MIJIN MARAINIYA PART 17 ***** KARSHE *****
MIJIN MARAINIYA PART 17
***** KARSHE *****
.
Godiya tayiwa baffa sosai sannan tasa hannu ta daga
ummi ta kaita gaban mahaifiyar ta. mama rahane kin
amsawa tayi ta juyar da kanta gefe sai da hajiya tasa baki.
baffa yana rike da safna mama rahane tazo tarike safna
tana fadi ya sunanki ne? safna shiro tayi tana zunbura baki,
hajiya tayi murmushi tace sunan ta safna ai fushi take daku
tace dama cen baku son saudatu tunda har kuka manta da
ita. baffa yace ayya yarinya barashin so bane akwai yanayi
na rashin wayewa ada bakamar yanzon ba, amman munji
mun dauka kiyafe mana kaddara ce .
.
kowa agurin murmushi yayi banda jalal dake tsaye, alhaji
yace kai kuma yaya zaka zo katsaya mana akai. yace
daddy inason naje gida ne , bana jin dadi. alhaji yace ka bari
muma yanzon zamu tafi, baffa yace alhaji kafin kutafi bari
akira mamar ta rabi ta ganta, ya fara kira rahane dauko
mayafi kije gidan rabi ki gayo mata, cikin sauri ummi ta
mike tace bari naje, kiran jalal tayi suka fita tare. bayan sun
dau hanya ummi tace jalal me ya hadaka da safna? mamaki
ne ya kama jalal dan haka yace ummi wani ne yace miki
munyi fada. hararar shi ummi tayi tace ina tambayar ka
kana tambaya na, dan baka da kunya. bahaka bane ummi
ai naga baki cikin gidan ne lokacin. toh ina sauraron ka me
ya hadaka. ummi rashin kunya take min kwata kwata ta
raina ni. dakatar dashi ummi tayi jalal inason kayi hakuri da
duk wani abu da safna zata maka bana son in sake jin ance
kunyi rigima kajiko, kuma yan zon kaje ka bata hakuri. da
sauri jalal ya kalli ummi yace inbata hakuri fa kika ce ai ita
ce tamin laifi ita ya kamata tabani hakuri.
.
eh na sani ka dai bata hakuri bana son ganin yariyar cikin
bacin rai. ummi ni gaskiya bazan bata hakuri ba, kin ga inda
take gaya min magana ne. ummi shiru tayi bata sake cewa
jalal komai ba har suka isa gidan, yana tsayawa ta bude ta
fita bata jima ba sai gata sun fito da yaya rabi har da yarta
aliya sai murna suke. baya suka shiga ummu na gaba suka
kama hanya ahanya ne jalal ya kalli aliya yace ummi na
dade banga aliya ba tun tana karama , sai kuma naga
kamar tana kama da safna. ummi banza tayi dashi sai yaya
rabi ce tace ikon Allah itama zaliha haka tace, nina zaku ma
naganta wlh. jalal ya juya gurin ummi yace ummi lfy kuwa?
banza ta sakeyi dashi, yaya rabi tace zaliha abduljalal na
magana kinyi banza dashi. rabu dashi yaya, jalal bashi da
kunya ninace mai yayi abu yacemin shi gaskiya bazaiyi ba,
kiri kiri. nan da nan yaya rabi tashiga yiwa jalal fada , har
suka isa gidan fada takemai. suna shiga ta gane safna ta
juya barayin ummi tace amman zaliha kin ban mamaki da
har kikai zama mai tsayi da safna baki gane taba, hannu
tasa ta daga safna, safna ma gani tayi kamar mamarta
sunyi kama da mamarta sosai dan haka ta rungume ta tana
kuka take taji son yaya rabi ya kama ta jinta take kamar
mahaifiyar ta, duk da cewa da kaga yaya rabi kasan tana
cikin yanayi na talauci. aliya tazo ta baya ta tsaya tace anty
safna.
.
Cikin sauri ta waigo sukayi arba da juna safna sakin yaya
rabi tayi ta rike aliya haka sukaita murnan ganin juna sai
gurin la,asar suka fito, safna na rike da aliya wai ita adole
sai dai sutafi da ita. mama rabi tace safna kibari ran suna
in munzo sai tazauna tamiki kwana biyu kinga yazon kayan
ta duk suyi dauda. safna tace mama toh basai ta saka
nawa ba. ummi tace yaya ai hakuri zakiyi kawai mutafi da
ita. mama rabi tace toh Allah ya tsare sai munzo suna.
bayan sun dauki hanya hajiya tace toh kodai zamuyi gaba
daya ne daga nan mu wuce gidan goggo safna cikin murna
tace eh Hajiya. alhaji ne yace toh bari akira jalal agaya
mishi dan motar sa daban kar ya wuce gida. bayan alhaji
yagama waya da jalal yace yaran dai zamani basu da
kunya kunga wai jalal tunanin yaran shi yake wai cewa yayi
za,a kwasar musu iskar mota, dariya sukayi ummi ta kara
rufe jariran ta rungume su ajikin ta, suna isa gidan malam
musa alhaji da hajiya ne kadai suka sauka amotar suka
shiga gidan da sallama, goggo ta fitoh daga daki tana fadin
wai wai hajiya kece da kanki sannun ku da zuwa tabarma ta
shin fida bayan sun gaisa goggo tace bari naje na sowo
muku shinkafa da wake.
.
hajiya tace a,a ni ba zama nazoba nazone naga jikokina.
cikin fadowan gaba tace aiko basa nan iro yana gun yansan
da an kamashi itako salame yanzon ta dauki tallan gyada.
cikin mamaki hajiya tace a,a batayi aure ba? hawaye ta fara
sharewa tace ai ya fasa tunda yagano ciki gare ta. hajiya ta
girgiza kai tace toh kizo ki raka mu gidan da dayar yariyar
take naganta. goggo tace ayya ai sun bar garin nan kwata
kwata yanzon bansan inda suke ba. alhaji yace tohfah
mukuma gashi ganinta mukazo ya sunan tane ? baki na
rawa tace safna , suna cikin haka saiga ummi sun shigo da
jalal goggo ta zabura tamike tami tana fadin yau na shiga
uku karya ta takare dan Allah ku rufamin asiri wlh bansan
inda safna take ba, nan da nan tashiga basu lbr tana kuka .
bayan ta gama ne hajiya tace to yanzon meye ribarki? babu
wlh kawai bakin kishi ne ya debeni har na aikata haka
gashinan alhakin ta na bibiya ta yara na duk babu nagari
kuka goggo taci sosai babu me lallashin ta hajiya fadi take
kigama kukan kije ki ne momin jikata dan ba yadda zanyi
ba. Idon goggo duk sun fito waje kuka harda majina.
alhajine yama jalal umarnin ya shigo da matar shi, dan haka
ya juya ya shigo da safna safna na shigowa goggo ta kara
tsorata , tace dama kunsan safna ne, a Ina kuka same ta,
zuwa tayi ta fara duba jikin safna tace ikon Allah safna ce
haka kamar yar wani hamshaki , ni inan cikin bakin ciki da
tashin hankali muta ne na nunani wasu suce min uwar
karuwa wasu sucemin uwar barawo, cikin kuka take
maganar ki yafemin safna na tuba bazan kara ba. hajiya
tace kima Kara mana, ina zaki ganta bare ki kara ita da take
dakin mijin ta cikin fada tace ku kuma kutashi mutafi, duk
mikewa sukayi suka fita safna ko tsayawa tayi tana kokarin
daga goggo hajiya tazo ta jata.
.
Lokacin da suka koma gidan hajiya mangariba tayi dan
haka alhaji yana sauke su hajiya da su safna suka wuce
gida harda jalal, jalal dai fushi yake da safna sosai dan har
suka rabo basuyi magana ba. suma suna sauke ummi
masallaci suka wuce saida sukayi sallar ishsha suka dawo
gida. bayan sunja girki ne jalal ya mike yace daddy bari naje
gida. alhaji yace me zaka je kayi agida bayan matarka
batanan kayi zamanka mana anan, koba haka ba zaliha?
ummi tabe baki tayi tace alhaji ni yanzo jalal yafi karfi na.
Alhaji yace me kuma ya faru kai jalal dawo nan ka zauna,
jalal na zama alhaji yace me yake faruwa, me ka mata?
sunkuyar dakai yayi yace daddy akan maganar safna ne,
yanzun kwata kwata ta rainani rashin kunya take min, kuma
wai ummi tace wai dole ni zan bata hakuri, daddy ai ni ya
kamata taba hakuri, amman yaya za,ayi kuma ace ni zan
bata hakuri ai sai taji dadi nan gaba ta kara yimin. alhaji
yace zaliha yaya haka, haka ake hukunci? alhaji nifa bana
son ganin safna cikin bacin rai, dan haka ni dai kawai kaje
ya bata hakuri, shi wanene da bazata mai rashin kunya ba,
ai nima gashi nan kanamin rashin kunyar, wlh inhar bakaje
ka rarrashi yariyar nanba zakaga abin da zan maka. kallon
ummi yayi yace toh shike nan ummi naji, a han zar ce ya
bar wajen dakin sa ya nufa. alhaji yabi jalal da kallo yace
zaliha bafa haka akeyi ba kina nufin yanzon kinfi son ganin
nashi bacin ran akan na safna?
.
Alhaji aishi babba ne kuma cewa nayi yayi hakuri yabata
hakuri.. Katseta alhaji yayi yace aiko indai haka zaki ringayi
bakice su zauna lafiya ba dan zaki samai tsanar ta, ai shi
amatsayin shi na namiji baxai so matar sa ta raina shiba,
kuma nina tabbata ta bata mai rai ne shiya sa yayi fushi da
ita amman yana son matar sa bakuma wai dan jalal yana
dana bane na yabe shi, dukkan su yaya nane kuma daidai
gwargwado nasan halin su. haka alhaji yayita ma ummi
nasiha me ratsa jiki. zuwa cen ummi ta fara kuka bakin ta
yana rawa tace alhaji akwai abin da yake damuna ina
tunanin idan kaji mgnr zaka tsora ta dani amman yazama
dole na fada dan innemi gafarar ka amman dan Allah ina
neman wani alfarma karka gayawa kowa wannan maganar
dan idan maganar nan ta fito toh lallai naji kunya kukanta
karuwa yayi saida ta waiga ko akwai wani dake tahowa
sannan tace alhaji gidan jalal daya kone... Alhaji be Bari
ummi ta karashi maganar taba yace nasan komai xaliha
bake da madina kuka shirya komai ba ai tuni nasa aka
kama madina da kanin ta duna sai da madina ta kwashe
sati buyu gurin yan sanda, shiko duna har yanzun yana
hannu . kuka ummi take sosai tana rokon alhaji gafara tana
fadin sharrin zuciya ne. alhaji ya fara share mata hawaye
yace bar kuka zaliha ni tuni na yafe miki komai yawuce sai
dai muce Allah ya kiyaye gaba. nagode alhaji har ina
tunanin inkaji wannan maganar zaka sakeni ashe kai
kallona kawai kake. alhaji yake yayi yace aitun lokacin
tarewar jalal nasan komai dan lokacin na tsane ki shi
yasama dazan tafi ban miki sallama ba dan gani nake zaki
iya kisa. washe gari karfe 7:30 jalal ya fito cikin shirin shi na
zuwa office sallama yayi ma ummi ta amsa bakamar yadda
jalal ya zata ba, sannan ya mike yace nafi. waigowa tayi
tace zaka biya gurin yan biyu ne sannan ka wuce ko? Jalal
yace a,a saina tashi office saina tsaya acen. a,a jalal be
kamata ba kadai biya ko atsaye ne ka gansu sai ka tafi, ga
kairat cen katafi da ita daman ta dame ni wai bataga yan
buyu ba.
.
suna isa gidan kairat ta fita aguje ta shi gidan lokacin da
jalal ya shiga ya same tana rike da yaran sai faman
jagwalgwala su take wai ita tana musu wasa . saida ya
gaida hajiya ya tabaye ta anty nusaiba bataxo ba, hajiya
tace na nan tafe. safna nazaune kusa da hajiya tace ina
kwana. kasa kasa ya amsa yamike yaje gaban kairat ya
tsuguna ya sunbaci yan biyu ya mike yace hajiya na tafi.
safna ta mike tabi bayan shi, yana fita daga falon ta rike
shi, juyowa yayi yace safna sakeni karki ya mutsamin kaya
anjima zan dawo . kara shagwar gwabewa tayi tana buga
kafa kamar yanda kananan yara keyi tare da kuka ahankali
. murmushi jalal yayi yasa hannu ya riko safna yace toh ya
isa haka safna, me kike so. cikin kuka tace bakai bane
kaketa fushi ko kallona baka yi. Jalal yace safna kenan
bake kikace na daina miki magana ba, har kina min rashin
kunya. toh kayi hakuri banzan kara ba. dadi jalal yaji yace
shikenan safna ya wuce shiga ciki idan na dawo zan zo .
haka safna tacigaba da zama gidan Hajiya cinkin kwanciyar
hakali kowa kokari yake ya faranta mata rai Ana gobe suna
su yaya rabi suka iso gidan hajiya ita da mama rahane
washe gari akayi suna nagani na fada alhaji da ummi sun
kashe kudi sosai, jalal kuwa ya tara abokan shi sosai itako
safna dama bawasu kawaye gare taba dan haka bawasu
mutane ta tara ba daga safiya sai halima su kadai ne
adakin sai kuma kanwar ta aliya haka taro ya tashi lfy
yaran sukaci sunan ummi da daddy wato yusuf da zaliha.
.
Washe gari suna saiga goggo da salame sunayin sallama
hajiya tace su fita mata daga gida kuka goggo ta saka tana
fadin hajiya dan Allah kiyi hakuri ki bari na neme gafarar
safna. safna tana daki ita aliya suka fara jiwo kukan goggo
fitowa tayi da sauri , goggo nagani safna tace safna naxo
neman gafarar ki ne karna mutu da wannan nauyin dan
Allah ki yafemin itama safna share hawaye tayi sannan tace
goggo kitashi ni dama na yafe miki komai ya wuce, kallon
salame tayi taga cikin ta har ya fara fitowa sai yama suka
tafi safna ta roko su har bakin gate ta basu kudi masu yawa
tare dace ma goggo idan suna bukatar wani abu su mata
magana. bayan shekara uku jalal da safna ne tafe a mota
daddy da ummi suna baya sai faman surutu suke , safna
tace yaya wai ina zamu ne? yace yau gidan ummi zamu tun
da ke baki cewa zaki, ke sai dai gidan mama rabi ko kunyar
ummi bakiji sai dai ita idan taji ganin ku tazo. kunya ce ta
kama safna tace ba haka bane yaya abin da yasa nafison
gidan mama rabi muna hira da aliya. hararan ta jalal yayi
bawani ai ummi ma tana jinki da hira saiki ta wani
zilzillewa.
.
daddy ne ya leko da kanshi saitin jalal yace abba ni gidan
baffa nake so bana son gidan ummi. tsawa jalal yayi mishi
tare da fadi daddy In na sake jin kace baka son gidan ummi
saina zane ka. cikin murna ummi tace yauwa abba kamai
balala ni ban da ni inason gidan ummi. Jalal yace yauwa
ummina ashe dai kin gane. Jalal ya juya barayin safna yace
kinga kin koya ma daddy kin gidan ummi ko. safna shiru
tamai domin miyau ne ciki da bakin ta daha suka isa gidan
Kairat ta fito da gudu ta rike hannun ummi da daddy suka
shiga ciki, sun same ummi da alhaji afalo gudu ummi
karama tasake hannun kairat ta fada jikin ummi daddy ma
da gudun shi ya nufi alhaji cikin dariya alhaji yace au wato
kun raba kenan safna ce ta shigo jalal nabinta abaya sai
fada yakeyi. alhaji yace na kula jalal so yake yazama
mafadaci daga shigowa sai fada. daddy wai yariyar nan
idan bata son tamin magana sai ta tara miyau abikin ta.
ummi tace a,a jalal bada gangan take ba saidai idan ciki
gare ta. cikin sauri jalal yace ummi ai idan tana da ciki
bahaka take yi ba daddawa take ci dariya sukayi gaba
dayan su sannan ummi tace jalal ai ko wani ciki da kalar sa.
.
*ALHAMDULILLAH* _anan na kawo karshen wannan lbrn