MIJIN MARAINIYA PART 13
MIJIN MARAINIYA PART 13
.
Abduljalal a tsora ce ya isa kofar dan gani yake kamar
ummi ce , yasa hannu ya bude kofar yariyar dake aiki gidan
anty nusaiba yagani tsaye da kayan abinci a hannun ta
wani haushi ya turnekeshi besan sanda ya daga hannun
shiba ya wanke ta da mari. a tsora ce yariyar ta dafa
kuncin ta, ta ajiye abin cin ta arta aguje, abduljalal ya
tsuguna ya dauki basket din yakoma afalo ya jiye yakoma
dakin safna ya same ta sai faman raba ido take, yace ki
kwatar da hankalin ki wannan yariyar ta gidan anty nusaiba
ce, mikewa tayi cikin sauri tace bari naje nasan anty ce ta
aiko ta kama hannuta yayi yace ai ta tafi abinci ne ta kawo,
koma wa tayi ta zauna tayi shiru tafara tunani, lallai ummi
bata son auren nan gashi yanzun tun daga gidan anty
nusaiba aka kawo mana abinci kuma ai munfi kusa da
ummi. muryar abduljalal taji yana fadi safna tunanin me
kike? yaya tunanin kairat nakeyi mun barta ita kadai. yace
karki damu idan muka gama cin amarcin mu zan dauko ta
tadawo nan da zama gaba daya. safna tace yaya ummi ko
zata bari? da sauri yace safna bar wannan maganar kisan
tunanin me nakeyi . gargiza kai tayi yasake cewa ina
tunanin gashi kin haifi yaro me kama dani. Safna tace nidai
yariya nakeso. nima inaso safna amman nafiso ki fara da
namiji dan nasa mishi sunan daddy.
.
safna tace toh yaya in mace ce wani suna za,a sama ta.
bude baki yayi ahankali yace na baki zafi. safna ta sake
cewa baza,a samata sunan ummi ba? mikewa yayi yace
taso muje muci abinci. safna ta lura yaya ko sunan ummi
beson yaji ta Kira suna cikin cin abin cin ne wayar abduljalal
tayi kara ya dauka yasa akunne sa, yana fadin ina kwana
anty. anty bata amsa gai suwan shiba ta shiga yimai fada
jalal me bilkusu tayi maka ka mareta har fuskarta ta
kunbura haka? anty zuwa tayi muna barci taita buga kofar,
safna duk tabi ta firge da sauri anty tace lallai jalal safnar
yariyar goye ce da zakace wani an firgita ta, har yanzun dai
kanan da bakar zuciyar ka , ita kuma safna tana kallo
kamari yariyar muta ne ko, toh shike nan idan ka kuma
ganin bilkisu agidan ka kasa bulala ka zaneta ba mari ba
yana kukarin yin magana ta kashe wayar. ture abincin yayi
gefe ya sake kiran ta bata dauka ba mikewa yayi ya shige
dakin sa. safna binshi tayi da kallo domin bata fahimci abin
da suke fada ba, ta fara kwashe kayan da suka bata takai
kitchen saida ta wanke su sannan ta fito har lokacin jalal be
fito ba, wuce wa tayi dakin ta tayi wanka kwalliya ta tsaya
tayi sosai sannan ta nufi dakin jalal tana tura kofar tajita
bude sallama tayi . jalal dake ciki ya amsa , tana saka kai ta
ganshi tsaye ga dukkan alamu wanka yayi dan daga shi sai
gajeran wando ga dogon wando a hannun sa yan kokarin
sakawa.
,
safna naganin haka ta juya baya , murmushi jalal yayi ya
aje wandon hannun shi ya iso gare ta jin shi kawai tayi ya
rogumeta, ta baya yana kaimata kiss ta ko ina kamar zai
hadiye ta, zuwa cen yadan dakata ya leko da kansa zuwa
daidai fuskar ta dan jalal dogo ne sosai, yace har kinyi
wanka, Allah yasa dai yauma ba haka kikayi wankan ba
sabulu ba. safna na rugume jikin jalal tace ai na samu wani
sabulu acikin akwati na bashi da wari sosai. jalal yace jinan
safna in kinji abu namiki wari ki daina cewa yana wari cewa
zakiyi bana son kamshin shi, dan kinsan Allah idan kika kara
cewa ina wari saina fasa miki baki. kallon shi tayi da
mamaki tace yaya yanzo nan kai sai ka dake ni. me zai
hana na dake ki ,kiyi abin dokan kigani. haba nina san
bazaka dakeni ba in kuma zaka iya bismillah. jalal yace ai
baki min komai ba yanzun. dan tureshi tayi kadan ta rike
hancin ta tace yaya jalal wari yake. murmushi kawai yayi
yace Ina binki bashin duka idan kika haihu zan miki. a,a ni
ban yadda ba yanzun nake so. matso wa yayi ya riketa yace
daidai ina zan daka. safna cikin ta, tanuna tace ka daki nan
dariya jalal yayi yace lallai safna ke muguwa ce ,toh naki.
haka zaman su yaci gaba da kasan cewa cikin farin ciki da
kwanciyar hankali jalal yana nuna mata so daidai
gwargwado har wani cika su kayi suka kara haske sukan
leka gidan hajiya da daddare gidan ummi kuwa tunda suka
tare ko jalal be leka ba bare safna, amman bata san cewa
jalal baya zuwa ba gashi har sun kwashe sati uku da
tarewa alhaji kuwa tun washe garin ranar da ya raka jalal
gidanshi yabar garin ko sallama bema ummi ba. itako ummi
ranar ta wayi gari daga ita sai kairat acikin gidan tayi
tunanin wato jalal fushi yake da ita ko ganin shi baya bari
tayi, alhaji kowa abakin kairat taji lbrin ta fiyar sa. tun tana
ganin abi kamar wasa ne har ta fara tsora ta. kiran alhaji
tayi har ta gaji be dauka ba, ta fara tunanin kiran jalal,
amman kuma da kunya takira shi bayan tace mai bata son
ganin shi, fadi tayi a fili me yake shirin faruwa dani ne,
iyayena sunki karbata saboda halina dagin mijina basa
sona saboda halina mijina dake takama dashi ya juyamin
baya saboda yana kuka da halina, dana dake matukar so
shima ya hakura ni ,afili take fadi kamar mahaukaciya
zuwacen ta sake kuka haka taita yi babu me rarrashin ta
yau ummi ta tashi da matukar so taga jalal tuni ta lura jalal
kwata kwata baya shigowa gidan a lissafin ta sati hudu
kena da barin su gida wata zuciya tace kodai tare sukayi
tafiyar da alhaji be. mikewa tayi ta nufi dakin jalal tana tura
kofar taji ta bude shiga ciki tayi me zata gani duk wani abu
na amfanin jalal babu shi adakin, juyawa tayi gurin da aka
aje a kwatunan safna nanma wayam babu komai. rawar jiki
ta fara tana haki take fadin na shiga uku, dakin ta tafada ta
dauki gyale drive takira tace zoka kai ni gidan hajiya, rabota
da gidan hajiya ta dade. hajiya na zaune taga ummi tashigo
kamar ankwato ta daga bakin kura.
.
Hajiya tsoro ne ya kama ta cikin kidima tace zaliha daga ina
haka? cikin kuka take fadi hajiya nazo neman gafararki dan
Allah kiyafemin a yanzun nagane kure na , kuka take sosai.
hajiya tace alhamdulillahi dama haka ake so naji dadi da
kika fahimce haka ni daman ban kullace kiba tunda ismail
yakawo ki amatsayin matar sa dole nasoki balle kuma ga
yara har biyu atsakani. ummi tace nagode hajiya tana share
hawaye. hajiya tace amman zaliha bayan wannan akwai
wani abun da yake damunki ko? hajiya aini duniyar gaba
daya ta cakude min iyayena suki karbata amatsayi yar su
saboda lefin da na aikata , nan ta shiga bawa hajiya lbr
hajiya tace ikon Allah abin mamaki baya karewa , toh zaliha
banda abinki ina kika taba jin mutun yaki iyayen sa, toh ai
dole kirasa kwanciyar hankali kadan ma kika gani, ai iyaye
ba abin wasa bane, karki kara ai kata nakaman cin wannan,
kinji ko? In Allah ya yarda bazan kara ba nagode hajiya.
hajiya tace tashi kije kitchen ki debi abinci. hajiya bana jin
yinwa naci abinci agida. shiru sukayi nadan wani lokaci
sannan hajiya ta kalli zaliha tace megidan fa yaushe zai
dawo? tofah hajiya ta sosa ma ummi inda yake mata
kaikayi wani sabon hawaye ne yake fita a idonta tace hajiya
aini rabon da naga alhaji sati hudu kenan sanda zaitafi ma
ko sallama bemin ba kuma ko kiransa nayi baya dauka jalal
ma basan inda yake ba, hawaye take sosai. hajiya ta
tausaya mata tace ya isa haka share hawayen ki, kikace
rabon ki dashi sati hudu? eh hajiya tace toh ai yadawo yayi
kwana biyu ya koma, yau kwana biyar da tafiyar sa, kina
nufin ba,a gida ya kwana ba kenan,toh ko kin masa wani
abune? shiro tayi tana ta share hawaye. hajiya tace toh
kidaina kuka ai tunda kukayi aure shekara kusan talatin ban
taba jin kan kuba, mijiki nasonki yayi hakuri da ke duk da
cewa yasan baki son yan uwan sa, ina ganin dai akwai
abinda kika masa. hajiya wayar ta dauka ta shiga daki
number alhaji takira bayan ya dauka tace me matar ka ta
maka katafi kabar ta babu ko sallama? alhaji yace lallai
zaliha bata da kunya gidan ki tazo shakaran ta nawa batazo
gidan ki ba.
.
hajiya tace nidai ba wannan na tambaye kaba babu
ruwanka , koma me tayi maka kayi hakuri bakaga inda ta
fita haiyacin taba ta rame tayi baki kai ko kunya bakaji
abokan ka su ganta ahaka, ai sai ace wahala take Sha.
hajaya kirabu da zaliha makirar mata ce, inda kisan halin ta
bazaki yarda da tubanta ba, kice mata kawai ta wuce gida
saina dawo. nidai nace ka kira ta, ka kwatar mata da
hankali abin ya mata yawa jalal ma kai ka hana shi zuwa
gidan kenan, toh yanzun yaya kake son tayi. alhaji yace
shike nan hajiya zankirata. ummi bata tafi gida ba har dare
gashi kuma har yanzun alhaji be Kira taba sai gurin 7:30
taga kiran shi jiki na rawa ta dauka tafara gaida shi be
amsa ba yace kina ina ? cikin sauri tace ina gidan hajiya.
yace toh maza kitattra kayan ki kije gidan iyayen ki sai
Nazo, kin shirya wani munafuncin ne dan kirabani da
mahaifiya ta, toh baki isa ba, kinyi kadan,maza ki bar
gidanan . hajiya nadaga daki tajiwo ummi tasaka kuka me
ban tausayi, fitowa tayi tace zaliha yaya akayi? ummi ta
gayawa hajiya abinda ya faru, ran hajiya ya baci afili tace
Ismail kuma abida beyi da kuruciyar shi bane yanzon zaiyi,
toh shikenan, ke kuma wannan ya isheki ishara dan yasan
baki da gurin zuwa ne shiyasa yace kitafi .
.
ummi kuka take sosai tace yanzun hajiya yaya zanyi baffa
yace idan nakara nufu gidan shi batare da nacika sharadin
da yabani ba Allah ya isa. hajiya nisawa tayi tace kizauna
anan kafin yadawo muji abinda yake nufi kuma ko yakiraki
awaya karki dauka, ke kima kashe wayar baki daya, dan
naga alamar ran shii a bace yake dake kar yazo ya aikata
abin da yafi haka . godiya tayima hajiya sosai suna zaune
sunyi jugun jigun saiga kairat ta shigo tana kuka ummi
shine kika tafi kika barni, kwantar da ita tayi akan ciyarta
tana rarrashin ta. ranar da ummi ta wayi gari agidan ummi,
jalal kuma agidan sa ya tashi da matsanan cin mura da
zazzabi tun yana daurewa har ya gaji yace safna zoki
rufeni, zuwa tayi ta taba jikin shi taji zafi rau tace yaya
katashine muje asibiti . cikin rawar murya yace safna bazan
iya tuki ba, bari sai anjima, rufeshi tayi ta fita zuwa kitchen
domin karasa girkin da ta daura.
.
bayan ta gama takoma dakin tasame shi ya ture bargon sai
faman kira sunan ummi yakeyi, ta dauka wasa yake saida
ta karasa kusa dashi ta gane da gaske yake yi, dariya ta
fara tace meye haka yaya saika ce kairat. ai ko sauraran ta
beyiba kiran ummi kawai yake yi zuwa cen ya jawo safna
zama tayi agefen gadon ya dago kanshi ya daura aciyar ta
sai faman sanbatu yake tun abin nabata dariya har yasoma
bata tsoro zuwa cen taga ya fara kuka hawaye shabe
shabe, da sauri ta sauke kan jalal daga jikinta karamin
hajjab tasa tayi waje. tana fitowa gate din gidan su gidan
dake jikin nasu ta nufa dan taga me gidan suna yawan
gaisawa da jalal, gate din gidan ta fara bugawa me gadi
yazo ya bode yace lfy ? safna ta rasa me zatace dan ko
sunan mutumin bata sani ba, hango shi tayi rike da hannun
matar sa zasu shiga mota hango safna da me gadin su ya
hana su shiga karasowa gurin sukayi safna ta gaida
mutumin tace ni makociyar kuce anan gidan nake ta nuna
gidan su da ahannu ,miji nane bashi da lfy dan Allah ku
taimaka min ku kaimu asibiti. mutumin yace kece matar
abduljalal dakai ta amsa, yace toh babu damuwa muje na
dubashi, duk suka rankayo har matar sa, suna shiga falon
suka tsaya, safna tace muje yana ciki, mijin yace a,a je
kigaya mai idan zai iya fitowa yafito inkuma bazai iyaba
saina shiga. safna tana shiga tasame shi yadda tabar shi
be daina surutun ba,tasan jalal batashi zaiyi ba tace yaya
dan Allah kadaina magana kayi shiru gayinan za,aduba ka,
bece komai ba sai kokari riketa yake taje tace wa mutumin
yace kashiga. safna bata koma ba zama tayi kusada matar,
ta kalleta tace ki kwatar da hankalin ki in Allah ya yarda zai
samu sauki , tasake cewa gashi muna kusa amman bamu
sanjuna ba, ya sunanki?
.
waigowa tayi gefen ta tace sunana safna kefa? tace nikuma
khadija, suna cikin haka mutumin ya fito yana murmushi
yace madam karki damu murace tamai mugun kamu
amman dazaran yasha magani zai samu sauki, yajuya
barayi matar sa yace khadija zomuje nabaki magani ki
kawo mata. bayan kadija takawo magani tare da yi mata
bayani ruwa ta dauka ta nufi dakin ta same shi kwance
yadai rage surutun da yakeyi tace sannu yaya tashi kasha
magani. jalal ya bude baki cikin murya kalan na me
sambatu yace aini bana shan magani safna ki tambayi
ummi kiji. kalon shi tayi da mamaki tace toh ai ko saika sha
yama za,ayi kace wani baka shan magani saikace wani
karami yaro. nidai gaskiya katashi kawai kasha. jalal ya
sake cewa safna ki aje maganin nan ko ganin shi bana son
yi. kuka ta saka da karfi, tana fadi toh ni ya kake son nayi
gashi bacci nakeji kaikuma sai faman sambatu kakeyi. jalal
yana kokari jan bargo ya rufe jikin shi saka makon zazzabin
da ya dawo mishi yace zoki kwanta na bari. ni sai kasha
maganin zan kwata yace toh naji kawo nasha. mika mishi
tayi ya karba yasa abaki ya karbi kofin ruwa yakai bakin sa,
kasa hadiyewa yayi ya fara sheka amai. safna na rike dashi
har ya gama hawaye nata zubo mata gashi itama ba kwari
gareta ba haka ta kamashi takai shi bayi ta wanke mai jiki,
dakinta ta wuce dashi sannan ta dawo ta gyara wajen
tanayi ne tana kuka bayan takoma gurin jalal ta dauki wayar
jalal takira alhaji. yana dauka yace jalal, safna tasaka kuka
tace daddy yaya bayi da lfy kuma yaki shan magani,
saikiran sunan ummi yakeyi. alhaji yace toh fah, tashin
hankali, ciwon jalal wuya gare shi, to ya isa ki daina kukan,
share hawayen ki, bari nusaiba zata zo yanzun.