Breaking News

RABONA CE PART 1

RABONA CE PART 1
.
By Hauwa jabo
.
Gude yake sosai saman dokinsa, fari tass dashi, dokin ba
wani kwalliya aka masa ba, linzami ne kawai sai sirdinsa,
dokin shima da alama ya saba da maishi, sabida yanda
yake bada had'in kai ake gudu ba sassautawa, sai tsallake
abubuwa yake, da kin ganshi kinsan yana cikin nishadi,
alamar baida matsalar komai a rayuwarshi, yayi gudu sosai,
har saida yakai dai- dai wata bishiya, sai kuma naga dokin
ya tsaya da kanshi ba tareda mahayin ya ja linzamin dokin
ba, haniniya dokin yayi ya wani d'aga k'afafuwansa na
gaba sama, sai naga guy d'in da ke saman dokin yayi
murmushi yace "bravo my maverick "(sunan dokin kenan)
Ya sauko saman dokin yabi wani sak'o yadan gangara
kad'an dokin nashi yana biye dashi, sai gashi gaban wani
babban rafi, ya kalli ruwan yayi murmushi, ya tsinko wata
flowers ya rik'a wurgawa a ruwan a hankali har ya wurga ta
k'arshe, ya bita da kallo saida ta k'ure ma kallon sa,
tsugunawa yayi gaban ruwan yana kallon su suna gudana,
farare tas daga,
.
daga wani dutse suke fitowa suke biyowa hanyar suna
wucewa, yakan zo nan ne, dan gun yafi flowers, so ya fi
sakashi nishadi, a hankali ya saka hannun sa a ruwan, ya
d'ibi ruwan ya watsa ma dokin sa a fuska, sai naga dokin
shima ya matso ya shiga ruwan yasha ruwan ya fito, ya
mik'e tsaye, ya shafi dokin nasa sai kawai suka fito, ya
tsinko wata flower, yana tafe yana wasa da ita, sunyi tafiya
mai d'an nisa shida dokin sa, sai da flower hannun sa ta
k'are sannan ya hau dokin sa, suka fara gudu bai tsaya ko
inaba ba sai wani babban gida, mai kamar gidan gona, ya
shiga ciki kai tsaye, haniniyar dawaki kawai naji, it same
like duk sun sanshi, ya bud'e wata 'yar k'ofa, yasaka dokin
ya kulle, yabisu a hankali yana shafasu yana basu chiyawa
suna chi, saida ya k'are kaf sannan yabi ta wata hanya, mai
d'an tsayi, gurin akwai shuke shuke, yana kaiwa sai gashi
wani tintimemen gida, kai tsaye palon ya nufa, yana shiga
ya bud'e fridge ya d'auko table water d'aya ya d'aga kai ya
kwankwada, ajiyar zuciya yayi yadan yarfa hannuwansa
yabi wani lungu sai gashi d'akin sa, toilet ya wuce ya sake
ma kanshi ruwa, saida yaji ya gamsu da wankan sannan
yayi alwula ya fito,dan an kusa Magreeb, ya sa wani boxes
da 'yar shirt, ya saka turare ya kunna TV ko minti biyar
ba'ayiba aka fara kiran sallah, jallabiya ash color ya saka ya
fito yaje masallacin dake gidan yayi sallah, yana dawowa ya
tarar da miss call har 8, abokinsa ne Osama da suke kira
donsimon, ya kira shi ya kirashi, yana d'auka ya ce" hello" "
haba Mujaheed nafa gaya maka daurin auren nan gobe ne,
kuma kama Yusuf alk'awarin cewa zakazo amma na jika
shiru" ya Allah.!!" abinda Mujaheed ya iya furtawa kenan "
Allah donsimon na manta ne kwata -kwata, gashi dare yayi,
nama isa nak'i zuwa auren Yusuf, ai sai nasha gori har
mutuwata, amma gobe zan duba idan akwai flight sai na
biyo na safee," tsaki yaja "ina zaka sami flight gobe, kawai
tunda asuba ka kamo hanya" " kaima kasan yanda nake da
baccin safee ba wani tashi zanyiba, amma zan gani, Allah
zanzo" haka suka k'are wayar sukayi sallama, Huuuuuuuu
iska ya fitar a bakinshi, idan ma yace zai yi sammako yasan
bazai iyaba, golden morn ya hada yasha, ya bude wardrobe
ya dauko wasu kayan da abubuwan bukata ya dauki key, ya
fito, "Ammi zan tafi d'aurin auren Yusuf," ta dafee kirji, "da
darennan Mujaheed?" No zanje gun su Habeeb da asuba sai
mu wuce, sabida idan na kwana anan zan iya bacci motar
su Habeeb zamu tafi," "OK to yanzu naji zance, to Allah ya
kiyaye hanya, kacewa Habeeb please yayi tuk'i a hankali
nasan halin ku da mota sarai," murmushi ya mata kawai ya
fice, Allah ya kiyaye ta bishi dashi...
.
***************
"Mumy na okay bye bye," ta fada tana daga mata hannu,
Muhammad k'aninta ya had'e fuska dan yaso a tafi dashi
amma tak'i, Mumy kam yake kawai ta mata, "sai kun
dawo", Mumy tace hadi da zama kan kujerar dining table, ta
janyo hannun Muhammad da ya riga ya shiryawa kuka, taja
akwatinta k'eeeey ta fito, driver dama ya shirya ita yake jira
suka kama hanyar Abuja, ba a dad'e da tafiya ba bacci ya
d'auketa.
.
*******
Mujaheed saida yaje wani babban mall yayi sayayya
sannan ya d'au hanyar Kaduna, dai-dai jaree yaga kamar
anyi taro ga traffic sosai a dayan express, a tunanin sa
accident akayi a gun, har ya wuce abinshi, sai ya dawo
shima ya baiwa idonsa abinci, yayi parking gefen hanya ya
d'auki phone d'insa yana haskawa ya tsallaka, yaje d'ayan
express d'in, koda yaje jini saman titin ko ina, Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un!!! ashe y'an fashine ne sukayi operation a
gun, sun kashe mutum shida, sun harbe mutane da dama,
dashi aka taimaki mutanen da ke gun aka sakasu motaci
aka dawo kaduna dasu, aka janye motocin da ke saman
hanyar, mujaheed ya sami ruwa ya wanke hannuwansa, ya
tsallaka zai koma, sai ya tuna ashe da phone dinsa yazo sai
ya dawo again, ya dauko phone dinsa, daga kan da zaiyi sai
kawai yaga kamar mutum kwance, da sauri ya haska da
wayansa, sai yaga mace kwance a sume, da sauri ya
k'arasa gunta, ya kashe wayar sa ya saka aljihu duk'awan
da zaiyi ya d'auketa sai yaga hannun wani mutum shima
zai d'auketa, amma mujaheed ya rigashi kai hannuwan sa,
sai wanchan ya janye hannuwan sa, Mujaheed ya masa
murmushi, zan iya ai, mutum ya juya ya wuce, ya
sungumeta, Allah yaso akwai sauran police a gurin sai
d'aya daga cikin su yabi Mujaheed, ya sakata mota suka
wuce Kaduna, aka kaita wani private hospital a Kaduna, da
yake suna tare da police so baisha wahala ba gurin samu a
karb'eta, tuni likitoshi sunyo kanta, aka samu aka fitar da
bullet din a hannun ta aka mata treatment, bata farfad'o ba
sai zuwa asuba.! Mujaheed kuwa bayan asibitin sun
kar6eta sai kawai yaje ya kama hotel, yama abokinsa waya
akan yazo ya sameshi ya bashi address din hotel d'inda
yake, dan yasan idan ya kwanta bazai sami zuwa daurin
auren ba yanda yayi dare ga gajiya. Bayan an d'aura Aure
anyi duk abinda akeyi na shagalin Aure, Mujaheed ya dauko
phone d'insa, zai kira Amminsa, sai lokacin ya kula da miss
calls da yawa, bayan yayi waya da gyatumar sa, ya kira
numbers d'inda ya sani, sauran kuma yayi ignored dinsu,
amma akwai call d'inda yaja hankalinsa, wanda sau bakwai
ana kiransa da wannan number, sai kawai yadan yi tsaki
har bazai kiraba sai ya kira, Hello, " Sir patient d'inka ta
farka, tun d'azu saidai bata magana har yanzu, kana iya
zuwa ka dubata" " patient?" Mujaheed ya maimaita, " ina na
sami patient kuma? " tambayar da ya yiwa kansa kenan, "
sorry wrong number ne, saboda banida wani mara lafiya a
halin yanzu" d'ayan bangaren yace "Sir ba kai ne Mujaheed
Kabeer ba?" "Yeah nine" " ranar juma'a da misalin k'arfe
d'aya na dare ka kawo patient d'inka wacce yan fashi suka
harba a hannu ka tuna sir?" "Okay..... Na tuna Dr. Kuyi
hakuri na manta but ina hanya please " ya kashe wayar duk
cikin turanci sukayi maganar, ya fito ya fad'a motar sa yana
tafe yana murmushi, shi sam ya manta da wata wai ita
patient d'insa....