HAUSA NOBLE'S
SO NEH... PART (3)
Ina bude message na farko naga ta turomin adress nata ne,
dakuma cikakken sunanta Fatima Bulama, sannan kuma
daga kasa akwai hotunanta guda uku, tsayawa nayi na
kasa motsi ina kallon hoton nata, ba komaine yasa ba sai
saboda tsananin kaywun ta.
Fatima ta kasance kyakykyawar mace ta gaban kwatancen
mai kwatance, sannan ta kasance black beauty ce amma
ba baka can ba, bakin ta ya kasance madaidaici wato
chocolate colour ce wanda duk wanda ya ganta sai yaji
inama ace shine zai aureta, inanan zaune na kasa motsi sai
kallon fuskar Fatima kawai nakeyi wanda a lokacin naji na
fada cikin tunani.
saida na shafe kimanin mintuna 10 ina zaune ina kallon
hoton, sannan na fito daga message din, na bude na biyun,
ba komai na ganiba a cikinsa sai sako daga MTN mai cewar
an saka mini credit a waya ta na naira dubu biyu, na duba
lambar da aka turomin sai naga lambar Fatima, a lokacin ne
na fara zargin anya kuwa Fatima ba wata manuface a ranta
ba? Amsar da na kasa baiwa kaina kenan, haka na fito
daga cikin dakina naje na gaishe da iyayena sannan na fita
waje domin zuwa wajen karyawa.
Haka na wuni cikin rashin sukuni a wannan rana, koda
wanne lokaci na zauna sai tunani, abokina Aji ya tambayeni
shin menene ke damuna yau gaba daya na chanza, sai
nacemasa bakomai, haka ya gaji da tambaya ta nikuma
naki fada masa komi saidai nacemasa bakomai, haka ya
hakura amma bai gamsu da amsar da na bashi ba.
Lokacin da dare yayi naje na kwanta na dauki wayata na
bude facebook ina chat da abokaina har bacci ya fara
dauka na, sai na ajiye waya ta akan tebur sannan na
kwanta domin nayi bacci sai baccin ya gagareni sai tunanin
Fatima, ina cikin hakan ne naji wayata tana ringing.