Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 3

MIJIN MARAINIYA PART 3
.
ummi kuka ta fara ta fita adakin da sauri ta shige nata
dakin. alhj ya kalli abduljalal yace akan wannan har kake
zubar da hawayan ka, meyasa tunda kaji kana son ka tai
maketa baka kirani awaya ka gaya min ba, kar ka kara
zubar da hawayen ka, bama wannan yariyar ba duk wanda
kake son ka tai maka ma kamin magana kabar biyewa
ummin ka kaje ko. jalal kwanciya ya da da yi ajikin daddy
yana murmushi. alhj ya sake cewa jalal zamu zauna tare da
yarinyar nan zan sata makaranta zan riketa kamar yarda na
hai fa idai har zakai farin ciki da hakan, amma da sharadi
guda daya, sai nayi binkece na tabbatar maganar da
yarinyar nan ta fada gaskiya ne. Jalal tsuguna wa yayi yana
ma alhj godiya tare da amicewa da maganar alhj. har alhj
ya fita ya dawo ,yace jalal raka yarinyar nan dakin kairat,
kar na sake ganinta a barayin ka. cikin sauri jalal ya amsa ,
haka yakai safna har dakin kairat ,kairat batayi bacci ba
dan haka taji dadin ganin anty safna a dakinta. bayan alhj
ya shiga dakin ummi ya same ta tana zaune bakin gado
tana share hawaye, kusa da ita yaje ya zauna ya dafata
yace zaliha meye kuma abin kuka. dole nayi kuka alhj naga
kana neman ka tona min asiri agaban dana har da wata
bare, wadda bamusan asalinta ba, kuma ni din da kake
neman wulakantani ai a gaban iyaye na gaje ka aure ni,
kuma duk gorin da zaka min nasan be wuce kace ka ganni
ne lokacin da nake kora shanon mahaifina ruga ba har kaji
kana sona , ai baza a hada da wannan banzan yarinyar ba,
kuma ni abinda yafi damu na kar fa jalal yace son yarinyar
nan yake dan nikam ko zanyi yawo tsirara bazan bari yaro
ya aure taba. alhj ya gama sauraran ummi cike da mamaki
yace zaliha kina bani mamaki to meye a ciki dan yace yana
son ta, ni dai na dauki alkawarin zan riketa kamar sauran
yarana, kuma kema inason kireta kamar yar da kika haifa.
.
ummi tace naji zan riketa amman sai dai in jalal yayi min
alkawarin ba aure tsakanin shi da ita. Hmmm zaliha kinan
dai akan bakan ki kenan yanzun kuma amiki magana kice
ammiki gori, to shi jalal din da kikace sai yayi miki alkawari
bazai ce zai aure ta ba, yasan gaibu ne, be saurari me zata
sake cewa ba ya fita adakin afusace. ummi kasa bacci tayi
dan haka washe gari da safe ta nufi dakin jalal ta same shi
kwance akan gado ya najin shigowan ta ya miki, kusa dashi
taje ta zauna yace ummi dama yanzun nake shirin nazo na
ganki nasan kina fushi dani ummi safna abin tausayi ne ,
tausayin ta ya kamani. cikin dibara ummi tace na fahimceka
jalal komai ya wuce safna zata zauna tare damu amman da
sharadin nan gaba baza kace zaka aure taba dariya sosai
jalal keyi cikin dariyar yake fadin haba ummi dama akan
haka kike tada hakalin ki , idai wannan ne ki kwantar da
hakalin ki , ummi me zanyi da safna ga haddadu babys a
gari haba ummi ni wlh ummi kin ma bani mamaki yama za
ai haka ta faru. ummi ji tayi zuciyar ta fes tundaga ranar ta
fara jan safna ajikin ta, hakalin safna ya kwan ta ta koma
makaranta ita da Kairat suke ta fiya . akwana atashi gashi
yau safna kusan shekaran ta daya da wani abu agidan jikin
ta yayi kyau ya murje tayi fes in kasan safna ada kagan ta
yanzun zaiyi wuya ka iya shai da ta, fari tayi sosai har
nema take ta wuce ummi a fari ga gashin har gadon baya
ga cikar halitta ummi ayanzun inta kalli safna har mamaki
abin yake bata saika rantse yar wani hamshakin mai kudi
ce. shiko jalal rabon shi da ganin safna yama manta dan
tunda ya lura ummi bata son ya rabeta ya rege shiga
barayin su gaba daya saidai jefi jefi yakan shiga amman
allah besa sunci karo da safna ba, sai dai yana samun
sakon gai suwata agun kairat dan kulum sai taje dakin sa
kuma tana shiga zata ce yaya anty safna na gai da kai
hakan na mishi dadi. itako ummi tunda ta lura safna
kyakyawa ce murna ta kamata lallai ta samu jari dan haka
tafara hada ta har ka da yayan manyan mutane dan
acewan ummi safna matar manya ce.
.
yaran masu kudi ne ke zuwa gun safna duk da cewa SS 2
safna take ayanzun amma ita ummi barin ta kudi. yauma
kamar kulum safna na zaune ita dawani saurayin ta a
harabar gidan ,halal ya faka motar sa bayan yafito yakalli
gurin da su safna ke zaune, sultan ya gani zaune agefe sai
dai yarinyar be gane ko wacece ba amma fah Allah yayi
halitta agurin nan, azuciyar shi yake tunani me ya kawo
sultan da budurwar sa tadi gidan su, inda wani shashi na
zuciyar shi kecewa Ina ma ace ya mallake yarinyar nan,
dawan nan tunani ya shiga gida, yana shiga ya samu ummi
zaune a falo , zuwa yayi ya kwanta ajikin ta. ummi tace
yaya dai yaro, lfy naga jikin ka a sanyaye? ummi wata
yarinya nagani ita da sultan awaje. murmushi ummi tayi
tace jalal safna ce baka gane ba. jalal tashi yayi ya zauna
yace ummi kina nufin safna ce ke tadi da sultan? ita ce
mana ai safnar tamu ta waye sultan ya rikice akanta, ummi
bata gama fadan maganar bakin taba taga jalal ya mike
cikin fusatan da bata taba ganin shi cikin saba, itama
mikewa tayi tana fadin me ya tada maka hankali ne jalal.
.
waje yayi da sauri ummi bayan sa tabi tana kiran jalal jalal.
amman ina besan ma tayi ba sai da ya isa gurin ya kare
mata kallo riga da wando ne jikinta sun kamata sosai tabas
kamanin ta basu bace masa ba, cikin fada yace da sultan
malam tashi ka fita agidan nan. sultan cike da mamaki
yace ban gane na fitaba ai ba gurinka nazo ba. eh koma
gurin wa kazo karna kara ganin ka gidan nan, cikin tsawa
yace ke tashi kishiga gida. cikin sauri tamike zata bar
wajen, sultan ya tashi ya rike safna yana fadin babu inda
zata sai mungama maganar da muke. duk abinda suke
ummi na daga kofa tana kallon su, jalal ji yayi ya kara
kulewa waton sultan ya saba rike safna kenan, jalal jiki na
rasa ya fara kaiwa sultan naushi
.
ummi karasowa tayi da gudu ta rike jalal tana fadin jalal
baka da han kaline ,me yayi maka, da ker ummi ta janye
jalal daga jikin sultan, hancin sa har ya fara fitar da jini.
ummi matsawa tayi kusa da sultan tace sultan jeka gida
zan zo na same mamar ka, yace ummi amman dai kin ga
abinda yayi min ko? na gani kuma zanyi maganin sa, ka
kwantar da hankalin ka. sultan girgiza kai kawai yayi, ya
shiga motar sa yabar wajen. Jalal na tsaye sai huce yake yi
, safna kuwa dama tun da taga fada ya kaure ta ruga da
gudu ta shiga gida ummi ce ta juyo ta kalli jalal dake tsaye
ban da huce babu abin da yake yi, tace muje ciki, gaba ya
shi ga ummi nabin sa a baya. suna shiga ummi tace me
kake nufi da kake koran ma safna saurayi. sai da ya dukar
dakai sannan yace ba abin da nake nufi ummi kawai
tarbiyan da akama safna ne ban ji dadin ganin ta ahaka ba,
kuma ummi be kamata abarta tana kula samari ba, ummi
sultan fah ba mutumin kirki bane lalata yaran muta ne
kawai yake yi. sai da ummi ta karewa jalal kallo san nan
tace, jalal ni fah na haifeka kar ka manta kamin alkawarin
babu aure tsakanin ka da yarinyar nan , to meye naka na
tada hankalin ka dan ka ganta da wani, to bari kaji na fada
maka daga yau babu ruwan ka da safna sultan auren ta zai
yi kar na kara ganin kaje kusa da su , inhar kana son
azauna lafiya. amman dai ummi ai be kamata ace za,a
mata aure yanzun ba. babu ruwanka ba abinda ya shafe ka,
suna cikin haka suji sallaman hajiya baturiya mahaifiyar
sultan tana rike da hannun sultan, jalal be sauri me zasu ce
ba, ya nufi dakin kairat ya samu safna kwance sai kuka
take, ya dade tsaye akanta bata ma san ya shigo ba, sai da
ya kare mata kallo sannan yace safna, da sauri ta dago ta
kalleshi. Ya sake cewa safna kina kuka na korar miki
saurayi. gargiza kai tayi tace ba haka bane yaya ni fada ne
bana son naga anayi.
.
Jalal murna ta kama shi ashe dai tana da hankali. yace
safna daga yau karki kara zuwa gurin sultan , ba auren ki
zaiyi ba kamar yadda ummi take fada, in na kara ganinki da
sultan ranki zai baci, ya sake kwantar da murya yace ko
kina son sultan din ne? Shiru tayi, tayi kasa da kai dan jalal
ya mata kwar jini da yawa, dan gani tayi ya kara mata kyau
duk wanda tayi dace ta samu jalal a matsayin miji ta more.
Jalal sake maimaita tambayan sa yayi safna nace ko kina
son sultan din ne. kanta akasa tace ni dama ummi ce take
tura ni. dadi yaji sosai ban da shi akwai wasu da ke zuwa
gurinki ne? eh tace dashi. to daga yau koma wanene yazo
karki Kara fita, kuma safna me yasa kike fita waje a haka,
har ki zauna kina hira da wani dubi jikin ki fah duk awaje
yake, kanki ko dan kwali babu, haba safna sai kace ba yar
musulmai ba, baki da hijjab ne ko gyale. safna ta kalli
jikinta gaskiya jalal ya fada kwata kwata be tace ba, tace
ina dashi yaya amman ummi tace na dai na sanya hijjab
idan zan fita. Jalal shiru yayi nadan wani lokaci san nan
yace karki kara saka irin wadan nan kayan, mijin kine kawai
ya kamata ya ganki da su, kuma inzaki fita ki sanya hijjab
ko gyale , kinji ko? juyawa yayi zai fita safna ta bishi da
kallo har ya kule. lokacin da jalal ya fito ummi kadai ya
samu a falon dan haka besan me suka shirya ba, zuwa yayi
ya wuce ummi da sauri ya shiga dakin sa, ummi binshi tayi
da kallo ta mike ta shiga dakin safna, wani mugun kallo ta
mata sannan tace jalal nan ya shigo? eh. me yace miki?
cikin in ina tace ba komi. saukan mari taji a fuskar ta ke
dan ubanki ni zaki ma karya zaki gayamin ko sai na miki
illa. safna tana kuka tace cewa yayi karna kara fita gurin
wani. Lallai kuwa ashe ba zaman lafiya kinzo har gida zaki
rabani da dana, to baki isa ba Bayan kwana uku da yin haka
jalal yasa ma safna ido sosai dan yanzun yana zama agida
sosai .
.
yau ko ya kula ummi shirye shiryen fita takeyi, ya name guri
ya zauna afalo duk da cewa ummi fushi take dashi, ba
kamar da ba. kalon shi tayi taga bashi da niyar tashi tace
yau bazaka fita bane? zan fita amman sai an jima. tabe
baki tayi ta kira safna tamika mata wata leda tace kaya ne
aciki maza ki sa kizo mutafi, ta karba ta juya. jalal ko jira
yake yoga wani irin kaya ne. ummi ta gaji da jira, ta sake
daga murya tace wai me kikeyi har yanzun. cikin sauri tace
ummi ganinan zuwa ta kara kasa da murya ummi yaya jalal
fah yace na daina yawo a haka. ummi tsaki tayi, ki fito kina
bata min lokaci, ta mike ta fita, jalal na zaune saiga safna
ta fito ta matse riga da wando ne jikin ta sai wani dan kamin
gyale, a tsorace ta wuce shi ya bita da kallo, har ta fita yaga
bazai iya jurewa ba ya mike yabi bayan su Lokacin tuni
ummi ta shiga cikin mota,itako safna kokarin shiga take,
jalal yace safna karki sake ki shiga cikin motar nan. cikin
fada ummi tace wai kai jalal Ina wasa dakai ne ko ni
abokiyar wasan ka ce, ummi wlh safna bazata fita tsirara
ba