HAUSA NOBLE'S
3.GANGAR JIKINSA NA AURA P3 NA JAMILA UMAR TANKO
(JUT) Ya ce "Wai shin
me kake tambaya ne? *Yar makaranta ka
kawo daliba ko kuma mai aiki kakawo gidan
Malamai a nuna maka gidan Malamai(staff
quaters)? Malam Habu ya ce "A'a daliba
nakawo 'yar makaranta ce. Su duka suka
kyalkyaleda dariya suna tafawa wani harda
buga kafa akasa. Abun ya daurewa Hanne da
Mahaifinta kai. Menene abun dariya?Konan ba
ita bacemakarantar 'yan mata ta gwamnatin
tarayya dakeKazaure? Malam Habu ya
tambaya suka ce "Nan cemakarantar daka
ambata amma watakila kayibatan kai ko baka
ji dai-daiba. Malam Habu ya ce"Batan kai
kamar yaya? Daya ya ce "Nan makaranta ce ta
'ya'yan masu hannu da shuni,'yan birnimasu
kokari, ba haka kawai dan ance 'yarka
tacimakaranta ba kaje ka suyo akwati da
katifa kazoka zabi makarantar da ranka yake
so ka shiga kacega daliba. Daya ya ce "Ko dai
waccan makarantar ceta gwamnatin jiha
suka rasa suka shigo nan. Koda yake ko can
dinma dakyar su kwashi wannan.Sannan na
karshe ya ce "Ku dai ku tsaya babumamaki
nan din taci abun ai na Allah ne, Malam
inatakardar shaidar taci nan makarantar?
Malam Habuya ce "Mu babu wata takardar
shaidar cinmakaranta a tare damu, ni dai
kansilan garinmu yazo har gida ya ce
jarabawar da *yata tayi a birnita fito kuma
duk karkararmu ita kadai taci, maigarinmu
ma ya turo inje ya shaida min ya ce lallai-lallai
nan taci in kawota, ya ce min makarantun'yan
mata a Kazaure guda biyu ne data
gwamnatintarayya data gwamnatin jiha, ta
gwamnatin tarayya taci in kawota. Amma ni
babu wanda yayi minzancen takarda. Suka
sake kecewa da dariya. Dayaya ce "Malam sai
kuyi waje don baza ku shiga bababu takardar
shaida, ku koma ku sami kansila komaigarin
naku su baku takardar shaida sai kuzo
kununa sannan mu barku ku wuce. Yau gashi
kusan wata daya ke nan da aka riga aka
gamakawo yara har sunyi nisa da fara karatu,
kai saiyanzu kake kawo 'yarka. Malam Habu
ya ja 'yarsaa sanyaye suka yi waje, zuciyarsu
cike damummunar damuwa.Hakika Nigeria
muna cikin wani hali lokacin da yake ajiye
kayan dake hannunsa a waje,yakamawa
'yarsa akwatin dake kanta suka saukekasa.
Suka tsaya suka yi cirko-cirko suna kallon
masu gadinnan,wadanda har yanzu basu
daina yabo musubakakenmaganganu ba.
Malam Habu ya nisa ya ce "AllahSarki rayuwa,
Allah Ka fimu sanin halin da muke ciki kaizaka
fitardamu, 'yar Baba zauna a gefen akwatinki
kinjikafin mugayadda Allah zai yi damu. Isa
kansila da maigarisuka ja mana wannan
wulakancin. Ni nasan a rina, shi yasa dafarko
nakifur da akace za'a kaiki birni daukar
jarabawa,kuma kema daakayi kiranki me yasa
ki amsa musu? Kika ce kinason karatun, ga
irinta nan ai. Hanne ta zauna a hankali
jikintayayi sanyi,wanda ko yatsanta wuyar
dagawa yake yi mata.Zuciyarta cikeda
damuwa, babu abin da take tunawa
illakomawarta gida haduwarta da iya Abu
kishiyar uwarta da'ya'yanta.Irin tsananin
azabar da suke gallaza mata dabautar ta din
daake tamkar baiwa alokacin cinikin bayi.