijuwan mata ce ta fito daga daki
tana fadin , kin fara ko, dama ke idan tsohon munafunci ki
ya tashi ba mutunci gareki ba, wlh uwarki ta bar miki
mugun gado, ki zauna kiyi ta kuka salon iya ta ce ana miki
wani abu, matsuwa tayi ta rike mata kunne tace ai baki ga
komai ba safna sai rada na koreki gidan nan , zakiyi kuka,
yadda uwar ki tasani kuka ta tura min bakin ciki kema sai
na tura miki bakin cikin da zai kashe ki . Safna taji zafin
wannan ruko, fitsari ne yake bin kafafun ta, tace goggo dan
allah kiyi hakuri , indai kuka ne na daina. Kar ma ki daina
dan jakar ubanki, tashi maza ki wanke kafafunki ki dauki
rake , kuma karki dawo gidan nan sai ya kare. Jiki na rawa
safna ta mike ta dauki bukiti taja ruwa a rijiya ta shiga bayi,
cikin sauri safna ke wanka dan gudun fadan goggo. goggo
na tsaye safna ta fito da bukitin wanka a hannun ta goggo
ta bita da harara , da sauri tashiga dakin ma haifiyar ta,
wanda a yanzun ita kadai take kwana acikin sa, cikin sauri
ta jawo ledan kayan ta, ta fara cirowa tana dubawa duk
tsun mukara ne , masu dan kyan goggo ta kwashe tayi
kyauta dasu, haka dai ta dauki daya daga ciki ta saka,
tadauki raken goggo ta kama hanya. tafe take tana hada
hanya domi ita bata iya tallah ba sai dai idan mutun ne
yakira ta ,haka tai ta tafiya ko nera ba tayi ba, ta gaji ta
koma gida. goggo na zaune a tabarma ita da yaran ta guda
biyu iro da salma, safna ta shigo , goggo ta mike yanzun
nan dawo min da raken nan kikayi , iro tashi kaba yarinyar
nan kashi rashin duka ke damun ta. Kamar jira yake yamike
da sauri ya fara kai mata duka daga kar she ma dukkan su
suka taron mata wannan na duka wannan nayi , sai da suka
ga bata iya motsi suka bar ta
.
WAIWAYE
malam musa mutumin kirki ne matan sa biyu goggo itace
uwar gida, sai mahaifiyar safna wanda suke kira Inna, tunda
malam musa ya auri goggo ta haifi iro bata kara haihuwa
ba dan haka iya mahaifiyar malam musa ta matsamai ya
kara aure, duk inda malam musa yaje neman aure ba a
bashi saboda masifar matar shi, wata rana malam musa na
cikin tafiya akan tsuhuwar mashin dinsa yaci karo da wata
bafulatana batafi shekara sha biyar ba tana tafiya tana
kuka, tsayawa yayi ya tam baye ta lfy take kuka, sai da ta
share hawaye sannan tace wata yaya tace tayi aure a binni
tunda mijin ya tafi da ita har yau bamu sake ganin ta ba,
shine muka fito neman ta su baffah suka ce na jira su
karkashin wata bishiya tunjiya har yanzun basu dawo ba,
malam yace ina ne garinku , kame kame takama malam dai
yagane bata san sunan garin su ba, goya ta yayi abayan
mashin din sa dan su kara duba wajan ko iyayan ta sun
dawo, suna zuwa suka duba babu kowa awajan , dan haka
malam musa yace ma wani abukin sa dake zaune a waja
bayanin cewa ko da iyayan ta sun dawo ya kawo su gidan
shi. malam musa gidan iya ya wuce da yar fillo saudatu dan
yasan halin matar sa, iya ta kar beta hannu biyu tare da
mamakin wauta irin na filani, sai da saudatu tayi shekara
biyu awajan iya ba labarin iyayan ta ,dan haka iya ta
matsawa malam musa ya auri saudatu, malam musa yabi
umarnin ma haifiyar shi dan shima yafara tunanin haka.
bayan an daura musu aure da wata uku goggo ta sake
haihuwan salma itako amarya saudatu sai da ta shekara
biyu sannan ta haifi safna , saudatu tasha wahala a gun
goggo dan ma tana samun kariya agun malam safna nada
shekara sha hudu tafiya ta kama malam zuwa kauyen su
iya dan kai masu ziyara, iya tace atafi da saudatu tunda
bata taba zuwa ba. lokacin safna nazuwa makarantar
primary tana aji shidda dan haka suka barta gun goggo,
bayan wani dan lokaci da tafiyan su labari ya same su,
motar da suka shiga ta kone kurmus babu wanda yayi rai,
haka su kai ta kuka a yanzun haka shekaran su daya da
rasuwa inda goggo tahana safna makaranta sai tallan rake.
.
Abduljalal wani matshin yaro ne me ji da kanshi daka
ganshi kaga dan gata bazai wuce shekara ashirin da
bakwai ba, dogo ne sosai yanayin tsawan shi sai ka zaci ya
wuce shekarun shi haka fari ne tas, bashi da yawan fara,a.
Idan kaga jalal na dariya to da ummin sa ne , ko kuma cikin
abokan sa, zuwa yayi ya samu ummin sa zaune a falo, yaje
ya fada jikin ta yana fadin ummi yinwa nake ji. ummi tace
jalal karfa ka karya ni, wai kai baka san ka girma bane.
haba ummi wanni girma nayi ne, kodan kinga kin samu
wata.
.
tace ba haka bane jalal ya kamata ka fahimci cewa ka
girma yanxun fan ba da bane, ga abinci nan kaci , karani
gida hajiya sahura. cokali daya ya kai bakin sa yace ummi
na gaji zo ki bani abaki. gargiza kai ummi tayi ta matso ta
fara bashi abaki sai da ya koshi yace ummi bar shi haka na
koshi. sai da ummi ta shiga ta gama gyara wa sannan ta
fito, ta samu jalal na zaune a falo kanan kaya ne a jikin shi
yayi kyau sosai, idan kaga jalal da ummin sa sai ka rantse
yayar sa ce, jalal ne ke jan motan ba, suna tafiya suna hira
. sunyi nisa sosai sun shiga unguwan su hajiya saratu
abduljalal ya hango wata yarinya tana tafe tana kuka ga
kuma rake akan ta, yace ummi ji wata yarinya yar karama
an daura mata talla, yanzu dan Allah ummi wa zai sha
wannan raken kofa kan kare shi ba,ayi ba. ummi tace kai
kake ganin haka jalal kazamai yan uwan ta zasu sha. jalal
na kawowa kusa da yarinyar ya tsaya ya kira ta da gudu ta
karaso, yace me yasa meki kike kuka? tace idan na koma
gida raken nan be kare ba duka, duka za,ayi min, jalal ya
tausaya mata ya kalli jikin ta yaga shedan bulala, yace
ummi zan saya raken nan. da sauri ummi tace amman dai
ba a mota ta zaka zuba wannan kazamin raken ba. yace sai
ta bawa almajirai , ya sunan ki ya tam baye tace safna sai
da ya maimaita sunan sannan yace raken na nawa ne? tace
nera dari, dari biyu ya ciro ya mika mata, tamiko hannu zata
karba , ummi ta daka mata tsawa taja baya da sauri, jalal
yace ummi me tayi ? yaro ban yadda ku hada hannun da
yarinyar nan ba ka aje mata akasa sai ta dauka.
.
Jalal yace haba ummi ai ba taba ta zanyi ba, bata kawai
zan yi. ummi tace ashe tsaftar ka ta banza ce , idai ka bawa
yarinyar nan da hannun ka kuwa. juyawa yayi ya ajewa
safna kudin akasa, da saurin ta ta tsuguna ta dauka tana
ma jalal godiya, ummi ko hararar ta kawai take. bayan sun
dawo gida ummi ta lura jalal fushi yake da ita, dan haka ta
bishj har dakin sa, tace jalal me ya same ka, kake ta fushi?
abduljalal be iya boye wa ummi komai dan haka yace ummi
yarinyar nan ce take bani tausayi, ummi da,a kwai yadda
zanyi dana tai make ta. ummi hada rai tayi tace yaro halin
ka yana bani mamaki in banda abinka ina ruwan ka da
yayan talakawa da har zaka damu kan ka, akan wata banza
yarinya kazama, da kikiya. ummi bazaki gane ba nasan da
dady ne zai fahimce ni, ummi raken nera dari ne fa akanta,
ummi kuma gashi yarinyar kyakyawa da ita. zoro ido ummi
tayi tace yaro kai ne kuwa, kaga yarinya mumuna kace
kyakyawa ko dai gamu kayi ne, to naji kyakyawa ce me
kake nufi yan zon. ummi ni ba abinda nake nufi kawai dai
inason ki tai maka mata ne. kaga jalal karna kuma jin
manar yarinyar nan abakin ka, ta mike da sauri tabar wajan.
itako safna zuwa tayi gurin wasu almajirai tana raba musu,
iya na daga gefe tana kallon safna, saida ta gama ta juya
zata tafi iya ta kwala mata kira , ai tana ganin iya ta roga da
gudu ta kamkame ta, cikin rudu iya ta daga kan safna tace
a ina kika samu rake kike rabawa Jama,a? Safna ta kwashe
labari kaf ta fadawa iya, salati iya ta shiga yi, tana fadin ina
can zaune za,a lalata min jika, wanne dan iskan ne, yabaki
kudi? iya nima ban san shi ba kawai gannin su nayi amota.
be miki komai ba dai ko?
.
ba abinda yayi min, iya tasa keyar safna tayi tace muje na
samu goggon taki, in kaskiya ne ta daurawa salma mana.
suna shiga iya ta fara fada taita fada tundaga ranar rokon
safna yadawo hannun iya, safna dadi takeji sosai agurin iya
babu ta kura, iya duk ta. hada dan kudin da take da shi ta
mai da safna makaran ta, haka iya tai ta wahala da safna
ana haka safna ta gama primary schools, gashi iya nason
safna ta ci gaba da karatu kuma bata da kudi Dan haka ta
fara toya kosai a kofar gida, iya bata barin safna tazo gurin
tuyan kosan ta sai dai aikace aikacen cikin gida duk da
cewa iya ba wani karfi gareta ba, amman safna ta murje
tayi kyau kamar ba ita ba. a yanzun safna tana J S2 dan
haka iya ta fara tunanin aurar da safna dan duk da cewa
safna bata wuce sha bakwai ba, itako safna babban burin
ta shine ta tayi karatu me zurfi. ana cikin haka rashin lafyya
ya kama iya dan kosan da take yi ya gagara, safna ta rasa
ya zatayi , tana kuka ta nufi gidan goggo, ta gaya mata iya
babu lafiya. fada ta fara tana fadin aiga irin ta nan, kina nan
muna neman kudi tazo ta dau ke ki, sai yanzun da ciwo
yakama zaki taho to bamu da kudi, wacce ki bani waje
karna kara ganin ki gidan nan, haka safna ta juya tana tafe
tana kuka. haka safna ta dawo ta samu iya kwance cikin
amai, ta shiga gyara wajan bayan ta gama ta fara tunani
yadda zata samo ma iya abincin da zata ci, tashi tayi ta fita
ta gama bulayin ta bata somo komai ba ba yadda zatayi
dole ta koma wurin goggo sai da ta gama zagin ta sannan
ta bata ragowar tuwan jiya da sauri ta nufi gida tana ta
sauri , tun kafin ta isa kofar gidan ta hango muta ne tana
shiga gidan kara kamkame tuwan ta tayi ta sheka da gudu
tana shiga taga an lulube ta da zani, safna fadawa tayi jikin
ta tana kuka. Wata makociyar su iya ta taho ta dafa safna
tace kiyi hakuri safna ki daina mata kuka Allah ya karbi
abinsa kuma ya fimu santa dan haka sai muraka ta
da.ardu,a haka safana taita kuka har aka kai iya makwanci
ta safna bata bar kuka ba. bayan anyi bakwai da yamma
goggo ta hada kayan ta ko salama batawa safna ba ta
wuce gida, gidan iya kuwa safna ce ka dai aciki sai ta tsince
kanta cikin matsanan cin tashin hankali, haka safna ta
kwana ita kadai acikin gidan, safna na tashi hankalin ta
kara tashi yayi musamman da ta leka dakin iya taga wayam
dan haka ta tsoguna abakin kofar iya ta saki Kara.
makociyar iya baba dije taji kukan safna aguje ta zagawo
tace Ina goggonki . safna tace ta tafi tunjiya au yanzu nan
nufinta baza ta rike kiba, lalai abin nata babba ne, tashi ki
hada kayanki na rakaki .
.
cikin tashin hankali safna ke hada kayan ta tana ganin ita
meye amfanin ta tuda ba iyayen ta iyar ma da take takama
da ita ta tafi ta bar ta itama da mutuwar kawai tayi. suna
shiga gidan goggo suka same ta tana tankadan garin tuwo,
tana ganin safna ta hada rai, bayan sun gaisa tace yazaki
tafi kibar yarinya ita daya acin gida. cin sauri goggo ta fara
rantse rantsan ita sam bazata rike safna, baba dije ta
fahimci da gaske ta keyi tace to naji to me zai hana ki kaita
gun dangin iya. cinkin sauri goggo tace ina naga kudin
motan da zan kai ta. kwance haban zanin ta tayi takwaso
gudin wajan duk ta mikawa goggo ta sannu ta karba harda
fadin yauyau zan kai ta. goggo bata tashi kai safna ba sai
gaf da mangariba tace dauko kayanki mutafi , safna ta
dauki kullin kayanta suka kama hanya, motar cikin gari suka
hau , safna tace azuciyar ta dama motar garin su iya acikin
gari ake hawa ,take farin ciki ya rufeta ko banza yau zataga
gidaje masu dan banan kyau . suna isa aka sauke su garin
kamar rana saboda fitilun da suke haka ko,ina gidaje kuwa
fadan kyansu bata lokaci. suna ta tafiya taki karewa ita dai
safna bin goggo kawai take suna zuwa gurin wata katuwar
bishiya, goggo tace safna zoki zauna anan naje na dawo ,
haka banzayen kakannin ki sukama uwarki har ta mutu bata
kara saka su a idon taba.