RABONA CE PART 6
RABONA CE PART 6
.
Juyowa tayi ta harare shi, yaro sai bak'in kini bibi, tace "Kai
Muhammad waya kasa dakai, yaron nan kullan idan muna
magana sai ya rik'a tsoma kuturin bakinsa" aka saka dariya
baki d'aya, Muhammad kam ya k'ule disgashin da akayi, ga
kuma dariyar da aka masa, yayi tseet kamar bashiba
Ummey tace"Dady baka fad'a mana minene ba," ya gyara
zama, ya kalli Muhammad da ya had'e rai sai kunburi yake
kamar an hura air chamber yaso yayi dariya amma sai ya
kame, ya gyara murya, "zo nan Muhammady na "ya mik'e
yana rangaji, irin zaku sani d'innan, yaje gun Dady ya
zauna, Dady ya shafa kansa ya rungume shi da gefen
hannun sa, Ummey sai hararan sa take, sannan ya kallesu,
"dama transfer aka min zuwa babban Branch office d'inmu
dake Niger Minna, kuma seriously banason barin Kaduna
sabida akwai wasu business da nake son k'ullawa, ko nace
ma muka fara, dan dogaro dakai," suna tsakiyar zancen sai
ga Ummul-khairi ta shigo, Muhammad da gudu yaje ya
rungume ta yana mata sannu da zuwa,"Anti ina
Mudhahhar?" Kamin tayi magana sai ga Mudhahhar
yashigo yaro kyakyawa dashi d'an shekara biyu, amma
yana magana kamar parrot, nima Jabo saida ya burgeni a
raina naji kamar ace nawane, sun gaisa Muhammad yace
"Auntie ina Uncle Abdallah ?" Tace " yana gida yana
gaidaka, gama sak'o ya bani na baka, tare mukaso muzo
sai wani aiki ya taso masa," ta mik'a masa ledar hannun ta
yana janyo hannun mudhahhar dan yanason yaron kamar
me, anan aka bata labarin an yima Dady d'in su transfer
bataji dad'i ba Amma tama musu fatan alkhairi, da fatan
hakan ya zamo alkhairi garesu, a rayuwa ummul-khairi ta
iya tsara magana, sukam yara sunji dad'i, bama
Muhammad ba da yake son kullum ayita yawo, wasu na
murna wasu na taya Dady jaje.. Haka Alhaji Ibraheem ya
tattara komai nashi ya bar kd suka koma babbar birnin
Minna, da zama, A minna Ummey ta zana neco ta zauna
jiran result, Kullum sukan yi waya da jaheed amma har yau
ya kasa bayyana mata abinda ke damunsa, kusan wata uku
kenan kullan saidai su gaisa, haka ma Dady, suna k'are
waya da ita zai kira Dady ya gaidashi, shi yasa Dady yake
ganin mutuncinsa ba kad'an ba, kuma yana k'addarashi
sosai a ransa.
.
************
" Gani a k'ofar gidan Ku fa, dama naso nayi surprise d'inki
ne " k'ofar gidan mu?" Ta tambaya, yayi dariya, "kina
mamaki ne," ya kalli Yusuf ya kanne masa ido tab'e bakinsa
Yusuf yayi, yaci gaba da wayarsa," Of course, k'ofar gidan,
ku" ita kam mamaki ya cika ta, yaushe ma ta gaya mishi
sun bar kd da har yasan suna minna, tace "to zan aiki
Muhammad ya shigo dakai," Muhammad ta tura ya shigo
dashi ciki, ya dawo "Anti ni banga kowa ba," dama haka
yake kiran ta wata rana sister wata rana Anti " kai wallhy
anyi mara natsuwa anan, ina zaka ganshi kana kallon
wannan tsinnanen basketball d'in, ko kallonta baiyiba yaci
gaba da kallon sa, ta shiga d'aki ta dauko hijabinta ta saka,
ta fito waje amma wayam, harda d'an zazzagaya ko yayi
nisa ne amma bata ganshiba, ta koma cikin gida, shi kuwa
Mujaheed suna k'are waya ya fito ya nufi gate d'in gidan
direct, ya dad'e baiga Muhammad d'in ba, sai wani soja ya
gani yana gadi, sun gaisa da harshen turanci, yake gaya
mishi yazo gun yarinyar gidan ne, sojan ba tare da damuwa
yace OK, yayi waya ciki akace su shigo, ya daga ma Yusuf
hannu, ya k'ara so suka afka cikin gidan, komai na gidan ya
chanza, amma dai basuyi magana ba, suka zauna chan
wata mulmulalliyar yarinya ta fito, yar gajera da ita d'an
inaga da kadan benaxir ta fita tsawo, amma tafi benazir
haske dan kunsan benazir kamar taya take da bak'i,
Mujaheed a ransa yace wannan batayi kama da Yar aikiba,
ta k'ara so ta gaishesu cikin ladabi, " dama emeka ne yace
nayi bak'i " ta fad'a tana kallon Yusuf, suka kalli juna shida
isihu, sukayi tseet kamar ruwa yacisu, chan dayaga Yusuf
bashi niyyar magana sai yace "dama muna neman Ummey
ne" "yarinyar tace " ayyah ai sun kwana biyu da tashi, baku
sani ba kenan,mutane da yawa suna zuwa neman su, sun
koma minna" wata yar tsohuwa ce ta kawo masu abin
tabawa, shikam Yusuf ya kora abin sa, sukayi godiya suka
fito....
.
Yusuf ko alif baice ba, dan haushi ya gama cikashi,
Mujaheed ya kalli Yusuf " kaga ashe sun tashi, shine ko ta
gaya mini" cikin fushi Yusuf yace " ta gaya maka dan kana
wa a gurin ta?" Amsar ba zata yajita, ya kalli Yusuf, yaga ya
d'aure fuska, yayi tsaki shima, wayarshi tayi ringing ya
d'auka, " hello nifa duk na zagaye unguwar mu ban ganku
ba, ko kunyi batan hanya ne?" " no munzo akace kun tashi" "
laaa Ashe kd kaje, ai mun kwana biyu da tashi, na manta
ban gaya maka bane," sama sama yake bata amsa, tayi
godiya da ziyarar sada zumunci ta kashe wayar, ya shiga
mota Yusuf yaja suna tsaka da tafiya naji wata irin dariya,
wacce ni kaina Jabo saida na razana, Mujaheed sai kallon
sa yake, ya sami gu yayi parking.
.
" Amma yau naga surprise had'ad'de, Allah naji dad'in
wannan abin, ta koya maka yanda ake surprise ba kamar
yanda kayi ba," yaci gaba da tukinsa,har suka isa gidan sa,
bayan Mrs Yusuf ta kawo musu abin tabawa, Mujaheed ko
kallon su baiyiba, nan take tambayar ya akayi suka dawo da
wuri, anan mijinta ya bata labari tayi dariya kamar me, itada
da mijinta, Mujaheed baice musu komai ba, saida suka
k'are sannan Yusuf ya fuskanci abokinsa ya dafa
kafad'arsa ya shiga masa bayani, "ka gane, aboki ita mace
ba'a mata haka, idan har kana sonta wallhy just tell her,
sabida ko wane lokaci tana iya samun wani wanda yake
sonta, kuma zata iya amincewa, kuma tanada hak'k'i na yin
haka, so anan kaga kai ba kada ikon cewa ta yaudareka,
sabida kayi sakaci, baka gaya mata ba, kaga madam,
wallhy ranar dana ganta ranar na bayyana mata abinda ke
raina, sabida banason nayi missing target d'ina, so dole ka
fito ka gayawa Ummey ra"ayinka akanta, kullan kana cewa
yayi sauri wai secondary school take, shez too small, bla
bla bla... A boki, ina gaya maka a haka zaka bayyana mata
dai-dai da fahimtar ta ta yaran da kake tunanin itace,duk da
ni nasan mace komi k'ank'artarta ba'a raina girmanta
musamman yaran yanzu, a hankali zaka shigar da ita, daga
nan har kayi gini a zuciyarta, ta yanda ba wanda zai iya
rusaka, amma ina gaya maka matuk'ar ka tafi akan
k'aramace Allah zaka rasata one day one time, zakasha
mamaki" numfashi ya sauke a hankali "to ai abinda ya kawo
ni kenan, yau nayi alk'awarin gaya mata abinda ke raina sai
haka ta faru," Yusuf yace " y not yanzu ka d'auki waya ka
sanar da ita?" girgiza kai yayi, " no sai na k'ara shawara
kuma nafison gani gata naga reacting d'in ta" yayi baya da
kanshi ya rufe idon sa, Yusuf bashi wuri yayi dan haushi ya
gama cikashi .....