Breaking News

HAUSA NOBLE'S

14. GANGAR JIKINSA NA AURA P14 NA JAMILA UMAR
TANKO(JUT) Saura malamai ma suka yi musu nasihohi
akan suyiamfani da abunda principal ta fada musu
damataimakinta. Sai kuma daga karshe malami uku da
suka zo bautar kasa suka yiwa dalibanmakaranta sallama
akan in sun tafi sun tafi kenanba zasu dawo ba. Malaman
yan bautar kasar suneuncle haisa, rose iliya da hassan
bawa. Dalibaimasamman ma yara sunji ba dadi saboda sun
sabada malaman. Musamman haisam saboda kirkinsa da
wasa da dariyarsa yasa kowacce daliba tahi tanasonsa.
Musamman daliban da take koyarwa sunamatukar bakin
ciki da rabuwa da malaminsuwanda ya kware wajen koyar
musu da geography.Nanfa dalibai suka rode da surutu
wasu na kukawasu na fadin'' we miss you ! We miss you so
much!! Uncle haisam, we miss you more, stay don'tgo
please. A haka dai principal da sauran malamaisuka fice
suka umarci daliban suma su tafi dukwacce aka zo dauka.
Hannah da nusaiba a bakinbarandar hall din wajen
jakunkunansu suka zauna.Nusaiba tace'' allah yasa dady
na tun jiya yaxo kano daga abuja. Ya kwana a kano yau da
safennan ya kamo janyar kazaure. Kar ace yau zai
tahodaga abuja gaskiya sai yamma zai karaso
kazaurewallahi murna nake yi kaman za'a sani a
aljannah.Dama ace ina rufe idona na ganni a gida''
hannahtayi murmushin karfin hali don babu walwala a
zuciyarta dama ace duk wanda son zuwa gida yadaga
hannu sai tafi kowa daga hannu dan ta zaunaa makaranta.
Nusaiba ta kallo hannah wacce tunsafe bata murna.
Musamman ma yanzu da taji ancehutun kwana arba'in da
biyu za'ayi sai ranta yasake baci. Ga kuma babban tashin
hankali haisam zai tafi. Nusaiba ta kula hannah ko irin dan
dokintafiya gida bata yi. Sai surutu take ita kadai
hannahbata sauraron ta sai wani tunani take
daban.Nusaiba ta dan zungureta da gefen hanni tace''waike
hannah meke damunki ko murna bakya yigida fa yau zamu''
hannah ta nisa sannan ta sake yin murmushin karfin hali
tace'' me kika gani ?Wallahi nima ina murna dama na bude
ido in gannia gida yanzu'' nusaiba tahi dadi da
wannangudunmawar hira da hannah ta fara bata tace''
nikuma ina zuwa gida fruit salad zansa ayi min in ciwallahi
shi nake marmari ''Nusaiba ta zabura tace'' meye
makani,kwatantamin yadda yake nima idan naje gida incea
soyamin'' hannah tace'' ai shi makani dafa shi akeyi. Ba
kisan gwaza ba ? Nusaiba tace'' gwaza!gwaza!! Menene
ma gwaza ? Oh cocoam zaki cemun. Kai allah ya sawake
inci gwaza sai kace wata yar kauye ? Hannah tayi shiru don
tasan ita yarkauye ce kuma acan su gwaza abun marmari
ne.Nusaiba tace. A ina kuke samun gwaza ni banaganin ta
ma ko a kasuwan abuja'' hannah tace mumuna samu'' uncle
haisam ne ya tunkaro wajen dasuke zaune , su duka suka
mimmike tsaye don girmamawa gami da cewa , good
morning sir'' yace'' morning hannah, good morning nusaiba.
Yauyammata sai gida naga nusaiba sai murna kike yiko ?
Nusaiba tace yaya haisam murna yau nakelamar za'a
sakani a aljanna. Haisam yayi dariya yace '' hannah kefa,
kema kina murna kaman za a sakaki a aljannah ? Hannah
tayi murmushin karfinhali tace'' eh'' ina murna nima,
shigowar wata motakirar end of discussion ce ta katse hirar
da suketazo ta tsaya. Kafin mutumin da yake ciki ya
fitodaga motar nusaiba idris ta daka tsalle mike dagudu ta
nufi wajen motar nan tana cewa babama oyoyo. Ya taho
shima da saurinsa ya rungume ta suduka murna suke yi.
Nusaiba ta ruko hannunmahaifinta ta nufo wajen da malam
haisam dahannah suke zaune su duka suka mike
dongirmamawa. Nusaiba tace, ga class master mu danake
baku labarinsa a wasika nace shi yake kula damu uncle
haisam sunansa. Alh idris yayi dariyayace. Oh uncle haisam
duk wasikun nusaiba sai tarubuto mana labarinka da kai da
kawayentahannah da rauda. Haisam yayi murmushi yace
allahsarki ai ga kawarta hannah , hannah ta duka tagaishe
shi ya mikawa haisam hannu suka gaisa. Nusaiba tace''
baba daga wannan hutun unclehaisam ba zai dawo ba.
Alhaji idris ya ce da haisam''ai dama teaching practice kake
yi ananmakarantar ? Haisam yace ''eh bautar kasa
(N.Y.S.C)nayi kuma mun gama. Alhaji idris yace badadi
yara sun saba da kai gashi zaka tafi, mun gode allah ya
saka da alheri. Haisam ya ce '' ba komai aikannena
ne.nusaiba ta ciro takarda daga jakarta dabiro ta mikawa
haisam tace ya rubuta mata lambarwayar sa. Ya karba ya
rubuta mata. Ta karba tamikawa hannah tace '' hannah
rubuta min lambarwayar ki a kasan ta uncle haisam''
hannah tayi turus ita bata taba taba wayar bama balle ta
sanyadda ake amfani da ita har ta san wata lamba.Haisam
yayi sauri ya ce a'a ke rubuta mata taki zatakiraki. Nusaiba
ta rubuta lambar wayarta ta mikawahannah, hannah ta
karba. Daga karshe hannah takamawa nusaiba jakarta
suka nufi wajen mota. Alhaji idris ya bude but haisam ya
kama ya saka.Nusaiba ta rungume hannah su duka
sunahawaye. Nusaiba tace'' kina zuwa gida ki kirani awaya
kuma kullum zamu dinga waya munagaisawa. Alhaji idris ya
dafa kansu ya ce '' ku dainakuka hutu za kuje yana karewa
zaku dawo ai baku rabu ba gaba daya.