Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 14 & 15


MIJIN MARAINIYA PART 14
.
Bayan ta aje wayar ta zauna ta zuba tagumi zuwa cen taga
bacci ya dauki jalal itama kwanciya tayi nan da nan bacci
ya dauke ta lokacin da anty tazo gidan shiru ,tai ta sallama
babu amsa zama tayi afalo ta shiga kiran wayar safna, aza
bure ta tashi ta nufi wayar tasa akunnen ta, anty tace safna
gani afalo, wani sanyi taji azuciyar ta ta nufi falo da sauri
bayan sun gaisa anty tace yaya yace jalal babu lfy ko, yana
Ina safna tace yana kwance ya samu bacci. jeki tasoshi
yasha magani anty ai baya iya tashi bakiga inda ya ragwar
gwabe ba. anty tace muje nagani Suna shiga anty ta fara
tashin jalal yabude ido yafara fadin ummi kaina zai fashi
cikin fada anty tace ya fashe din dan baka da lfy kuma duk
sai kabi ka damu mutane da surutu saikace karamin yaro.
jalal yasake cewa safna kira min ummi.
.
safna hannu tasa ta dauki wayar jalal anty nusaiba tace
safna ajiye wayar nan baza akirata ba idan kamatsu
katashi katafi da kan ka katon banza kawai, haka zaka haifi
yara suga ubansu yana wannan tabaran jalal yace toh naji
tashi ki tafi gida. tace babu inda zani tashi zakayi kasha
magani dan me shagwaba kan bata nan. kalon safna yayi
yamaida idon shi ya rufe daker anty ta shawo kan jalal
yasha magani saida ta dama mai acukali. bayan yasha be
jima ba bacci ya kwasheshi . washe gari jalal yatashi jikin
shi yayi sauki sosai ya shiga bayi yayi al,wala yafito ya fara
tashin safna tashi kiyi sallah. mamaki ne ya kamata ta kasa
daurewa tace yaya kaji sauki ne? daure fuska yayi yace eh.
safna kwashewa tayi da dariya tana fadin Allah yakara
sauki. kara tamke fuska yayi yace to meye abun dariya
kuma, juyawa yayi yana tafiya yana fadin bari nadawo zaki
sani. 12:42 alhaji ya faka motar sa ahabar gidan jalal
awaya yakira shi yace yajiki jalal yace yayi sauki daddy
yaushe zaka dawo? alhaji yace nadawo gani ma akofar
gidan ka mikewa yayi cikin sauri ya bude kofar ya fita , yana
isa ya rugume daddy. har cikin falon alhaji ya shigo ya
zauna jalal yace daddy bari nakira safna. cikin murna tafito
tana yashe hakora bayan ta gaida alhaji bata zauna ba
kitchen ta nufa ta fito da abinci. daddy ya kalli safna yace
wanna fah nida nazo duba mara lfy kuma sai na bige da
cinye muku abin ci safna ta bata rai tace dan Allah daddy
kaci ai shi yaji sauki dama fa mura ce kawai amman duk
yabi ya langwabe harda su kuka. dariya alhaji yayi safna
ma dariya take yi daddy yace jalal wai haka ne kayi kuka?
jalal yace karya take daddy ,ya juya yana hararan safna.
alhaji kalon jalal yayi yace nasan kayi ne jalal idan bakayi
ba bazata fadaba, kaga irin abinda nake fada maka ko?
jalal yayi murmushi yace daddy dandai ba ita bace shi yasa
take fadan haka bata San abinda nakeji bane, kuma kukan
ma ai itama tayi. safna kasa tayi da murya tace amman
aini ban ta kiran sunan ummi ba , duk da tayi kasa da
murya be hana daddy jin abinda tace ba. jalal kuwa filon
dake hannun sa ya wurgawa safna, tare da fadin ina wasa
dake ne.
.
daddy dariya yayi sosai sannan yace wlh jalal ka canza
halinka kai ga son girma kuma ga.... jalal ne yayi wa daddy
alama da hannu karya fada, dan haka daddy yabar
maganar, bayan alhaji yaci abinci yayi musu sallama ya tafi,
tare da dubin farin cikin yadda ya samesu gwanin ban
Sha,awa.
*************
gidan hajiya ya nufa yana shiga yaga ta daure fuska
bakamar daba. bayan ya gaisheta yaji bata kara cewa komi
ba dan haka shima yayi shiru, zuwace yaga ummi tayi
sallama ta shigo ya daga kai ya kalleta , batace mishi komai
ba ta shige dakin hajiya. alhaji yace hajiya zaliha kuma me
takeyi agidan nan? cikin fada tace inaruwan ka da ita dama
jiranka nakeyi kadawo kagayamin abinda kake nufi, tunda
ninayi magana baka dauki maganata abakin komai ba.
alhaji yace hajiya kiyi hakuri bawai nakijin magarnar ki
bane, Ina sone ta gane wani abu wanda shekara da shekaru
ta kasa fahimta. aikoma Meye tunda nasa baki sai ka bari
yanzun bakajin kunyar jalal yaji ka korar mai mahaifiya.
alhaji yace hajiya ai jalal yasan halin ta, shima ba magana
take masa ba , dan ko gaisheta yayi bata amsawa . hajiya
tace me yayi mata shi kuma? duk akan auran nan ne
bansan abin da yasa ba zaliha kwata kwata bata kaunan
yariyar nan. Hajiya ta daga murya takira zaliha bayan tazo
ta zauna alhaji azuciyar shi yake fadin jita kamar mutuniyar
kirki. hajiya tace zaliha zokibawa mijinki hakuri kuma duk
abinda kike kinsani ki gyara halinki. tun anan ta fara bawa
alhaji hakuri , baza yayi da ita bece mata komai ba. hajiya
tace bakaji tana magana ne ko maganar bata wuce bane,
da girman ka inda kuma jalal yayi kace masa me? alhaji
yace to shikena hajiya ya wuce, ki shirya anjima zamu tafi
gida. ummi dadi taji sosai, ta farawa hajiya godiya. Firace
ta barke tsakanin hajiya da alhaji ahirar ta sune ummi ta
fahimci jalal yatare agidan sa, dan taji yana bawa hajiya
lbrin ciwon jalal.
.
basu tashi tafiya gida ba sai yamma, alhaji yace ni nafita
kisame ni a mota . ummi gyalan ta ta dauka tana cikin yiwa
hajiya sallama saiga alhaji da wata mata yar kwaye yana
rike da kullin kayan ta, suna shiga falon matar ta zauna
akasa, hajiya binta tayi ido dan bata gane taba, alhaji ya
lura da haka yace hajiya baki gane ta bane, matar marigayi
yaya musa ce. hajiya tace Allah sarki kiyi hakuri bangane ki
bane, yaya yaran. tace suna lfy yanzun ma bikin salame ne
ya tashi nace bari nazo na fada muku. ummi ji tayi kamar
tasan muryan dan haka tazo har gaban matar, take gabanta
ya fadi tace kamar goggo kishiyar saudatu.
.
godiya agare ku makaranta wannan novel gaskiya naji dadi
sosai ganin jiya kadai banyi typing ba na samu kiran muta
ne da dama, suna tambayar lfy ta nagode sosai ina muku
fatan alheri * Itama matar dago kanta tayi takali ummi
gaban ta yake ya fadi cikin da burcewa take fadi a,a bani
bace, ina ganin dai kama ce. ajiyan zuciya ummi tayi
sannan tace amma ko kamar tayi yawa bayan sun gaisa da
matar ummi ta karayi wa hajiya sallama ta fita tana
waiwayen matar.
.
itama hajiya kara gaisawa sukayi da goggo sanna ta farawa
hajiya bayanin bikin salame ne ya taso nace bari naxo na
sanar lokaci sai kara tahowa yakeyi amman bani da komai
da zan kai mata. hajiya ta nisa tadayi murmushi sannan
tace hanne kenan sai yanzon kika tuna da mune dangin
ubanta, aida cen kin manta damu dan kinga babu idon iya
sai yanzon da matsala ta kawoki? goggo tace hajiya wlh ina
son zuwa kudin mota ma gagara na yake, yanzon ma
mokota nashiga na ranto. toh aishi kenan yanzon wacce ce
zatayi aure , yar wajen kice ko yar wajen amaryar ki? tace
ta wajena ce ai waccen tana gurin dagin mahaifiyar ta.
hajiya tace Allah sarki ai lokacin rasuwan iya tana karama
yanzon nasan itama ta isa aure, me yasa baki turo mana su
, zumun ci fah ba abin wasa bane, irin wannan saika hadu
da naka baka san shiba, niyanzon ba kamar da bane girma
ya kamani . toh hajiya in Allah yarda zanturo su, shiru
sukayi na dan wani lokaci zuwa cen goggo ta kalli Hajiya
tace hajiya wannan matar da suka fita da alhaji wacece ?
.
hajiya tace matar sace. goggo ta sake cewa ya kara aure
ne? a,a itace dai matar sa maman abduljalal , suma basan
zumun cin suke ba, ai inaga ko iya ma bata santa ba bare
ke. haka suka ci gaba da tattaunawa goggo ta tsorata sosai
da taji ummi surukar hajiya ce dan tasan indai asirin ta ya
tonu ta shiga uku, dan haka washe gari goggo na tashi
tashirya tayiwa haji sallama bayan ta hada mata sha tara ta
ar ziki.
.
itako ummi bayan sun koma gida hakalin ta kara tashi yayi
so kawai take taga ta daidaita da iyayen ta dan haka ta
farawa alhaji kuka ya taima keta ya daidaita da iyayen ta
hakuri ya shiga bata ki kwatar da hankalin ki baffa yayi
rantsuwa babushi babu ke tunda kikai silar rabowan shi da
'yar shi har ta mutu basu ganta ba, zaliha nazaci idan baffa
yasan cewa saudatu ta rasu hankalin shi zai kwanta
amman sai naga hankalin shi ya kara tashi, zaliha abinda
na lura dashi babu abinda baffa yake so ayanxon illa yaga
yariyar da saudatu ta haifa. kukanta karuwa yayi tace nima
haka alhaji ina matukar son naga yariyar nasan yanzon ta
girma , kuma alhaji idan nakalli huto yariyar sai naga kamar
na taba ganin hoton. alhajj yace kin taba gani mana tunda
yariyar da saudatu take kama. haka sukaci gaba da ta
tattaunawa akan yariyar saudatu , zuwa cen ummi ta sako
maganar jalal alhaji ashe jalal ya tare shine ko kugaya min
atakai ce yace eh ya tare. ta sake cewa Amman alhaji ya
kamata ace yana zuwa gida ana gaisawa. toh ganinayi
gurin wa zaizo ni bana gari ke kuma ba amsa masa
gaisuwa kike ba, toh me zaizo yayi. toh alhaji komai ya
wuce kabashi hakuri dan Allah yazo gida. washegari da
safe daddy yayiwa jalal waya ya tambaye shi jiki yace yayi
sauki, dan haka alhaji yace idan zaka iya fitowa kazo gida
ummin ka nason ganin ka . toh kawai jalal yace, ya juya
yace safna shirya muje gida cikin sauri suka shirya suka
kama hanya. Suna shiga jalal ya nufi dakin daddy safna
kuwa falo ta zauna tana raba ido. lokacin da jalal ya shiga
dakin ya samu ummi sunata hira da alhaji dan haka
murmushin dake fuskar shi ta ragu, daddy ko murmushi ya
saki yana fadin jalal ka iso. kusa da alhaji yaje ya zauna
bayan ya gaida alhaji ya juya barayin ummi yace ummi ina
kwana.
.
cikin sakin fuska ta amsa tare da tambayan shi jikin shi,
bayan ya amsa ta sake cewa ya safna? dadi sosai jalal yaji
yace lafiyar ta lau tare muke tana falo. alhaji fada ya
farawa jalal yazaka bar ta afalo saikace wata bakuwa jeka
shigo da ita. jalal zuwa yayi ya riko hannun safna suka
shiga falon alhaji bayan ta gaida alhaji ta juya ta gaida
ummi ta amsa ba yabo ba fallasa. ummi kara kallon safna
tayi sosai gani tayi takara cika tayi kyau sosai cikinta harya
fara fitowa, juyawa tayi gurin jalal ta fara janshi da hira
harya fara sakin jikin shi. sai yamma su safna suka bar
gidan su ummi jalal sai washe hakora yake . kwanci tashi
ba wuya gashi har cikin safna ya isa haihuwa suna jiran
haihuwa ko yau ko gobe , komai sun tanada anty nusaiba
na kula da safna sosai dan akai akai take zuwa dubata da
tace ina son kaza anty nusaiba saita nemo itako ummi ta
rage nuna tsanar safna afili jalal kuwa jitake kamar ta
hadiye shi, babu abinda yake damun ummi ayanzo ila
rashin samun yar da saudatu ta bari . safna ce ta fito daga
daki tana fiya daker, har ta isa gurin jalal tana zama ta kalli
jalal dake kwance ya rufe ido, taba shi tayi tace yaya ka
tashi nasan idonka biyu. tashi yayi ya zauna yace safna
nasan maganar muguwar matar nan zakiyi min, ni kuma
bana sojin ko sunanta.
.
safna kasa tayi da murya tace yaya dan Allah kayi hakuri ka
kaini inason naga nima ina da 'y an uwa kamar kowa kaga
ko badan goggo ba kodan yaya iro da salame ai naji . kara
daure fuska yayi yace yan zon kina nufin harkin manta da
wula kancin da mahaifiyar su tamiki toh bazaki ba indai
nine mijinki bazaki wajen wannan muguwar matar ba idan
ma kina tunanin ni zan kaiki toh kima cazan tunani dan wlh
bazan jeba, waima me kike nema awajen su, me kika nema
kika rasa da zaki nace sai kinje wajen su?
.
kuka safna ta fara tace yaya yan uwa nane fa, bani da kowa
fa sai su kara kulewa jalal yayi ya fara magana cikin fada
baki da kowa saisu ko, haka kice ko, ni ma ba komai bane
awajen ki ko, duk abin da ake miki baki gani, kin raina ko?
a,a yaya ba haka nake nufi ba nidai kawai inason naje naga
yan uwa na dan Allah kayi hakuri ka barni naje. Jalal kara
daukan zafi yayi yace wlh safna idan kika kara cemin
'yan,uwan ki saina mareki susan tarajar kine suka wurgar
dake a titi. safna ta kara fashewa da kuka tace yaya gori
kuma kake min? eh ammiki gorin kiyi abinda zakiyi wawiya
kawai mara wayau. safna daki ta nufa cikin matsanan cin
bacin rai taita kuka. shikuwa jalal bayan ya gama fadan
gidan ya bari sai dare ya dawo, ya samu dakin safna rufe
dakinshi ya wuce dan yasan fushi take. Washe gari bayan
ya gama shir yawa ya fito yaga falon na nan yadda yake
yagane safna fata fitoba ji yayi babu dadi a zuciyar shi ya
isa bakin kofar yayi ta bugawa taki budewa hankalin shi ya
kara tashi waryar shi ya ciro ya dannan number daddy yana
dauka ya fara fada mai safna ta rufe daki tun jiya taki
budewa. alhaji yace wani abu ya farune ko kunyi fada ne?
shiro jalal yayi bece komai ba dan ya tuna kargadin daddy
akan safna. Alhaji yace jalal baka da gaskiya kenan, bari
nakira safna. safna dake zaune adaki taci kuka ido duk sun
kunbura taji ankira wayar ta tana dubawa taga daddy ne
tasa wayar akunnen ta tana kuka ahankali alhaji yace safna
me ya faro ne, jalal ne ko, gayamin me yayi miki? kasa
magana tayi ta kara fashewa da kuka. alhji yasake ciwa
jinan safna daina kuka bakisan wannan kukan zai iya miki
ila ba, tashi maza ki shirya ya kawaki koma me yayi miki
zanyi maganin sa, kinji ko. jalal na zaune amota safna ta
fito ya kalli fuskarta yaga tayi jawur saboda kuka dogowar
rigace jikinta da hajjab madaidaici .
.
suna isa ta bude motar ta fita , ta samu alhaji shida ummi
afalon ummi ta mata wani irin kallo, zamatayi akasa ta
gaida su, suna cikin amsawa jalal ya shigo alhaji yace kai
jalal baka da hankali ko, waya gaya maka ana tayar ma me
ciki da hankali? shiro yayi yanemi guri ya zauna. Alhaji ya
kara cewa ina murna zan samu takwara ko mata zaka
mana sa... be karasa maganar saba ummi tace Allah ya
kiyaye karku sake kusa sunana dan ni ba sa,ar wasan ku
bace asa mata sunan uwar ta amman bani ba. safna ta
daga jajayan idanun ta, ta kalli ummi ta fashe da kuka, tare
dajin matsanan ciyar tsanan ummi azuciyar ta . alhaji yace
zaliha tashi ki bamu guri tunda ke ba,a magar hakali dake.
tana tashi alhaji yace safna gayamin me jalal yayi miki?
Cikin dashashiyar murya ta gawa alhaji abinda ya faru.
alhaji yace ah ah jalal yayi laifi sosai toh kai jalal banda
abinka haka akeyi ba yafiya, tunda tace tanason ganin su
aisai kayi hakuri ko baka so kabarta taje, itama ta hakura ta
yafe bare kai. sai alokacin jalal yayi magana daddy ai itama
dan bata da hankali ne shiyasa ta yafe. murmushi alhaji
yayi yace jalal ai wannan abinda tayi shine hankalin abun
da kawai ban yadda tashi ba tafiya da ciki dole kiyi hakuri
har ki haihu nida kaina zan sa akai ki, kai kuma ka kiyaye
bakin ka inrai ya baci hankali baya gushewa, haka alhaji
yayi ta musu nasiha sannan yace kutashi kuje gida. tana
mikewa jalal yace zomuje muyiwa ummi sallama haka
safna tabi bayan shi badan ranta yaso ba. sun sami ummi
zaune abakin gado tayi ta gumi jalal yace ummi zamu tafi
tace ku gaida gida safna ta juya zata fita ta daga kai taci
karo da tangamemen hotun iyayen ta tana rike ahannu su,
daga hannun ta tayi sama tana nunawa jalal , yaya kallah
bata karasa ba jalal yaga tana kokarin faduwa
.
MIJIN MARAINIYA PART 15
.
Da sauri jalal ya tare safna ta fada jikin shi, ganin inda
safna keta nuna hoton yasa ummi ta zaro ido ta mike tazo
kan safan tana fadin kar dai ace safna yar saudatu ce, jalal
be saurari me ummi take fada ba kiran sunan safna kawai
yake amman shiru babu amsa ummi ce ta lura jini na zuba
ta kasan safna da gudo ta fita tana fadi alhaji dauko mota
safna babu lfy . da ummi da jalal ne suka kinkimi safna
suka sakata amota, jalal ya fita haiyacin shi ummi ko kamar
mahaukaciya sai fifita takewa safna da gyalen ta, bayan
sun isa asibitin aka shiga da safna ciki jalal yaso ya shiga
suka dakatar dashi. Komawa gefe yayi amman ya kasa
tsayuwa guri daya sai naushin hannun shi na hagu yake da
hannun shi na dama. ummi kuwa tunani ne ya dame ta dan
haka ta matsa kusa da alhaji tana share zufa tace alhaji
kasan abin da safna ta gani ta shiga wannan halin, hoton
saudatu ta gani. da sauri alhaji ya mike ya cire hular sa ya
fara fifita da ita ya na zaware kamar yadda jalal keyi, ummi
ta mike tabi bayan shi tana kokarin magana alhaji ya
dakatar da ita karki ce komai kibari muga lfyr yarinya
tukuna. komawa tayi ta zauna zuwa cen ta sake mikewa.
daga cen su kaga an turo kofar Dr sulaiman ne ya fito
dasauri alhaji yabi bayan shi, jalal ma mikewa yayi amman
alhaji ya waigo yace koma jalal. bayan ya shiga Dr
sulaiman yace alhaji haihuwa ce sai dai muna tunanin
yariyar bazata iya haihuwa dakan ta ba sakamakon jinin ta
ya hau sosai saida kuyi ta mata andu,a . haka alhaji ya fito
jiki babu kwari jalal ya mike yace daddy mutuwa tayi. a,a
jalal tana nan daran ta haihuwa ce amman jalal kayi ta
mata andu,a Allah ya rabasu lfy . jalal be yadda da abinda
daddy ya fada ba dan haka ya fara share hawaye. alhaji
yakira anty nusaiba yagaya mata halin ta suke ciki nan da
nan saiga su ita da matar baba salisu suna rike da kayan
baby ganin ummi agurin abin ya basu mamaki. 2:46pm
sukaji safna tayi kara mikewa jalal yayi zai shiga anty ta
rike shi ta bude baki zatayi magana suka sake jin wani ihun,
wannan karon sai da alhaji yasa hannu suka iya tare shi,
yana fadi daddy kuka fah takeyi haka sukai ta bashi baki
juyawa yayi ya fita yasamu wani dan dutse ya zauna yata
share hawaye. yana zaune agurin anty ta fito da gudu tana
dariya jalal albishirin ka. mikewa yayi yana kokarin share
hawayen shi yace anty ta haihu ne? Jalal mu godewa Allah
safna ta sauka lfy mun samu yan biyu. jalal ya zaro ido
yace anty da gaske cikin sauri ya nufi ciki ya same su alhaji
sai dariya suke alhaji ya dafa jalal yace jalal kuka ya kare
ko?
.
kunya ce ta kama jalal yayi kasa dakai yana murmushi
yace daddy wai da gaske yan biyu ne? alhaji yace 'yan buyu
ne jalal mace da namiji kana mamaki ko, ikon Allah kenan.
bayan angama gyara jarirai aka basu damar shiga ummi ce
kan gaba tana shiga ta sauke idanun ta akan safna da sauri
ta rintse ido gurin ta ta nufa takira sunan ta taji shiru, alhaji
yace zaliha kirabu da ita kila bacci takeyi daidai lokacin
nusaiba ta dauki macen takalle ta sannan tamikawa alhaji
tace yaya ga matar ka ta juya zata dauki dayan ta ganshi
hannun matar baba salisu haka suka taro suna kallon yaran
gwanin ban Sha,awa. Shiko jalal gurin gurin matar sa yake
son zuwa amman ummi tana jikin gadon dan haka ya kasa
zuwa wajen. alhaji ne yace jalal yanaga ka koma gefe kazo
kaga yaran mana. sosa kai yayi ya kalli safna yace daddy
ina zuwa. alhaji ya fahimce shi yace kazo ka gansu mana
safna ai bacci take. da saurin sa yace daddy ba bacci take
ba idon ta biyu. sai da alhaji ya kalli safna sannan yace
zaliha fito daga nan gurin. cikin sauri ummi ta fito daga
gurin duk arude take so take kawai safna ta tashi . Jalal
yana isa gurin ya duka yanawa safna magana cikin kunne
zuwa can ta fara magana ahankali cikin kuka, jin safna na
kuka yasa duk suka maida hakali gurin su, amman basajin
me suke fadi, jalal ya dago hankalin shi atashe ya kalli
ummi ya hada rai. ummi ta tsargu tace jalal me safna tace
maka. yi yayi kamar beji ba ya mikawa alhaji hannu ya
bashi yaran ya kure su da ido. lokacin da aka sallame su
,alhaji yace awuce da ita gidan hajiya motan jalal ta shiga
su anty nusai ba ma haka.
.
hajiya ta tare su da murna nusaiba ta mika mata yaran ta
kalle su tace ikon Allah ga jalal ga safna , hajiya fatima ta
shigo rike da safna ta zaunar da ita akan kujera jalal ma ya
shigo dauke da kaya ya ajiye agefe hajiya ta kalli jalal tace
yaya haka kuma jalal menene haka kaida ka samu karuwa
kuma menene naka na hada rai, ta kalli safna tace au kema
kuka kikeyi toh abin naku bana lfy bane anty tace jalal nima
nakula akwai abun da yake faru har anty zaliha ma akwai
abun da yake damun ta ko kallon yaran batayi ba hajiya
tace tunda sunki mgn ku kiramin alhajin har zalihar ,wannan
ai iskanci ne Allah yayi muku kyauta kuzo kuna tur bune
mana fuska. suna cikin haka alhaji ya shigo ummi na bishi
abaya hannu ta rike da wanan huton. bayan sun zauna
hajiya tace nifa kun sani aduhu wai me yake faruwa ne?
alhaji yace hajiya wani babban al,mari ne yake shirin
faruwa ya karbi huton ahannu zaliha ya mikawa hajiya yace
wannan haton safna ta gani kawai sai gani sukayi ta fadi
shine muke tunanin ko ta sansu ne . hajiya kallon huton tayi
tace wannan ai musa ne. alhaji yace hajiya wani musa
kuma ? tace musan iya mana ko kana nufin baka gane shi
bane. alhaji kallon huton yayi sosai yace innalillahi wa,inna
ilaihir raju,un Safna na daga gefe kuka kawai take murya
hajiya taji tana fadin safna kinsan musa ne? cikin dashewar
murya tace babana ne. hajiya ta zaro ido a,a safna ko dai
kama suka miki wannan fa dan yayata ce uwar mu daya
uban mu daya, yanzun nan kina nufin ke jikar iya ce. cin
kuka tace eh. kowa afalon gumi ne yake karyo mishi itako
ummi hankalin ta yafi na barawo tashi. hajiya ta share
zufan da ya karyo mata tace ke zaliha Ina kika samu
wannan huton ? jalal najin anyi ma ummi wannan
tambayan ya fita afalon dan yanajin kunyar abin da ummi
tayi. cikin kuka tace hajiya wannan matar itace kanwa ta da
nake baki labari, zaro ido safna tayi ta mike tace ummi kina
nufin kece yar mahaifiyata, ina wlh wlh bazai wuyo ba gara
naga mutuWA ta da naga wannan ranar.
.
Anty nusaiba ta kama safna ta zaunar da ita tana fadin
safna ki natsu mana baki san jikin ki babu kwari ba ne.
safna tace anty ni ki sakeni tafiya zanyi wlh bazan zauna
ba. kowa afalon share hawaye yake sautin kukan ummi
kawai kake ji.
.
alhaji yayi gyaran murya yace safna zo ki zauna, batayi
musu ba kusa da hajiya ta zauna , hajiya ta kalli safna tace
tabbas biri yayi kama da mutun lokacin da hanne tazo gidan
nan zaliha ta tambeye ta amman sai tace ba, ita ba ce,
kuma nima na tambaye ta ina yar da kishiyar ta tabari sai
tace min tana gurin dangin mamar ta , hajiya ta nisa takara
cewa toh me hanne take nufi da haka. alhaji ne ya dago
yace hajiya ga dalilin ta nan bata san inda yarinyar take ba
kame kame take tunda su tace musu tana gun dangin baban
ta ke kuma ga abinda tace miki. hawaye ne yake zuba
afuskar hajiya tace amma ko indai haka ne ni kaina naci
amana, dan tun lokaci da aka ma iya aure da baban musa
dangin mu duk suka guje ta saboda mijin da ta aura bame
karfi bane babu me zuwa inda take sai ni dama mu biyu ne
mata sai yayyen mu maza guda uku haka in naje iya zatai
ta min korafin ita ba me zuwa gurin ta, nice me lallashin ta
har sai naga hankalin ta ya kwanta, ana cikin haka nima
aka aurer dani, tun daga lokacin ban sake zuwa garin ba sai
da iya ta haifi musa mijinta dakan shi yazo ya fada balefi
dagi sunje tun daga sunan musa ban sake zuwa ba sai dai
ita tana zuwa gida na akai akai dan haka ban cika damuwa
ba ,dan bata rufe wata bata zoba haka muka ci gaba da
tafiya sai dai rashin lafiya ko wani babban abu muke zuwa
gurin ta duk da cewa ita ko da yaushe tafe take, kuma duk
wani Sha,ani sai dai in bataji ba, ko koma bata da lfy bana
mantawa zuwan ta na karshe gidan nan nasiha tai tamin
akan zumunci ko sati daya ba,ayi ba mukaji lbrn rasuwan
ta kuka ne yaci karfin hajiya ta jawo safna tana fadin naci
amanar iya. safna lafewa tayi jikin hajiya tana kuka hajiya
ta dafa kan safna hawayen ta na diga jikin safna tace safna
ki yafe min nina saka ki a halin da kike ciki da ace sanda
nazo gaisuwar iya na dauke ki da haka be faru ba, ninayi
tunanin hanne zata hada da nata tarike, sai nake ga kamar
idan idan aka dauke ki zata ce annuna mata banban ci ,
bansan cewa bakin hali gareta ba. safna kara rugume
hajiya tayi dan ita duk wani abu da yashafi iya gir mamashi
take kuma ai tun haduwan ta da hajiya na farko bata nuna
mata tsana ba, kuma bata taba nuna mata babbaci tsakanin
ta da jalal da yake jikan ta ba, dan haka hajiya da 'ya'yata
sun gama mata komai tun da sun sota alokacin da basu
san waye ita ba, dan haka ta dago ta fara sharewa hajiya
hawaye da hijjabin ta. ummi ko tana cen gefe uwa kazar da
aka tsamo ta daga cikin ruwa. anty nusaiba ce ta katse
musu shirun ni dama tunda naga safna sai da naji ta a
raina, take naji son ta ya kamani ashema 'yata ce. alhaji
yace ai irin abin da nake gayawa zaliha kenan yazun gashi
inda abu ya koma, yanzon me zakice wa yarki safna.
.
Ummi kuka kawai take ta kasa cewa komai, ana haka
jarirain suka soma kuka anty nusaiba tace safna tashi muje
kiyi wanka kiba yaran nan nono, kamar jira take ta mike ta
shige dakin hajiya. bayan anty ta gama gasa mata jiki suka
fito ta sanya kaya ta haye gadon hajiya ta kwata anty tace
safna ba kwanciya zakiyi ba kibari yaran sudan ji dumin
jikin ki mana. anty nifa nagaji bacci nakeji. ban ga ne kin
gaji ba me kike nufi ko kallon yaran nan bakiyi ba fah . anty
ni bana so akai ma ummi ta rike ai su bazata ce basu da
dangi ba. anty kallon safna tayi tace karki haka safna yaran
nan basu suka miki laifi ba, zadai kidau hakkin sune kawai,
ai irin haka jalal bazaiji dadi ba. ai ni dama banson yaji dadi
duk wani abu da ya shafe ummi ban son shi me sonshi ma
bana son gani wani sabon kuka ta saka tace anty dan Allah
ku sa shi ya sakeni wlh bana son shi ko ganin shi bana
sonyi. anty tace inalillahi wa,inna ilaihir raju,un kar ya kike
safna kina son jalal, kar ki yadda laifin ummin sa ya shafe
shi dan baya goyan bayan ta suna cikin haka hajiya fatima
tashigo da yaran ta daura macen jikin safna tace bata nono
tasha sai kuka takeyi. safna kallon yariyar tayi take taji son
ta ya kama ta amman tana bakin cikin kallon wani abu da
shafi ummi dan haka ta fara kuka, hjy fatima tace safna
bata mana. sukuyar dakai tayi ta rufe ido, anty tace ai tace
bazata basu nonon taba. hajiya fatima ta bude baki zatayi
magana su kaga jalal ya shigo bece komai ba illa mika
hannu da yayi hjy fatima ta saka mai na mijin ya sake cewa
bani dayar batayi musu ba ta daukota ajikin safna tamika
mai juyawa yayi ya fita.
.
yana fitowa ya samu ummi makure taci kuka har ta gaji ya
tsuguna ya mikawa ummi yaran yace ummi gasu safna
tace bazata basu nonon taba. cikin tashin hankali ummi ta
mike, dakin ta nufa ta samu safna ta kifa kai tana kuka
ajeye yaran tayi abayan safna ta tsuguna tarike kafar safna
tace safna dan girman Allah kiyi hakuyi kiyafe min, nasan
na tafka babban kuskure nayi nadaman abin da na ai kata
safna ina cikin wani hali, dan Allah ki tausa yama yaran
nan, haka ummi taita magana safna batace ta komai ba ga
yaran sai faman kuka suke, gani tayi safna bazatayi
magana ba ta mike ta fita zuwacen sai gasu da alhaji .
alhaji na shigowa ya zauna akan wata kujera dake gefe
yace safna wannan hukuncin da kika dauka yayi tsauri da
yawa ni bance karki nuna fushin ki ba, amman inason
fushin ya tsaya akan zaliha ka dai, ya sake cewa safna
indai kin daukeni uba agare ki toh na umarceki da ki dauki
yaran nan kibasu nono. cikin sauri tasa hannu ta dauke
mace dan ita ke kuka na miji har yagaji yayi bacci, daddy na
kallon safna sai ciki cikin rike yarinyar take, yajuya yace
zaliha tashi mutafi gida. suna fita falon alhaji yace nusaiba
je ki nuna mata yadda zatayi, alhaji sallama yayi wa hajiya
suna fita suka samu jalal awaje ya hada kai da gwuiwa