Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 12

MIJIN MARAINIYA PART 12
.
Ummi kalon jalal tayi cike da mamaki batace komai ba illa
dafe kanta da tayi ta koma ta zauna jabar. alhaji kuwa
ajiyan zuciya yayi tare dayin hamdala azuciyar shi, kallon
jalal yayi yaga duk yabi ya rikice sai kace mara gaskiya
alhaji yace ni abinda nake son na sani shine yaya akayi
safna tabar dakinka bayan tun randa aka daura aure aka
kaita dakin ka? jalal ya bude baki zaiyi magana ummi tai
sauri tace alhaji yariyar ce, alhaji be bari ummi ta karashe
maganar taba yace ba dake nake ba ki rufemin baki, jalal
ina sauraran ka? cikin en ina jalal yace ai tun ranar tabar
dakin. alhaji yace saboda me? jalal juyawa yayi ya kalli
ummi yasa ke dukar dakai. alhaji ma kallon ummi yayi yace
toh toh na fahimta jeka abinka. da sauri jalal ya shige dakin
sa dan dama ya kosa ya bar wajen. yana shiga daki alhaji
ya farawa ummi fada zaliha al,amarin ki ya fara bani tsoro
dama nalura da take taken ki baki son auren jalal da safna,
yanzun saboda Allah zaliha abinda kikayi kin kwauta kenan,
akaiwa yaro amarya kije ki raboshi da ita dan dai ki lalata
masu farin cikin su, toh gashinan Allah yanuna miki iya
karki dan yanzun nusaiba takira ni take gayamin safna ciki
gare ta, ni abinda yake daure min kai wai me yariyar ta mike
da har kike neman ki raba su? shiru ummi tayi tana dafe
dakai idon ta a rufe. alhaji yace toh bari kiji karki kara gigen
raba musu aure dan idan har auren su ya mutu kema naki
zai mutu, mahaukaciyar banza mahaukaciyar hofi. da sauri
ummi ta bude idon ta da sukayi ja takalli alhaji tunda take
alhaji betaba fada mata bakar magana kamar nayau ba. shi
kuwa yana gama maganar sa yayi waje, ko sallama be
mata ba.
.
ummi tana son ta zubar da hawaye amman ta kasa ashe
kuka ma rahama ne, jitayi duniyar na juya mata tun daga
nan bata kara sani me ya faruba. jalal ne ya fito ya same
ummi cikin ma woyacin hali kinkiman ta yayi ya nufi motar
sa da it a. bayan sun isa asibiti aka mata yan gwaje gwaje
suka tabbatar wa jalal jininta ne ya hau sosai sun so
sukwatar da ita amman taki yadda, dan haka suka bata
magun guna suka koma gida. jalal dakan sa ya bata magani
tasha sai da yaga tayi barci ya koma dakin sa. ya koma
daki da tunani kala kala azuciyar shi yana son yaje ya duba
jikin safna kuma baya son yabar ummi. har dare jalal be fita
ba sai zarya yake dakin ummi, zuwa cen yaji da wowan
alhaji dan haka ya shirya ya fito da nufin tafiya gidan
hajiya. dakin ummi ya fara shiga ya same ta zaune ta fito
wanka neman guri yayi ya zauna yace sannu ummi ya jiki?
Waigo wa ummi tayi tace tashi ka fita kabani guri dan iska
kawai, na barwa safna tunda ka zabeta akai na ,kai dadi
mata har ace ina cikin gidan nan kuka maidani baho.
tsugunawa yayi ummi dan Allah karkiyi min haka kiyi hakuri
ummi gani nayi mata tace. au zakaci gaba damin rashin
kunyar ne, ai gara kanuna min ka girma, saida nagama cin
kashin ka da fitarin ka, ni bazan ma baki ba amman karka
kara zawa inda nake niko ganin ka bana sonyi. da sauri jalal
ya mike yace ni ummi baki son ganina, me nayi miki da zafi
haka, kuka ne ya kwace masa, amma duk da haka be bar
maganar ba, sake cewa yayi ummi anya kuwa ke kika
haifeni? ummi tace au mamaki kake yi ai dan ma bagida na
bane da koran ka zanyi. jalal ya fara share hawaye yace toh
ummi nagode da saurin sa yabar dakin. dakin sa ya koma
dan bazai iya fitaba yana shiga ya sake kuka kamar
karamin yaro.
.
safna kuwa tun bata damu da rashin zuwan jalal ba, har ta
fara tunanin meye ya hana shi zuwa.gani tayi har dare yayi
ta zauna tayi tagumi, gurin karfe 8:30 mijin anty nusaiba
yazo daukan ta. safna tace anty tafiya zakiyi? anty tace au
da kin dauka kwana zanyi toh ko na kwana ne? cikin shirin
kuka tace a,a ba haka nake nufi ba, yaya ne yaki zuwa har
yanzun. murmushi anty tayi tace safna ai na dauka baki
son jalal yazo kusa dake ne, tun da kina son ganin shi bari
na kira shi, anty takira wayar jalal tajita kashe dan haka ta
musu sallama ta wuce. safna mikewa tayi ta shige dakin
Hajiya kuka ta fara ta dauki wayar ta tagwada kiran jalal
har yanzun wayar shi kashe take, kukanta karuwa yayi ita fa
gaskiya in bataji muryar sa ba zata iya barci ba hajiya ce ta
shigo ta samu safna sai faman kuka take tace ke lfyr ki
kuwa? mikewa tayi ta nufi gadon hajiya tana fadin ba yaya
bane yaki zuwa. hajiya tace ikon Allah yaran zamani babu
kunya, yanzo nan duk kukan jalal din ne. kwanciya tayi ta
juya baya tayi shiru. hajiya ta dauka bacci tayi dan haka
itama ta kwanta, gurin 10:45 hajiya ta farka ta fara juwo
kukan safna kasa kasa, daukan wayar ta tayi ta kira alhaji,
alhaji yana dauka yace lfy kuwa hajiya hajiya tace lfy lau
ina abduljalal ne yau bamu ganshi ba, nusaiba takira shi
wayar shi kashi. toh inaga yayi barci ne gobe zai zo da
safe. ai ni safna ta hanani barci sai faman kuka take bataga
mijin taba. alhaji dariya yayi yace bari na tado shi tunda ta
hana ki bacci gara kowa ya tashi.
.
Sauko wa yayi ya nufi dakin jalal ya tura kofa yajita kulle
dan haka ya shiga bugawa. jalal dake kwance sai faman
juyi yake agado ya bude baki a hankali yace waye? muryar
daddy yaji yana fadi nine, sakowa yayi cikin sauri ya bude
kofar alhaji ya shigo ya kalli fuskar jalal yace me ya same
ka? shiru yayi yasa kan sa akasa. girgiza kai alhaji yayi
sannan yace kai da mamar ka ne ko?
.
jalal be amsa ba kuma be daga kai ba. alhaji ya sake cewa
me tace maka? ba komai daddy kwai dai nasan tana fushi
dani ne. toh dan wannan kake tada hankalin ka, kabar ta
zata sako , kaji ko, me ya hana ka zuwa ka duba jikin
safna? daddy naga ummi bata da lafiya ne, kar na fita kuma
jikin ta ya tashi. kai ka dai na biyewa ummin nan taka
wanne irin ciwo take lafiyar ta kalau dama abin da take so
kenan. jalal yace wlh daddy bata da lfy jininta ya hau sai da
nakai ta asibiti dazun. shiru alhaji yayi zuwa cen alhaji ya
matsa bakin gadon jalal ya zauna yace matar ka keson
magana dakai, warshi ya danna ya mikawa jalal sannan
yace inka gama ka kawo min daki , dakin ummi ya nufa,
yagan ta kwance tana bacci dan haka ya wuce dakin sa.
shikuwa jalal bayan yasa wayar akunne sa murya hajiya
yaji tana fadin an tado shiko? jalal yace hajjaju ya gari, har
yanzu bakiyi bacci ba, yanzun fah 11:14. ina ni ina barci
safna tasani gaba sai kuka take. kuka kuma, me aka mata?
hajiya tace wai dan rashin kunya tun dazun take kuka wai
baka zoba. duk da halin da yake ciki sai da yayi dariya,
sannan yace Ina take? hajiya na mikawa safna wayar ta
tashi ta fita. safna na karbar wayar ta saka mishi kukan
sha gwaba, jalal ya rasa yaya zaiyi mata inama suna kusa
da juna. a halin yace safna ya isa haka, kiyi shiru, kara
sautin kukan ta tayi . jalal ji yayi yana yin jikin shi ya fara
cen zawa babu abin da yake so ayanzu ila ya ganshi kusa
da safna. daker ya bude baki cikin kashe murya yace safna
kina tayar min da hankali fah, dan Allah kiyi shiro gobe zan
zo. cikin kuka tace ni yan zon nake so. jalal yace safna
bakiga dare bane yanzun, kibari gobe da wuri zan fito. toh
naji karfe nawa za kazo, jalal yayi murmushi yace ke zaki
fada tace karka wuce 9:00 am. toh ba damuwa insha
Allahu zan zo haka din, yaya jikin ki? wlh yaya ni babu wani
saukin da naji karuwa ma yake yi, yanzun ma fah ko ruwa
bana son gani miyar nan ma dana ke sha yanzon bana son
ta, kasan me nake son ci yanzun? jalal yace sai kin fada.
zugale nake so da mangoro gobe inzaka zo kataho min da
shi.
.
jalal yace a,a safna ban miki alkawari ba ni bansan inda
ake sai dawa ba , ki gayawa hajiya ne. toh mangoro fah?
Jalal yace ai yanzun ba lokacin ta bane, jalal gani yayi zata
sake rikice mashi, yace toh ya isa zan duba kwanta kiyi
bacci, da haka sukayi sallama kallon agogo yayi yaga har
12:03 yasan yan zon daddy yayi bacci ajiye wayar yayi ya
kwanta ya rungumi filo tunani ya shiga yi wato safna cikin
nan bayan kwadayi har da surutu yasa ta jalal be samu
bacci ba sai da yayi sallah asuba ya kwan ta dan haka be
tashi da wuri ba, koda ya tashi ya duba agogo sha daya
saura da sauri ya tashi yashir ya ya fito sai da ya duba
dakin ummi bata ciki dan haka ya wuce dakin daddy acen
ya sami ummi bayan ya gai da alhaji yace ummi ina kwana,
kin amsawa tayi alhaji yayi kamar besan me suke ba jalal
yasa ke cewa ina kwana ummi, wayar ta tasa akune tafara
magana, alhaji ya kalleta yace jalal tashi mu tafi, mikewa
yayi suna cikin tafiya alhaji yace jalal nagama gyarama
gidan da zaka zauna sai dai karami ne, ban sani ba ko zaka
so hakan. da saurin sa yace ina so daddy . alhaji yace
yauwa jalal shiyasa nake son ka kwata kwata baka dauki
duniya da zafi ba, mamar ka ko ban san ina ta samu
wannan karyar ba, kaga wancen gidan ma daya kone sai da
tayi korafin yayi maka kadan, toh yan zon yaushe zaku tare
dan anriga anzuba komai agidan. daddy ni duk ranar da
kace. murmushi alhaji yayi yace nifa so nake ku tare ayau
dan bana son kowa ya sani hanta mahaifiyar ka kuwa.
kwana alhaji yayi yakai jalal gidan ya gani gidane karami
mai kyan gaske me dauke da dakuna biyu kowan ne da bayi
aciki sai falo da kitchen jalal ya yaba tsarowan gidan sai
yaga kamar ma yafi wancen kyau girma kawai wancen zai
nuna ma wannan, gadiya ya shiga yiwa daddy. lokacin da
suka nufi gidan hajiya daya saura dan haka ya samu safna
ta cika tayi taf, alhaji kawai ta gaida ta juya ta shige daki,
alhaji ya kalli jalal yace duk wayar da kuka kwana kunayi
baku shirya ba.
.
jalal yana dariya yace daddy time ta bani nikuma bacci ya
kwasheni ban tashi da wuri ba yana fadan haka yamike
yabi bayan ta , hajiya na fadin kardai ka zama mijin tace
yana shiga ta mike ta zata fita falo jalal ya tare ta nan da
nan ta saki kara sakinta yayi da sauri yana fadin baki da
hankali ne bakiga daddy na falo ba, safna bata tsaya
sauraran jalal ba ta nufi falo kujerar dake kusa da ta alhaji
taji ta zauna akasa, tana zama jalal ya fito yasan ta zauna
agurin ne dan kar yaje kusa da ita dan haka kujerar bayan
ta yaje ya zauna. yana zama yasa kafarsa abayan ta yana
dan zungurin ta, dakewa tayi kamar bata jishi ba zuwa cen
ya fara mata waiwayi ta fara gan tsarewa tunda daddy yaga
safna tana zabure zabure yasan jalal ne amma sai ya dauke
idon shi daga waje. shikowa jalal so yake ya dame ta har ta
gaji ta koma daki, zuwa cen yasa kafar sa ya daga rigarta
ta baya ya fara mata cekulkuli, zabura tayi tare da sakin
kara ta matsa cen tana soshe soshe. daddy ya waigo yace
safna lfy.? daddy wani abu ya saka min ariga. alhaji yace
kaga jalal karka firgeta yariyar nan tashi daga gurin nan
kadawo nan. jalal mikewa yayi yakoma cen gefe kusa da
hajiya. alhaji yace safna ki shirya anjima nusaiba zata
rakaki gidan ki. dasauri tace daddy abari ba yanzun ba.
.
Alhaji ne ya kalli safna yace sabo da me zakice bayan zon
ba? daddy abari sai naji sauki bani da lfy fah daddy d'aga
hannun shi yayi ya mata dakuwa kinci gidan ku, yau din nan
zaki wuce dakin ki kin fi son ki zauna anan kina hana hajiya
bacci ko? daddy nifa bance kada tayi bacci ba ita da kanta
tashi ta zauna, dariya hajiya tayi tace toh safna ba dole na
tashi ba ni ina bacci nafara jin gunjin kukan ki. to aini kaina
ne yake min ciwo lokacin. alhaji yace ai ko bakin kine yake
ciwo yau zaku tafi, nima hankali na ya kwanta tunda aka
daura auran nan hakali na ba,a kwan ce yake ba, buri na
kulum be wuce nagan ku acikin gidan Ku ba. Safna shiru
tayi ita gaskiya fushi take da jalal, muryar daddy taji yana
cewa safna kuyi hakuri da junan ku ban da fada , kai jalal
kaine babba banda saurin fushi , babba da hakuri aka
sanshi, ke kuma safna ki sani jalal mijin ki ne dan haka
kimai biyya, tuni safna ta fara kuka ji tayi auren ya dawo
mata sabo. alhaji juyawa yayi gurin jalal yace jalal ya
maganar karatun safna, ina fatan dai kana da burin taci
gaba karatu? eh daddy insha Allah . alhaji yace to yayi kyau
Allah yayi muku albarka ya baku 'ya'ya masu albarka. gaba
dayan su kasa amsawa sukayi sai hajiya ce ta amsa. safna
kuwa ta kifa kai sai faman kuka take. alhaji yace jalal zan
tafi ko anan zan barka? a,a daddy tare zamu tafi ai ban fito
da mota ba sun mike zasu tafi safna ta dago jajayan idonta
ta harari jalal, yace Allah ya huci zuciyar ki. daddare kamar
yadda alhaji ya tsara nusaiba tazo ita da matar baba salisu
suka raka safna gidan ta, har bakin gado suka zaunar da ita
sai faman kuka take. wurin takwas suka ceto mufa zamu
wuce dare nayi. safna tace anty dan Allah karku tafi tsoro
nakeji. nusaiba tace wani irin tsoro to bari na kira jalal.
.
shikowa jalal lokacin da anty nusaiba ta kira shi yana kokari
zuba akwatunan su amota ta kofar dake baya yake fitar da
akwatin daddy na sakawa amotar har suka gama, jalal yaso
yayiwa ummin shi sallam ko bazata amsa ba amman daddy
yace ya rabu da ita, dakan shi ya raka jalal har cikin falon
su , su anty nusaiba kuwa suna jin zuwan su suka tafi
bayan daddy yasa musu albarka ya wuce gida , da niyar
shima da safe zai wuce gurin aikin sa alhaji na fita jalal ya
mike ya leka dakin safna daga bankin kofar ya tsaya ya kalli
fuskar ta da sauri ta dukar da kai kasa, murmushi yayi yace
ina zuwa, waje ya fita yafara ciro akwatunan su daga cikin
mota, saida ya fara shigar mada safna nata sannan yashiga
da nashi daki, yana ajewa ya shiga wanka bayan ya fito
yasa ka kaya marasu dauyi ya nufi dakin safna. yana shiga
ya same ta daidai ta fito wanka tana goge jikin ta tana
ganin shi ta jawo hijjabi ta dake gefen gado tana kokarin
sakawa. dariya taba jalal sosai ya matso kusa da ita ya
zauna, yace to meye kuma na saka hajjabi me zaki boye
min. gani yayi ta kara rudewa dan haka ya matsa ya riketa
yace safna meya sameki? cikin muryar kuka tace bacci
nakeji. murmushi kawai jalal yayi dan yasa ba gaskiya ta
fada ba. yace to waye ya hanaki bacci. shiro tayi. Matsawa
jalal yayi yace zoki kwan ta. zuwa tayi ta kwata ta kudun
dune cikin hijjabin ta jalal ya fahimci safna bata sone ya
nemi wani abu awajen ta, kollon ta yayi ko mai bata shafa
ba, yace safna. amsawa tayi batare da ta waigo ba, yace
haka zaki kwanta baki shafa mai ba bare kuma turare. yaya
ai ni yanzun bana shafa mai. saboda me? tace wari yake
min jalal yace wari man nakine yake wari, kitashi kawai ki
shafa ke da kin ga baki son abo saikice yana wari, haka
ranan kikace ina wari.
.
Wlh yaya ban son warin man ne , sabolon ce ma na bayi na
kasa wanka dashi ahaka niyi babu sabulu. jalal yace kina
nufin ba sabulu kikayi wanka, kice ba wanka kikayi ba kin
jiko datti, ai irin wanna saiki fada irin wadda kike so asiyo
miki. batace komai ba ta juya tayi shiru ganin ta kwanta
shima ya hau gadon ya kwanta zuwa cen ya fara kai
hannun shi jikin safna , yi tayi kamar tayi bacci ahankali
tafara jin hannun shi acikin hijjabin ta har zuwa marrar ta
taso ta rike hannun amman sai tai tunanin in yaga tayi barci
zai barta dan haka tayi kamar tana bacci saiji kawai tayi
yana kwance towel din da yake daure jikin ta dasauri ta rike
hannun shi, tace yaya jikina fa akwai datti , bakace na tayar
da datti ba. cikin rauna nan niyir murya jalal yace ni banji
wani datti ba yace gaba da abinda yake tun safna na ture
jalal har sakon ya fara kaiwa gare ta, ta fara mayar mai da
martani, nidai daga sun rikece, nayi waje aguje na jawo
musu kofar. washe gari da safe 9:10 akafara buga kofar
falon su da karfi, safna dake kwance jikin jalal ta zabura
shima mikewa yayi da sauri ya saka jallabiya ya fita har
yanzun buga kofar ake...