RABO NA CE PART 12
RABO NA CE PART 12
.
Suna tafe yana mata hira dan ta saki jikinta har suka isa
gida, ita har wani kunyar Dady takeji, to Ina ta sami cutar
ita kam abinda take tunani kenan har suka isa gida, Dady ya
musu bayani komai anata jajantawa.
.
*****
"Uncle Shaheed ni banga tana kwance ba, kawai munje
asibiti likita yace wai hy patatos take dashi, ni kuma ban
san wani hy patatos ba, kuma bata rame ba saidai tana
kuka sosai, kai kasan ciwon hy patatos?" . Muhammad ne
yake yiwa Shaheed bayani a waya. "OK Muhammad nima
ban gane abinda kake nufi ba da hy patatos, Allah ya 'kara
mata lafiya ka gaidata" sukayi sallama, Tun daga ranar da
sukaje asibiti Mahbuob bai k'ara kiran Ummey a waya ba.
Da yake ta daina zuwa makaranta na d'an lokacin so bata
had'u wa dashi, k'arshe dai tace bari taji ko lafiya, tunda bai
saba mata haka ba, ta kirashi amma sai yak'i d'auka, sai ya
mata SMS yace. "Ummey kiyi hak'uri, nasoki kuma naso
ace kin zama second wife d'ina Amma gaskiya bazan iya
auren ki da wannan mummunar cuta ba! So Ina ganin mu
hak'ura da juna yafi, Allah ya sadamu da alkhairi." ta dad'e
tana karanta sak'on nashi tana zubar da hawaye, wato
sabida ciwo yake gudun ta. har zata masa reply tamasa
bayanin cutar, ta gaya masa cewa Ana iya mata riga kafi,
sai kawai ta shareshi, ta nunawa Anti Najma, Najma tace
tamasa reply da ta gode Allah yasa hakan shi yafi zama
alkhairi.
.
Sun koma asibiti Anyi VIRAL LORD d'in, result sai wani wata
zai fito. Haka aka matsa mata ta koma makaranta, bada
son ranta ba ta koma. Tunda ta shiga skull jikinta ya mutu
ta rasa mi yasa taji hakan, batayi gigin bin hanyar office
d'in su Mahbuob ba, sai kawai ta zagaya, tana fatiya suka
had'u da gul -gul uwar gulma. "Ummey Ibraheem kwana
biyu Shiru, mun d'auka ma bikin ne akayi" Ta fad'a tana
washe hak'oranta kamar delewa (WADACE na bingel )
Ummey ta kalleta, "Ba'ayi ba Soon insha Allah dai za'ayi
auren" "Laaa shine ko a gaya mana? Waye gwanin? Dr
Mahbuob ko Prof Dan jumma?, ranar naga yana miki
magana kila ya kyasa," ta fad'a tana kanne ido, "Sadydy
waye Dan juma kuma?" "Lallai har kin manta dashi ranar fa
na ganku kuna hira" Zare ido Ummey tayi "Hira dawa
Sadiya?" "Hummmm share kawai, inaga ban gani da kyau
ba, yanzu waye gwanin ?" Ta kalleta kawai tace
"Muhammad sunan shi" Haka suka rabu tana mamakin
gulma da sa ido irin na Sadydy, yarinya kamar Yar aljannu
duk abinda yake faruwa a dan fodiyyo a idonta ne. kamin ta
isa ajinsu, ta had'u da wannan lecture d'in sai lokacin ta
gane wanda gul -gul take nufi, ita miye had'inta da shi
oho.....
.
Bayan wata biyar.. Abubuwa sun faru inda Ummey yanzu
take soyayyah da Shaheed sabida kasawa da Muhammad
yayi ya tsare, Suna soyayyah kullan sai aikin baiwa
Mujaheed hak'uri takeyi Amma Ina ya nace. Su Ummey sun
dawo daga bauchi gurin sunan yayar ta Ummul-khairi
wacce ta haifi twins, yaran son kowa k'in Wanda ya rasa,
yaran kwakwawan gaske dasu, sabida tsaninin birgetan da
sukayi, yasa taji itama tanason tayi Aure ta haihu,
musamman ma ganin yanda Shaheed ya sakata gaba da
zancen Aure, suna isa gida ko hutawa batayi ba tayi shirin
zuwa makaranta, sabida sunada wani hatsabibin test
wanda tasan idan batayishi ba to C.O ya tabbata akan ta,
haka da gajiyar tafiya ta wuce makaranta, tayi test d'in ta
lafiya, dama cikin mota kamin su iso tayi karatunta so abin
yazo mata da sauk'i. Bayan sun fito tayi karo da Prof d'an
jumma, yayi tsaye yana kallon ta har tayi nisa sai kawai ya
kirata "Ummey Ibrahem" Ta waigo ta amsa dawowa tayi
tazo gurin sa, sabida da ganin sa babban malamaine.
.
Tana zuwa ya aiketa guraren library, bata k'i tafiya ba
Amma abokan tafiyarta sun wuce abinsu, Najma ce kawai
ta tsaya jiran ta, Taje gurin daya aiketa amma bata gane
ba, ga gurin tseet ba kowa saida takai k'arshen gurin ta
joyo zata fito kawai sai taga Prof d'an jumma gaban ta,
"Sorry sir ban gane gurin ba," "Tnx Ummey nagode mu
shiga ciki na baki Abu ki kaiwa Anti Najma tana jiran ki
wajee," Jin ya anbaci sunan Anti Najma yasa ta biyoshi,
Amma har ga Allah tad'an ji tsoro kadan dan guraren ba
kowa, sun shiga ya tsaya dube duben k'arya, jin kawai tayi
k'ofa ta rufe da kanta kuma an saka key, ta juyo ta kalleshi
watso mata murmushi yayi, "Ummey tun ranar dana fara
ganin ki Allah ya saka min matsananciyar sha'awar ki a
cikin zuciyata, nayi kokari na danne Amma na kasa, shine
nake son ki bani had'in kai please" d'ago kai tayi cikin
mamaki da tsoro Amma ta kasa magana, Sai kawai ta fara
kiran sunan Allah cikin ranta. Da yaga tayi shiru batace
komai ba, "Kin amince kenan Ummey" Gyada masa kai tayi
alamar A'ah, tasowa yayi ya fara cire kayan jikinsa ita kuma
tayi gurin k'ofa da gudu tana kuka tana bubbuga k'ofar
Amma Ina, ba Wanda zai jita wani Abu ya d'auko cikin wata
drowa yazo ya ya bud'e ya hura mata, yana hurawa da
sauri a shige wani d'aki sai kusan minti biyar ya fito tayi
kwance ba abinda take iyayi sai hawayen da suke bin
kumatun ta, ya d'auke ta ya shiga da ita ciki ya shinfidar da
ita ya cire mata kayan jikinta tsab, Saida ya k'are kallon ta
sannan ya fara sarrafata son ransa, a haka har ya a kawar
mata da budurcinta, ba abinda Ummey ke aikin sai zubar
da hawaye bata ko motsi, ga zafin abinda ya mata gashi ya
kashe mata jiki da wannan abin.
.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
.
Bayan ya k'are abinda zaiyi ya maida tufafin sa ba ko
tsoron Allah bare tausayi a zuciyar sa, ya tsaya kallon ta.
Shi kadai yasan mi yakeji, farin ciki fall a zuciyarsa tunda
ya biya buk'atar sa, sannan ya saka mata tufafinta, tana
kwance sai hawaye suke gangaro wa a idonta sabida har
yanzu jikinta a mace yake, na Wannan abin daya hura
mata, bayan ya saka mata kayan ya tsaya yana kallon ta
wata sha'awar ya k'ara ji sai kawai ya hauni kissing d'in ta
ya gaji Dan kanshi ya bari. Tunanin sa d'aya yanda zai fitar
da ita daga office d'in ba tare da an ganshi ba, ya fito ya
lellek'a waje ba kowa a gurin, gashi yamma tayi, haka ya
tallabota saman kafad'arsa ya fito waje da ita, ya sami
wani lungu da ba kowa ya ijiyeta, har zai bar gurin sai yaji
hayaniyar yan mata da dariya, duk da ya dad'e a harkar ya
dad'e yana bata yan mata wasu da son ransu wasu bada
son ransu ba kamar yanda yama Ummey, ya rud'e ya fara
dan barwa, su Sadydy ne da k'awayenta ba Wanda yaga
Ummey sai Sadydy wani ihu ta saka ta kalli prof d'an
jumma. "Mi ka mata!?"
.
Ihun ta ya janyo hankalin sauran yan matan da suke tare,
d'an jumma kuwa ko kallon su baiyiba ya wuce da sauri ya
shiga motar sa yabar makarantar, Sadydy da sauran yan
matan ne suka taimaka suka d'auke ta dukan su sun gane
abinda ya mata musamman sanin halin sa a makarantar
kuma ank'i a mishi magana, suna fitowa suka had'u da
Najma tana neman ta, nan suka mata bayayin halinda suka
same ta, wani matsanancin kuka Najma ta saka tana kallon
Ummey, Jikin ta ya mutu na ganin yar uwarta cikin wannan
halin, Haka tayi kama kama itada su Sadydy aka samu
napep suka shiga sai gida. 57 Suna isa gida Najma tayiwa
Mumy bayanin abinda ya faru, Mumy da bata kuka gaban
yara sai ta shiga d'akin ta, yau sai gata gaban su ta kece da
wani irin kuka, duk Wanda ya tambayi Najma a cikin yan
uwan su maza, sai ta kasa yi musu bayani, dai-dai lokacin
Dady ya Shigo aka masa bayanin abinda ya faru gaba daya
gidan ya hargitse, su mazan basusan mi yake faruwa ba
kawai sunyi jugun jugun manyan ne ma da sukazo aka
musu bayani, hatta Dady saida ya chanza kala, kamar zaiyi
kuka dan bak'in ciki, wannan wace irin rayuwace ace
malamai suna yiwa daliban su fyade, Anti Najma ta kira
yayar su Ummul-khairi ta mata bayani, koda ta k'are ta juyo
taga Muhammad tsaye ya kafa mata na mujiya yana kallon
ta. Sai guraren isha Ummey ta d'an jita dai-dai, Anti Najma
ta taimakamata ta shiga wanka, Wani matsanancin kuka
take Wanda ba hawaye ko digo d'aya a idon ta, wai itace
take wankan janaba batare da tayi Aure ba, wannan bala'in
dame yayi kama. Ta dad'e a bayin saida Anti Najma ta
bubbuga k'ofar sannan tayi d'an sauri ta fito, tayi sallah
dagyar, jikinta duk yayi tsami.
.
"Hajiya wallhy ni bazan bar wannan mutumin ba," Dady ne
yake cewa sai yayi k'arar prof d'an jumma, Mumy tana
hanawa, "Abinda zaka kula idan ma munyi k'arar, na farko
mun tonawa Yar mu asiri ne, na biyu banajin za'a d'aukar
mana fansa, idan ma an d'auka wallhy baya wuce ace sai
ya Aure ta, to kaga gara kawai mu binne maganar nan
Dady" Wani gwauron numfashi yaja ya sauke, "Wato Hajiya
Al amarin kasar nan yana d'aure min kai, yanzu fa mutumin
nan ance ya dad'e yana aikata haka, kuma school
authorities sun san da hakan Amma kinji ba abinda sukeyi
akai, kuma wannan ibtila'in yana faruwa a gurare da dama
cikin k'asar nan, fyade fyade kakeji, amma ba wani mataki
da ake d'auka sai d'aid'ai ku, Amma nidai gaskiya sai nayi
magana, kuma sai an d'aukar mana fansa akan wannan
mutumin" "To Dady tunda haka ka zaba sai kayi k'arar,
Amma nidai da za'abi shawarata da zance a hak'ura ne
kawai Allah ya d'aukar mana fansa akai" ta fad'a tana share
k'wallan idonta. Haka dai suka rik'a tattaunawa daga
k'arshe Dady ya hak'ura akan Allah ba azzalumin kowa
bane. 58 Wayar Ummey ce tayi k'ara, Shaheed ne yake
kiranta Amma ta kasa dagawa, har ta tsinke yayi ta kira
tak'i d'auka sai ya kira Muhammad d'in sa. "Hello Uncle
Shaheed" cikin shauk'i yake masa magana, "Ohhh my broo
miss u, Ina Anti Ummey take ne, na kira bata d'auka ba, ka
kaimata wayan yanzu kaji broo na!" Muhammad yayi Shiru
chan yace "Kasan miye? Ni naga Sister Ummey tana ta
kuka mai hawaye, kuma kowa yayi tagumi harda su Dady,
Mumy fa hadda kuka tayi d'azun Ina tsoron naje ta dakeni,"
"Subhalallahi" ya fad'a da k'arfi. "kuka kuma? Ko rashin
lafiyar ne ya motsa munyi waya da ita fa d'azu tace zata
shiga test idan ta fito zata kurani mi ya sameta kuma daga
lokacin Muhammad??" "Na gaya maka nima bansaniba
kawai naga Anti Najma ta shigo da ita, sabida ko tafiya ma
bata iyayi, kuma naga Mumy na kuka Dady yayi tagumi, sai
kuma naji Anti Najma tana waya da Anti Ummul-khairi tace
wai an mata ko minene sunan abin na manta sunan abin da
tace an mata." "Muhammad please ka tuna ka gaya min mi
ya sami Ummey na!!!" Muhammad yayi Shiru yana tunani,
"Wallahi Allah Uncle na manta mi ta fad'a ko na tambayo
maka Anti Najma ne?" Shaheed shiru yayi, har zaiyi magana
sai Muhammad ya katseshi, "Yauwa Uncle na tuna, kamar
fade ne ko fide, inaga..... .
.
Da k'arfi Shaheed ya dakatar dashi... "What Muhammad??
fyade??? How? When? who? Were??.... " Muhammad zaiyi
magana sai yaji ya kashe wayar, Shaheed daga tsaye yabi
bango har ya tsuguna yana wani irin numfashi da huci da
k'arfi. "Waye wannan ya mini haka Ummey na? miyasa ke
Ummey? Miyasa aka min haka? Wanene ya keta miki hadda
Ummey na! Wallahi sai na d'auki fansar ki akan ko
waye....!!!" .