Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 10

MIJIN MARAINIYA PART 10
.
Sai alukacin jalal ya kalli kayan sa sun yamutse amman
saiya dake ya kalli jikin shi yace muje kawai ummi. Wlh
bazaka fita a haka ba ,kai kadai ne me mata, ko akan ka
aka fara, haka kaga sauran maza suna fita? shiru yayi mata
bece komai ba. suna cikin haka alhaji ya fito yace me yayi
ne naji kamar kina mai fada? cinki daure fuska tace jifah
kayan shi wai haka zai fita. alhaji yace me kayan nasa
sukayi? jifa inda kayan shi suka ya mutse sai kace akan shi
aka fara aure. alhaji hada rai yayi yace jalal jaka abin ka. da
sauri jalal ya juya ya shiga dakin sa. alhaji ya kalli ummin
yace wai zaliha ko hauka za kiyi ne, ina ruwan ki da kayan
sa, irin wannan ai sai ya raina ki, yaya mutun da matar sa
zaki saka masa ido. alhaji bazance sa ido bane maganar
gaskiya ne, ai wannan rashin kunya ce. toh shikenan nasan
maganin abin ai in da suna gidan sune baza ki saka musu
ido ba, haba na menene zakibi kita kurawa yara wucewa
yayi ya fita ya ta fada. bayan jalal ya canza kaya ya fito
suka dau hanya ahanya ne ummi ta kalli jalal taga fuskar
shi murtuk tace jalal fushi ka keyi dan na gaya maka
gaskiya . a,a ummi ni ba fushi nake ba. ta sake cewa jalal
ni bawai ina kinka da safna bane, abinda yake damuna
shine sultan ya taba neman safna kuma kasan sultan ba irin
yan iskan da be nema ba, ina jin tsora kar ace ya shafa
mata ciwon zamani shiya sa nake tsoron karka kusan ce ta,
ta shafa maka. jalal yace ummi dan Allah karki kara irin
wannan maganar ba komai atsakanin su kuma lfyr ta kalau.
.
kar kace zaka shede ta dan ni na taba ganin su da ido na .
jalal yace dan Allah ummi kibar maganan nan ni bana so. ai
ina gaya maka ne dan ka kiyaye. toh zan kiyaye eh ummi
naji zan kiyaye. ganin da tayi kamar ya shiga damuwa yasa
ta murna tafara nasara. shikuwa jalal yasan cewa shi ya
fara bude matar sa a leda, amman zuciyar shi ta fara raya
mishi anya kuwa sultan be lalube safna ba kuwa , dan haka
ya kosa ya koma gida ya tuhu meta. da haka suka isa kofar
gidan yaya rabi , ummi ce kadai ta shiga, jalal ya tsaya a
mota. ummi ta shiga tare da sallama yaya rabi ta fito daga
cikin dakin ta sukayi ido biyu da ummi. ta fara fadin zaliha
kodai gizo idona kemin. ummi tace ba gizo bane yaya rabi
nice. aguje yaya rabi ta fada jikin ummi tana kuka, ummi
ma kuka ta saka , haka sukai tayi babu mai lallashin su .
bayan sun natsu suka shiga tattauna wa akan halin da suke
ciki, ummi ta kwashi duk yadda sukayi da baffa ta gayawa
yaya rabi. yaya rabi tace banga lefin baffa ba zaliha . ummi
tace nima banga lefin saba amman matakin da ya dauka
yayi tsauri yanzun a ina zan nemo saudatu, kawai ina ganin
bazai yafe min bane shiyasa yace saina nemo ta. toh nidai
abinda nake gani zaliha ki jaraba ki gani ko Allah zaisa
adace. toh ni yanzun ta ina zan fara, alhaji yace min wai
agidin wata bishiya aka bar ta ko? dan Allah ina son ki
tambaye min su baffa wacce bishiya ce kuma awace
unguwa ne. murmushin takaici tayi sannan tace zaliha
kenan ko kisan saida nayi shekara biyar ina zuwa gidin
bishiyar ina zama ko Allah zai sa na ganta amman ko me
kama da ita ban gani ba. ummi nisawa tayi sannan tace
kuma kin tamya agurin? tambaya kuma ai sai da na zama
kamar mahaukaciya duk wanda nagani saina tambaya.
ummi shiru tayi sannan tace yaya rabi banida saura wata
dama ila kawai ki gayamin gurin inje in jaraba ingani yaya
rabi tace kusa da unguwar ku ana cewa unguwar 'yan
mangorori, akwai wata katuwar bishiya agurin ada amman
ayanzun babu bishiyar amman akwai wata tsohowa tana
kasa kayan miya. tuni ummi ta gane kwatance domin tasan
unguwar sosai sai dai unguwar talakawa ne. jalal ne ya fara
kiran ummi awaya tace au na manta nabar jalal awaje yaya
rabi tace shine ya tsaya awaje sai kace bako. mikiwa sukayi
suka fito tare, jalal na zaune idon nan jawar ya kosa ya
koma gida ya tambaye safna ko sultan ya taba taba mata
jiki. bayan sun gaisa da jalal suka dau hanya jalal yaso su
wuce gida amman ummi tace sai sun biya yan mangorori.
suna isa ummi ta sauka ta isa gurin tsohuwa me kayan
miya bayan ta gaida ta , tace dan Allah mama tambaya
nake? yar tsoha cikin murna tace Allah yasa na sani hajiya.
dan Allah mama shekaran ki nawa agarin nan? ai ni hajiya
agarin nan aka haife ni ban taba zuwa ko ina ba. nan ummi
tashiga karanto mata tambayar ta. tsohuwa tsayawa tayi
tayi shiru zuwa cen tace, nidai kamar nasan lbrn nan
amman na manta tasake yin shiru ummi kuka tashiga yi
tana fadi mama ki nutsu ki tuna ahankali, ko kudi kike so
zan biya ko nawa ne kowa.
.
tsohowa tace yarinya ki kwatar da hankalin ki insha allahu
zan bincika miki kinga yanzun zan tattara kaya na gobe ki
dawa kin ga gidana cen koda baki ganni anan ba sai ki
shiga ciki. haka ummi ta aje ma tsohuwa kudi masu yawa
ta wuce. Suna komawa gida jalal ya fita amotar da sauri
yariga ummi shiga gida , ummi binshi tayi da kallo tazata
maganar da tagaya mishi ne yake damun shi , shikuwa jalal
cewan da tayi ta taba ganni su da idon ta shine abinda yake
tayar mai da hankali. yana shiga falo yaga safna kwance
tana bacci besan lokacin da ya finciko taba yafara janta
yana kokarin shiga dakisa da ita. safna cikin firgita ta fara
ihu dai dai lokacin ummi ta shigo , hango jalal tayi yana jan
safna idon shi arufe. ummi tarogo da gudo tana fadin jalal
metayi maka. ai jalal babu magana jan safna kawai ya keyi
Daker ummi ta kwaci safna ahannun jalal ta kaita dakin su .
da sauri ta juya ta nufi dakin jalal dan tana tsoron kar
yagayawa alhaji dan idan yaji maganar nan kashinta ya
bushi. tana shiga ta same shi sai faman share zufa yake
tace jalal kardai maganar da mukayi dazun ce tasa ka
shiga cikin wannan halin ? jalal yace ummi kefa kikace kin
taba ganin su da idon ki a,a jalal bahaka na ke nufi ba,
karufa min asiri kar alhaji yaji wannan maganar, nidai nace
kayi hakuri kabari ayi mata test , kuma ko safnan ban ce
kagayawa waba bare baban ka. toh ummi ai bai kamata ayi
shiro ba ya kamata kowa yasani. nidai nace karka gayawa
kowa, kai wlh duk kabi karice akan safna. jalal kallon ummi
yayi cike da ta kaici wato haryan zun tana nan akan bakan
ta saita raba mu , wai ita ummi bazata gyara halin taba ne,
tana cikin wannan halin baza ji da abin da yake damun
taba.
.
yace shike nan ya wuce, ummi mikewa tayi ta fita, dasauri
jalal ya dauki wayar shi yakira safna bata dauka ba saida
yakira sau biyar yaji shiru ya tabbatar safna fushi tayi
mikewa yayi yaje kofar dakin su yaji ta kulle, yasan ko ya
buga ba budewa zata yi ba haka ya koma dakin sa.
washegari 8:00 jalal ya fito cikin shiri shi na tafiya office
bayan yayi wa ummi sallama ya leka dakin safna har yan
zun kofar akule take, ya juya ya fita. ummi ma guri 12:00 ta
bar gida ta nufi yan mangorori, sai safna kawai ta rage
agidan, dan kairat ma tana makaranta. safna na zaune ita
daya agidan dan me aikin gidan ma tayi tafiya ga yunwa ta
dame ta rabonta da abinci tun jiya da rana gashi kuma yau
hakanan ta tashi da son cin zogale .
.
mikewa tayi ta shiga kitchen ta duba bataga wani abu da ya
bata Sha,aw ba bude wata roba tayi nan taci karo da garin
daddawa murna ce ta kamata tun daga nan tafara lasa tana
lumshe ido, da sauri ta daura miyar daddawa tana gamawa
tayi tuwo ta dai dai cikin ta tafito falo ta fara ci ,saiga kairat
ta dawo makaranta, zuwa tayi ta zauna zata saka hannu
dan sun saba cin abinci tare. kairat tace anty wannan miyar
meye na ganshi baki. safna tace kedai in zakici kici miyar
daddawa ce. da sauri tajanye hannun ta tana toshe hanci
anty dama anayi miyar daddawa ne. safna tace ke nidai
kawai yunwa nakeji ,bayan ta gama cin towan ta dauki
miyar ta fara sha kenan saiga jalal ya shigo. safna naganin
jalal ta mike da miyarta ahannun ta zata bar wajen. da sauri
jalal yasha gaban ta ya tsareta da ido sai kallonta yake,
itako kasa tayi da kai. jalal yace miye wannan kike sha?
banza tayi dashi tana kokarin aje miyar dan ta samo daman
guduwa tana aje miyar kuwa ta mamaye shi ta sheka aguje
ta shige daki. jalal binta yayi da kallo yasan safna nashiga
rufewa zatayi dan haka bebi taba. tsugunawa yayi ya dauki
miyar ya koma ya zauna yalli kairat dake kwance akujera
yace kairat faten meye wannan? kairata ta kwashe da
dariya tace yaya ba fate bane , miyar daddawa ce. miyar
daddawa kuma a ina ta samo shi? ita tayi da kan ta tace
yinwa takeji yunwa babu kayan abinci ne a kitchen din sai
daddawa, mikewa yayi yace kairat tashi kije ki zubar da shi.
ummi bata dawo ba sai yamma jalal na zaune aharabar
gidan yana shan iska , ummi ta nufoshi tun daga nesa jalal
ya fahin ci babu nasara. bayan ta zauna jalal yace ummi
akwai nasara kuwa?
.
ummi tace ba wata nasara jalal , yau nasha bakar wahala
jalal , rabon da na wahala haka na manta, munyi yawo nida
tsohowar nan har mun gaji amman bamu dace ba, duk
gidan wani tsoho da yake garin muje amman babu lbrn ta,
ummi ta fara share hawaye jalal ina cikin wani hali banda
me tausaya min duk duniyar nan sai kai, sai kuma yaya rabi
dubi duk abin da na mata bata juya min baya ba, amman
dubi alhaji yana shirin ya juya min baya, babu ruwan shi da
damuwa ta kamar ma dadi yakeji. ummi ki daina fadin
haka kuma ki kwatar da hankalin ki insha allahu indai tana
raye za,aganta ummi fashewa tayi da kuka to yanzo jalal
inta mutu ne yaya zanyi kenan su baffa bazasu yafe min
ba. jalal yace ummi insha allahu zasu yafe mike amman
ummi kunje har gidan me unguwa? ummi tace a,a Jalal
yace ummi ni gobe zanje na bin cika. washe gari da wuri
jalal ya fito yasamu ummi afalo kamar jira take ya fito ,
mikewa tayi tace jalal mutafi. jalal yace a,a ummi ki zauna
agida ki huta. ummi tace nidai kawai mutafi haka suka tafi
badan ran jalal yaso. suna zuwa gidan me unguwa suka
tambaya aka nuna musu bayan sun isa sun tarar da wajen
cike da mutane dukkan su suka sakko suka isa gurin tare
da sallama, ummi ce tayi bayanin abin dake tafe da su. me
unguwa ya nisa yace da kamar wuya ku me yasa tuntuni
baku nemeta ba sai yanzun, aiko tana raye kila bata garin
nan, har sun mike zasu tafi me unguwa yace amman bari
akai ku gurin babana kuyi mishi bayani ko zakuci sa,a ya
fahimci me kuke fada, dan ya dade kwance babu lfy. bayan
an kaisu gurin shi tsoho ne sosai ummi ta mai baya ni.
tsoho yayi shiru zuwa cen ya kira dan sa me unguwa yana
magana ahankali me unguwa yasa kunne me kake cewa
baba. baba tsoho yace karaka su gidan iya me kosai. me
unguwa yace baba ai iya ta dade da rasuwa. sai gani
hawaye sukayi yana bin kuncen baba tsoho ya sake cewa
kukai su gurin danta malam musa. Me unguwa ya sake
cewa baba malam musa yariga iya rasuwa sai dai matar
sa.