== RAYUWAR NIHILA 1 ==
== RAYUWAR NIHILA 1 ==
Nihila!!! Nihila!! Nihila!! Tana bacci taji mominta na kwala
mata kira ta tashi jiki duk a mace ta amsa da naaam ina
zuwa momi ta fita zuwa parlor wurin mommy ai dama aikin
kenan baccin asara in bashi ba ba abunda kika sa a gaba
ke kullun kenan aikinki bacci wuce kije ki daura dinner
daddyn ku na dawowa tana magana a shagwabe tace
momy bakya sani naji dadi tace au kaji mun yarinya daga
cewa ki daura girki in baki daura ba uwar me zakiyi me
amfanin mace ba girki wuce dalla tun kan nayi koli koli dake
ta shige kitchen ta fara aiki gadan gadan spaghetti ta daura
wanda yaji ganye da vegs ko ina ya dau kamshi bayan ta
gama taje ta shiga wanka ta fito tayi sallah ta idar kenan
taji wayanta na Kara tana dubawa taga Wanda tayi zaton ne
kuwa.
.
Ta dau tana murmushi tace hello on the other side kuwa
yace ran gimbiyad my life saina kiraki anjima tace toh
babe tare da kashe wayan. Tunani fal a ranta akan hisham
ganin in mamanta ta gane suna waya dashi zata shiga
babbar matsala Dan ko tace bata yarda ba Allah be yarda
ba.
.
Nihila Muhammad yarinya ce yar kimanin shekara 16
tanada chocolate complexion mai kyau wanda yaji madara
idan ka ganta kaman black americans tanada kyau masha
Allah ga dara daran idanu Allah ya mata lips pink masu
kiran heart wanda sukayi daidai da fiskanta tanada shape
wanda yayi fitting dinta daidai ba'ace bata dashi ba komai
dai nata daidai yake batada makusa 'yace a wurin
Muhammad Tahir Wanda Allah ya wadata da arziki masha
Allah suna zaune a abuja a unguwar garki itace last born a
gidan su tanada sisters biyu sausan da bahijja to kunsan
dama ance Allah mai hadi jininta bai taba haduwa da
sausan ba hasali ma itace silar shiganta matsaloli da dama
duk da tana blood sister dinta kaman step sisters suke
amma suna shiri sosai da bahijja wanda itace secret keeper
dinta dan kuwa nihila tana rufa mata asiri sosai in tayi wasu
abubuwan...
.
Ta hadu da hisham ne a social media wanda Allah ya hada
jininsu daga frndship suka dawo soyayya shi kuwa a gombe
yake da zama amma yana cyprus yana karatu watansu 8
da haduwa ko taba ganin juna basuyi ba amma in suna
waya zakace Sun yi shekaru da sanin Juna.. sausan tasan
da wannan maganan sabida haka ta gulmatawa momin su
ita kuwa momin su tace allanfir bata yarda da wannan
soyayyar ba mutumin da ko taba ganin shi batayi ba kuma
suna nisan duniya tayi kuka sosai dan kuwa tana son
hisham irin mazan nan masu shiga rai hes so caring n
loving Dan haka ta biyema zuciyanta suka cigaba da waya.
.
Dan safe ta shirya tsaf abun ta ta tafi school kasancewar
yau ranan Monday bta gaji da weekends ba da jimawa ba
zasu fara zana paper gama ss3 tana ta dokin ganin frnd
dinta habibaty tana zuwa ta rungumeta tace kai qawata
nayi missing dinki tace nima haka ana haka sai ga jawad
seat mate dinta kuma abokin shawaranta sun saba sosai
dan kuwa tun suna jss 1 ajinsu daya jawad yana da hankali
ga kuma tarbiyya saidai yana fiskantan matsaloli dayawa a
gidansu irin na jarrabawar ubangiji Ga wanda yaso yace
ooh kudai ba'a rabaku Kaman en biyu tace to ya zamuyi
gamon jini.. daga bisani suka tafi assembly.
.
A break me take ba Wa jawad da habiba labarin yanda
sukayi da mominta akan hisham sun dai bata shawarwari
akan tabi abunda mahaifiyarta tace saidai inaaa tayi nisa
batajin kira.. ( umm nima nace mata if u know wats good
for u, u will listen to your mother) ..
.
Amma jawad yace mata ya kamata tayi bincike akan
hisham dinnan tunda ba taba ganin shi tayi ba kuma garin
su ba dayaba hasalima yana wata uwaduniya Itama haka..
Kwanci tashi asarar me rai Sun fara shirye shiryen sana
paper dinsu na waec da neco suna ta faman karatu Dan
kuwa sunada hazaka da son karamun.. Wani yammacin
la'asar ta dawo daga makaranta tilis ta gaji sabida paper da
suka rubuta a ranan sait