Breaking News

RABO NA CE PART 16 ********* KARSHE *********

RABO NA CE PART 16
********* KARSHE *********
.
Wata zuciya na turata tayi girkin wata na hanata, har
guraren azzahar bata San mafita ba, sai WASWASI (Na Mrs
Jabo) take, daga k'arshe ta yanke shawarar yi masa danbun
shinkafa, ta saka mai ganye da kifi a ciki, ta had'a mai
salad na lansir yaji zaitun, sannan tayi fruit salad, batason
tayi wani girki wani special ya d'auka ta kamu ya rainata,
cikin WASWASI ta k'are girkin, koda akayi Magreeb duk ta
kammala, idan aka tambaye ta zatayi bak'ine, sai tace eh
wata course mate d'in ta ce zasu zo, Sam bata bari nafee
anka ta mata koda yankan Al basa ba dan tasan idan akayi
haka girkin bazaiyi dad'i ba yanda nafee bata iya girki ba,
tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga tayi kyau, sai sak'a
take a zuci, tanayi tana kallon agogo, har lokacin yayi amma
bai zoba, Chan ta hango Muhammad tare da Dady sun fita
wajen gida, tana kallon su ko Ina zasu Ohoo.
.
Har k'asa ya tsuguna ya gaida Dady cikin girmamawa
sannan yace masa yana neman alfarmar auren Ummey,
kuma yana son a barshi ya rik'a zuwa tad'i kamin iyaye su
shigo ciki, Dady ya amince da b'uka tarsa kuma ya musu
fatan alkhairi, anan yama Dady bayanin kansa da aikinsa
da komai, Dady fatan alkhairi kawai yake musu ba ragi ba
k'ari, bayan nan yace masa iso gun Ummey, Muhammad na
tsaye yana kallon sa yana tunanin inda ya taba ganin sa
Amma ya kasa tunawa. Dady ya wuce cikin gida "Ummey ki
bud'e d'akin bak'i kije kinyi bak'o," Saida yayan cikin ta suka
juya ta had'iye yawu ta kalli k'anin ta Ammar da ya zuba
mata Ido cike da tambayoyi, ta yatsineshi Dady ya wuce
d'aki, Ammar ya biyo bayan ta, "Sister new broo ne aka
samo mana ne?" Ta d'aure fuska "Wai Ammar yaushe muka
fara wasan raini dakai? Duk Kabi ka raina ni wallhy" Dariya
yayi "Hajjaju makkatu Ashe shi aka yiwa girki, shine akace
course mate su course mate manya," Tsayawa tayi tana
kallon sa, ya d'aga hannu sama alamar ya daina, ta wuce
d'akin bak'i ta d'an gyara sama-sama dama a gyare yake
tun dazu, zata fito kenan taga ya shigo ta d'ayar k'ofar
turus tayi ta kasa motsi, ya mata murmushi, "Matata ta
kaina" Ta kwabe fuska, a ranta tace wai matarka, suna ko
dad'i babu, yace "Nifa wannan shagwabar a ijiye min
kayana sai bayan Aure sai ki rik'a min," Ya fad'a yana
shigowa ciki, ya nemi gu ya zauna, "Waya gaya maka
shagwaba nakeyi? Idan ma zanyi ai mamata zanyiwa ba
wani..." Murmushi yayi, " ki k'arasa mana, Hmmm, nidai na
zauna koda batace in zauna ba," K'arasowa tayi kamar
mara gaskiya ta zauna itama, "Kinata jira ko?
.
Nasan kila har girkina yayi sanyi, gashi banason abinci mai
sanyi. wallhy na tsaya gun Dady ne" Itakam kallon sa take
yanda yake magana kamar d'an gida banza tayi dashi
kamar bata ji mi yake fad'a ba. Lokaci d'aya ya sauya
kamar bashi ba, Kiran sunan ta yayi ta kalleshi, dai-dai
lokacin nafee anka ta shigo da kwanukan abinci had'i da
sallama, girkin da Ummey tayi ne, wato kowa ya gane shi
tama girki harda biyota dashi, anka kuwa sai kallon sa take
a ranta tana cewa inama itace da wannan santalelen guy,
saida Ummey ta karb'i kwanukan ta maka mata harara
ganin yanda take kallonsa, ta fita da sauri, Ummey ta ijiye
kwanukan abincin ta zuzzubasa ta ijiye gaban sa, tamai
bisimillah ya kalleta shima kamar wani yaro "To ki bani a
baki mana" "A baki?" Ta fad'a tana toshe bakinta, ai ko
Muhammad ya wuce a bashi abinci a baki bare kato kamar
ka, cikin zuciya take zancen, shi kuwa ko motsi haka ya
fuske sai ta bashi ita ma ba alamar zata bashi, da taga da
gaske yake tace yaci yanzu next zata bashi a baki, yana
dariya yacinye yanaci yana watso mata zance, Itakam
kunyar sa takeji ga rashin sabo saida ya k'are ta tattare
kwanukan sannan ya ijiye wasa gefe ya fara abinda ya
kawoshi. "Wato Ummey na dad'e Ina sonki kuma nasan
kema Kinsan da haka, please ki fahimceni Ina buk'atar
had'in kanki da soyayyar ki, burina kawai na aureki, fatan
ns kawai ki amince dani a matsayin mijinki," Shiru tayi na
lokaci, ta tuna ciwon da take d'auke dashi, sannan ta tuna
fyaden da aka mata, idan har zata amince dashi tabbas
akwai buk'atar ta gaya masa, sannan akwai buk'atar su
fahimci juna, Amma lallai da wuri zata gaya masa dan kada
sai sunyi nisa a sami matsala, dan har cikin ranta ya mata
tun ranar farko kuwa.... "Tunanin me kikeyi Ummey?
Yanada kyau kiyi magana." "Dama....." Sai kuma tayi shiru
hawaye suka biyo bayan shirun nata, wani tausayinta da
k'aunar ta ne suka k'ara kamashi, ya taso zaizo gurin ta da
sauri ta dakatar dashi da hannu alamar ya tsaya, yaja burki
ya tsaya. "Ka zauna in maka bayani," Ta fad'a tana kallon
sa, Murmushi ya mata ya koma ya zauna. "Nagode da
k'aunar ka gareni Amma gaskiya ni banida lafiya inada......"
.
"Shhhhhheeeeeeeeeeeeee....!" Ya katseta ta hanyar d'ora
d'an yatsan sa akan Leb'en sa, "Ummey I know everything
about u, kuma wannan bazai Hana na aureki ba, I love u
since 5 years ago, zanso ki dai-dai ta natsuwar ki dan kisan
wanene ni da kuma Asalin had'uwata dake har na Allah ya
saka min k'aunar ki, na fara ganin ki a gurinda aka muku
fashi, wanda Ina kallo aka harbeki a hannu lokacin Amma
ba halin taimako, Ina boye a wani gu idan na fito police
zasuce dani akayi operation d'in, sai kawai na fake, bayan
mutane sun watse sai naga ba Wanda ya ganki, lokacin da
na fito d'aukar ki lokacin Mujaheed shima ya dawo d'aukar
wayarsa, nayi niyyar d'aukar ki a lokacin Amma sai ya
rigani sai kawai na wuce na barki, wannan ne karo na farko
dana ganki kuma a gurin na fara ganin ki.
.
naje asibiti dubaki kusan sau hud'u ba tare da kin ganni ba,
wani lokacin ma ta window nake lek'en ki, nasha zuwa baki
magani Amma baki San cewa ni ba Dr. Bane sabida
abokina Yana kula dake a lokacin, Wanda yayi tunanin ke
Matar Mujaheed ce, sannan lokuta da dama Ina biyo bayan
ki idan kina tafiya saidai kawai naga kina kalle kalle kina
neman Ina k'amshin turarena yake fitowa, a lokacin na
fahimci cewa u like my perfume, so daga lokacin naji Ina
mutuwar son turaren, nasan soyayyar ku da Mujaheed
yanda ta fara, da yanda ya mutu akan ki amma ya kasa
fad'a miki sabida yana kallon ki young a lokacin, yana
tunanin kanki bazai d'auki kalmar love ba, har Mahbuob ya
riga shi, idan zaki tuna akwai lokacin da kuka bata, kuka
rasa hanyar da zaku bi keda Anti Najma, na turo wani yaro
ya nuna muku hanya har gida, kuma Ina biye daku, har
kikace a k'ara sauri kin kula Ina bibiyar ku da yake da
darene sai bakiga fuskataba, kuma nasan idan nazo da
kaina nace zan nuna muku hanya ba yarda zakuyi ba,
shiyasa na turo muku wannan yaron, haka farkon
had'uwarku da Shaheed naje gurin Amma da naga kin fara
waige waigen nemana sai kawai na bar gurin. Sannan
nasan zaki tuna lokacin da kika fad'a ruwa Mahbuob yayi
k'ok'arin cetoku Amma ya kasa, idan kin tuna wanine yazo
ya fitar daku, to nine mutumin daya fitar daku, sannan
nasan duk abinda ya faru dake daga kan abinda aka miki a
udus har zuwa rashin tafiyar ki, da butulcin da Mujaheed ya
miki da abinda iyayen Shaheed suka miki, da Wanda Abban
twins d'in ki ya miki."
.
Ya fad'a yana kallon ta, tunda ya fara magana take kallon
sa, ko kyaftawa batayi, shi kuma ya tsurawa wani frame ido
kamar yana karantawa, saida yazo gun zancen Abban twins
sannan ya kalleta, sunkuyar da kanta tayi tana mamakin sa,
yasan komai akanta, yaci gaba "Sabida haka banason kiyi
wani tunani akaina duka family na sun sanki kuma sun
amince dani, sunada labarin ki daga farko har k'arshe,
kawai abinda ya faru a udus ne basuda labari, na samu
goyon bayan iyayena 100% akan auren ki, Sunana Hameed,
haifaffan sokoto ne mu yan garin yabo local government ne
amma na sami aiki a Abuja, basai na miki dogon bayani ba,
kawai inason kisan cewa na sanki so kada ma kiyi tunanin
komai akaina, kuma nasan zaki soni sabida na hadda ce
Qur'ani" Ya fad'a yana kallon ta, d'an murmushi tayi, Amma
batace komai ba, har cikin ranta ta gamsu da Hameed
kuma taji ya mata tun farko, amma dole ta bashi lokaci dan
kada yayi tunanin wani Abu, ta mishi tambayar miyasa bai
zo tun lokacin ba, yace mata na farko yabar Nigeria ne yaje
karatu, koda ya dawo tana tare da wani sannan na biyu ma
baya nan, Amma da yake RABON SA CE gashi duk sun
wuce shi zai d'auka. Haka dai suka k'are zancen su,
sannan ya wuce gida akan cewa zai dawo ranar laraba yaji
amsarsa, ya karb'i number ta sannan ya wuce..
.
Soyayyah ruwan Zuma inji Hausawa. Nidai M. Jabo Yar
rahoto nayi rashin lafiya so ban lek'a gun su Ummey ba
saida naji sauk'i na bazama gidan su, koda naje abinda na
gani ya bani mamaki wani massg da na hango Ummey tana
rubutawa.... "My style, I love u without knowing how? Or
when or from where, I just wake up na sami kaina a
soyayyar ka you're my perfect match in every way." Ta
dad'e tana karantawa sannan ta tura masa ta rik'e wayar
saida taga delivery report, alamar cewa mssg d'in ya shiga
sannan ta kwanta fuskarta d'auke da murmushi, Hmmm
har ankai haka banida labari.
.
Wayar tace ta fara ringing, tayi murmushi amma tak'i
dagawa har ta tsinke mssg ya shigo, "Every minutes I want
call u so a I can here ur voice, I look forward to every test
message that we share, because it let's me into ur thoughts.
Most importantly I'm get full for what we share, hakan yana
k'ara sakani cikin kogin begen ki, gud nyt." Kamar zata
mishi reply sai kawai ta share, ta kwanta fuskar nan cike da
farin ciki, kamar bata taba shiga damuwa. Soyayyah suke
tsakani da Allah, ba yaudarar juna, a lokacin ne har aka
fara zancen Aure sabida ko wane bangare a shirye suke Anti
Najma lokacin har ta haihu, an saka auren 20/ may (daidai
ranar bardy d'in Jabo) Muhammad sai rawar kai yake
lokacin da ya gaya ma Shaheed zancen auren, bawan Allah
fatan alkhairi kawai ya musu sabida baya ma Nigeria gaba
d'aya kuma yak'i Aure, baya ma zancen auren.
** ** ** ** ** ** **
Yaune fa aka d'aura auren Ummey Ibraheem da Hameed
Aliyu, auren daya sami halarta mutane da daman gaske ciki
harda mai girma Architecture Jameel Wanda shiya haskaka
gurin kuma shine babban bak'o a gurin.
.
A gurin dinner yan matan amarya su Aisha yagani sai kai
kawo ake Ana neman kasuwa ko za'a dace, ranar hatta
nafee anka 'yar aikin gidan sai iyayi take, kamar wata
Hajiya bata kula dai-dai ita su masu gadi sai ki ganta tana
washema masu manyan motoci hak'ora, ita ba wani kyau
ba gata Yar aiki. Amarya da ango kuwa kamar su sukayi
kansu dan kyau, nima dai Jabo dagyar na gano Ummey
ranar sabida Nafesa Aliyu (Mrs Sanam) fitacciyar make up
artist d'in nan ta rangada mata kwalliya, Iyayen Amarya sun
shiga sun fita sun kaita gun Hajiya Mearmu, (Mrs Jabo )ta
gyarata da had'ad'dun tsimi na gargajiya, haka Suma su
madam Aysha Statu wacce daga Abuja tayo tattaki tazo
bada tata gudummuwar ta bada nata kayan mu na mata, su
Sady Jegal Suma sun taka rawar gani wajen ganin Amarya
ta dawo Yar Leda, saidai basusan cewa idan an rasa
budurci an riga an rasashi bane, Amma zai iya yuwa
Amarya ta sami ni'ima mai yawa ta hanyar magungunan
Amma budurci kam ya riga yatafi, to haka nake fatan
Ummey ta sami ni'ima gangariya, anyi duk wani event daya
dace ayi, aka kai Amarya d'akin mijinta inda naga nafee
anka tare da wani guy mai suna Muhammad inaga baisan
Yar aiki bace da ya gudu, yan kai Amarya sun watse aka bar
Amarya da ango, Ikon Allah wai yau Ummey ce a gidan miji,
Hameed yayi iya k'ok'arin sa har ta daina yan koke koken
da takeyi na munafunci da mata sukeyi, sun gabatar da
addu'a da sallar daren farko, cikin dabara irin ta maza ya
lallab'a kayan sa a daren suka raya sunnar baban Zahra
S.A W suka kashe arna dubu cikin dare d'aya, Allah ya bada
ladar kashe arna. Da safee ma ya taimaka mata ta shirya
jikinta dan abubuwan da su Sady Jegal suka narka mata ba
k'aramin tasiri ya mata ba, sabida sun had'e ta sosai
budurcin ne kawai babu, so tad'an ji jiki. Amarya fa sai
barsar amarci takeyi shi kuwa gogan naku sai wani fresh
yakeyi ya k'ara haske.
.
**************
"My Style Nafa shirya kai kad'ai nake jira," Hameed ya fito
yana saka boturan gaban rigarsa, suka bazama asibiti
domin wata shidan ta yayi, dama bayan duk wata shida mai
ciwon hanta zaije a dubashi dan a bashi magani idan akwai
buk'atar haka if not kuma a k'ara karanta masa abubuwan
da ya dace ya k'ara kiyayewa, shima Hameed saida yayi
rigakafi daga d'aukar cutar tun kamin Aure, bayan sunyi
GENOTYPE dukan su AA ne, sun isa asibiti aka duba ta fito
kenan taga wani mutum da sanda a hannu, kamar ta sanshi
amma ta rasa ina ta sanshi, saida na natsu sosai sai ta
gane Prof d'an jumma ne, ta matsa kusa dashi ta mai
sallama, dama tanason ta ganshi tace masa Allah ya isa.
Kamin ya d'ago ya bata amsa wata nurse ta fito da
takardun sa a hannu ta, tana masa bayani, akan hantar sa
ta rube, sabida rashin kula, yanada Cancer a hantar sa
sabida haka dole sai an cire hantar sa an dasa masa wata,
gashi bashi da aje bashida d'auko, Ummey dariya tayi, ta
fasa Allah ya isan Al ready ya isar mata tunda ya had'a d'an
jumma da HEPATITIS, Ta kalleshi da kyau, "Ka ganeni ko?
Ummey Ibraheem ce" Ya kuwa ganeta cikin kuka yake
rik'onta gafara, Hameed ne ya fito daga gurin likita kamin ta
baiwa d'an jumma amsa, ya fara mata magana, tayi banza
da d'an jumma dake k'ok'arin kiranta, saida tayi nisa ta
juyo ta masa kwalo ta wuce Allah yasa mufi karfin zukatan
mu amin. Bayan shekaru...... A Abuja, "Please ka d'auki
sajjad in d'auki Sajeeda Allah bazan iya d'aukar su su biyu
ba," Ya kalleta ya yamutsa fuska "Malama ban aikeki
haihuwar twins ba bare ki dameni da sai na d'auki d'aya,
kawai ms su kashe min kasuwa" Galala tayi tana kallon sa
"Haka ma zaka ce,? To wallhy zaka sani ne" "Mi zan sani
ne?
.
Bayan abinda na riga na sani, kalli wasu flowers chan suna
zuwa, d'an bani turaren nan in fesa ko zan chinyesu da
k'amshi na kamar yanda na cinye wata," Tama rasa abinda
zata fad'a d'aure fuska tayi ta mik'a wa babban yaron ta
Wanda zai kai 12yrs sajjad ta rik'e Sajeeda ta juyo ta kalli
d'ayar yarinyar Yar kimanin shekara shida Ke kuma Fatima
Rik'e min jakar nan, haka ta rarraba su, yauwa Ku muje, ko
kallon sa batayi ba ta wuce abinta, Ummey da yara hud'u
Muhammad babban sai kuma Fatima sai twins d'in ta,
sajjad da Sajeeda. Hameed dariya yayi, yasan ya janyo ma
kansa yau, ya kulle motar ya biyo su baya, sun tsaya suna
gaisawa da wata Yar dattijuwa mata wacce zata kai 40 Yar
gurguwa da ita, "Anti Sumy Ashe kina duniya?" Sumy Cillire
tayi dariya "wallhy inanan," Moh ne ya fito daga wani guri,
"Waye yake magana da kayana" Hameed dariya yayi,
yabaiwa Moh hannu suka kashe, "Kayana ce take magana
da kayana ka" Duk suka saka dariya sun gaisa sannan suka
wuce inda zasu, Hameed yanata magana ta masa banza sai
Harare hararee takeyi, har suka dawo gida, Haka dai ya
lallabata ya mata wayon su na maza suka shirya, dama
tsokanarta yake yi dan ya saba. Kwanciyar hankali had'i da
natsuwa suna gurin mutumin da ya mikawa Allah Al amarin
sa komai zaizo masa da sauk'i, (َّ ﻭَﻣَﻦ ﻳَﺘَّﻖِ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻳَﺠْﻌَﻞ ﻟَّﻪُ ﻣِﻦْ
ﺃَﻣْﺮِﻩِ ﻳُﺴْﺮًﺍ ) Allah yayi gaskiya, sabida rayuwar Ummey cikin
kwanciyar hankali had'i da farin ciki, ta haifi lafiyayyun
yaran ta har guda hud'u, wayanda dukan su AA ne. Sannan
har yanzu tanada HEPATITIS, (ciwon hanta,) amma da yake
tana kula sosai to baya wani damunta, ga mijinta da ta
samu mai k'aunarta, kullan dad'a bata kulawa yakeyi, Allah
ya bar k'auna.
.
TAMMAT BI HAMDI LILLAH.
Godiya da Allah madaukakin sarki daya bani ikon kammala
wannan littafi.