Breaking News

RABO NA CE PART 5

RABO NA CE PART 5
.
"Kema kinsan Mumy bazata mana girki ba, ai kawai muyi
sauri muje," " Ummey kin cika gaddama, nasan Mumy Allah
da kin gaya mata cewa surukinta zaizo da gudu zata had'a,
" hararan ta tayi, "waya gaya miki surukinta ne!?" Ummey ta
k'ara sauri, ta wuce abinta, Najma ta biyo bayan ta, tana ayi
mu gani, Sunna isa gida ta tatar da Dady ya dawo, "sannu
Dady! Kasan jaheed yazo kuwa, kuma wai zaizo ya gaidaka,
" cikin murna ya amsa yana jin dad'i " Allah ya kawoshi
lafiya yaron kirki," sun d'an taba hira da sauri ta fad'a
kitchen ta d'an masa abin motsa baki, tunda zuwan ba zata
ya mata, guraren k'arfe biyar sai ga d'an halak ya iso, shida
abokinsa suke gurin Dady ya tsaya sun dad'e suna hira har
yake tambayar aikin da yakeyi duk ya masa bayani, Dady
yaga kamar bashida niyyar tafiya gurin Ummey, dan ya
d'auka gurinta yazo, ya mik'e yace " bari na shiga ciki, zan
turo maka Ummey d'in, " cikin kunya Mujaheed yace " NO
Dady dama gurinka nazo mu gaisa, yanzu zamu wuce,"
Dady ya dawo sukayi sallama ya rakasu har k'ofar gida
sannan ya dawo ciki, Dady aranshi yake cewa ashe bama
abinda nake tunani bane, suna fita Yusuf ya haushi da
maseefa, " amma Allah Mujaheed baka had'u ba, taya
zakazo gun yarinya sannan ka wani cewa baban ta gunsa
kawai kazo, " Mujaheed ya sosa kai "Allah aboki na kasa ne,
bari na kirata nace mata na wuce kawai" " idan ma kunya
kakeji tunda yace zai kira sai kace to kawai," tsaki Yusuf
yayi ya rungume hannayensa, ya juya masa masa baya, ya
d'auko waya, ya danna number ta ringing uku na hud'u ta
d'auka, tana d'auka tace " jaheed ya ka tafi bamu gaisaba,?
Yanzu Dady yake gayamin ka wuce" " sorry please dama
gurinsa mukazo na d'auka zaki fito ne, gashi har mun kama
hanya," haushi ya kama Yusuf baisan lokacin da ya kwace
wayar ba, " hello Ummey, kiyi hak'uri yanzu zamu dawo mu
gaisa dake, nima naso mu gaisa sai kuma anata kiran mu a
waya, Amma yanzu already mun bada sak'on, yanzu zamu
shigo" " okay na gode sai kun iso" ta kalli anti Najma " harfa
sun wuce abokinsa ne yace zasu dawo, wai sako suka
bayar" ya kalli Mujaheed " wallhy zaka mutu a banza, kana
son yarinya amma ka kasa approaching nata, wai tayi
k'arama, yanzu kalli yanda kake wani cewa mun kama
hanya, da saidai ka k'ara kwabe komai, Mujaheed kam d'an
sosa kai kawai yayi ya dafa kafadar Yusuf, ai tunda ka
gyara abin mu shiga ciki ko.
.
Suka shigo ciki ,Mujaheed sai sunkuyar da kai yake kada su
had'u da Dady, dan kunya yakeji a gansa ya dawo, sun
had'u da ita a palo, suna had'a ido ta watso mai hararan
wasa, saida yaji wani shock, " yanzu dan Allah sai ka tafi
bamu gaisaba, Allah ka bani mamaki," ta fad'a tana musu
iso cikin main palon nasu, "sannun Ku da zuwa Malam.......
"
.
"Yusuf " Mujaheed ne ya k'arasa mata dan ya gane hakan
take nufi, sun gaisa da Yusuf tana ta korafi, shikam Yusuf
sai bata hak'uri yakeyi, cikin barkwanci, anti Najma ce ta
shigo ta kawo musu hadden zobon da aka had'a yaji abarba
da cucumber, da kayan yaji, had'in na gargajiyane, sai
k'amshi yake tashi, da d'an snacks da suka had'a a
gurguje, sun gaisa Najma ta mik'e zata fita Yusuf yace
"sister please muje ki nuna min gunda ake siyar da kati,"
yayi haka ne dan ya baiwa Mujaheed gu su d'an zanta,
Ummey tace " ai ku dawo zan siya maka " ta fad'a tana
k'ok'arin janyo wayarta, " no ki barshi na gode, ya fice
abinsa" aka barsu su kad'ai, a d'akin, a hankali ta tashi ta
zuba mai zoben da snack d'in ta ijiye masa gaban sa"
bismillah ko" ta fad'a tana kallon sa, murmushi yayi ya
d'auka, ya fara ci, " kai amma zobonnan yayi dad'i " tace "
na gode " shikam duk a dabirce yake ya kasa ta b'uka
komai, itace ma taga shirun yayi yawa, ta fara masa
magana, " ya mutan gida?" " suna lafiya suna gaidaki da
jiki" " Allah sarki ina amsawa na gode " sun d'an taba hira
sama-sama dan ma maganar Ummey tafi tashi yawa sosai,
aran ta take cewa "anti Najma da take cewa yana sona ni
banga wani so anan ba, mutumin da ko kallonna bayayi" a
haka har Yusuf ya dawo, "aboki ina ka tafi wannan dad'ewa
haka," " Ina ruwan ka, an gaya kowa irin kane? " ya gane mi
yake nufi sai ya basar, "okay bari mu wuce ko Ummey"
Yusuf ya fad'a kan kujera ya zauna, " nikam sai na huta
gaskiya, " ya fad'a yana tsiyaya zobo a cup, yasha shima
yayi santin zobon " Ummey ya ake had'a wannan zobon na
gayawa matata ta rik'a man irinsa" duk aka saka dariya,
Mujaheed da ya mik'e tuni ya dawo ya zauna dan ya fahimci
Yusuf bashi da niyyar wucewa, yaso haka shima har cikin
ransa saidai ya rasa mi yasa duk ya sukurkuce, anti Najma
tace" saidai ka bamu number ta mu tura mata had'in ina
zaka iya haddacewa" yace "kedai fad'a min kawai ina jinki,"
tayi dariya ta fara masa bayani " kaga zata tafasa zobon ta
yanda takeso, amma gun tafasar ta saka masoro kanunfari
da citta kad'an dai-dai zobon ta, tana iya tafasawa da
bawon abarba idan tana buk'ata, sai ta sami abarba da
cucumber ta markada da ijiye gefe, ta tace zobon ta tace
wannan markaddaen abarba da cucumber, ta juye su cikin
zobon, ta suka suga, tasa flavor na abarba, ta saka foster
clak idan tana buk'ata, ta saka sugar ta juyasa, ta saka
cikin fridge yayi sanyi shikenan ta had'a wannan zobon da
kake santi " suka saka dariya gaba d'aya, Yusuf yace "
kawai zan baki number ta sai ki tura mata, dan ban gane ba
gaskiya, " duk aka k'ara saka dariya, Ummey tace" dama
nasan baza iya ba, wannan sai mu mata" sun dad'e suna
hira da taimakon Yusuf, jaheed sai satar kallonta yake, sai
guraren Magreeb sannan suka tashi zasu wuce, Yusuf yace
" ya kamata muyi hoton tarihi, Mujaheed kamar ya rungume
shi dan murna, " Yusuf ne mai d'auka, shi baya yi wai yana
tsoron madam d'insa ta gani...
.
Suka shigo ciki ,Mujaheed sai sunkuyar da kai yake kada su
had'u da Dady, dan kunya yakeji a gansa ya dawo, sun
had'u da ita a palo, suna had'a ido ta watso mai hararan
wasa, saida yaji wani shock, " yanzu dan Allah sai ka tafi
bamu gaisaba, Allah ka bani mamaki," ta fad'a tana musu
iso cikin main palon nasu, "sannun Ku da zuwa Malam.......
"
.
"Yusuf " Mujaheed ne ya k'arasa mata dan ya gane hakan
take nufi, sun gaisa da Yusuf tana ta korafi, shikam Yusuf
sai bata hak'uri yakeyi, cikin barkwanci, anti Najma ce ta
shigo ta kawo musu hadden zobon da aka had'a yaji abarba
da cucumber, da kayan yaji, had'in na gargajiyane, sai
k'amshi yake tashi, da d'an snacks da suka had'a a
gurguje, sun gaisa Najma ta mik'e zata fita Yusuf yace
"sister please muje ki nuna min gunda ake siyar da kati,"
yayi haka ne dan ya baiwa Mujaheed gu su d'an zanta,
Ummey tace " ai ku dawo zan siya maka " ta fad'a tana
k'ok'arin janyo wayarta, " no ki barshi na gode, ya fice
abinsa" aka barsu su kad'ai, a d'akin, a hankali ta tashi ta
zuba mai zoben da snack d'in ta ijiye masa gaban sa"
bismillah ko" ta fad'a tana kallon sa, murmushi yayi ya
d'auka, ya fara ci, " kai amma zobonnan yayi dad'i " tace "
na gode " shikam duk a dabirce yake ya kasa ta b'uka
komai, itace ma taga shirun yayi yawa, ta fara masa
magana, " ya mutan gida?" " suna lafiya suna gaidaki da
jiki" " Allah sarki ina amsawa na gode " sun d'an taba hira
sama-sama dan ma maganar Ummey tafi tashi yawa sosai,
aran ta take cewa "anti Najma da take cewa yana sona ni
banga wani so anan ba, mutumin da ko kallonna bayayi" a
haka har Yusuf ya dawo, "aboki ina ka tafi wannan dad'ewa
haka," " Ina ruwan ka, an gaya kowa irin kane? " ya gane mi
yake nufi sai ya basar, "okay bari mu wuce ko Ummey"
Yusuf ya fad'a kan kujera ya zauna, "
.
nikam sai na huta gaskiya, " ya fad'a yana tsiyaya zobo a
cup, yasha shima yayi santin zobon " Ummey ya ake had'a
wannan zobon na gayawa matata ta rik'a man irinsa" duk
aka saka dariya, Mujaheed da ya mik'e tuni ya dawo ya
zauna dan ya fahimci Yusuf bashi da niyyar wucewa, yaso
haka shima har cikin ransa saidai ya rasa mi yasa duk ya
sukurkuce, anti Najma tace" saidai ka bamu number ta mu
tura mata had'in ina zaka iya haddacewa" yace "kedai fad'a
min kawai ina jinki," tayi dariya ta fara masa bayani " kaga
zata tafasa zobon ta yanda takeso, amma gun tafasar ta
saka masoro kanunfari da citta kad'an dai-dai zobon ta,
tana iya tafasawa da bawon abarba idan tana buk'ata, sai
ta sami abarba da cucumber ta markada da ijiye gefe, ta
tace zobon ta tace wannan markaddaen abarba da
cucumber, ta juye su cikin zobon, ta suka suga, tasa flavor
na abarba, ta saka foster clak idan tana buk'ata, ta saka
sugar ta juyasa, ta saka cikin fridge yayi sanyi shikenan ta
had'a wannan zobon da kake santi " suka saka dariya gaba
d'aya, Yusuf yace " kawai zan baki number ta sai ki tura
mata, dan ban gane ba gaskiya, " duk aka k'ara saka dariya,
Ummey tace" dama nasan baza iya ba, wannan sai mu
mata" sun dad'e suna hira da taimakon Yusuf, jaheed sai
satar kallonta yake, sai guraren Magreeb sannan suka tashi
zasu wuce, Yusuf yace " ya kamata muyi hoton tarihi,
Mujaheed kamar ya rungume shi dan murna, " Yusuf ne mai
d'auka, shi baya yi wai yana tsoron madam d'insa ta gani...
.
Haka suka fito cike da nishadi sabida Yusuf akwai ban
dariya, bayan sun shiga mota Yusuf yana driving, " na bud'e
Bluetooth d'an watso min pics d'innan," Yusuf ya masa
banza ya k'ara maimaita wa, " kada ka dameni please,
bakai na daukowa ba, madam zan kaiwa ta gani," saida
Yusuf ya k'are masa wulak'anci sannan ya tura masa pics
d'in, kamar an sakashi aljanna yakeji sai kallon su yakeyi
yana zooming, ya kalli Yusuf " mun dace ko?" " ka fini sani
ai" saida Yusuf ya masa fad'a akan ya dace ya gaya mata,
dan kada yayi sake reshe kama ganye, yaji hud'ubar
abokinsa amma bana jin zai iya aikatawa
.
*********
"Mujaheed wai miyasa baka son fita da wancha dokin"
Habeeb ya fad'a yana nuna wani doki, Mujaheed ya kalli
dokin " kai wanchan dokin Allah ko mace ta fishi k'ok'ari "
Habeeb kam dariya ya shigayi, " what is funny " " No thing, I
just wana laugh ne " "kai mugune baka dariya haka kawai,
miyene please" Habeeb wuceshi yayi ya kwance dokin da
aka cewa kamar mace, ya shafashi, Mujaheed na biye
dashi, ya dorawa dokin sirdi, ya had'a linzami da komai, ya
haye, ya kalli Mujaheed, " kazo mu fita mana" ba musu
Mujaheed ya kwanto dayan dokin shima ya hau, suka fito
gida, sun fara gudu, bawai tsere sukeyiba, gudu kawai
sukeyi, Habeeb yace " ya zancen Ummey Ibraheem d'in ka" "
wani murmushi yayi ya kyara zama akan dokinsa, "
tananan, ko d'azu mun gaisa" da k'arfi suke magana sabida
gudu suke sosai saman dawakin, " kai kullan sai kace kun
gaisa, ana soyayyah ba ci gaba, kullan sai gaisuwa, kai ka
kasa gaya mata abinda ke ranka" yayi tsaki, "Allah na kasa,
kullan na kirata da wannan niyyar nake kiranta amma har
yau na kasa fad'a mata sai nake ganin har yanzu k'arama
ce, kanta bazai iya d'aukar kalmar soyayyah ba" Habeeb
yayi dariya, "ka tsaya sauna saidai kaji nakai sadakinta na
gayyaceka ko ta gayyaceka d'aurin auren mu" kamar bomb
ya tashi a garin maba, haka Mujaheed yaji a ransa ya wani
ja linzamin doki da k'arfi, ya tsaya, Habeeb har ya wuce ya
dawo yana dariya, " please bana son irin wannan magana,
idan ma wasa ce banason irinta"
.
Munafuki dama ashe sonta kakeyi, shiyasa kullum kake min
zancen ta, " dariya Habeeb yayi sosai sannan ya matso
kusa da dokinsa gun jaheed, Mujaheed ya kauce, ya k'ara
matso wa ya saka shi gaba ta yanda bazai iya kaucewa ba"
ni ba sonta nakeba yalllabai, nayi amfani da word d'in kai
na ne, because ina son ka gane mi nake nufi, gashi kuma ka
gane da kyau, kaga idan har baka gaya mata ba, kawai
zakaji ta gayyaceka d'aurin auren ta, kaga kuma mace
irinta dole ta sami masoya, so dole ka bayyanar da
ra'ayinka," murmushi Mujaheed yayi, " Allah ba kaji yanda
nawani ji na tsanekaba da ka fadi maganar d'azu ba, ka
daina mun irin wannan misalin please" "share kawai, aboki
amma yanzu d'an hasko min pic d'inta mu gani," " ank'i" ya
fad'a yana k'ok'arin gyara kan dokin sa, dariya Habeeb yayi
sosai, sannan shima ya gyara kan dokinsa sukaci gaba da
gudunsu, sai da sukayi mai isar su sannan suka dawo gida,
yayi wanka yaci abinci.
.
**********
" Dady lafiya na ganka somehow ?" Ya kalleta " Ummey Yar
Dady, ke kad'ai kike gane damuwar Dady lokaci d'aya" "ai
kuwa Dady nima ina ganewa, kawai yanzu sister ta riga ni
fad'a ne, amma nima naso nayi magana nace ka daure
fuska" ita kam Mumy kallon su kawai take, Family ne mai
cike da had'in kai da girmama juna, Mumy itace Matar
Alhaji Ibraheem, wanda shine M.D na fitacciyar jaridar nan
tamu ta k'asa, basai na fad'i suntaba kunsanta, Allah ya
azurtashi da yara masha Allah, har guda bakwai, Maza
biyar mata biyu, Mahmoud shine babba sai kuma Aliyu
zakin fama wanda duk sunyi Aure su, sai kuma mace
ummul-khairi, wacce itama tayi Aure harda yaron ta d'aya
mudhahhar, sai kuma Al-Ameen, sannan Rukayyah wacce
suke kira da Ummey, sai Ammar, sai kuma autan su sarkin
kiriniya Muhammad, suna gudanar da rayuwar su cikin
natsuwa da jin dad'i dai-dai kwarkwado, sun sami tarbiya
Alhamdulillah, Najma yarinyar Kanin Alhaji Ibraheem ce,
wacce tun tana k'arama jinunsu ya had'u da Ummey, dukda
ba sa'ar ta bace amma tare suke komai nasu.