Breaking News

RABO NA CE PART 14

RABO NA CE PART 14
.
Abdul Hakam, da gudu ya tashi ya fad'a jikin baban sa yana
masa godiya, shi kuma tsohon yanata murmushi, sabida ba
abinda yake buri a Duniya da ya wuce farin cikin d'an sa.
Abdul Hakam ya tashi tsaye, "Abba zamu kawo full name
d'in sa da komai nasa sabida cikin gaggawa muke son a
duk'ufar dashi," Ya k'arasa fad'a yana dariya shima tsohon
nashi dariya yayi, Shaheed yayi dariya shima dan yaji
kamar an sauke masa wani k'aton Abu akan sa. Suka fito
suna tafe suna hira Abdul Hakam yanason Shaheed, sabida
ya iya wasa, shine best player d'in sa.
.
Ummey zaune tsakiyar d'akin ta tana karanta wasik'ar jaki
tunani take kala-kala D'ill taji alamar sak'o ya shigo
wayarta, ta d'auka ta duba Mujaheed ne, kamar ba zata
bud'e ba sai kawai ta k'ara jin shigowar wani sak'o,
Murmushi tayi a ranta tace "ba kalar bak'in cikin da ban
gani ba, nasan mssg d'in ka baikai bak'in cikin da nake ciki
ba yanzu.!!" Ta bud'e sak'on, "Mrs HEPATITIS, anje garin
shakatawa an kwaso HEPATITIS, sabida iya sanina ta
hanyar saduwa da namiji ake samun cutar ko hihuwa, I
don't know ko haka aka haifeki, Amma nafi kyautata zaton
Mrs HEPATITIS gun jin dad'i aka samoshi, kuma akaso a
lik'a mana, lol u are too funny Ummey." K'arshen mssg d'in
kenan, Kamar ba zata bud'e dayan ba haka ta daure ta
bud'e "Sai kuma naji wai anyi ma Mrs HEPATITIS fyade
hahahahaaaa.!! Ashe Ana yiwa mutum mai hankali fyade?,
na d'auka yara k'anana ake yiwa fyade, Ashe hadda
manyan mata irin su Mrs HEPATITIS, duk da cewa hanyar
kice wannan. Ina dad'a godiya ga Allah daya bayyanamin
matsayin ki tun kamin na aureki, da nasan har k'arshen
rayuwa ta ina dana sani. A k'arshe Ina cewa Allah ya had'a
ki da dai-dai ke, nikam virgin ne kuma sai virgin Yar uwata
zan aura." Wasu hawayee ne suka gangaro mata, tasa
bayan hannu ta goge, ta d'aga kai ta kalli wani hoton ta da
tayi murmushi, da hawayee a idon ta sake yin murmushi, a
ranta tace "Ummey try and keep smiling everyday" Hawaye
basu daina sauka a idonta ba, sabida taji zafin kalaman sa,
bata tab'a tunanin haka daga Mujaheed ba.! Haka tayi shiru
Amma kuma bata tunanin komai, ta rasa abinda takeji, tashi
tayi ta d'auko Al Qur'ani ta karanta suratul Yusuf, nan
danan ta sami natsuwa a ranta tana k'are wa ta kwanta sai
bacci. Abubuwa sun faru ciki harda sallamar Prof d'an
jumma daga d'an fodiyyo bayan an lallata masa takardun
sa, kuma ba wata hanya da zai k'ara samun takardun har
abada, saidai idan zai dawo secondary school ne ya sake
karatu, to Nigeria ce fa komai kayi akwai dai-dai kai, kuma
zaka samu dai-dai kai. Ummey ma tabar d'an fodiyyo
sanadiyar maganar fyaden ta ya game skull, ta hanyar uwar
gulma Sadydy tada baza zancen kowa ya sami rabon sa.
Haka iyayen Ummey dukan su sunyi VACCINE ( riga kafi)
dan kaucewa d'aukar ciwon hanta, Amma duk a b'oye aka
musu allurar dan kada Ummey ta gani taji ba dad'i, d'an
Mumy ma kam dagyar ta yarda aka mata allurar ta riga
kafi. Ummey ma bayan result d'in ta ya fito an bata allura ta
shekara daya da zata yi, idan an dace zata warke gaba
d'aya, duk da cewa HEPATITIS d'in ta CHRONIC ne, Amma
zata iya warkewa idan Allah yaso, muna fatan zata warke
taji sauk'i. Soyayyah tana guduna Ummey da Shaheed duk
da cewa har yau Ummey bata jin komai akan sa Amma dai
sabida son da Muhammad yake masa take sonsa, bugu da
k'ari ga halaccin daya mata bayan kowa ya gujeta shi
lokacin ma yake sonta, sannan ga abinda yasa aka yiwa
Prof d'an jumma, sabida ma daga baya suka sami labari,
Dady ya masa fad'a sosai akan revenge d'in da ya d'auka,
sabida wani lokaci bashida Amfani barwa Allah yafi, amma
Dady har cikin ransa yaji dad'i dan ba amfanin barin irin su
Prof suna amfani da damar su suna lalata yaran Al umma.
.
** ** ** ** **
Shaheed ya shigo da maganar Aure akan zai turo
magabatansa ayi zancen Aure, Allah bashi idan tayi Aure sai
taci gaba da karatun ta achan garinsu d'in, Dady ya amince
sabida ya kula Shaheed yana son Aure tun tuni. "Baffa,
zancen yarinyar nan dana muku 'yar sokoton nan, Ummey
d'ina dai, to dama itace iyayen ta sukace na turo ayi zancen
Aure," kansa a k'asa yake zancen, Mamar sa da take zaune
gefe tace, "Kai yaron nan akwai kwashe-kwashe, yanzu duk
matan duniyar nan da suke sonka, ka rasa ta Aure sai 'yar
sokoto, k'auyawan da basu waye ba har yanzu" Shaheed ya
d'aure fuska "Gaskiya Hajiya banason haka.! duk abinda
zanyi a duniyar nan sai kin kushe, to anji yan sokoto
k'auyawa ne, Amma dai ba munafukan mutane bane! Haka
ba mak'aryata bane! So gara suyi ta zama da k'auyancin su
da kike ganin kamar sunadashi, da su rik'a munafunchi,
kuma wallhy sai kinje garin ki raina kanki, sabida idon su a
bud'e yake kawai yanayin zancen sune" "Nagode babana,
yau nice munafuka kuma mak'aryaciya, sabida nace
sakwatawa k'auyawane wato sabida na fad'i gaskiya akan
garin su budurwarka." Baffa dariya yayi, "Ke madam daga
baki misali sai kice dake ake, saidai idan Kinsan garin Ku
haka kuke sai ki tsargu Amma idan Kinsan ba haka kuke ba
miye naki na damuwa" Cikin gatsine tace "Ai mu wallhy
kanawa kowa yasan koda mi kazo an fika, kowa yasan
wannan," Baffa yace "Sosai, kowa yasan wannan tunda
koda mi mutum yazo kun fishi, to kenan kunfi sakwatawa
k'auyan ci da munafunchi da...." "Haba Alhaji ya kake min
haka gaban yaron nan, nidai abar zancen" "Da dai ya fiye
miki rufin asiri" Ta gyara zaman ta, ta bar su suna zancen
su. Sunyi akan za'ayi binciken Asalin yarinyar da tarbiyar ta
sannan suje zancen Aure.
.
Bayan sati biyu, An kammala binciken da mahaifin Shaheed
yasa ayi masa, kuma an tabbatar da cewa iyayen yarinya
mutanen kirki ne kuma gidan gaba dayan su mutanen kirki
ne. Saidai an bada shedar cewa ita yarinyar korar samari
take, bayan ta cinye musu kud'i su kuma sun biya buk'atar
su da ita, haka kuma tanada cutar HEPATITIS, dukda cewa
Ana VACCINE (riga kafi) kuma bincike ya nuna cewa gurin
mu'amala da maza ta sami cutar. Haka har a university d'in
su an kamata da wani professor suna lalata, wanda har
yarinyar data kamasu saida mukayi magana da ita Ana
cewa da ita Sadydy, ta tabbatar mana da haka, sabida haka
Shaheed ka hak'ura ka nemi yarinya mai mutunci ka aura,
Amma ban aminta ba kuma bamu yafeba ka auri Ummey.
.
Shaheed zunbur ya mik'e, "Baffa wallahi tallahi sharri ake
mata! Baffa kaima kasan bazan taba yarda nayi soyayyah
da yarinyar da ban aminta da tarbiyar taba.! Baffa gun
mak'iyan Ummey kuka nemi shaidar ta Amma Sam ba haka
bane!, ka ganni nan,nine nasaka aka kori mutumin da ya
mata fyade daga makaranta, kowa yasan fyade aka mata
bayan ya hura mata wata powder mai kashe jiki, sannan ya
mata abinda zai mata, kuma wallhy Baffa HEPATITIS d'in ta
samu tayi a wani wajen ba gun lalata ba, haka samarin da
ake cewa tana kora Ina mai tabbatar maka sabida wannan
museeba data sameta ne yasa suka gudu, Baffa kasan
sakwatawa Allah basa k'arya please Baffa ka...." Katseshi
yayi da cewa ya zauna Amma ya kasa zama saida ya janyo
hannun sa ya zaunar dashi sannan ya zauna fuskar nan
tashi kamar me, ya turnuk'eta sai wani huci yake kamar ya
fito daga filin wasa.
.
"Shaheed bawai ban yarda da duk abinda ka fad'a bane, no
duka na yarda wallhy, hasali nafi yarda da zancen ka akan
duk shedar da aka kawo min, Amma abinda nakeson ka
gane shine, duk macen da zaka Aura kaji zagi ya fito akan
mutuncin ta to gani nake ka barta kawai, sabida wannan
zagin da gorin har jikokin ka yana biye daku, to gani nake
ka hak'ura kawai" "No Baffa wannan nazari naka ba haka
yake ba, idan kuwa har mutum zaiyi aiki dashi, to tabbas
zai dawwama a dana sani ne, kuma bazai taba samun ci
gaba ba, mutumin da ba'a zagi ko zargi ba kowa bane,
kuma ni bazan iya hak'ura ba inason Ummey" "To sai ka
aurawa kanka ita nida mahaifiyar ka duk bamu aminta ba"
Ya kalli mahaifin nasa yama rasa abinda zaice masa dan
haushi, "Nasan duk zancen ku bazai wuce Habeeeba ba, na
muku Alk'awarin zan auri Habeeeba matuk'ar kuka amince
da Ummey, idan na auri Ummey sai na aureta, kai ni Baffa
kawai ma zan auresu tare ne a d'aura auren rana d'aya,
please Baffa Ku amince" Mamanshi da take zaune kamar
bata gurin ya juyo ya kalleta, "Hajiya please kisa baki, Allah
zan auresu duka biyu, Allah inason Ummey," "Ai dole kasota
tunda ta asirceka ta hanyar mayen k'anin ta shekara kusan
uku kullum zancen ka Ummey, Muhammad ba wani zance
sai wannan, to muna gaya maka da babbar murya bada
hannun mu ba, ga arziki na binka kina gudu sai gun wacce
batada daraja a idon mutane" yayi rarrashin su har ya gaji
Amma sunk'i aminta har yayi fushi shima, Amma bazai iya
gaya musu magana ba, sai kawai yace. "Baffa Umma, Ku
iyayenane kuma inason Ku, nasan duk abinda zanso bazai
kai Wanda zaki soni dashi ba, sabida nasan kunfisona akan
kanku, Amma Ku sani ba lallai bane kuso abinda zai zama
ni inason shi ba, dai-dai da rana d'aya banji inason
Habeeeba ba, bawai d'an tanada abin k'i bane," ya d'aura
hannun sa saman k'irjin sa dai-dai gun zuciyarsa yaci gaba,
"Wannan, Zuciyata ce, kuma zuciyata Ummey takeso
batason Habeeeba, soyayyah ta da wata bazata sa na
bijirewa umurnin Ku ba, tunda ba sabon Allah ne kuka
umurneceni ba, zan hak'ura da Ummey sabida biyayyah
gareku.
.
Zan hak'ura da Ummey sabida Ku ka kasance cikin farin
ciki, sabida banason nakasan ce cikin jerin mutanen da
suka fandarema iyayen su akan mace, banason na aikata
kuskuren da Moh ya aikata sabida soyayyah sa ga Sumy
Cillire, dukda cewa nima Ummey itace HASKEN IDANIYA ta
amma bazan taba aikata wannan kuskuren ba, sabida ba
abinda yake biyowa bayan haka sai nadama, na gode da
k'aunar Ku gareni." Yana kaiwa nan ya musu Murmushi ya
bar palon, iyayen suka kalli juna, duk jikin su yayi sanyi
Amma banajin akwai wanda ya sassauto daga cikin su,
haka suka k'are shawarsu akan tunda yanajin maganar su
kuma sunsan bazai tsallake umurnin su ba su aura masa
Habeebar kawai, daga baya zaisota, Habeeeba yarinyar
gwamnan Minna ce, tanason Shaheed kamar ranta Amma
shi bayason ta, duk hanyar ta zatabi tabi Amma yak'i kulata
kuma bai tama mata wulakanci ba musamman yanda yaga
tana hidima da iyayen sa. Bayan Shaheed ya samu ya
daidoto natsuwarsa dan kad'an ya rage yau yayi kuka dan
bak'in cikin abinda ya faru dashi, yanaji yana gani za'a
rabashi da Ummey, baima San yanda zai bulloma abin ba,
daga k'arshe ya yanke shawarar ya gayawa Dady. Haka
kuwa akayi ya shirya yaje sokoto ya sami Dady ya masa
bayanin komai da yanda yayi da mahaifan sa. Dady yace
kada ma ya damu duk abinda Allah yayi dai-dai ne, ya
d'auki wannan a matsayin tashi kalar jarabawar, sabida ba
akanshi aka fara ba, sau da yawa Ana k'ulla Aure iyayen
yara Suki aminta, to ya kasan ce mai biyayyah ga iyayen sa
zai zamo mai nasara akan dukkan Al amuran sa, kuma
Muhammad duk lokacin da kake buk'atar sa zan baka koda
baka auri Ummey ba, Idon Shaheed sun kad'a sunyi Hulu-
Hulu ya rasa mi yake masa dad'i ji yake kamar ya had'iye
numfashi ya mutu ya huta da wannan bak'in cikin. Sukayi
sallama da Dady, yaso yaga Ummey Amma bazai iya ba
Dady ma ya kula da yanayin sa baice masa komai ba kuma
ya tausaya masa wani abin sai iyayee.
.
Tofa Ummey ta dawo zero ba saurayi ko d'aya