Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 16

MIJIN MARAINIYA PART 16
.
Alhaji yace jalal tashi muje gida, jalal beyi musuba ya tashi
ya shiga mota ko acikin mota babu me ma wani magana
har suka isa gida, ummi taso suyi magana da alhaji amman
yace ta bari sai gobe, haka ta shiga daki badan ran ta yaso
ba. alhaji ko rike hannun jalal yayi suka shiga daki bayan
sun zauna alhaji yace jalal ka kwatar da hankalin ka insha
Allahu komai zai wuce. cikin sauri yace daddy naji fah abin
da safna take fada wai bata sona har tana cewa wai ace
min na sake ta. alhaji yace ya isa jalal kayi hakuri bacin rai
ne ya sata fadan haka, kama ta uzuri yariyar tana da
hankali,lallashin ta zakayi zata sakko. washe gari jalal yana
shir yawa ya nufi gidan hajiya yana zuwa ya samu hajiya da
anty nusaiba suna hira bayan ya gaida su hajiya tace dama
yanzon muka gama mgn akan sunan da za,a sama yaran
nace sai asa sunan iyayen ka. jalal yace a,a hajiya abarsu
da sunan su ummi ma bata so asa sunan ta.
.
hajiya tace ai jiya muyi mgn da ita tace asa ma macen
saudatu. hajiya dan allah ki dai na biyewa ummi kuma ni
nafison abar su da sunan su, be sake cewa komai ba ya
shige dakin ya sami safna zaune tana cin tuwo hada fuska
tayi nema guri yayi ya zauna kusa da ita. shiru tayi bata ce
komai ba, jalal yace safna ba gai suwa. gani yayi bata da
niyar magana yace toh ni bari na gaida ki inakwana ? ban
za tayi dashi ya sake cewa safna fushi kike dani to me na
miki? daga kan ta tayi tace kawai ganin ka ne banaso, sabo
da tun da na samu lbrn mahaifiya ta naji na tsani dangin ta,
mahaifiya ta tayi rayuwar bakin ciki na rashin iyayen ta har
ta koma ga Allah bata gansu ba wannan ya nuna min basa
kaunar ta da suna kaunar ta basu manta da ita atiti ba dan
haka bana son wani abu ya hadani da dangin ta bana sonsu
bana kaunar su. shiru jalal yayi ya dukar da kai zuwa cen
yace safna kinga duk cikin wannan abun ummi ce me laifi
tunda ita ce ta bata musu rai har suka manta sun taho da
ita. ciki kuka safna tace bawani bacin rai da zaisa ka
mance da danka yan zon Kai zaka dauki dan ka ka,ajeshi
atiti kace mai bari kaje kadawo, su mahaukata ne? jalal
yace naga alaman baki da hankali mikewa yayi zaifita safna
ta bude baki tace kaine dai baka da hankali. juyo wa yayi ya
dawo yace abin har yakai haka? eh yama wuce haka tun da
kafito ta tsotson ummi. jalal ji yayi kamar ta caka mishi
allura azuciyar shi , yace safna kar ki manta fa ummi
mahaifiya tace.
.
safna bude baki tayi tace jalal ai uwa batafi uwa ba. tun da
suke da safna bata taba kiran shi da sunan shi ba sai yau,
kara kule wa yayi yace toh nagane abin naki rashin mutunci
ne toh kisan magar da zata rika fitowa daga bakin ki dan
bazan dauki wula kancin ki ba inkuma kina ganin wasa ne
kikara fadan wata magana kiga ni wlh mugun duka zan
miki. daidai lokacin su hajiya dake falo suka soma jin
hayaniyar su aguje suka shigo daidai lokacin da safna take
cewa sai dai mudake juna, jalal kuwa yayi kanta gadan
gadan anty ce ta riko shi iya karfin ta amma sai kwacewa
yakeyi hajiya ce ta shiga tsakiyan su ta girgiza jalal tana
fadin abduljalal dubeni nan me yayi zafi hake, kai da nake
yabon ka. yace hajiya wannan yar karamar yariyar zata
duga fadamin mgnr da taga dama ni sa,anta ne? hajiya tace
a,a kayi hakuri fita muje, juyawa yayi ya fita yana huci anty
tabi bayan shi. Hajiya ta kamo hannu safna data manne da
bango ta zaunar da ita bakin gado tace safna kintaba jin
laifin wani ya shafi wani, shi meye nashi, me lefi daban
wanda ake hukun tawa daban, karki kara safna dan Allah
kisawa zuciyar ki salama. safna kuka take sosai tace hajiya
toh kice mishi ya sake ni. cikin fada hajiya tace yazon dai
kina nufin babu wanda zaigaya miki mgn kiji ko ? girgiza kai
tayi bahaka bane Hajiya ni cewa nayi ya dai na min
magana.
.
haba safna ban da abinki ta yaya zakice ya daina miki mgn
mijin kine fa dan Allah karna kuma jin wannan mgnr abakin
ki kuma kije ki bashi hakuri, safna ki daina gayawa jalal
munanan mgn akan ummin sa uwa uwa ce safna kuma
hannun ka baya rubewa ka yanke kayar , safna yanzon
zaliha ta gane kuran ta ya kamata ki yafe mata, tana cikin
wani hali ki taimaka mata ta samu ta daidaita da iyayan ta,
saboda ayanzon ke da baki da iyayen kin fita kwanciyar
hankali dan kin rabo dasu lfy , itako ga iyayen tana kallon su
amman ba dama taje gurin su, sabo da suna fushi da ita,
toh dan Allah kiyi hakuri ki yafe mata, yanzon anriga an
zama daya, ban da matsayin ta na yar mahaifiyar ki, kuma
ga jikokin ta nan agaban ki, dan Allah mu yafi juna kwata
kwata duniyar ma guda nawa take. jikin safna yayi sanyi
tace shikenan hajiya amma ni abin da yake bani haushi
yaya za,ayi mutun ya manta da dan sa. hajiya tace bar
wannan maganan safna kandara ce haka Allah ya so. tace
dama hakane sai mutun yayi abu da gangan yace wai
kaddara ce. hajiya tace safna bar wannan maganan tashi
kije kibawa jalal hakuri dan naga yayi fushi sosai . suna
fitowa suka samu anty nusaiba tana rarrashin jalal yana
zaune idon shi ja wur kallon safna yayi ya girgiza kai itama
kallon shi tayi ta neme guri ta zauna tayi shiru. anty nusaiba
ciki ta shiga hajiya ma barin gurin tayi aka barsu su biyu,
cikin sauri jalal ya mike zai fita safna ta tashi ta riko rigar
sa, kallonta yayi yaga tayi kasa dakai bece mata komai ba,
ahaka suka tsaya safna na rike da rigar jalal har tsayon
minti 15 ba wanda yace wa kowa komai
.
Gani yayi bata da niyar magana dan haka ya zame rigar shi
yayi gaba. safna naganin ya wuce ta fara kuka, sai da ta
gaji da tsayowa ta wuce daki, ta shiga ta samu jarirain sai
kuka suke, cikin tausayawa ta dauke su ta sasu acinyar ta.
tana cikin haka taji muryan alhaji da ummi suna gaida
hajiya, bayan yaran sun sha nono ta kwantar dasu tamike
dan gai da daddy sai da ta saka hajjabi sannan ta fito.
.
alhaji naganin ta ya washe baki , gwaiwan ta tasa akasa ta
gaida shi ya amsa, ta juya barayin ummi kanta akasa ta
gaida ta, amsawa tayi cikin farin cikin . safna mikewa tayi
zata bar wajan alhaji ya dakatar da ita. ahaji yace wata
magana nake son muyi me mahimmanci hajiya kisa mana
baki dan naga safna har yanzon bata huce ba, hajiya gyara
zama tayi. alhaji yace yazon daga gidan baffa muke
nashiga ni kadai na mai bayani abin da ke faruwa amman
kwata kwata yaki saurara ta wai mun shirya karya ne nida
zaliha daga karshe cewa yayi indai da gaske ne , toh
nakawo mai yarinyar. alhaji na kaiwa nan yayi shiru hajiya
tace toh amman da naso abari ayi suna tukun, shiru suka yi
na dan wani lokaci zawacen hajiya tace, safna tashi ki
shirya. mikewa tayi cikin daure fuska ta shiga daki ,bata
jimaba ta fito ,ummi ce tabita da kallo taga bata fito da
yaran ba, bata ce komai ba ta mike ta shiga ta kwaso yaran
ta fito ganin inda safna ta daure fuska yasa hajiya ta mike
tana fadin bari na dauko gyale na, naraka ku. bayan sun
shiga mota hajiya tace ina jalal ya kamata ace tafiyar nan
dashi akayi ta. alhaji yace kwarai kuwa bari na kira shi,
daga wayar shi yayi ya kira jalal, yana dauka alhaji yace
jalal kayi maza ka same mu gidan baffa gamu ahanya
harda safna. jalal najin an abaci safna yaji ranshi ya baci
dan haka yace daddy bani da lafiya ne kaina namin ciwo.
alhaji yace ka daure dai kazo ina jiran ka, bayan ya kashe
wayan yace safna halan kunyi rigima da jalal ko? shiru tayi
bata ce ko maiba, sai hajiya dake zaune kusa da safna tace
ai kowa dai yau anyi tsiya sosai dan naga jalal ya tun zura
alhaji yace yauwa dan indai kaji jalal na fadin kansa na
ciwo toh akwai bayani. nan dai alhaji ya farawa safna
nasiha har suka isa gidan. bayan sun fito daga motar
dukkan su suka shiga cikin gidan safna tun akofar gidan ta
fara kuka. sun shiga da sallama wata dattijiyar mata ta fito
daga daki cikin sauri safna tabi da kallo ,cikin sauri ta
karaso ta rike safna ta kalli fuskar ta sosai ta juyar da
idonta kafar safna cikin kuka ta fara kiran baffa tana mai
magana cikin fillanci. fitowa yayi arude ya nufi safna kafar
ta ya kallah shima kuka ya fara yana fadin Allah da girma
yake tabas yar saudatu ce kafar su iri daya cikin sauri yace
rahane sa mana tabarma. bayan ta shinfida tabarma kowa
ya zauna ummi ko sai rabe rabe takeyi. Itako safna tunda
baffa ya rike hannun ta be sake ba tana zaune kusa dashi,
abayan sun gaisa alhaji ya gabatar da mahaifiyar shi agurin
baffa da matar sa rahane, baffa dadi yaji sosai sannan ya
shiga yi mata godiya akan abinda alhaji yake mai yabon
alhaji yayi sosai daga bisani ya shiga saka mishi albarka.
.
hajiya ma dadi taji sosai ganin inda baffa kesawa danta
albarka dan haka tace toh baffan yaudai gaka ga yar
saudatu dan haka yanzon sai mu yafi juna dan Allah abar
tuna baya dan zaman duniya dan hakuri ne, kuma in mune
yau ba mune gobe ba dan Allah ka yafewa zaliha . sai
alokacin baffa ya kula da ummi data makure agefe yace
hajiya ina jin bakin ciki idan na tuna rashin mutuncin da yar
isakar yariyar cen tamin tasani atashin hankali da bakin ciki
badan ina da tsawon kwana ba toh da bakin cikin yariyar
nan ya kasheni tun lokacin da aka daura mata aure da
alhaji babu wanda yasan gidan sai yayar ta rabi, dan haka
da muka ta dade bata zoba na yanke shawaran nadauki
mahaifiyar ta da kanwarta muje mugano ta ita da danta har
gidan yayarta naje tamin kwatan cen gidan . bayan mun
sauka amota sai muka fara tafiya da kafa dan iya kudin mu
kenan kona komawa gida bamu dashi tafiya taki karewa
har saudatu ta fara gaji danaga ta gaji sosai gata ba
karama ba bare adauke ta , sai muka zauna gindin wata
bishiya saudatu na zama ta fara gengyadi ganin yama na
karatowa mamarta ta tashe ta amman sai tace bata huta ba
dan haka muka barta wajan mukace bari muje mudawo,
cikin ikon Allah muka isa gidan tunda me gadin ya fada
mata ga baki sai gata rike da hannun jalal yana karami cikin
bacin rai tace wai lfy kuwa.
.
har yau na kasa mance wannan kalmar haka na daure nace
naga kusan wata shida baki zo bane nace bari muduba ko
fly, cikin sauri tace lfy ta kalau kuje gida inanan zuwa,
mahaifiyar ta na kokarin magana tace a,a mama dan Allah
kuyi sauri kar kawaye na su fito su ganku zasumin dariya
har tana kiran me gadin wai ya bude mana kofa. haka muka
baro gidan cikin bacin mahaifiyar ta ttun anan ta soma kuka
haka muka zauna mukayi ta kuka sai yamma likis muka
tuna da saudatu saida mukayi tafiya me tsayi muka isa
wajen, wayam muka samu gurin babu kowa duk muka duba
unguwar bata ba lbrin ta gashi dare yayi ganin haka muka
nufi gida akafa ko Allah zaisa gida ta nufa, sai tsakar dare
muka isa gida tunda lokacin ban sake samun lfy ba har yau
sai dai sauki kowa agurin kuka yakeyi daidai lokacin jalal ya
shigo ya same su cikin wannan hali. ummi mikewa tayi taje
gaban baffa ta tsuguna tana neman gafarar shi. bece mata
komaiba yana rike da hannun safna, dan haka hajiya taje
har gabasa itama tsunawa tayi tace baffa kaduba girman
Allah yafewa yarinyar nan, ganin hajiya da yayi akasa cikin
sauri yace Allah ya yafe mana baki daya.