HAUSA NOBLE'S
SO NEH... PART (8)
Haka na shafe tsawon kwanaki banida wani ishashshen
sukuni, kullum sai tunanin Fatima, har hakan ya fara
zamarmin jiki.�*** ***
A can gidansu Fatima kuwa tun daga ranar da na jeni na
baro gidan Fatima ta fada cikin mawuyacin hali, abin har ya
fara tafiya ga rashin lapiya, tun ana mata magani har aka
kaita asibiti aka kwantar, kullum abu sai kara gaba yakeyi,
hakan ya jefa mahaifan Fatima cikin matukar damuwa, ana
cikin hakan ne wata rana likitan ya fara yiwa mahaifin
Fatima tambayoyi akan farkon rashin lapiyar Fatima, a nan
ne ya sanar da likitan duk abinda ke faruwa, likitan ya danyi
shiru zuwa wani lokaci sannan yace dashi 'a gaskiya
wannan rashin lapiyar ba ta magani a asibiti bace bakuma
maganin gargajiyaba, a takaice inaso in sanar dakai cewa
indai kanason lapiyar yarka dole ne ka nemo Abba'
Shidai mahaifin Fatima kasa magana yayi anan likitan ya
barshi, daga wannan lokaci ya fara neman lambar wayata
amma sai ya rasa, ya nemi lambar a wayar Fatima ya sai ya
tuna da cewa ya goge lambar, hakan yasaka ya rasa yadda
zaiyi, a cikin dakin Fatima suka ga lambar a jikin wani hoto
na ta ta dauka a facebook ta wankoshi tare da sunana da
lambata.
Ya dauki lambar sannan yayi amfani da wayar Fatima ya
kirani, ina zaune cikin abokaina naji wayata na ringing, bisa
mamaki da na duba domin naga wanene ke kirana sai naga
sunan FATIMA, wani abu naji ya doki zuciyata da karfi
wanda bansan menene ba, nan fa na tsaya ina tunani cikin
zuciyata, a lokacin da nayi yunkurin daukar kiran ne wayar
ta katse, inan nan dai a tsaye na kasa yin komai sai naji
wayata ta sake ringing, na daga kiran sannan na kara
wayar a kunnena.
Muryar mahaifin Fatima naji sakamakon na dade da gane
muryarsa, cikin sauri na katse kiran tare da dauke wayar
daga kunnena, sannan na tsaya ina tunanin menene dalilin
da yasa zai kirani? Amsar da na kasa baiwa kaina kenan,
karar wayata ne ya dawo dani daga cikin tunanin da nake, a
wannan lokacin saida ya kirani sau 10 amma ban dauka ba
har ya hakura.
A wannan rana har dare yayi haka na kwanta ba wani
sukuni, a zuciyata na ce muddin ya kara kirana sai na
dauka naji ko menene, ai kuwa gari na wayewa naji wayata
na ringing, ai kuwa sai na daga kiran sannan na kara wayar
a kunnene.