Breaking News

ALLON SIHIRI 1

ALLON SIHIRI
Littafi na daya(1)
Part 4
Mutum na biyu mai mallakin barin Allon shine
Sarki
Darmasu na birnin Kimrasa,sai kuma barin Allo na
uku dake hannun boka Saryanu Ibn
Daumur.Karbar
wadannan barikan alluna guda uku a hannun
wadannan mutane daidai yake da tashin matacce
ya
zama rayayye saboda kowanne a cikin bashi da
burin da yafi ya sami ragowar barikan biyun da
nashi dasu ya hada nasa domin zama sarkin
duniya,ya kasance komai da kowa na karkashin
mulkinsa.Lokacin da boka Mugaru yazo nan a
zancensa sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar
mugunta.Nan take ya kawo alheri mai yawa ya
baiwa boka Mugaru sannan sukayi sallama ya
tafi.
Daga sannanne Yarima Mangul ma ya dage da
baiwa kansa horon yaki dare da rana kafin cikar
lokacin ranar gasar ya gama shirinsa tsaf.Na
take
kuwa yayi shiri shi da mahaifinsa Sarki Alkas
suka
durfafi Birnin Zamral tare da dakaru masu yawa
suna take musu baya.
Ba isowarsu Birnin Zamral suka iske
cewa garin ya cike makil da baki daga kowanne
bangare na nahiyar.
Ba komai ne ya haddasa
wannan
cikowa ba face anzo kallon gasar kisan juna da
za'ayi tsakanin Yarima Mangul da Yarima
Lubainu kan kyakkyawa Yazarina.Kai tsaye sarki
Alkas tare
da dansa yarima Mangul suka wuce fada.Tun
kafin
su karasa sarki Sailur ya fito kofar fadar ya tsaya
tare da fadawansa suna jiransu.
Ai kuwa da zuwansu
sai Sarki Sailur ya karbesu cikin tsananin farinciki
ya
rungume sarki Alkas yana mai cewa lale
marhaban da babban abokina.Hakika nayi
mutukar farinciki
dakuka amsa wannan gaiyata tawa.
Abinda ya
daurewa su Yarima Mangul kai shine basu ga
Yarima Lubainu ba a wajen taryarsu.Nan take
sarki
Sailur ya kama hannun Sarki Alkas ya jashi izuwa
cikin fada inda aka zauna gaba daya tare da
dukkan jama'arsu.A sannanne kuyangi da
hadimai sukai ta
kawo abinci,ruwan inibi,ruwan sha kowa ya
kimtsa
kansa ana ta hira da dariya masu shewa nayi
saboda santi.
A wannan lokaci Yazarina da Yarima
Lubainu nacan a zaune cikin lambun gidan attajiri
Abu Yazarina suna hira irin ta ma'abota soyayya
inda Yazarina ta dubi Lubainu a lokacin da
hawaye
ya zubo mata tace,yakai masoyina kayi sani cewa
tun daga ranar dana sami labarin wannan gasa
da
mahaifinka ya shirya na rasa sukuni kuma na
kasa
yin bacci a kullum idan na kwanta akan
gadona,har
ya zamana cewa ina tayin mugayen mafarkai
akan wannan gasa da zakuyi don haka ko yaushe
zuciyata
a cikin bugawa da karfi take.Bani da abinyi sai
kuka
saboda fargabar zuwan wannan rana gashi kuwa
rana bata karya saidai uwar 'ya taji kunya tunda
gobene za'ayi wannan gasa.
Lokacin da Yazarina tazo nan a zancenta sai
Yarima Lubainu yayi
murmushi kuma yasa tafin hannunsa biyu ya
share
mata hawayen a lokacin da ya dago habarta suka
dubi juna yace,ki kwantar da hankalin yake abar
kaunata kiyi sani cewa nine da nasara a cikin
wannan gasa lallai da izinin gunki Salhat babu
abinda zai sameni.
Koda jin wannan batu sai
Yazarina taji dan sanyi har murmushi ya subuce
mata amma sai ta sake hade rai ta dubi Lubainu
cikin alamun damuwa tace,yakai masoyina
waishin
menene dalilin da yasa mahaifinka ya shirya
wannan
gasa ne alhalin na tabbatar da cewa yana
tsananin kaunarka fiye da komai.Koda jin wannan
tambaya
sai Yarima Lubainu yayi ajiyar numfashi sannan
ya
dubi Yazarina yace,sau tari sarki yakan dannen
son
zuciyarsa domin ya nemawa kansa martaba da
kima
a idanun talakawa.Wannan shine abinda ake kira
sarauta,kuma shine abinda sarki yayi domin ya
kawar da rashin jituwa tsakaninsa da tsohon
abokinsa kuma ya kawar da tsegumi da kace
nace
tsakanin al'ummar kasashenmu.Idan kin Fahimci
wannan bayani nawa zaki gane cewa sarki yayi
daidai bisa wannan hukunci daya yanke.Lallai ina
son ki kwantar da hankalin kawai ki cigaba da
yimin fatan sa'a da nasara.Haka dai Yarima
Lubainu Da
Yazarina suka cigaba da hira har izuwa lokacin
mai
tsawon gaske .
Da zarar yayi mata sallama zai tafi sai
ta bijiro masa da wata sabuwar hirar da hillatar
da
zance mai dadi saboda bata son su rabu.Yarima
Lubainu dai bai ankaraba sai gani yayi dare ya
soma kuma gashi yana so