HAUSA NOBLE'S
9&10. GANGAR JIKINSA NA AURA P9&10 NA JAMILA
UMAR TANKO (JUT)
Wannan rana ita ake kirada '' social night''
uncle haisam kuma shine social master wato
shine malamin da yake kula da dalibaiyake
kula da c.d din da ake kunna disco da
bidiyoda talabijin din da ake kunnawa. A
wannan dare anyarjewa dalibai su saka
kayansu na gida{persinal}kowane iri ne kama
daga leshi ko shadda riga daskit kai har jeans
da tea shirt duk zasu iya tsukewa. Rauda
sarkin rawa ita har tunanin wannan
asabardin wacce irin rawa zanyi don har fili
ake batakowa ya koma gefe yana kallonta
rawa salo salohar wasu suke kiranta janet
jacson wai kanwarmacheal jacson nusaiba
kuwa ita da hannaah babuabinda suka fi so
irin kallon bidiyo hausa fim masu kyau malam
haisam yake samowa ko nigerian fims.Social
night din wannan asabar din bata
yiwahannah da nusaiba dadi ba saboda
bidiyo talalacebabu kallo sai dai c.d aka kunna
aka ware kida dukmai bukata yaje ya cashe
wasu na rawa wasukuma na gefe suna kallo.
Amma wasu suna kan barandar wajen hall
din a zazzaune basa sha'awaryin rawa ko
kallon masu rawa kungiya kunkiyakowanne
da group dinsu suna waje suna
zazzaunesuna hirar duniya. Hannah da
nusaiba suna dayadaga cikin wadanda basu
shiga cikin hall din bawajen kida suna
zazzaune a can kan wata barandar ofishin
malami suna hirar duniya, hirarma ma jifa jifa
suke yi saboda duk rayukansu abace yake
yau babu kallo kuma wani
hadaddenamerican film mai suna''mr
bones''uncle haisamyayi musu alkawarin zai
saka musu. Nusaiba tayiajiyar zuciya tace
anya kuwa yau zan iya bacci saboda bakin
ciki na kudiri niyar danin firm dinnan,wallahi
fim din akwai abin dariya muna dashi fa
agidanmu. Hannah tace na last week ma yayi
kyauga abin dariya osofia in london yaya
haisam ya iyazabo man films masu kyau. Wata
murya ce abayansu tace na kamaku kuna
gulmata'' suka juya da sauri sai suka ga yaya
haisam ne su duka sukatuntsire da dariya ya
zagayo suka matsa masa yashiga tsakiyarsu
ya zauna yayi murmushi ya cekuna gulma ta
ko, dan ban kunna muku kallo bako ?
Nusaiba cikin shagwaba tace'' yaya haisam
harkwalla nayi fa wallahi yau duk ranmu a
bace yake. Haisam yayi dariya yace'' kai haba
harda kwalla ?Ke fa hannah kema kinyi
kukan ? Tayi murmushitace a.a banyi ba uncle
haisam. ''yaci gaba da jansuda hira yana
zolayarsu kamar yadda ya saba wasada
dariya da dukkanin daliban
makarantarmusamman da wadannan ukun.
Ya ce dasu '' ga rauda can a hall tana
cashewa kuje ku tayata manako kuma kuyi
mata liki. Suka danyi dariya suka ce ''mu
bama rawa'' suka ci gaba da jugum , haisam
yalura yau dai nusaiba da hannah babu kanta
basason magana balle doguwar hira yace
nusaiba,hannah yaya haka kowacce tayi
zugum babu nishadi kamar yau ba ranar
social night ba. Nusaibatace''yaya haisam
tsabar bakin cikin rashin kallonnan ne yake
damunmu.'' yace shi yasa baku fara'a?To
yanzu daya bayan daya sai kun yimin waka
darawa tunda yau social night dole kuyi
murna'' cikinshagwaba nusaiba tace''yaya ni
bana iya waka ba sai dai hannah ta fara
tunda itace karama. Hannahtayi dariya tace to
bari inyi muku wakan sarkingarinmu,''
hannah ta fara tafi ta fara rero waka.Haisam
yace'' to tsaya tafi akeyi muma mu
dingatayaki muna muki amshi ? Tace'' ai da
kwarya akekida dan dai babu kwaryar ne.
Yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan abun
busar daya karba awajenta ya ce zai ajiye
mata ya ce'' ga abun busarkima ki busa mana
ki rero mana wakar kiwo'' cikinfarin ciki
hannah ta karbi abun busarta ta
haujujjuyashi tana cewa'' allah sarki abun
busata nadade ban busa kaba,'' nusaiba tace
'' lah busa muji yadda akeyi'' hannah ta
kaikaice ta fara busa abunbusarta tana rera
waka kamar haka. muyi kiwosamari. Kuyi
kiwo yan mata kiwo baiwa ne. Wakabaiwa
ce. Haka busa ma baiwa ce kuyi
soyayyasamari. Kuyi soyayya 'yan mata ke 'yar
budurwaina naki gwanin ? Ni nawa gwanin
baya nan. Yayi tafiya amma koda bana tare da
gangar jikinsa.Ruhinsa yana tare dani. Haisam
yace '' hannahtsaya meye koda gangar jikinsa
bata tare daniruhinsa yana tare dani ''? Tayi
shiru can tace ohonima haka ya mun wakar
nusaiba tace meye ''ruhi ? Hannah tace ''
nima ban sani ba, ina jin larabci ne , haisam
yayi dariya ya ce '' yarinta mai dadi. Kwanci
tashi yau kwanan hanna arba'in amakaranta
har an kafe musu tine table dinjarabawa
wato end of 1st teem
examinationkasancewar daman dalibai sai da
suka yi kimaninwata guda da dawowa
makaranta sannan akakawi hannah babu
abunda yaya haisam yake yi sai nasihohi da
yake yiwa yan ajinsa wato j.s.s 1a dakowacce
ta cire wasa tasa littafin karatu a gabantadon
suci jarabawa. Haka kuma wasu lokuta ya
kankira kannansa rauda, nusaiba da hannah
yanakara musu fada dasu dage sufi kowa cin
jarabawaya sake xewa'' hannah bana jin
fargabar su rauda kamar ke don haka ki dage
duk abunda ba ki saniba ki tambayi nusaiba
ko rauda idan sun sani sukoya muki, idan
kuwa basu sani ba to kuzo kutambayeni.