Breaking News

RABO NA CE PART 2

RABO NA CE PART 2
.
Kai tsaye ya wuce d'akin da yasan an bata gado da daren,
amma bata gurin, ya duba ko ina amma bata ba labarin ta,
ya gama zagayen sa bai ganta ba, sai ya k'ara kiran
number da aka kirasa amma no answer, yayi d'an tsaki,
"ina busy fa, ina son na koma gida akwai aikinta zanyi,"
wata nursing ce zata wuce yayi sauri ya sha gaban ta,yana
tambayar ta " please am looking for my patient " matar ta
kalleshi tace " okay, ya sunan ta.?" Turus yayi dan baisan
sunan taba, " no wata da aka kawo shekaran jiya da dare,
wacce yan fashi suka harba a hannu!!" " Her name please "
yadan sosa kai, yayi tsaki kadan yad'an waiga bayansa,
yana shafa kansa da hannun hagunsa, " kin gane anan
dakin akayi admitting dinta" " sorry sir, batada sunane?
Kace majinyaciyar ka ce amma ko sunan ta baka saniba
sorry please ana d'an jirana." Ta wuce ta barshi yana waige
waige yana shafa kai aranshi yake cewa " to ina aka kaita,
bayan nan gurin na barta, ya ci gaba da yan lek'e- lek'en sa,
amma bai hango komai ba, chan ya hango wani Dr. Direct
gunsa ya nufa ya masa bayanin da yama matar, " eh da
kasan sunanta zanfi ganewa da sauri, but ka haura sama
Room number 8 ka k'ara tambaya wa, my be su ganeta" ok
Dr. Na gode " ya haura sama da saurin sa, gun da aka masa
kwatance ya nufa, ya shiga wani, aka ce ba nan bane aka
turasa d'ayan office d'in, office d'in da aka nuna masa ya
tura kai ya shiga, bayan sun gaisa ya masa bayani, likitan
yace " Mrs. Mujaheed kake nufi?" Yadan shafa fuska, ya
maimaita sunan a ranshi,"Mrs Mujaheed" yayi murmushi na
gefen fuska " eh Dr. Itace," ya fada ne kawai dan yanason
ya gani ko itace d'in " haba Mlm Mujaheed ya zaka kawo
matarka tun Friday amma sai Sunday zaka nemeta!? Shima
d'in dan mun kirakane, da baka saka number gun cika file
ba da ya zamuyi tuntub'eka, idan ma kun sami matsala da
juna ne sai ka bari sai ta sami sauk'i sai kuci gaba da
rigimar ku, amma haka bai dace ba" Dr. Sai zuba yake
kamar kanya, shi kuwa Mujaheed yana sauraren sa ne
kawai, saida ya k'are wa'azinsa da fad'an sa sannan Dr. Ya
tashi yakaishi gunta, suna isa bakin k'ofa likitan yace "okay
ga tanan, please ka bita a hankali dan har yanzu a firgice
take tak'i magana sai dai tayi ta kallon mutane, so please
kasan yanda zaka mata," yadan daki kafadar Mujaheed "be
a man,' ya fita. Mujaheed ya matso kusa da ita ya tsaya
yana k'are mata kallo, sanye take da kayan marasa lafiya,
sky color, tana bacci, hannunta an d'aure shi da bandegi,
kyakyawa ce ba laifi, "basai na tsaya bayaninta ba, komai
tanada na mace mai kyau" idonsa yakai akan gashin kanta,
gashin kanta kamar na hammata, an mata wata kalaba duk
ta mik'e tsaye kamar nonon maza, aranshi yace "dama
akwai matan da basuda gashi, har haka? Shikam
k'anwarsa siyama tana da gashi," ya dad'e yana kallonta
yayi murmushi, " of course, zata iya zama Mrs Mujaheed "
.
Kamar taji abinda ya fad'a ta bud'e idonta a hankali sukayi
ido biyu, lokaci d'aya ya sake mata murmushi, binsa kawai
tayi da kallo, ya matso kusa da ita ya tsaya, " sannu, ya
k'arfin jiki?" Kallon sa ta sakeyi, yaci gaba "dama zanje
daurin aurene sai mukaga an muku fashi a hanya to shine
dai aka d'auko kowa sai ba'a ganki ba, nayi mantuwa a gun
koda na koma sai na ganki shine na kawoki asibi " tunda ya
fara take kallonsa saida ya k'are, " yanzu kiyi magana sai a
nemo su Dady da Mumy suzo su daukeki " yanda ya fadi
sunan iyayenta kamar yasan yanda take kiransu, " likita
yace bakya magana tun ranar, please say something to me
kinji, " dago kai tayi sukayi ido hud'u, a hankali tace " ka kira
Dady ya tafi dani, " hamdala yayi ganin tayi magana, "Ok
gaya min address d'in gidan ku sai naje na gaya musu" a
hankali da muryanta garo garo, ta mishi bayanin gidan su,
dukda bawai ya gane bane, amma zai nomo d'an gari ya
masa kwatancen da ta masa sai ya nuna masa gidan, ya
fito har yakai bakin k'ofa ya juyo yace " kinci abinci?" Gyada
masa kai tayi alamar aah ya fita da sauri ya samo mata
abinci mara nauyi ya kawo mata, "tashi kici" kallon sa kawai
tayi, dan bazata iya tashiba, "ko a kwance zakici? " nan ma
kai ta gyada masa alamar Eh, a kwancen kuwa ya matso zai
bata abincin, Kwankwasa kofa akayi, likita ne ya shigo,
karaf idonsa akan Mujaheed zai bata abinci a kwance "haba
Mujaheed ya haka? Still baka hak'ura ba!? Ka zaunar da ita
mana," nurse ce ta shigo da abinci da magani, Mujaheed
yace " pls d'an taimakamin ki tayar da ita zaune " ta kuwa
tayar da ita zaune, dama ita kanta ta gaji da kwanciya likita
Ya mik'o masa takardar magani da kud'in gado sauran su,
da sauran ya karba yana godiya. Haka yayi ta bata abincin
abaki tanaci har ta k'oshi ya mata maganin ta tasha, " a
kwantar dake? " gyada kai tayi alamar aah. " ok zanje na
nemo su Dady na gaya musu kinji " binsa tayi da ido, a
hankali ta runtse idonta tana tunano abinda ya faru da ita,
ko ina ummaru driver? oho!!!
.
Basu sha wuyar gane gidan ba da yake baban ta sananne
ne sosai a unguwar, yana cikin dattijawan unguwar, yayi
sallama da Dady, akace ya shigo ciki, ya shiga ya kora
musu bayani daga farko har k'arshe, hankalin su dama a
tashe yake tuni ya k'ara tashi, haka suka dungumo zuwa
asibitin, sunata sakawa Mujaheed albarka, Mumy hadda su
tuntube garin gani y'arta wacce take d'an kunya sabida
sunan surukarta ne da ita, suna isa asibitin suka gun ganta
nan Mumy ta fara kuka Dady kam murna yake, dan sun
d'auka ma tama mutu, tunda bata ba labarin ta, nan suka
k'ara godewa Mujaheed akan taimakon da ya musu, yayi
godiya shima, akan zai wuce Abuja sai sunyi waya yaji
lafiyar jikinta, har yakai bakin k'ofa ya waigo ya dubeta "
sister Allah ya 'kara sauk'i ya k'ara tsarewa" Mumy tace
amin ta harareta, yayan ta dake tsaye ya ce " Waike
Rukayyah bakyaji ana miki sai anjima?" "Um banji ma
yaya," ta d'ago kai ta kalleshi " Tnx Broo jaheed sai munyi
waya" Yak'e kawai yayi ya fito asibitin A ranshi ya rik'a
maimaita sunan, Jaheed! Yadan yi murmushi "Jaheed &
Rukayyah.."