Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 4

MIJIN MARAINIYA PART 4
.
Bude murfin motar tayi ta fito, ta zagayo ta rike safna tana
tura ta cikin motar, jalal ma riketa yayi yace ummi ki dai na
irin wannan babu kyau fah, cikin tamke fuska tace sake ta
jalal idai ba kana son ranka ya baci bane. ummi dan Allah
kibari ,ta canxa kaya sai ku tafi. zuwa tayi gaban shi tace
wlh wlh in baka sake yarinyar nan ba ranka zaiyi
mummunan baci, kasake ta kawai. dukar dakai yayi ya kara
rike gefen rigar safna ciki tashin hankali ya dago ya kalli
ummi ya sake dukar da kai. Safna na tsaye tsakiyar su tayi
tsuro tsuro, ummi ta sake cewa ba dakai nake magana ba,
gani tayi ko motsi ba yayi dan haka ta taho gadan gadan ta
kwashe shi da mari. da sauri jalal ya saki safna ya dafe
wajen dan shi atunani shi babu wanda ya taba dukan shi.
.
jalal kallon ummi yayi cike da mamaki, yace ummi nine fah,
jalal dinki ne fah. ummi bata saurari me jalal yake fada ba
ta tura safna mota suka bar wajen. binsu yayi da kallo yana
bakin cikin wai mahaifiyar shice take wannan dabi,a wai
yaushe ummi ta canza , shi dai yasan ummi na son farin
cikin shi. Yana nan tsaye drive ya dawo da kairat daga
makaranta, tana fitowa ta hango jalal da gudu ta karaso ta
rikeshi, gani hawaye tayi yana bin kuncin sa tace yaya waye
ya dake ka. Jalal da besan hawaye na fita ba yasa hanu ya
shafa idon sa yace idona ne yake ciwo, riko hannuta yayi
suka shiga gida, kairat taso ta bishi dakinsa yace mata
bacci yake ji. tunda jalal ya shiga daki yasa key, yau dau ki
waya ya kira mahaifin sa har ta katse be dauka ba, ya ajiye
wayar ya kwanta ,da matsa nan cin bacin rai yau da ummi
ba mahaifiyar shi bace da sai ya dauki mumunan mataki
akanta, shi bema san me yake damun saba illa dai kawai
yasan yana matukar kishin safna wanda ko mace yar
uwanta baya son yaga ta cika kallon ta da yawa, bare kuma
na miji. su ummi basu dawo ba sai wajan 9:00 shiko jalal
tun yamma zazzabi ya rufe shi dan ko sallah ma a daki yayi
ta. ummi na shigowa hara bar gidan taga motar alhj tace
wai nikam me yasa alhj yake min haka, inzai dawo bazai
sanar dani ba saidai na ganshi kwatsam. da sauri ta fito
safna ma ta fito ummi tace ke dakata duba cikin ledan cen
ki dau hijjab ki sanya, safna ta juya ta dauko wani
zumbulelen hijjab har kasa ta sanya. suna shiga alhj na
zaune afalo ya rufeta da fada, kwantar da kai tayi tai ta
bashi hakuri, safna kuwa sumi sumi ta shige daki. sai da
yagama zazzaga bata sannan yace ina abduljalal tare kuka
fita? a,a mun barshi gida. toh ina yaje kuma sunce kwata
kwata yau beje office ba wai me yasa yaron nan yanzun
duk yabi ya rikice ne, shifa ya matsa sai na bude mai
kamfani kuma dan me yanzun zai sanya wasa, dazun
nakira shi wayar shi kashe take, wai me yaron nan yake nufi
ne. ummi tace haba alhaji sai faman fada kakeyi kayi hakuri
duk ma inda yake nasan hankalin sa na gida.
*********
barin zancen sukayi suka kama wata hirar, kairat ce ta fito
tana dari daddy daman kadawo shine baka kirani ba. cikin
murmushi ya rike ta yace kairat na rude ne har yanzun
abduljalal be tadawo gida gashi wayar shi kashe take. cikin
sauri tace daddy dazunfa an daki yaya jalal a office din su
yana ta kuku, amman sai yayi min wayau yace wai idon shi
ke ciwo kuma yaki bari na bishi daki wai shi barci yake ji,
cikin shagwaba ta karasa zance ta. ummi kuwa Cikin ta
kara ya fara dan bata zaci zai dau abin da zafi haka ba.
.
alhj ko kallon ummi beyi ba yatashi ya nufi dakin jalal ya
tura kofar yajita kulle , juyowa yayi ya kira ummi yaron
nanfah bashi gidan nan, cikin rudewa tazo ta wuce alhj ta
isa kofar ta fara Kira yaro yaro shiru, jalal jalal nanma shiru
kuka ta saka tana fadin nashiga uku, alhj ya daga murya
yace abduljalal, da sauri ya amsa na am daddy. yace zoka
bade min kofa. yana rawan sanyi yazo ya bude kofar rige
rige suka fara kowa na kokarin kai hannun shi jikin jalal
komawa gado yayi ya kwanta . alhj ya dafa jalal yace me ya
same ka, waye ya tabaka dan waye agarin nan, ka gaya min
waye uban sa. ummi ce ta kawo hannu zata tabashi, yace
daddy kace mata karta tabani daddy kace ta fitan min
adaki. alhj yace jalal ummin kace fah wai baka cikin
hankalin kane. ina sane daddy cikin hakali na nake kawai
bana son ganin ta ne. tsawa alhaji yayi wa jalal mahaifiyar
ta ka kake cewa baka son gani kar na kara jin wannan
kalman abakin ka. shuru jalal yayi yana kuka kasa kasa
ummi na makure jikin bango , alhj ya dago yace to ya isa
dai na kuka sai kace ba namiji ba lallai ummin ka tayi laifi,
abduljalal gayamin me ummin ka tamaka da zafi haka har
kake zubar da hawaye. Jalal juyar da kansa gefe yayi
sannan yace daddy ummi nasa safna nayin shigan banza
tana fita waje, kuma nayi magana ummi ta mareni. mari ?
zaliha ke kika mari jalal akan me, alhj mikewa yayi ya daki
kirjin shi yace dana kika Mara
.
Akan wani dalili kika mare shi ? ciki sanyi murya ummi tace
alhj mun shirya zamu fita da safna har nashiga mota
amman jalal yasa hannun shi yarike safna wai bazata shiga
ba dan ya raina ni. Jalal ya bude baki yace ai shigar da tayi
ne be kamata ta fita dashi ba. Cikin fada ummi tace kasan
shigan da tayi be dace bane kai kasa hannun ka ka taba ta,
ko muharramar kace ita. shiru yayi ya juyar da kansa gefe
alhj yace to ya isa ke zaliha daga yau karki kara dukan jalal,
inbanda ma abinki ya za,ai ki mareshi gaban safna, kanwar
sace fah. haushi ya bani alhj. to shikenan kisan yanzun me
zai faru, daga yau kar safna ta kara fita gidan nan inhar ba
makaranta zata ba, ya juya yace jalal magana ta kare ko ?
shiru jalal yayi alhj ya sake cewa ko akwai saura ne halal eh
daddy, da sauri ummi ta harareshi dan haka yayi shiru. sai
da alhj yasake cewa ina jinka abduljalal meye kuma? daddy
kuma fa har samari zuwa gurin safna suke kuma ai karatu
take. alhaji dariya yayi yace abduljalal kai duk matsalan ka
agurin safna take, toh jalal kodai son safna kake ne? sai da
ya kalli ummi san nan yace a,a. itama ummi kallon sa take.
alhj yace ya hausan a,a jalal karfa kai kwauron baki wani
yama kafa ya sake yin dariya, san nan yace ke zaliha kina
fah shige mana hanci, kuma daga yau kar safna ta kara fita
wajen wani. haba alhj wai me yasa kakeyin haka jalal ne zai
rinka juyamu agidan nan duk abinda ya fada kawai sai ka
yan ke hukunci. murmushi yayi yace naga kamar yana son
ya fiki hankali ne, be jira me ummi zata ceba ya fita adakin
itama bayansa tabi.
************
suna fita yaji zuciyar sa tamai fes tare da mamakin ya akai
daddy ya dago shi ai lokaci beyi ba, ba yan zun ya kamata
su sani ba sai ya samu soyayar safna neman zazzabin yayi
ya rasa. washe gari ana kiran sallan subahi ummi ta nufi
dakin jalal yana kwance yana bacci ummi ta fara tashin shi
yaro tashi kayi sallah, tashi yayi ya zauna, ummi tace yajiki
ko asibiti zamu, da saurin sa yace naji sauki ummi nama
warke. bayan ya dawo daga masallaci be koma barci ba
kamar yadda yake yi ada sai ya fara shirye shiyen fita
kananan kaya ya saka yayi kyau matuka ya fito falo ya
zauna babu kowa afalon ya nan zaune safna ta fito da gudu
bata san cewa da mutun afalon ba taci karo da kafar jalal
har ta fadin kasa kara ta sake dan taji zafi sosai. da sauri
jalal yamike yazo gaban ta ya tsuguna yace sorry safna
kawo na duba miki. cikin kuka tace bana so bakai bane
kasamin kafa, badu baki yayi cikin mamki yace yazanyi
nasa miki kafa bake kika fito da gudu ba, be jira me zata
ceba ya kama kafar ya matsa, fashewa tayi da kuka sai da
su ummi da alhj suka fito suna fadin lfy. ganin jalal sukayi
rike da kafar safna itoko kuka take cikin daga murya ummi
tace me ya faru? Jalal yace faduwa tayi ina tunani kamar
buguwa tayi .
.
ummi tace alhj wai wannan ne kake cewa yana da hankali ji
inda ya ke taba ta . mikewa yayi yana fadin ummi wani irin
magana kikeyi, safna tashi muje asibiti ummi bata so jalal
yakai safna asibiti ba, domin bata son sultan yagan su tare
dan suyi da hajiya baturiya yau zasu turo mata makudan
kudi, tayiwa safna sayayya duk da cewa hajiya baturiya
tasan halin danta ba aure ne agaban saba, amman duk
yarinyar da ya nuna yana so sai taita kashe kudi dan ta
faran ta mai rai. Jalal kuwa tundaga ranar ya kasa ya tsare
safna bata fita ko ina dan ummi na tsoron mijinta kwarai.
jalal ko jan safna yake ajiki sosai harta fara sakin jiki dashi
kullum daddare zai aika kairat takira safna suyi ta hira suna
dariya. ummi na kwance adakin ta taji sai dariyar jalal da
safna take ji ta daga kai ta kalli agogo 11:38 gaban ta ya
fadi karfa ace jallal soyayya yake da yarinyar nan wani
bangare na zuciyar ta nacewa ai kwanakin baya baban sa
ya tambaye shi yace a,a to amma kuma wannan wani irin
sabon salon ne, koma dai menene bazata taba bari jalal ya
aure safna ba, yarinyar da sultan yayi soyayya da ita kilama
yanzun tana dauke da cuta da wannan tunani ta zabura,
tana fadi baza ta sabu ba cikin sauri ta fito jalal naganin ta
yace ummi bakiyi bacci ba. eh banyi ba, tashi ka wuce daki
tun daga ranar ummi ta hana safna fitowa hira jalal na
zuwa falo saidai yaga ummi har tsawo sati daya besa safna
a idon saba hankalin jalal ya tashi, itama safna kewan jalal
take sosai. washe gari da safe jalal ya fito cikin shirin shi na
tafiya office bayan ya gaida ummi yamike ya nufe dakin
safna, ummi ta kirashi ya dawo ina kuma zaka, inace office
zaka tafi?
.
eh fita zanyi amman ina son naga safna kafin na fita. Me
zaka mata? ummi na dade bansa ta a idona na ba fah
,ganinta kawai zanyi na wuce wai yaro ni zaka munafunta
karka mance kamin alkawarin bazaka aure safna ba inma
ka fara tunanin aure ne sai kaje gida yayata ka auri yarta
aliya dan tun tana karamar ta take sonka. toh ummi naji
munyi waya da daddy yace yau zai dawo inya dawo sai
muyi maganar adawo lfy, jalal yasake cewa ummi naje
naganta kona minti biyu ne? Kiri kiri ummi ta hana haka ya
tafi jiki babu kwari yamma likis jalal ya nufu gida yana
shiga falon yaje jikin alhaji ya kwanta ummi bata gurin sai
safna da kairat dan alhaji fira yake sosai da su safna ta
juya takalli jalal taga yayi dare dare jikin daddy ta kwashe
da dariya tace daddy kace ya daina hawa maka jiki karya
karya ka. daddy ma dariya yayi yace safna ai ke bakiga
komi ba sai in beda lafiya zakiga har kuka yakeyi. Kairat da
safna sukara saka dariya. jalal yatashi ya zauna yakali
safna yaga sai dariya take yace ke ya isheki, daddy kaga
zakasa suraina ni. suna cikin haka ummi ta fito tana fadin
ai jalal ya girma ne besan ya girma ba dazun nace mai yaje
gurin aliya su daidai ta. alhj yace wacce aliya yar wajan
Rabi? eh ita kuwa ashe baka manta suba. au yanzun kuma
kintuna dasu, inace zuwan su gidan nan nawa kina musu
korar kare, to waima bari na tambaye ki, kisan inda su baffa
suke yanzun, ummi mikewa tayi zata bar wajan, alhaji yace
dan dakata zaliha na samar wa jalal yarinyar da zai aura
safna ma na mata miji. Jalal zabura yayi yamike ya rike
kafan daddy yace daddy karka min haka dan Allah
.