RABO NA CE PART 10
RABO NA CE PART 10
.
Yaci gaba da tunanin sa, in banda nima, Ya za'ayi inason
mace nace tayi k'ank'anta, wani tsaki yayi a ranshi yaji
haushin kan shi da kanshi, ruwan ya kalla, yama rasa mi
zaiyi, dan haushi, kawai zan matsa mata lamba,ne har ta
amince, ya mik'e ya kama hanya ya dad'e yana tafiya a
k'asa shida dokinsa, sannan yahau dokin ya k'arasa dashi
gida, yana shiga gidan Siyarmerh tazo tace, "Yaya ga
Muhammad d'ina zai gaidaka" ya d'ago kai ya kalleta,
"Waye Muhammad d'inki kuma" Rufe fuska tayi tana
murmushi, wani saurayi ne ya shigo madai daici ya tsuguna
har k'asa ya gaidashi, ya amsa cikin sakin fuska, sannan ya
tashi ya wuce, bayan sun wuce ya bisu kallo, aranshi yace
my guy wllhy kayi dabara, ya tuna tun Siyarmerh nada
shekara 16, yaronnan yake zuwa gurinta, yanata jin haushin
sa, ashe yasan mi yakeyi, gashi har takai 20 yana tare da
kayanshi, tsaki yayi ya shafa fuska shi da taji lallausan
gashi a kwance, ya lumshe idonsa, zuciyarsa sai bugawa
takeyi ya rasa abinda ke masa dad'i, tashi yayi ya wuce
d'akinsa ya d'auko waya, ya danna number Yusuf yana
d'aukar waya, "Yusuf please ka taimakeni mana! Yarinyar
na dana matsa mata sai cemin tayi fa, wai tama wani al
kawari kuma kaima sheda ne Ina tsananin sonta wallhy"
Yusuf dariya yayi son ransa sannan yace, "Aboki na kenan,
to mi zan maka?
.
Kanaso naje nace ke ki daina son wani kiso abokina tunda
ya dad'e yanason ki bai gaya miki bane ko Yaya?" Shiru
Mujaheed yayi, yama rasa abin cewa, Yusuf saida ya mayar
masa da duka zancen da sukayi last 2year ago, da yaji
shirun yayi yawa sai ya bashi tausayi sanan yace. "kazo
Kaduna sai mu wuce sokoto tare," Wani farin cikine ya ratsa
zuciyar Mujaheed, "Nagode abokina" Haka suka rabu akan
zai sami Yusuf suje tare a sokoton. Bayan wata uku.
Ummey ce ta fito daga d'akin ta taci karo da Muhammad ta
kalleshi ya kalleta, "Sannu sister" Ya gaidata, Gyada masa
kai kawai tayi ta fita gidan, dama makaranta zataje, na
kalleta, duk ta rame ta fita hayyacin ta, idonta sun wani
fad'a da ganinta kasan tana cikin damuwa, kada kuce fa
Mujaheed ko Shaheed ko Abban twins dayan su ya dage
k'afa, ko alama dukan su su nanan kowa ya matsa lamba,
kuma ko wanne yasan da zaman wani, ta rasa yanda zatayi
dasu ne, bama wanda yafi Mujaheed naci a cikin su, sabida
shi kamar ma abin ya tabashi ne, musamman yanda ya
mayar da sokoto kamar Kaduna da Zaria, kullum yana
hanya, Shaheed kuwa Muhammad ke kai masa rahoton duk
motsin Ummey, shiyasa bai cika zuwa sosai ba, saidai yana
damunta da waya, sai ya kira ayita waya fiye da awa uku,
har ta rasa abin cewa, idan kuma tak'i d'auka sai ya kira a
table d'in Muhammad, Muhammad jiki na rawa zai kawo
mata, Abban twins kam bashida matsala sabida tana
kulashi sosai tunda shine take ganin kamar wanda zata iya
Aure. Makaranta ta nufa tana shiga taji k'amshin da anyi
shekara kusan uku tanajin irinsa Amma har yau bataga mai
wannan k'amshin ba, Chan ta hango gul -gul uwar gulma
tareda wani saurayi ragajabul daidai ita, tana wani washe
hak'oranta kamar jaba taso kiss, girgiza kai kawai tayi ta
nufi hall dinsu, a hanya tayi karo da wani Lectr ya kirata
tana dubansa ta gane malamine shi yasa taje daya kirashi,
ya tambayeta sunan ta ta gaya mishi da dptmnt d'inta duk
ta mishi bayani baice komai ba yace ta wuce shi kuwa
akwai abinda ya kulla a ranshi , ta wuce tanata tunanin
waye wannan, ta k'ara juyowa ta kalleshi sai taga gul -gul
ta labe tana kallon su sai ta wuce abinta...
.
********
"Yauwa Dady kalli jikina, wasu k'uraje masu k'aik'ayi suka
fito min saima da dare suyi ta damuna da k'ai k'ayi su
hanani bacci," " Subhalallahi Ummey shine baki fad'i ba sai
a nemo miki ampicls ki sha ba, naga yana maganin k'uraje
sosai kwana biyu zasu k'ame" "Eh wallhy dan duk sunbi sun
dameni, kwana biyun nan Dady duk zazzabi nakeji sai na
rik'a jin amai, , kuma, inaga sune suke saka haka ko?" "Zai
zama sune idan na fita anjima zan siyo miki maganin duk
zasu bace" " Allah ya 'kara sauk'i" suka amsa da ameen,
.
*******
"Maman twins ya dace muje a mana GENOTYPE (awon jini
dan aga ajin da jinin ka yake ciki) koya kika gani?" Mahbuob
ne ya fad'a Murmushi tayi " OK Abban twins, idan ka shirya
sai mu tafi," sukaci gaba da hirar su har ya k'are sukayi
sallama, Ummey zaune itada Anti Najma tana shafa mata
mai akanta, sabida tun lokacin da khaleeesa Hydar ta bata
wannan tip na gyaran gashi ta mak'ale masa kullan cikin
gyaran gashin ake, ana shafa mai, kuma alhamdulillah
gashin yanzu yayi laushi sosai, sabanin da, da yake kamar
gashin doki, wani k'arfi yake dashi kamar me, Amma yanzu
yayi laushi, kuma ya chanza sabida yanzu tana iya
tattarashi tayi parking, Amma dachan bata taba iya had'e
shi guri d'aya, baya ma kaiwa, " Anti Najma kinsan
masokiyar nan tana damuna sosai," "Ki shafa turare mana,
kina shafa turare zata daina" Tace "to". Ta janyo turare ta
feffesa kasan k'irjin ta dan guraren ake sukarta, wani
lokacin idan aka soketa ko Ina na jikinta sai ya amsa,
"Yauwa na manta in gaya miki nifa yanzu bak'in kashi
nakeyi" Anti Najma ta k'yalk'yace da dariya, "Dama Ana
farin kashine Ummey" ta d'aure fuska, "Ke wallhy ba'a taba
maganar arziki dake, ai kinsan kashi Normal kalan shi ba
Black bane, Amma ni yanzu nawa bak'i ne fa" Ta koma yin
dariya, " kedai kin zama anti matsala, kullan da matsalar
dake damun ki, yau kasala, gobe zazzabi, jibi amai, sai
kace sabuwar kamuwa," Cikin kulewa Ummey ta k'wace
kanta da take mata kalaba tana shafa mata mai, "Eh
sabuwar kamu ce ciki nake dashi" ta fad'a idon ta sun kad'a
sunyi jaa "Allah ya baki hak'uri daga wasa, sai fushi," ta
janyo hannun ta tana bata hak'uri dagyar ta hak'ura ta
zauna, tayi shiru, itakam wannan guntun ciwon yana damun
ta, dole taje a dubata asibiti, dan batason kullan tana yan
ciwace ciwace, Wayarta ce ta dawo da ita daga duniyar
tunanin da taje, Uncle Shaheed ne ya kira. Ta d'auka tana
zunbo baki,wannan sarkin nacin, "Ko me zaki kirani dashi I
deserve it Ummey," toshe baki tayi tace "Laaaaaa bafa
dakai nake ba, Muhammad ne yazo yana damuna, shine
nace sarkin naci," yayi dariya mai sauti, "Ummey kenan!!!,
Muhammad har ya dawo makaranta yanzu," ta kalli anti
Najma ta yamutse fuska, "No ba Muhammad nace bafa
Mudhahhar nace yaron Anti Ummul-khairi," nan ma dariya
yayi, "Malama ki bada hakuri kawai, ai da Mudhahhar yazo
sokoto da tuni, Muhammady na ya bani labari" Zata kirbo
wata karyar sai kawai ya katseta da tambayar lafiyar ta, ta
d'an sosa kai naji sauk'i...
.
Yace Allah ya k'ara sauk'i, ya rik'a gaya mata kalmomin
soyayyah duk da bawai bashi amsa takeba haka yake ta
sakosu, har ta gaji tace chajinta ya k'are sannan sukayi
sallama, idan ta Shaheed ne baik'i su kwana suna wayaba
shikam bashida matsala.
.
"Mumy zamuje asibiti naga likita daga chan ma zanyi
GENOTYPE, nida Abban twins" Mumy tace "To sai kun dawo,
Amma bari na gaya ma Dadyn ku tunda yana nan." Ummey
tace to, ta nemi guri ta zauna, Mumy ta sami Dady tamai
bayani yace saidai a tafi tare da Al Ameen tunda yana gida
bai dace su tafi su kad'ai ba, aka gaya ma Al Ameen baiso
tafiya ba, amma bai isa ya kauce umurnin Dady ba, haka
suka tafi, Abban twins ne yazo ya d'aukesu sai asibiti, sunje
suka sami gurin a cike, suka sayi kati suka d'an bi layi da
yake laboratory d'in da mutane sosai. " Yauwa, Bari muje
muga General Dr. Sabida kwana biyu bana jin garau," ta
fad'a tana kallon Abban twins, "Muje tare mana," Abban
twins ya fad'a yana kallon ta shima, "To idan muka kai ga
layi bama nan fa,!" Ta tambaya, "Sai a k'ara bin wani layin,
tunda abinda ya kawo mu kenan" Al Ameen ya fad'a yana
wani d'aure fuska, dan a takure yake, an wani had'a shi
zuwa asibiti da mata, sunje suka sami likita, ita kad'ai ta
shiga, Ta masa bayanin ciwon ta. "Dama wasu K'URAJE
suka fitomin masu k'aik'ayi a jiki, kuma sai cikin dare suke
motsawa da k'aik'ayi, duk sai su hanani bacci, Bayan nasha
wani magani sai suka warke, but yanzu ZAZZABI nakeyi
sosai lokaci-lokaci, sannan ga KASALA kamar banida lakka
a jikina, haka duk abinda naci sai na rik'a jin AMAI, bayan
haka yanzu KASHINA YA ZAMA BAK'K'IRIN," ta fad'a tana
ya mutse fuska, Likitan ya jinjina kai, yayi yan rubuce
rubucen sa, ya d'ago ya kalleta, ya taso ya haska mata Abu
a ido, ya bude idonta yayi yan lek'e lek'en sa a idon komai
ya hango ohoo, ya dawo ya zauna yayi rubuta, ya sauke
glss d'insa na likitochi yace, "Ba wani Abu da yake damun
ki bayan wannan da kika lissafa?
.
" Girgiza kai tayi alamar babu, ya sake rubutawa, "Sorry Dr.
Na tuna wani Abu," ta fad'a tana kallon fuskarsa, " kasan
girjina KAMAR ANA SUKATA,kamar dai masokiya ko tsaye
na tashi sai naji wani iri" Ya girgiza kai, fuskarshi ta nuna
alamar tausayi matuk'a, ya rubuta ya sauke numfashi, "Na
rubutu miki BLOOD TEST, (awon jini) Dan zaifi a gane
hak'ik'anin abinda ke damunki, Allah ya 'kara lafiya" ya
fad'a yana mik'a mata takardar, tayi godiya ta fito tana
fitowa Al Ameen yace, "Na d'auka Chan zaki kwana ai,"
batace masa komai ba, dan batada lokacin sa, dan sai
yanzu su sayar da hali gaban Abban twins, dama duk suka
had'u guri d'aya sai sunyi fad'a bare yanzu da ba aka son
ransa yazoba. "Kasan likitannan ya k'ara turani
LABORATORY (Wajen awon su jini da sauransu) wai sai an
mini awon jini sannan za a gane takamaimen mi yake
damuna," "To ai da sauk'i tunda guri d'aya ne ma," suka
wuce Allah yasa ba mutane sosai, so basu wani dad'e ba
layi ya kai garesu, suka shiga ta mik'a ma Matar takardar
da likata ya bata, bayan ta d'ibi jinin ta, sannan suka fito,
results sai ranar littanin, a hanya ya kaisu wani had'ad'den
restaurant sukaci abinci, sai lokacin Al Ameen ya saki jiki
har yana hira, bayan ya saukesu gida ya wuce, tana shiga
gida ta wurga jaka saman kujera cikin fushi tace, "Wallahi
Allah Mumy kada a k'ara had'a ni da wannan mutumin fita
unguwa, kinga yanda ya rik'a disgani gaban Abban twins"
Harara ya watso mata, " hw is Abban twins? Ba Abban
twins ba Abban world , Mumy fa shanyani tayi, taje tana
tad'i da likata " Ta dafe k'irji ta zaro ido, "Kinji sharri Mumy!!
Amma guy d'innan baka had'u ba wallhy" ta fad'a tana
barin gurin dan haushi ya isheta. "Ai ke kin had'u, kinga ta
gudu ko Mumy, batada gaskiya ne" Shi yama Mumy bayanin
komai ita kuma tama Dady.
.
********* Ranar Monday tunda safee Al Ameen ya gudu dan
kada a had'a su zuwa asibiti tare, k'arshe da Nafee anka
Yar aikin su suka tafi, sabida Dady yace bazasu tafi su
kad'ai ba, yazo ya d'aukesu sai asibiti.
.
Sunje gurin likita, ya basu result (sakamakon awon) d'in su,
da yake duk HEMATOLOGY ne (Kwaji na Abinda ya shafi
jini) Abu biyar ne nata, shi kuma nashi hud'u da BLOOD
GROUP HB GENOTYPE HIV 1&2 HCV HBsAG, Amma shi
nashi ba HCV d'in HCV Ta duba da kyau BLOOD GROUP
nata A+ shi kuma nashi B- HB GENOTYPE nata AA, shi
kuma SS, Sai ba HIV dukan su negative (basu dashi kenan)
Sai HCV shima duka basu dashi, HBsAG kuma ita positive
shi kuma negative, ta kalleshi, "miye wannan HBsAG d'in"
Ya kalla inaga wani Abu ne nasu, "Ni dama nafison naga
kashin da jinin mu yake, sabida kinga Maman Hameed ita
SS ce nima SS, sai aka rik'a samun matsala wallhy, yaran
mu duk sickle ne, shiyasa kika ga na damu a mana
GENOTYPE d'in nan, kuma gashi komai yayi alhamdulillah"
tayi dariya, "To ai sai ka mini bayani nifa kasan dalibar gona
ce so bana gane wanni AA da SS, kawai dai na gane cewa
is different alphabet" Dariya yayi, wacce take nuna tsananin
farin cikin sa, "To zauna sai na miki bayani dalla- dalla" suka
nemi kujera suka zauna, "Yauwa kinga idan mutumin da
yake AA yayi aure da AA ko, to zasu haifi yara masu lafiya
sosai ba ruwan mutum da tunanin wani GENOTYPE, yaran
sa zasu kasan ce cikin lafiya. sai kuma AA da AS, shima ba
laifi is good, Amma kinga baikai AA and AA ba, zaku iya
samun yara dukan su AA, ko AS idan anyi rashin sa'a yaran
duk zasu iya zama AS Amma dai ba za'a sami SS ba. Sai
namu AA da SS ne wanda shi kuma badai good bane,
Amma dai ba laifi zamu haifi yara masu AS, ko kuma SS
kawai ba zamu haifi AA bane, Amma dai ba laifi, insha
Allah. And sai AS da SS su ne kam bai dace suyi Aure ba
gaskiya, su wannan kima bar zancen SS da SS shi kawai
zasu jefa yaran su cikin hadari ne da rashin lafiya, sabida
duk yaran da zasu haifa SS ne, SICKLE, shiyasa likitochi
kullum suke ma mutane bayani akan ya dace kamin Aure
mutum yayi GENOTYPE dan samun lafiyayyar zuri'a, wai
kina ganewa kuwa" Tayi dariya, " Ni wannan AA, AS SS,
kawai ne ban san ma'anarsu ba, kai kuwa sai kawosu
kaketayi," To wannan sai ki nemi littafin "RABON KA YANA
BAKIN KURA" (na Amatullahi chuchun gaye tayi bayanin
komai dalla dalla.)
.
"Laaaaaa kaima kana karanta novel ne?" Ta fad'a cikin
mamaki, "No yayarki ce take karantawa, ita ma ta mini duk
wannan bayanin, saboda duk yana nan cikin littafin chuchun
gaye, tace tayi bayanin komai dalla-dalla," "Ai kuwa sai na
nemi book din dan nasan ma'anar su AA AS SS, d'innan"
Kinga ni SS yayarki ma SS shiyasa yaran duk ba lafiya,
muna ma tunanin dakatar da haihuwa kar mu rik'a cutar da
yaran, kullan ba lafiya, musamman Hameed" ya fad'a yana
dan sosa kai, "Eyyah Allah ya 'kara lafiya ya tsare gaba,"
"Amin ya Allah. abin yana damuna matuk'a ya dace mutane
su farka su rik'a yin GENOTYPE kamin Aure dan su
samarwa yaransu lafiya ingantacciya, tunda kinga yanzu
zamani ya chanza, komai ana ganewa ta hanyar kwajin
likitochi. Yanzu fisabillihi ki duba yara nawa suke da shan
inna? Sabida rashin kulawar iyaye kamin aure, idan
mutanen dauri sunyi sakaci ya kamata na yanzu su farka,
kuma fa dai kin gani ba tsadane dashiba, bare suce Yar
Buhari ake yanzu." Tayi dariya "Wai Yar Buhari yanzu ko Ina
ka tab'a 'yar Buhari." Shima dariya yayi, Wayarsa ya d'auko
cikin aljihu, "Oya selfie" ya gyara d'aukar hoto,itama ta d'an
yi murmushi ta matso da kanta, shi kuma ya turo baki
kamar Benaziratu zata d'auki hoto, wai ita gayu, sukayi
selfie sunyi kyau sosai, ya mik'e tsaye. "Mu tafi ko?" Ta
d'an yamutsa fuska tace, "But nidai inason a duba min
wannan HBsAG d'in, dan gaskiya bai kwanta min, inason
sanin miye shi." Duk da baiso ajeba amma ba yanda ya iya
ta nace, sai yace su tafi aga miye HBsAG d'in. Haka suka
koma gurin likita ya karb'i results ya duba, ya karanta yace
to "HCV yana nufin HEPATITIS C.wanda bakuda shi, HBsAG
yana nufin HEPATITIS, B. (Duka ciwon hanta ne)" Likitan ya
kalleta, "Ummey kina d'auke da ciwon hanta, kuma B ne
shine mai tsananin, so ki zama very careful, sabida mugun
ciwone, musamman naki da yake HEPATITIS B.
.
ne, kinga na farko bashi da magani, kuma ana daukar shi ta
hanyoyi da dama, zan iya ce miki gara HIV da HEPATITIS
gaskiya musamman B. Irin naki," tunda ya fara magana
Ummey ta sandare a zaune, jinsa kawai takeyi, amma ta
fita hayyacin ta, liktan yayi yan rubuce rubucen sa, "Ki
tuntubi Dr. John specialized (kwararre) ne a gurin aikin
hanta, aikin sa kenan," Ya rubuta mata wani abu, ya mik'a
mata "Kinga wannan VIRAL LORD ne, dole kiyishi shima
wani gwajin jinine, a nan za'a ga k'arfinsa a jikin ki, sannan
a baki wasu magungunan da zasu sa kiji sauk'in su zazzabi
kasala da sauransu, Amma bashida magani gaskiya." Kuka
ne yaci k'arfinta, har likita ya k'are bayanin sa, kuka takeyi,
Mahbuob ya mutu a tsaye, dan yama kasa rarrashin ta
tunanin sa d'aya kawai, ina ta samu wannan mugun ciwon?
Babbar matsalar shi ma yanzu, cewar da akayi Ana d'aukar
ciwon harma yafi HIV hadari.!! Gaskiya da sakee, inada iyali
bazan yab'a musu cuta ba, yayi nisa da tunani saida likitan
ya dawo dashi ta hanyar masa magana, sannan ya farka
daga dogon tunanin da ya tafi, ya motsa. "Ina zuwa likita"
fita yayi waje, ya kira 'yar rakiya Nafee anka, "Kizo ki
taimaka a fito da ita wajee kuka takeyi," Cikin mamaki ta
shigo taga Ummey na kuka a rud'e ta tallabota, Amma Ina
Ummey bata iya ko mik'ewa tsaye bare tafiya, sabida gaba
d'aya jikinta ya mutu, da taimakon wasu nurse aka fito da
ita wajee, a waje yakebe da d'aya daga cikin nurse d'in da
suka kawota waje, " please ana d'aukar CIWIN HANTA ta
numfashi.?" Da yake nurse d'in kidahuma ce irin masu kuri
da uniform ce kawai batasan komai ba, sai tace. "Sosai ma
kuwa, ai mugun ciwone, gara kanjamau dashi, bakaga
saida muka toshe hancin mu ba." Toshe baki yayi ya wuce,
ya tsaya daga nesa dasu, "Nafee bari na samo napeep ta
kaiku gida" sabida motar tak'i tashi, ya fito wajen asibitin ya
nemi napeep ya durasu ciki, ya tsaya kallonsu har suka
bace masa. " Ummey duk Sonda nake miki WALLAHI bazan
Aure ki kinada HEPATITIS (ciwin hanta)ba!!!"