RABO NA CE PART 9
RABO NA CE PART 9
.
Yana yin k'asan ruwan mutanen dake gurin suka fara kuka
suna ihu, wasu na cewa dama bai iya ruwa ba miya kaishi?
ita kuwa Ummey a hakan ta kamo hannun sa ta rik'e, amma
itama ta gama galabaita, dan kuwa ta d'irki ruwa ba kad'an
ba, mutum kawai na gani gabana ya nannad'e kafar
wandon sa na Jens, da wata yar singilegi fara ya fad'a cikin
ruwan, yana iyo cikin kwarewa har yakai gunsu ya janyo su
duka biyun ya fito dasu, banga fuskarshi ba,kawai wucewa
yayi abinshi yana fitowa dasu, nan fa yan makaranta suka
ci gaba da d'aukar su hoto, suna turawa a social network,
gaskiya wahalar da Mahbuob yasha Ummey batasha iriin
taba, nan dai aka musu abin da ya dace har suka dawo
hayyacinsu, bayan sun d'an natsu har suna magana anan
tama malamin godiya yana ba komai, suka wuce gida, Dady
yaji tsoro sosai dan har cewa yayi sai ta chanza course
amma yayarta Ummul- khairi ta nuna masa komai na Allah
ne, ko ina take hakan na iya faruwa da ita, har ta bashi
misali da fashin da aka musu lokacin a hanya, wanda da
taimakon Mujaheed komai ya daidaita sannan Dady ya
amince, su Ummul-khairi akwai iya tsara zance. A hankali
Malamin da ake kira Dr. Mahbuob ya rik'a gaisawa da
Ummey shak'uwa mai karfi ta shiga tsakanin su, duk
abinda ya shige mata duhu a fannin karatun shi yake
taimaka mata, shima ganin natsuwar ta da takun ta, sam
batada rawar kai irin na student musamman Gul- Gul
Sadydy uwar gulma, hakan yasa bai gaya mata abinda ke
ransa ba, anyi sa'a wannan karon ta gane cewa sonta yake
amma tunda bai furta ba sai ta saka masa ido, itama.
.
*********
"Dady wani taimako nakeson ka mini!" Inji Muhammad,
yace " Yaron Dady ina saurarenka" " Dady kullum idan muna
hira da Uncle Shaheed, idan nace ya kaini gidan sa naga
yaran sa, sai yace bashi yara, ko mata bashida, shine yace
wai na samo masa mata, ni kuma nace bansan ina zan
samo masa ba, shine yace wai ko Sister Ummey na bashi
yanaso sosai, Dady dan Allah ka bani Ummey na bashi ita,"
ya k'arshe maganar kamar zaiyi kuka, duka palon aka saka
dariya Ammar harda kwanciya gurin dariya, Ummey kam
saida taji wani ras ta d'aure fuska, " kai bana son kicihin
banza, ga Anti Najma nan ba kace a bashi ba saini da ka
raina wallhy yaronnan ya raina ni zanyi maganin ka
kwanannan " ta k'arasa maganar tana kallon Dady, shima
ya harareta yace " Olooow!!! Dan ma kin samu zan bashi ke,
wallhy kowa sonsa yakeyi, har makaranta wata tazo tace
zata siya min komai nakeso idan na bata number sa kawai,
kuma kinsan mai kud'i ne, ga yan mata nan masu kyau, ke
wallhy ma ba indiya ma zan bashi mai gashi, keda ko gashi
bakida," zunbur ta mik'e tayi cikinsa yayi gun Dady da gudu,
ya b'oye, yace "kaga kawai dan na fadi gaskiya, zata
dakeni," kowa yana dariya ita kuwa oganyar ta k'ule, dan
haushi ma barin palon tayi, Dady yace "kai k'yaleta
Muhammad na baka ita kaba duk wanda kakeso, " yayi
wani ihu, yana tsalle a palon an bashi ita zai baiwa Wanda
yakeso Muhammad kenan.
.
********
Yauma Kamar kullan sun fito daga aji suna tafe suna hira,
wani d'an ajinsu yazo yace mata Dr. Mahbuob yana neman
ta, ba musu taje gunsa dan tana jin dad'in labaran da yake
bata, ta shiga ta tarar yana ma mutane signing saida ya
k'are sannan ya juyo gunta, sun gaisa sai yayi shiru "yau ba
hira kenan" ta fad'a tana murmushi, shima murmushin yayi,
suka had'a ido sai ta duk'ar da kanta, ya kira sunan ta ta
d'ago kai," Dama akwai wasu maganganu da nakeson mu
tattauna ni dake, idan har kin bani dama, inason nazo gidan
dan bazai yiwu mu yisu anan ba" zaro ido tayi hope dai
Lafiya ko?" "No kada ki damu alkhairi ne zai kawo ni insha
Allah, ina fatar zaki bani address d'in ku" bata masa
gaddama dan mutuncin da suke yafi k'arfin haka, ta rubuta
masa address d'in ta bashi," nagode anjima zaki ganni"
Kamar yanda yayi alk'awari haka ya cika shi, da yamma
saiga Dr mahbuob har gida, bayan ta tarbeshi a mutunce,
kuma ta nuna ma Dady shi a matsayin wanda ya ceceta a
ruwa, Dady ya k'ara masa godiya duk da cewa sunyi waya
tun lokacin, amma basu had'u ba sai yau, Mumy ma ta
masa godiya sun d'an jima tare da Dady suna hirar ya da
gobe, sannan ya basu guri, bayan Dady ya wuce suka k'ara
gaisawa yake ce mata" Ummey nasan tun lokacin da nace
zanzo zakiyi mama kin zuwana gidan ku, to dama so nake a
d'aura min aure dake gobe a kai min ke gidana," wani d'ago
kai tayi da k'arfi, ta zare idonta, ta dafe k'irji, dariya ya
shiga yi," ashe haka kike da tsoro" sai lokacin ta gane
tsokanarta yakeyi, ta d'an shagwabe fuska, " Allah har kasa
na fara ganin jiri" yayi dariya, "to ko na d'au keki hotone," ya
fad'a yana ciro cameran sa, tace "Hmmm, wato ko ina da
ita ake yawo kenan,?" " eh mana bana son nayi missing d'in
abubuwa masu mihimmanci kamar irin tsoron da kikaji
yanzu, kinga da tana hannu na, da d'aukanki kawai zanyi"
dariya tayi, sunyi shiru na wani lokaci sannan ya fara
magana a hankali "wato Ummey tun lokacin da na fara
had'a ido dake naji inasonki, kuma zuciyata 100% ta aminta
dake a matsayin matar da nakeson na aura, tunda ya fara
maganar jikin Ummey yayi sanyi, ko d'ago kai ta kasayi ta
kalleshi, har saida ya k'are, a hankali yake magana, da ka
ganshi kasan wayayyen mutum ne wanda yaji boko, cikin
natsuwa yace "Ummey kinyi shiru, idan har akwai wani
wanda ya gabaceni kina iya gaya min ba komai nasan Allah
ke yin komai idan har ke RABO NA CE zan aureki," nan ma
kasa tankashi tayi, yayi ta magana, saida taga kamar baiji
dad'i ba sannan tace masa " Allah ya zaba mana mafi
alkhairi " har cikin zuciyarsa yaji dad'i, Dr Mahbuob mutum
ne mai natsuwa, sannan kansa a waye yake, komai nashi
cikin natsuwa yake yinsa, sai dai bai cika shiga mutane ba,
sabida yanada saurin fushi, tun lokacin da ya fahimci
halayen sa sai ya d'auki matakin keb'an ce kansa da
mutane, sabida zakiga abinda baikai ya kawo ba, ya isa
yasa yayi fushi, Dr. Mahbuob kenan, bai boye mata ba ya
gaya mata yanada mata d'aya da yaron su uku, twins d'in
su Hameed da Hameeda sai kuma k'aramin yaron sa Aliyu,
bata k'i amin ce masa ba, kuma bata nuna amincewarta ba,
k'arshe ya barta yace tayi tunani zuwa wani lokaci.. Yana
tafiya ta kira anti Najma d'aki ta bata labarin komai, anti
Najma ta taya ta murna kuma tace mata kada ta tsaya
shirme kawai ta amince dashi, taci gaba da addu'a zabin
alkhairi, tad'an ya mutsa fuska, "but nifa Anti Najma
matsalata d'aya kishiyar ce, yanada fa mata har da yara
uku, yanzu da yarinta na sai naje na auri mai mata!!!" Anti
Najma ta kalleta, "lalle Ummey, to ke duk tunanin ki ya k'are
akan sai saurayi zaki aura? Idan har haka kike tunani kinyi
kuskure babba, lallai ya kamata kiyi nazari sosai, idan kika
duba yanzu adadin mu mata ko, Allah yafi na maza yawa,
idan har akace ko wace mace zata rik'e mijin mace hud'u
ita kad'ai mi kike tunanin zai faru? Wallhy mata da yawa
zasu zauna ba aurene, Yanzu fa mu mun riga mun girma,
kiyi tunanin k'annen mu masu tasowa mana, suma fa sun
girma, sannan ko wacce tana buk'atar tayi aure, to ta yaya
za'ayi aure idan har ko wace mace ta kame miji tace ita
kad'ai zata zauna ba kishiya,??
.
dole muna saka tunani a lamuran mu, yes kishi gaskiya ne,
kuma duk mace zata fi son ta zauna ita kad'ai gurin mijinta,
amma idan hakan bai samu ba sai ta hak'ura su zauna da
yar uwarta, " Ummey da tayi zaune tasha uban tagumi tana
sauraren Najma, taci gaba, " dan Allah Ummey ki ijiye
tunanin auren mara mata gefe, ki saka ma zuciyar ki zab'in
alkhairi, ko mai mata ko saurayi, duk wanda kika samu
kawai kiyi fatan alkhairi, shine kawai babban abinda ya
kamace mu, da yawa zakiga yan uwan mu mata sun zauna
zaman jiran saurayi har su tsofe gida saurayi baizo ba, tana
jiran saurayi, shi kuma saurayin yana kallon ta a matsayin
antinsa, sai kiji suna cewa ai wance tafi k'arfi na, sai kiga
samarin sunk'i zuwa gurin ta, k'arshe ta auri wanda bata so
kuma mai matar, to ina amfanin haka? sannan idan kin lura
yawan lalacewar yan mata a yanzu yanada alak'a da
abinda da yawan mata sukeyi, na hana maza k'ara auren,
sai kiga yarinya ta girma tanason aure amma ba miji, idan
anyi rashin sa'a sai yarinya ta rik'a bin maza kinga akwai
alhakin ta akan wacce ta shiga ta fita ta hana mijinta k'ara
aure, kinga da ta barshi ya k'ara aure da ya taimaki
wanchan matar, kinga an sami raguwar barna, amma ta
hana, karshe ma mijin ya rik'a neman matan banza, gara
tun wuri kawai ki cire wannan tunanin a ranki kima kanki
fatan alkhairi," haka ta baiwa k'anwarta kuma k'awarta
shawara mai amfani, har ta aminta, wadda da ace duk
mata zasu rik'a wannan tunanin da komai zaizo da sauk'i...
..
Ummey ta kalli Shaheed ta kalli Muhammad da yayi tsaye
ya tokare yana kallon su, ta rasa mi zatace, tayi k'arfin hali
tace "Muhammad ka shiga ciki ina zuwa" ya kalli Shaheed
wanda yayi wani iri dashi, Shaheed ya daga masa kai
alamar ya tafi, sai ya wuce, Shaheed ya taso tsaye ya
matso kusa da Ummey, "ina dankawalin ki?" Sai lokacin ta
tuna bata da d'an kwali, Allah yaso ta ba kalaba bace
akanta da sai ya gudu dan firgici, juyawa tayi zata fita, ya
kira sunan ta, "Ummey " taja ta tsaya, ya nuna mata guri irin
ta zauna d'innan, ya fara, "Ummey nasan baki jahilci cewa
ni mai k'aunar ki bane shekaru kusan biyu da suka wuce!
Miyasa kika zabi kiyi soyayyah da wani bayan nasan kina
sona? Miyasa kika kasa hak'uri har na furta miki kalmar so
kika tafi gurin wani maimakon ni? Miyasa..." Juyowan da
tayi da k'arfi suka had'a ido, shiya dakatar dashi daga
zancen da yakeson ya fad'a, yayi shiru, ta kalleshi da
raunatattun idanuwan ta da suke neman zubar da hawayee
tace, "Please uncle Shaheed kadama ka fara, please
banaso, bazan iya ba, Allah bazan iyaba!!" Ta karashe
maganar tana hawaye, duk da ya rud'e sai yake ganin
kamar hawayen da take na rashin sa da tayi ne, "Ummey
har yanzu bamuyi letti ba har yanzu munada lokacin da
zamu maida komai dai-dai, kada ki damu nasan halin da
kike ciki, amma miyasa kika kasa hak'uri?" Ita sam bata
gane kan zancen sa, sai yana gaba yana baya, goge
hawayen ta tayi ta sunkuyar da kanta, gani yayi ba zance
kwane kwane. "Ummey wallhy bazan iya rayuwa idan bake,
please Ummey, " shi kanshi baisan lokacin da ya tsuguna
mata ba yana rik'on ta ba," lumshe ido tayi ta fad'a saman
kujera tana kuka, yanata magana Amma sam batajin sa
sabida tayi nisa a tunani, itako haka Allah zai jarabceta da
maza uku, wayanda duk sun chanhanci ta auresu!!
.
Tayi nisa sosai a tunani, dan har ta manta da Shaheed, tana
tunani tana zubar da hawaye, Muhammad ne ya rik'a
jijjigata a hankali ta bud'e ido, ta kalleshi, toshe baki yayi da
yaga tana kuka, "Ashe dukan ki yayi Shiyasa ya fita da sauri
Ina masa magana ya kyaleni," ya marairaice, yasa kas'an
rigar sa ya share mata hawaye, "Allah zan daina sonsa
tunda yake sakaki kuka,kuma ma na fasa bashi ke tunda
mugune" ya k'arasa maganar yana hawaye shima, ta janyo
shi ta rungume shi tana kuka "bai dake ni ba Muhammad,
zuciya ya daka, sabida kai nakeson uncle Shaheed amma
bansan yanda zanyi da Abban twins ba, bansan yanda
zanyi dashiba!"
.
Ta karashe tana kuka, yayi shiru dan yaji sabon zance waye
kuma Abban twins tambayar da yake ma kanshi kenan, ya
kalleta "To kiyi shiru bazan k'ara fad'a masa wani yazo
gurinki ba, kinji, kuma bazan bashi labarin ki ba ta kalleshi.
"dama kai kake fad'a masa Abu akaina??" Ya gyara zama
ya d'an goge hawaye, "Bashine yace idan inason kullam na
zauna a gidan saba sai na bashi ke, kuma yace duk ranar
da naga wani yazo gurin ki na gaya masa, kuma ranar ma
shine...." Toshe masa baki tayi ya isa Muhammad, mik'ewa
tayi ta koma d'akin ta, kuka ta shiga rerewa, itakam zata iya
sadaukar da farin cikinta ta farantawa Muhammad rai! Zata
iya barin kowane namiji idan dai kaninta zai samu farin ciki,
maganar Dady da Mumy ta dawo mata akai, "Aike madam
zanfi kowa farin ciki idan har Ummey na ta auri Mujaheed,
sabida Allah ya d'ora min son yaron nan, dan gudun halin
yaran zamani, da na had'a Ummey na da Mujaheed Aure
sabida na yaba da hankalin sa.... " Nan ma wani kukan ta
saka, Dady yanason Mujaheed, Muhammad yanason
Shaheed, ita kuma tana tarayya da Mahbuob, ya zatayi, sai
lokacin ta tuna wani magana da M. Jabo tayi a group d'inta,
da wata take cewa tanason tara samari biyu suna
soyayyah wai da dad'i, M. Jabo tace " ba dad'i, 'yar uwa sai
rashin kwanciyar hankali da rashin natsuwa," tabbas
gaskiya ne, tayi burin samun samari yana burgeta, amma
gashi rana daya suna neman su birkita mata lissafi, a haka
har baccin wahala ya kwasheta.. Muhammad kuwa yana
fita ya goge guntun hawayen sa yayi tagumi, shikam yana
son Shaheed har cikin ransa, Amma kuma yafison anti
Ummey dashi, sai lokacin ya tuna tace Abban twins, to
waye Abban twins? Tambayar da yake ma kanshi kenan,
nafee anka tazo tana tambayar sa miye? Sabida idan zaiyi
wayarsa bayan kitchen yake boye wa, tace ta ara masa
waya, number Shaheed ya kira Shaheed kamar bazai
d'auka ba sai ya tuna Muhammad shine duk wani hope
nashi a gun Ummey, ya d'auka. "Uncle kayi hakuri kaji, wai
Anti Ummey tace ita batasan yanda zatayi da Abban twins
bane, wai sabida ni take sonka," a hankali Shaheed yace
"Muhammad waye Abban twins?" "Nima bansan shiba
Mujaheed kawai na sani?," shiru yayi ya rasa abin cewa,
yafi minti goma yana mata magana d'azu tayi masa shiru.
haka dai suka k'are wayar jikin ko wanne a mace, nafee
anka tace "Minene Muhammad " ya harareta " ina ruwanki
dani, bayan dazu kince min d'an gulma" ta toshe baki
"Bayan na baka hak'uri mun shirya ko ka manta ne" ya tashi
ya bar mata gurinta ko kallo bata isheshiba Yar aiki da
shishigi..
.
* * * * *
Mujaheed zaune bakin ruwa, sai yau yake fahimtar abinda
yake gani a film na mutane zaune bakin ruwa suna tunani,
tabbas ruwa suna da wata ni'ima wacce lokacin da suke
gudana idan mutum yana kallon su, tabbas zai sami wata
natsuwa mai cike da tunani, a hankali ya kalli sama, hadari
ya had'u Amma ba irin mai ruwan nan ba, mai ni'ima ne,
kad'a kansa yayi a hankali yace " Bazai yiwuba, kece
buruna Ummey, kece HASKEN IDANIYATA, idan har kika
barni komai zai iya faruwa dani," A hankali ya shafo sajen
fuskarsa daya kwanta lub lub a fuskar nan tashi, abinka da
bafulatanin mutum kuma ga hutu a tattare dashi, kyanshi
kullum sai dad'a bayyana yake, maganganun Yusuf suka
rik'a dawo masa a hankali, sai yanzu take tabbatar da cewa
yayi wauta, yayi saki rashe ya kama ganye, Amma kuma ai
Ummey batace min bata sona ba, kawai tace min Allah ya
zaba mana mafi alkhairi, runtse ido yayi, "Dady do
something please.!!!"