HAUSA NOBLE'S

SO NEH... PART (4)

Na tashi da sauri naje na dauki wayata na duba domin
naga waye ke kirana, sunan Fatima na gani alamar cewa
itace ke kirana, na daga kiran tare da kara wayar a kunnena
nayi sallama, cikin tattausar murya Fatima ta amsamin tare
da cewa 'Abba kawuni lafiya' na amsa mata da 'lafiya' kafin
na kara cewa wani abu sai tacemin 'Abba narokeka da ka
amsamin da kanasona idan ba haka ba zan fada
mawuyacin hali, tabbas son ka ya kai girman da bazai iya
fita daga zuciyata ba, domin bazan iya bacci ba sai naji
muryarka, a duk lokacin da nake jin lafazinka yakan
karamin karfin gwiwa, duk wata damuwa da nake ciki
nakan manta da ita a duk lokacin da nake magana dakai,
yaya na na durkusa bisa gwiwoyina ina rokonka da ka karbi
soyayyata kada na fada wani hali'.
A lokacin ne naji wani abu ya soki zuciyata wanda na kasa
ganewa menene, na danyi shiru sannan nace da Fatima
'kanwa ta kada ki jefa kanki cikin wani hali akan soyayya,
kuma inaso ki sani cewa komai nufine na allah, idan ya
nufa zaki zama matata to ba abinda zai hana, idan kuwa
yayi nufin bazaki zama matataba to ba yadda za'ai na
aureki, kuma furta soyayyata a gareki ba zai tasirin komai
ba'.
Cikin wata murya mai sanya tausayi Fatima tace dani 'yaya
Abba idan har ban aureka ba mutuwa zanyi, nidai burina ka
amince da soyayya ta kuma ka kaddara a ranka zan zama
matarka da yardar allah' na amsa mata da cewar 'idan allah
ya nufa kece mata ta sai ince allah yasa hakan shine mafi
alkhairi, idan kuma...'
Fatima ce ta dakatar dani kafin na karasa fadin magana ta
da cewar 'yaya Abba banaso naji kana fadamin wani abu
da ya danganci rabuwarmu da kai saboda idan har hakan ta
faru to zan rasa rayuwata'
Haka muka shafe a kalla awa guda muna magana da
Fatima amma bata nunamin alamar zata hakura da kiran
ba, sai nine na cemata 'Fatima ya kamata ki kwanta saboda
dare yayi' haka mukai sallama da ita amma sai taki
katsewa kiran sai nine na katse kiran sannan na ajiye
wayata na kwanta da tunanin Fatima a zuciyata, aikuwa
kwanciyata ke da wuya sai bacci ya daukeni...