Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 7

MIJIN MARAINIYA PART 7
.
Nusaiba bata ci gaba da sauraren suba ta wuce dakin
safna, anan ta samu su hajiya fatima, tace ya naga kun
dawo nan kuma. hajiya fatima tace to me gidan tace
mushiga daga ciki zatayi baki, shiyasa muka yo nan. anty
nusaiba nisawa tayi tace anya kuwa zamu zauna agidan
nan har agama biki, kodai zamu koma gidan hajiya ne muyi
namu acen, dan nifa gaskiya bazan dauki wula kanciba .
Hajiya fatima tace nima nayi tunanin haka amman saina
tuna hajiya fah da zamu taho tana ta gargadin kar muce
zamuyi fushi muyi hakuri da duk abin da muka tarar dan
haka gara mu hakura mu zauna ko dan kan ran hajiya ya
baci.
.
nusaiba tace bari na kira hajiya muyi shawara, ta daga
waya ta kira hajiya ta gaya mata halin da ake ciki har fadan
da alhaji yayi mata, ran hajiya ya baci tace kark taho ku
zauna nima gobe zan taho da Jama,a ta, washe gari kuwa
saiga hajiya ta dira agidan dan nata, da misalin 10:12 am
rabonta da gidan tunda tazo barkan abduljalal. jalal na
zaune shida wasu abokan sa, ya hango hajiya na fitowa
daga muta da sauri ya karaso yana cewa hajiya lfy kuwa?
hajiya na murmushi tace nazo bikin mijina ne. Jalal yace
hajiya kodan kishin nan bakiyi ne kama hannuta yayi, ya
waiga gurin da abokan sa suke yace faisal kuzo ga amaryar
ta iso, dariya sukayi suka matsu suka gaida hajiya sannan
sufara diban kayan da sukazo dasu suna shiga dashi cikin
gida. ummi na zaune ta fara ganin ana shigo da wasu kaya
tace wannan kayan fa daga ina? daidai lokacin jalal yashigo
yana rike da hannun Hajiya, ummi ta mike tana fadin sannu
da zuwa, hajiya ta amsa Mata ba yabo ba fallasa, sannan
tace ina su nusaiba ban gansu afalon ba, ko basukai su
zauna anan bane. ummi tace a,a ba haka bane naga dai
sun fita tun safe, ina sukaje? basu gayamin inda za suje
ba. hajiya ta sake cewa me gidan fa baya nanne, ummi tace
yana ciki bari na kira shi da saurin shi ya fito yana fadin
hajiya da kanki, Allah yasa dai lfy, lfy nazo ne ayi komai
akan idona dan ni bana son tashin hankali, nidai na gargadi
iya laina kaima inason ka gargadi matar ka bama son tashin
hakali. alhaji yace hajiya ki kwantar da hankalin ki babu
wani abunda zai baru. tace toh nima ai nafi son haka.
wayar alhaji ce tayi kara ya dauka bayan ya sauke wayar
yace ina nusaiba cikin sauri ummi tace bata nan ta fita. alhji
yace kash gashi kuma kamafani da zasu kawa kayan safna
sun isa gidan. Hajiya tace ka Kira ta awaya mana. kafin
hajiya ta rufe baki, ummi tace alhji key na wajan tane. a,a
gashi agurina nusaiba tace ya kamata mace ta tsaya
agurin. ummi tace hakane alhji toni ai da nasan gidan da
naje, alhji dadi yaji sosai yace ai jalal nannan awaje sai ya
kaiki. hajiya taso ta hana sai kuma taga karta cika takura
masu dan haka tayi shiru.
.
itako ummi dadi taji dan dama jira take afadi gidan da jalal
zaizauna su cika kudurin su ita da kawar ta madina. bayan
sun dauki hanya dukkan su gaba suka zauna ummi ta daga
waya zuwa cen tace dona madina tama bayani ko ? , jalal
beji amsan me aka bataba, ta kashe wayar tana murmushi
Kara kiran wayar tayi tace madina har yanzun baku zoba,
nagaji da jira gani ma zantafi gidan danki za a zuba kaya
agidan , bayan ummi ta gama waya jalal yace ummi naga
kina shashshare bikin nan ne. tace ba haka bane jalal aini
babu wadda yakaini farin ciki ayanzun na fahimci kana son
safna da yawa dan haka nima na fara jin Ina sonta , saidai
abu daya yake damu na , ban so ka aure yariyar da sultan
yayi soyayya da ita ba, saboda sultan fa dan duniya ne.
Jalal be gane inda ummi ta dosaba yace ummi ki daina tuna
wannan yariga ya wuce kuma sultan ai babu abinda ya isa
yayi min, nidai burina kawai adaura auren. ummi ma ta
gane jalal be fahimce taba, da wannan tunani suka isa
gidan, kan kace meye har angama gyara gidan, ummi
tsayawa tayi tana kallon dukiyar da aka zuba agidan, alhaji
ya kashe kudi saikace kairat zai aurar, badan madina tace
tabi komai ahankali ba toh da yau saisun kwashi rigima da
alhaji, haka suka kamo hanya ita da jalal amota jalal sai
santin gidan yake. gani inda yake ta murna ummi tace
gaskiya jalal guri yayi kyau. cikin murmushi ya waigo yace
ummi ai bakiga kyauba sai safna ta shiga gidan, zakiga
yadda zai kara haske. kulewa tayi sosai amman bata bari ya
gane ba tayi mai murmushi kawai.
.
Jalal kuwa dadi yaji ummi ta fara son safna tuni ya nemi
haushin ta da yakeji da ya rasa, dan haka yashiga zuba
mata shagwaba, ummi kinsan menene? tace a,a yaro sai ka
fada. yace safna fah sai kin dan mata fada bata sakin
jikinta dani, kamar ma tsorona takeji kuma dacen ba haka
take minba, cikin shagwaba ya fadi maganar. ummi
daurewa tayi tayi murmushi tace jalal manya, kabari mana
adaura aure duk zata Bari da haka suka isa gida lakacin
yamma tayi sosai, tana shiga falon sukayi ido hudu da
safna tana kusa da hajiya a zaune ganin tayi ta kara kyau
da sheki gawani zanen filawa wadan tunda take zuwa bikin
yaran kawayen ta bata taba ganin wada yakwai haduwar
wannan ba, sai satar kallota take , tare da kara jin haushin
anty nusaiba tasan tayi ne dan jalal ya rikice, bayan ta gaida
hajiya ta shige dakin ta. hajiya ta kalli safna tace me yasa
baki gaishe da ummin ku ba, maza ki bita daki ki gaida ta.
safna tashi ga da sallama ummi ta dago ta kalle ta, tace
yaushe kuka dowa? tace bamu dade da shigowa ba. tasake
cewa jalal yasan kundawo? nima basan ko yasani ba, tabe
baki tayi tace fita kibani waje. da daddare gidan ya kaceme
gidan biki sosai sai haya niya ake aharabar gidan kuwa su
jalal ne da abokan sa sai hayaniya sukeyi. zuwa cen
kawayen ummi suka fara shigowa wannan karon basu
tsaya a falo ba barayin ummi suka shiga, zuwa cen suka
saki sauti. bayan ansaka safna alalle tana ta kuka yau itace
za,ama aure ba dangin ta ko guda daya ita da zata samo ko
goggo ce tagani agurin bikin nan da zatayi farin ciki da
haka da ace babu kowa nata kasa bacci tayi sai juye take
babu wadda tafi fado mata arai kamar iya taso Allah ya bar
mata iya, haka taita share hawaye dan bata son anty
nusaiba ta juwota, daga cen ta fara jiyo muryar alhji yana
fadin innalillahi wa,ina ilaihir raju,un sai maimaitawa yakeyi
mikewa tayi ta zauna ,tana kallon su hajiya suka fita
akabarta ita kaidai adakin, dan haka tabiyo bayan su, gani
tayi duk sun tsaya sunyi cirko cirko, alhaji ko sai share zuba
ya keyi jalal na gefe daga shi sai gajeren wando, ummi
kuwa sai rusa kuka take, cikin rudu safna tace me yafaru?
anty nusaiba tace karku gaya mata saida safe. ummi tace
ai gara agaya mata tunda kowa yasani, safna gidan da
zaku zauna ya kone babu abinda aka dauka acikin sa. safna
neman kujera tayi ta zauna ta rufe ido bata sam ma me
zata ceba. jalal kuwa kansa akasa yake, yaki dagowa. alhji
yace bakomai kowa ya koma ya kwata saida safe Allah
yasa haka shine mafi alheri. ummi tace ai alhji bamuga ta
barciba munfah gaiyata muta ne gashi gobe ne daurin aure,
yaka mata asan abinyi, ni ina ganin kawai adaga bikin
kawai hankali kwance.
.
bata gama rufe baki ba jalal yace ni gaskiya ban yaddaba
ummi, ni dai kawai ayi. cikin fada alhaji yace kai jalal baka
da kunya ko ya manya suna magana zaka saka baki, ai biki
yazama dole adaga shi, wuce kaba mutane waje. da sauri
yabar wajen ya shige dakin shi ya bogo kofar. hajiya tace
toh yanzun8 kayanke hukunci ne kabamu umarni mu watse
koko shawara kake nema. sai lokacin ya tuna mahaifiyar
shifa tana wajen dan haka yace hajiya kiyi hakuri nayi
kuskure, shawara nake nema yanzun yay kamata ayi.
hajiya tace toh nidai ban yadda adaga ba kowa yaci gaba
da abinda yake biki nanan babu fashi
.
Alhaji yace shikenan hajiya duk inda kikace haka
za,ayi,haka kowa ya koma ya kwanta kowa zuciya babu
dadi, jalal kuwa bayan ya koma daki kuka ya saka gidan da
aka dade ana ginawa saida aka gama kashe kudi, zargi kala
kala ya ziyarci zuciyar shi gaskiya yana zargi sultan da
mahaifiyar shi ,kafin safe idon jalal yayi jazur sun dan tasa .
karfe bakwai jalal ya fito sanye da jallabiya fara sol , da
bakin glass a idon sa, saboda baya son afahimci halin da
yake ciki , saida ya fara gaida su hajiya sannan ya wace
dakin alhaji, yana shiga yacire glass din ya rike ahannun
shi, alhaji ya kalli jalal yace wai kai ba kasan kaddara bane
ji inda fuskar ka ta koma saikace ba musulmi ba. Jalal yace
daddy ba haka bane abin da yake bata min rai nasan gidan
nan kona shi akayi kuma wlh nasan bazai wuce sultan bane
dan nasan shi kadai ne zai min haka. dakatar dashi alhaji
yayi cikin fada karna kara jin kafadi wannan maganar
mubarwa Allah kawai shiyafi, kuma daurin aure nanan insha
Allah ajima za,a daura . dadi sosai jalal yaji yace daddy
nagode yana fitowa dakin ummi ya shiga suna saune ita da
wata kawar ta data kwana agida. ummi tace kardai
kacemin kuka ka kwana kanayi jalal kana sone kayi kanka
illa akan yariyar da badamuwa tayi dakai ba
.
. dokar dakai yayi yace ummi me yasa kikace haka, ni
nasan safna nasona kawai domuwa ne ya mata yawa
shiyasa ma nafi son adaura auran ko hakalin ta zai kwanta,
nima kaina hakali na ba,a kwance yake ba bare kuma
safna. hajiya adama kawar ummi dake zaune agefe tace
rabo da ita jalal kaji , ance maganar bikin nanan ko? eh
yana nan in Allah ya yarda hajiya adama tasa ke cewa toh
yanzun a ina zaka zauna kenan? yace nima ban sani ba.
jalal ya gaji da tambayoyin su dan haka yace ummi bari
naje bayan ya fito yayi tunani yaje yaga halin da safna take
ciki dan haka ya doshi daki, dakin cike yake da mutane, su
anty nusaiba ne sauran dai duk besan suba, bayan yagaida
su, ya hango safna daga cen bayan anty nusaiba, yace anty
dan turomin yariyar cen, yajuya zaita fi anty ta tsaida shi
tace zoka zauna kuyi maganar adaki dan abin ya fara bani
tsoro, mikewa sukayi suka fita jalal yashigo cikin dakin ya
zauna abakin gado yace safna tashi mana, ke wacce irin
amarya ce har yanzun kina kwance. mikewa tayi ta gaida
shi, jalal yace safna kinji abinda ya same mu ko, dan Allah
karki ce zakisa wannan abun a zuciyar ki ya dame ki, tace
bakomai yaya Allah yasa haka shi yafi alheri ameen safna .
ta sake cewa yaya me yasame ka a ido naga yayi ja? jalal
yayi mamakin ya akayi ta gani bayan ba kallon shi take ba
kanta akasa, dariya yayi yace ta yaya akayi kikaga idona
bayan ba kallona kikeba? juyar da kai tayi tace nifa gani
nayi kamar yayi ja Eh ai naji shine nake tambaya ko kina da
ido ne atakiyar kai dan ni kanki kawai nake gani. safna bata
ce komai ba tayi shiro tana wasa da yatsun hannun ta.
daidai lokacin aka kirashi awaya yadauka yana fadin amir
kun iso ne, ok to ganinan zuwa. juyawa yayi yakalli safna
yace, yarinya zama ki bari ne, dan yau a gado daya zamu
kwana.
.
dasauri ta kalli jalal ta sake yin kasa dakai. jalal yace a,a ki
kalleni da kyau. karfe 2:30 Jama,a da dama suka shaida
daurin auren abduljalal da safna acikin wa,inda suka shaida
daurin auran harda baffa wanda alhaji yaje ya taho dashi
yaso yaki zuwa amman alhaji yace yayi danshi, dan haka
ana daura auran alhaji yaba da mota aka mai dashi gida,
jalal kuwa da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki. acikin
gida kuwa safna ce da wasu kawayen ta su biyu bata san
waya gaya musuba sai dai kawai ganin su tayi,tana ganin
su kuwa suka shiga fira tuni ta manta da bacin ran dake
damunta anty tashigo ta ajewa safna wasu kaya tace maza
kisaka kije waje jalal na kiranki zaku gaisa da abokan sa.
tun safe safna bata fitoba sai yanzun tana fito falo su
hajiya ne da mutanen ta cike afalo suka saka guda, safna
kuka tasaka musu yau gata atsakiyan dagin miji bata da
kowa, dagin miji sune gatan ta wannan abu kawai in tatuna
yana sata cikin baccin rai sai a yanzun wani kalma na
goggo yake fado mata ki zauna anan bari naje na dawo
haka banzayen kakan ninki suka ma uwarki har ta mutu
bata kara sakasu a ido ba, goggo tana nufen mahaifiyar
tama haka abarta, ko shiyasa bata taba gani wani dan uwan
mahaifyar taba kara rushiwa tayi da kuka hajiya tace fatima
kawo ta nan, hajiya fatima ta kawota har gaban hajiya
kwatar da ita tayi ajikinta taita mata nasiha. bayan ta dan
natsu hajiya tace tashi kije ki gaida ummin ko, sai ki wuce
gurin su jalal din. sun shiga ita da kawayenta ta gaida su
suka amsa ba yabo ba fallasa. sun doshi gurin rinsu jalal,
jalal ya hango su tun daga nesa da sauri ya daga waya
yace anty dan Allah ki leko ki mayar da safna gida tasaka
hijjabi. dariya tayi tace haba jalal kabarta mana yau daya
dai kafin yakara wani magana sun iso wajen dan haka ya
daure fuska suka gaida su cikin sakin fuska suka amsa
dayan daga cikin abokan ne wadda suke kira amir ya
farawa safna tsiya amaryar mu kirike shi da kyau duk
abinda yake so abashi dan kinsan shagwabebbe ne ko
cokali be iya rikewa ba. jalal yace toh malam ya isheka
haka kuma. amir yace be isaba safna kinajina nina san
halin jalal tare mukayi karatu jalal bashi da matsala amman
yanada fushi idan antaba shi, ya kalli jalal yayi murmushi
sannan yace safna abu nagaba jalal nada tsananin kishi .
.
da sauri jalal ya kalli amir yace wai amir lfyr ka kalau kuwa,
ke ku wuce gida. amir yace yazaka koresu ka barsu mana
ai ban gama ba, hirace ta barke takanin safyya kawar safna
da amir amir , jalal zuwa yayi yakama hannu safna yashiga
da ita har cikin gida. da daddare mutane suka fara watsewa
bakin hajiya kowa duk sun wuce gidan ta ,sai hajiya da anty
nusaiba kawai suka rage barayin ummi kuwa daga ita sai
kawarta madina safna kuwa na dakin su da ita sai kairat,
kairat tace anty safna kikace da bikin ki zamuyi shagali
amman yanzun sai naga ba,ayi komai ba, natabayi yaya
yace wai kece baki so ayi. Safna tace haka yace miki
wayau yayi miki shine baya so,kairat tace ai dama yaya
yacika wayau haka ma da yace in kukayi aure zai tafi dani
yanzun kuma yace wai wasa yake min, kuma wlh bazan
yarda ba saina biku yaya zaku tafi kubar ni ni kadai agida
safna tace ai bama inda zamu bakiga gidan ya kone bane.
suna cikin haka jalal yashigo dakin yace safna kizo hajiya
nakiran ki tamike suka fito tare ahanyar su ne jalal ya ce
safna koda an tambaye ki Ina kike son zama kafin musami
wani gidan kice abarki adakina. dauri safna ta fara kuka
wlh yaya bazan iyaba . yace daurewa zakiyi safna ,ko kin fi
son hajiya ta wuce dake, ni indai hajiya ta wuce dake bazan
iya barciba wlh me zanyi agidan nan, to sai dai nima na
biko. gani tayi kamar ba,a cikin hakalin shi yake ba,
matsowa yayi yariketa safna ki taimakeni karki bari atafi
dake. safna ko azuciyar ta tafi son tabi hajiya dan gidan nan
kwata kwata baya yi mata dadi jita take kamar a kaya take.
Suna shiga falan alhaji ,suka ga kowa kowa ya hallara har
ummi da kanin alhaji bayan sun zauna aka fara yi musu
nasiha kanin alhaji baba salisu yace to jalal hajiya nason ta
tafi da safna gidanta kafin agama gyara ma gidan ka dan
haka nace bari muje ta bakinka tukuna dan yanzun kai kake
da iko da ita, meye ra,ayin ka? shiru yayi kansa kasa. Safna
ko tunani take azuciyar ta wato jalal shi yakasa magana ita
kuma zai sata tayi rashin kunya. Jalal beyi magana ba
saida baba salisu yakara maimaita tambayan shi.
.
sai da jalal ya juya gurin hajiya sannan yace toh hajiya
harda ni zaki tafi ko? duk falon dariya suka saka banda
safna da ummi dan ummi kara tamke fuska tayi. baba
salisu yace ja,iri ai dani zakayi magana bada hajiya ba.
Jalal bece komai ba sai faman sosa kai yakai yake. baba
salisu yace indai na kula da kyau, jalal be yadda atafi mai
da mata ba. anty nusaiba tace toh hajiya kibar mai matarsa
kawai tunda baso yake ba, da sauri ummi tace nima dai
abinda nagani kenan. hajiya tace a,a nima ba matsawa
nayiba kusha zaman Ku, in ma dakinka zaka kaita
bisimillah. hajiya ta sosa mai inda yake mai kaikayi dan
haka ya farawa anty nusaiba alama da ido , banza tayi
dashi kamar bata gani ba. baba salisu ya kula dan haka
yace jalal kamar kwai magana abakin ka, nusauba me jalal
yake gaya miki. dariya tayi tace yaya nima ban fahimce
shiba. yace toh kuje waje kuyi magana duk abinda yake so
ya fada kar yaji kunya ai matar sa ce. anty tace jalal kayi
hakuri mana kasan fa mamar ka bazata yarda dahaka ba.
anty nidai kawai ku kaita dakina ina da dalilina inhar kuka
tafi baku kaita dakina ba nasan ganin safna ma sai ya
gagareni ummi zata iya hanani shiga dakin su safna. suna
komawa anty tace yaya shifa wai so yake ta koma dakinsa.
baba salisu da alhaji suka hada baki to dan wannan shine
ka kasa fada kai da matar ka, nusaiba kai mishi matar sa
daki kizo mutafi. ummi mikewa ta tasaka kuka agidan nan,
za,yi wannan kwama calar wlh wlh bata isa ta hada gado
da jalal ba