MIJIN MARAINIYA PART 5
MIJIN MARAINIYA PART 5
.
Alhaji ya kalli jalal yace jalal ko kana da wacce kake so ne?
jalal ya bude baki zai yi magana ummi tace babu wata
wace yake so alhaji haka yayi daidai. safna mike wa tayi
tana kuka ta shige dakin su, alhj yabi ta da kallo, ya juyo ya
kalli jalal dake tsugune agaban sa, yace jalal in kana da
magana kayi mana. amman jalal da zaran ya daga kai zai yi
magana sai ya kalli ummi ya dukar da Kai.
.
alhaji ya lura da haka yace jalal tashi ka zauna an jima
kasame ni dakina sai muyi magana. Jiki babu kwari jalal ya
mike be zauna afalon ba dakin shi ya shiga. ummi ko abin
nema ya samu dawowa tayi ta zauna alhaji a ina kasamo
wa jalal yarinya? Yar wani amini na ce yarinyar akwai
hankali idai mukai sa,a jalal na santa toh gaskiya munyi
dacen sirika. ai alhaji ba biye musu zakayi ba daga shi har
safna. a,a zaliha ai ko zamanin mu ba,amana auren dole ba
bare yanxun, kina ganin jalal aka hadashi da yarinyar da
baya so akwai zaman lfy ne, ai gara ma safna ina ganin ko
bata so zata zauna dan naga yarinyar akwai hankali,
amman jalal ai rikitatce ne. amman alhaji gaski indai zaka
dauki shawara ta karka saurari kowa acikin su. alhji saida
ya kaikaice yace zaliha ban hankalinki, ina son kicire
hannuki cikin wannan maganar, ni akwai abinda na shirya
kibarni dasu in nagama magana dasu zan gaya miki.
amman dai alhaji bakayi min adalci ba, in ba azayi shawara
daniba akan auran safna ai kayi dani akan na jalal, saboda
ina da hakki akansa kuma nina san zafin sa. cikin fada da
hargagi alhaji yace nikuma bansan zafinsa ba saboda
roroshi nayi ko? a,a nidai ban ce ba gadai rorarriyar ce
wacce ba,asan asalinta ba, wlh alhaji idai kana son naci
gaba da zama gidan nan sai safna ta bar gidan nan, yau din
nan. toh dama dai akwai wani abu azuciyar ki akan safna
meta miki, me yakawo maganar safna toh safna bazata bar
gidan nan ba in kinga zaki tafi kitafi inzaki zauna ki zauna
wannan ruwan ki, baki isa ki juya ni agidan nan ba, dan
kinga inasonki yasa kikemin abinda kikaga dama, gashi ina
ji ina gani yan uwana basa zuwa gidana saboda sungaji da
bakin halin ki.
*******
ummi cikin zafin zuciya ta mike to alhaji nagode tunda idon
ka ya rufe akan tsintaciyar mage zakamin rashin mutunci
alhaji ma zafi ya dauka yana magana da karfi ai bakiga
rashin mutunci ba sai kinci gaba da mayar min magana zaki
gane koni Waye. Suna cikin haka jalal ya shigo yana share
hawaye yace daddy dan Allah kuyi hakuri ku bari. alhaji
kunyace ta kamashi ya manta yaran suna cikin gidan, yace
bakomai jalal jeka abin ka, kasa tafiya yayi ya nemi guri ya
zauna dan haka alhaji ya shige dakinsa, ummi ma tashi tayi
ta shige nata dakin. tun daga ranar gidan ya rikice kowa
zuciya babu dadi ana cikin haka alhaji ya gama kwanakin sa
ya koma, safna ko duk abinda yafaru ta sani har azuciyar ta
take tunanin itako me tama ummi ta tsane ta, jalal kuwa jira
yake yaga daddyn sa sun shirya da ummi ya gaya masa
shifa safna yake so. wata rana ummi na zaune afalo saiga
wata kawarta tazo ummi ta mike suka rungumi juna janta
tayi suka zauna ummi tace madina kinga yadda kika koma
kowa. dafa ummi tayi tace ke kowa ina gidan mijina
hankalina kwance bani da matsalan komi, ummi tariya tayi
tace hmm madina kenan, madina kar kacewa tayi tace
akwai matsala ne zaliha?
.
ummi bata boyewa madina komi ba, har rikicin su da alhaji.
madina fada ta farawa ummi ke ko sai kace wata karamar
yarinya meye naki na fada da miji, baki iya kissa bane har
zaki zauna kina bata ran ki, shima jalal ai be kamata ki
nuna mai baki son yariyar ba tunda kinyi sake ya fara sonta,
yanzun kina nuna baki sonta sai ya juya miki baya , madina
ta ciza yatsa Allah baya ba me wuka nama da nice da tuni
na wargaza su, haka madina taita ma ummi fanfu da
shawar wari iri iri , madina batabar gidan ba saida tasa
ummi ta kira alhaji tabashi hakuri. alhaji yaji dadi sosai dan
bashi da roko kuma yana son matar sa, bayan kwana uku
alhaji ya dawo, tabbas yaga canji agurin ummi iri iri , da
daddare ummi takaiwa alhaji abincin sa har dakinsa suna
cikin cin abinci jalal ya buga kofar alhaji yayi mai umarni ya
shigo ganin ummi a dakin abin yabashi mama yanai mi guri
daga gefe ya zauna, alhaji ya kalleshi yayi murmushi yace
zaliha sai naga kamar jalal ya rame, ummi kallon jalal kawai
tayi yake dan tasan kome ke damun sa. Jalal yace daddy
nazone muyi magana ba kwanaki kace zamuyi magana ba?
eh hakane jalal maganar auren ku ko? jalal bece komi ba ya
kalli ummi yace daddy ko mubari sai gobe ne? a,a ke zaliha
bamu guri zamuyi magana. dariya tayi tace haba jalal
yanzun nice bazaka iya magana gaba na ba, kuyi
maganarku babu ruwana nina kosa ma naji wacece sirikar
tawa. alhaji yaji dadin maganar ummi dan haka yace jalal
wacce yariyar kake so? jalal ya dokar dakai yace safna.
alhaji daure fuska yayi yace jalal lokaci ya kure nariga na
bada safna , saida na tambaye ka da farko kace basanta
kake ba.
.
Dagowa yayi da sauri ya kalli daddy yaga daddy ko ajikin
shi, abincin shi ma yaci gaba daci, ya mayar da kanshi
kasa, cikin murna ummi tace jalal kayi kuskure da kasani ka
fada da wuri gashi yan zun kama kan ka. ummi lokaci fa be
kure ba sai dai in kun zabi wani akaina, ya miki zai fita
alhaji yace kashirya anjima kaje kaga yarinyar, bece komi
ba ya fata adakin.
.
yana fita alhaji yayi dariya yace zaliha kifara tanadi dan
baza,a sa da yawa ba, cikin murna zaliha tace ai alhaji shiri
zanyi sosai yara biyu fah, jalal yana barin dakin daddyn sa,
dakin safna ya shiga ya same ta zaune tayi kuka idonta duk
sun kunbura, tana ganin shi ta durkusar dakai, jalal yaje daf
da ita ya zauna safna kuka kikayi har idon ki suka kunbura
haka , me yake damunki ko kema baki son auren ne? shiru
tayi ta kasa magana bazata iya gayawa jalal cewa shitake
soba itama kanta tana ganin lefin zuciyar ta datake son
wadda yafi karfinta, jalal ne ya katseta safna nifah bazan
bari amin auren dole ba, safana zan tambaye ki amman ina
son kimin alkawarin zaki gaya min gaskiya tsakanin ki da
Allah . me zai hana yaya jalal indai na sani zan fadama ka.
safna tsakani da Allah babu wani da kika taba jin kina son
ki aura. hawaye ne suka gangaro mata dan bata zaci
wannan tambayar ba ,tace akwai. jalal yace waye wannan
safna? yaya jalal mubar wannan maganar ai kai ma baka
fadamin yarinyar da kake so ba. Safna ni bani da budurwa
saidai ko zakimin hanyar kawar ki sai na aura. tace to
aigashin nan daddy yasamar maka. shi ko jalal so yake
yayiwa safna wayau yaji ra,ayinta kuma ya rasa tayaya zai
fara kuma yana tsuron karya fada tace bata sonshi, dago
kan shi yayi ya kalli safna yace, ni bana so ta gurin daddy ta
gurinki nake so. wai kai yaya dan Allah da gaske babu
wacce kake so?
.
jalal yace gaskiya akwai safna amman tsoron gayamata
nakeji kartace bata sona. safna mantawa tayi dawa take
magana tace , kai yaya jalal wacece zata kalleka tace bata
so. cikin dauki yace da gaske safna,saboda me kikace
haka. yaya wlh babu wacce zata ce bata soka komai kyanta
komai kudin gidan su sai dai kawai inbata samu ba, kai
baka san ka hadu ba ne, wlh yaya kai kyakyawa ne kana da
kyau sosai. dadi sosai jalal yaji ya kashe murya yace toh
safna ko zaki taimaka ne ki aure ni. Sai alokacin safna
tatuna tayi subutar baki ciki tashin hankali ta mike zata fita
tana fadin mezaka ci dani? da sauri jalal yamike ya rike
safna yace karki kara cewa haka safna, na dade Ina sonki
Ina tunani karkice baki so nane shiyasa ban gaya miki ba,
fashewa tayi da kuka tace me zakayi Dani rorarriya mara
dangi bani da kowa fah jalal , kaikuwa dan gata ne ummi da
daddy suna matukar sonka. tausayin safna yakama jalal
besan lokacin da yasata akirjishi ba itama lafewa tayi
kamar karama yarinya yace safna kema suna sonki, nima
kuma Ina matukar sonki dan haka karki kara cewa baki da
kowa, mune dangin ki. a,a yaya ummi bazata bari ka aure ni
ba. a hankali yace safna karki kara kiran sunan ummi akan
wannan maganar ba runwan ki ,nidai kawai abinda nake so
dake , idan daddy ya tambaye ki kice ni kike so , kinji? suna
cikin haka sukaji anturo kofar miryar ummi sukaji tace jalal.
zabura sukayi da sauri yasake ta. ummi tace zoka wuce
daddyn ka nakira, jalal wucewa yayi yana sosa kai yabar
ummi adakin.
***********
safna bakin gadon tabi ta zauna, ummi ta harare ta, tace
yar iska kawai zata koyawa yaro iskanci, in Allah ya yarda
saikin bar gidan nan, baza kizo ki lalata mana yaro ba.
bayan kwana biyu hakalin jalal ya kara tashi dan yaga sai
shirye shirye ake agidan ya sake koma wa wajan alhaji ya
kara gayamai shifa babu wacce yake so sai safna alhaji
yace wai dama da gaske kake ne, aina dauka wasa kakeyi,
to kabari zanyi shawara. ran jalal beso haka ba amman
yasan abinda zaiyi yace daddy yau gidan hajiya zani. alhji
yace ya kamata jalal inkaje ka gaida ta, yace tare da safna
zantafi, kafin alhj yace wani abu ummi ta shigo Ina zaka da
safnan kuma? gidan hajiya zamu. alhaji karma barshi ya
tafi da ita ban yadda da jalal ba ,ya canza hali. alhj yace
wani irin magana ne wan kuma. wlh alhaji rannan ganin
jalal nayi rungume da safna kaga kuma be kamata suna fita
waje tare ba. alhaji ya kalli jalal, yace abduljalal haka ne?
shiro yayi ya dukar da Kai, alhji yace tashi ka bani waje.
.
jalal yaso ya leka gurin su safna amman ya fasa ya wuce
gidan hajiya. hajiya mahaifiyar alhaji ce kakar jalal tana
matukar son jalal dan duk cikin jikokinta shi kadai ne namiji
sauran duk matane kuma kanana ne yayanta guda uku ne
mahaifin abdul jalal shine babba sai kaninsa wadan yanzun
ne ya samu haihuwa yarssa mace kusan garman su daya
da kairat sai kanwar su mace anty nusaiba bata dade dayin
aure ba tun lokacin da alhaji ya kawo zaliha amatsayin
wacce zai aura, hajiya ta nuna batayi na am ba, amman
daga baya taga ya matsa ta hakura akayi. bayan ummi ta
haifi jalal suka gane bata son mutane duk wanda yaje gidañ
saita mai wula kanci, dan haka suka hakura da zuwa gidan.
jalal ya shiga gidan hajiya tun abakin falo yake fadin
matassss. ah,ah dan duniya saiyau ka tuna damu daidai
lokacin jalal ya shiga falo yaje kusa da ita ya zauna, yace
wlh hajiya kina raina abubuwa ne suka min yawa, shiyasa
baki ganni ba. kai dai kace mahaifiyar ka ta hanaka zuwa
koda yake harda laifin baban ka aishi kullum yana zuwa ai
sai ya tasoka gaba, amman ku kuka sani, nidai kujera ce.
jalal yace hajiya kiyi hakuri ni bawan da ya hanani zuwa, ni
yanzun ma akwai abinda ya kawoni. toh ina jinka me ya
kawo ka. ya kwashe duk abinda yake faruwa ya gayawa
hajiya. dariya tayi tace jalal ai ina da lbrn komi baban ka
yagaya min komai tsokanan ka yake amman har an tsai da
ranar biki sati uku masu zuwa , karka kara tada hankalin ka
, me yasa baka taho da safna ba, ko baka son naga kishiya
ta. hajiya wai dan Allah da gaske kike yi? jalal na taba irin
wannan wasan ne dakai? hajiya bari naje gobe zan dawo
yana shiga gida yasamu alhaji afalo alhji yayi dariya yace
jalal kadawo daga kai karar tawa ne?
.
jalal ya sosa kai yace ba haka bane daddy ni gai sheta naje
. jalal kana nufin ban san halin da kake ciki bane, nagane
kana son safna tun ranar da naga kishinta karara a idon ka,
amman sai kamin karya kace basan ta kake ba, kuma nama
haka ne dan kar ka ga kasa meta asauki nan gaba kace
zaka wulanta ta jalal safna itama mutun ce kamar kowa
duk son da nake maka inhar ka wulakanta ta , zamu raba
hanya dakai kuma daga yau na haramta ma shiga dakin
safna, inzaku yi hira kuyi afalo , suna cikin haka ummi ta
fito , alhaji yace kafin kizauna kiramin safna. ummi ta shiga
ta kama kunnen safna ta rike sannan tace idan alhj ya
tambaye ki kina son jalal kice a,a, idon safna cike da kwalla
tace toh ummi. suna zuwa safna ta zauna akasa, ummi ko
tunkan ta fito tawashe fuska, alhj ya kalli safna yayi
murmushi yace yace safna ki fara shiri bikin ku nan da sati
uku masu zuwa na zaba miki yayan ki jalal. zufane ya fara
karyo ma ummi tace alhj ita baka tambaye ta ko tana
sonshi ba. a,a basai na tambaye taba nasan ma tana
sonshi ai dama tare muka gansu. Jalal ya kalli safna yayi
murmushi, itako safna kanta na kasa banda far gaba ba
abin da yake damun ta. alhj yace jalal naga kamar bakinka
akwai magana? daddy ranar ne naga kamar yayi yawa ko
za ,a dan rage ne ummi mikewa tayi ta buga tsaki tashige
daki, tashiga tunani gakiya nayi kuskure dahar na bari wata
alaka tashiga tsakin sultan da safna gashi aure yana
neman shiga tsakanin ta da dana kuma zaiyi wuya ace
sultan bashi da H.I .V