RABO NA CE PART 11
RABO NA CE PART 11
.
Saida suka bace ma ganin sa, sannan yayi ajiyar zuciya, ya
koma cikin asibiti ya d'auko motar sa, ya fito ya kama hanya
shima, a hanya Ummey tana kukanta kamar ranta zai fita,
ta kuwa rik'e results tamau kamar wani zai kwace mata,
Nafee sai aikin rarrashi take yi ita ba boko ba bare tasan mi
yake faruwa, Ummey a hankali ta d'ago idonta, motar
Mahbuob ce ta wucesu, dukda bata cikin hayyacin ta Amma
ta kula da chanji a fuskarsa sai take tunanin duk tausaya
mata ne yayi, haka dai har suka k'arasa gida. Nan hankalin
kowa ya tashi ganin yanda take kuka kuma tak'i bayani, ta
mik'a musu result d'in sun karba amma ba Wanda ya gane,
ita kuma sai aikin kuka take, abin ya ishesu, "To Ku yiwa
Mahmoud waya mana!" Inji Mumy, Al Ameen ya d'auko
wayarsa aka ma Mahbuob waya yayi musu bayani Amma
bai samu d'auka ba, Ammar yace, "Ko wani Abu ya sameshi
naga yak'i d'auka" Anka tace "Lafiyar sa lau shima ya saka
mu napeep sabida motar shi tak'i tashi" Ammar ya k'ara
dubawa, "To nidai ban gane komai ba, duk na wayanda na
gane lafiyan ta lau, wannan HBsAG ne da aka saka positive,
kuma shine ban gane ba, Amma ku tsaya" Datan wayan sa
ya kunna yaje Goggle, ya rubuta HBsAG, yayi Goggling,
abinda ya gani shine HEPATITIS B. ya k'ara danna wani
link, ya karanto, toshe baki yayi, "Ka yiwa mutane bayani
kaji! kaja ka tsaya kana wani toshe baki," Dady ne ya shigo
da sauri ganin yanda suke tsaitsaye ga Ummey tana wani
kuka mai tsuma zuciya, kukan ya k'ara d'aga masa hankali,
tsawa Mumy ta daka masa, ta kwace wayar, "Allah Mumy
ban gane turancin bane shi isa," Dady ya karba ya karanta,
yayi shiru Mumy kam an barta tsaye, ya kalli Ummey
tusayinta ya shige shi, ya kalli uwar yanda ta rud'e yace,
"Ciwon hanta take dashi" Mumy tace, "Shine abin tada
hankali, wallhy ko k'anjamaune iya firgitan da zanyi kenan.!
.
Allahn daya d'aura miki, Allah ya yaye miki Ummey" Haka
kawai ta fad'a ta wuce d'akinta, Allah sarki uwa kenan! tana
shiga d'akin ta fashe da matsanancin kuka, ji take kamar
ciwon ya dawo kanta gaba d'aya, tanajin labarin hatsarin
ciwon da illar sa, da zamansa lalura, sai yau gashi a gurin
yarta, kuka take kamar me. Dady ne ya shigo, "Haba
Rabi'a!! Ni gani nake bai dace ki zauna kina kuka ba,
yarinyar yanzu take buk'atar ki kinzo nan kina kuka" Haka
dai yayi ta baiwa Mumy baki har ta hak'ura, ta daidaita
kukan ta, ta tashi ta wanke fuska ta tafi dakin Ummey d'in,
Koda taje baccin wahala ya d'auke ta, tayi tsaye tana kallon
ta tana zubar da hawaye, ta dad'e a tsaye sai da taji
maganar Muhammad tayi sauri ta janyo mata k'ofa ta fito,
duk yan uwan nata a palo Ana jimami kamar anyi mutuwa,
ta wuce dakinta taci gaba da kuka..
.
Yiniin ranar farin ciki ya k'auracewa mutanen gidan gaba
d'aya, kowa ka kalla zaka ga damuwa tattare dashi,
musamman Momy da ko magana batayi, Wayar tace ta
tayar da ita daga bacci, Amma bata samu dagawa ba,
Shaheed ne yake kiran ta, a hankali ta bud'e idon ta suka
kunbura sunyi suntum dasu, tana tunawa da cewa wai
tanada ciwon hanta sai taji wani bak'in ciki ya turnuk'eta,
kukan zuci take dan ba hawaye Sam, haka ta tashi taje bayi
tayi alwula tayi sallah azzahar da la'asar tana zaune saman
sallaya tana addu'a tana kuka, saida taji ta sami natsuwa
sannan tayi shiru, Tabbas addu'a rahama ce sabida tunda
ta fara addu'a sai taji komai ya mata sauk'i, sai kuma ta
fad'a tekun tunani, Mahbuob ya fad'o mata a rai, ta janyo
wayarta ko zataga kiran sa, Amma ba miss calls ko daya
nashi, daga na Jaheed sai na Shaheed ta gani, kimtsa bakin
ta tayi ta d'ora kanta saman gefen gado, taci gaba da
nazarin ta, Mumy ce ta shigo ta dad'e tsaye bakin k'ofa
tana kallon ta sannan ta shigo d'akin cike da tausayi, ta
dafa kafad'arta, "Kizo kici abinci Ummey" Ummey ta kalleta,
da ganin mahaifiyar tata tasan kuka tayi dan itama idonta
sun kun bura, har fuskarta wani ja tayi dan kuka, bata musa
ba, dan tasan yau ta batawa kowa rai a gidannan, ta mik'e,
jiri take gani, Mumy tad'an kama hannunta suka fito palo,
nan Ummey tace saidai suci abinci tare da Mumy dan ta
kula bataciba haka suka zauna suna cin abincin ba um ba
um umm, sabanin da, idan Ana chin abinci hira da tsokanar
fad'a wannan ya tsokani wannan wanchan ya tsokani
wannan, har su k'are, dan har Dady yana tsokana idan aka
zauna chin abinci, happy family kenan.
.
Amma yau tseet, kowa duuum, sun k'are kenan Dady ya
Shigo, yazo ya zauna yana kallon matarsa da yarsa, duk
sunyi wani iri dasu, ya kalli sauran yaran duk sunyi zuru
zuru dasu, yayi murmushi, k'arfi da yaji ya rik'a bada
labarin dariya, Amma kowa ya d'aure, Ummey ce ma da
taga abin yayi yawa sai ta fara dariyar dole, a hankali da
sukaga ta saki jiki sai suma suka d'an saki nasu, kiran
Magreeb ya tayar dasu, sukaje sallah, Dady ya dad'e yana
mata addu'a Allah ya saka mata dangana da tawakkali ya
shigo gidan d'akinta ya wuce, ya sameta itama tana addu'a,
saida ta k'are sannan ya fara rarrashinta. "Ummey Kinsan
ko wane mutum da irin jarabawar da Allah yake masa, wani
da talauci Allah yake jarabtarshi, wani da mata, wani da
Yaya, wani da abokai, wata da mijinta, sabida mafi yawan
mata da maza Allah yake jarabtarsu, wasu kuma da ciwo,
to idan kinga haka kada kiyi tunanin cewa Allah baya sonki
ne ya d'au ra miki ciwo, Sam.!!! ya d'au ra miki ne dan ya
zama wata wasila ta jarabtar ki Ku zai zama shine sanadin
tsirar ki, Allah yana hakane ya gani shin zaki cinye
jarabawar koyaya??? To kiyi k'ok'ari ki chinye wannan
jarabawa ki zamo daya daga cikin bayi masu godiyar Allah!
" Haka dai Dady yayi ta mata naseeha da har ta sami
natsuwa a ranta, sannan ya tafi akan gobe zasuje gurin
likita dan ya k'ara musu haske a kan ciwon, yana fitowa
gurin Mumy ya nufa, itama ya mata akan ta daure ta kuma
rik'a kwantarwa da Ummey hankali bawai ta zauna tanata
kuka ba, I kuwa Mumy ji take kamar ciwon ya dawo jikinta
bawai ya tsaya jikin Ummey ba lallai UWA UWACE.
.
Mahbuob kwance saman sofa ya rufe idonsa yana tunani,
Matar shi ce tazo "Yaya Mahbuob lafiya tun jiya na ganka
wani iri?" Bud'e idon sa yayi ya mata murmushi, "ba komai
kawai ina d'an jin jikinane ba dad'i duk yayi tsami" "Eyyah to
bari na maka Massage ko ka sami sauk'i" ta fad'a tana
danna masa jikinsa a hankali, lumshe ido tayi yana tunani,
tabbas idan ya auri Ummey ya cuci matarsa, mace da
CIWON HANTA, gashi nurse tace masa ko ta hanyar
numfashi Ana d'aukar ciwon gaskiya bazai cuci iyalinsa ba,
Ummey saidai tayi hak'uri Amma bazan iyaba, mirginowa
yayi ya rungume matarsa a hankali ya rik'a aika mata da
nashi salon daga nan suka auka duniyar ma'aurata,
Hmmm. Namiji kenan..!!!... "Ina Ummey take?" Dady ya
fad'a yana kallon Mumy, Muhammad ne yaje da gudu ya
kirata. "Kizo inji Dady" Yana fad'a ya fito d'akin, "Dady
yanzu Anti Ummey bata sona, kaga ko Shaheed ya kira bata
d'auka," Dady ya shafa kanshi "Batada lafiya ne
Muhammad, idan taji sauk'i zata d'auki wayarsa," ihuuu
yayi dan yaji dad'i sosai. Ummey ce ta fito da hijabinta zasu
tafi asibiti, nan Muhammad yasa fitina sai ya bisu, bada son
ransu ba haka suka tafi dashi, suna tafe yana zance d'aya
har suka isa asibiti. Gurin Dr. John suka nufa akace sai
goma yake zuwa, haka suka sami gu suka zauna har goma,
sunji dad'in zuwa da Muhammad dan shi yayita musu hira
suna dariya ya debe musu kewa. Sun sami ganin likita
goma d'in ya karbi result d'inta ya duba, Dady yace "please
muna buk'atar K'arin bayani akan shi kanshi HEPATITIS
d'in," Likitan ya gyara zama "HEPATITIS is a virus (HBV)
that effects the liver, and couse liver inflammation celled
( HEPATITIS ) and it cant course both a self......
.
HEPATITIS wani kwayar cutane (HBV) da yake taba hantar
mutum, sai ya haddasa ma mutum ciwon hanta, Wanda
wannan kwayar cuta a cikin jinin jiki take, Kuma shi kanshi
HEPATITIS d'in ya kasu kashi biyu Akwai (ACUTE) akwai
kuma( CHRONIC) ACUTE shine wanda da kansa yake
warkewa bayan yan kwanaki a jikin mutum sabida bashi da
tsanani sosai. Shi kuma CHRONIC shine mai tsananin,
Wanda baya warkewa, Wani ACUTE din zakuga yanada
alamomi da suke nunashi, kamar zazzabi, ido da jiki su
zama yellow, da kuma kasala da ciwon jiki, sannan zakuga
wasu sunada ACUTE din fite da wata 6 Amma bai zama
CHRONIC d'in ba, sabida da yawa zakaga ACUTE ne yake
juyawa ya zama CHRONIC. CHRONIC gaskiya yanada
hatsarin gaske, sabida yana damege din hanta ne gaba
d'aya," Wasu hawayee suka gangaro a idanuwan Ummey,
ita kuma ciwon hanta ne zai karta lahira...... Likita yaci
gaba....
.
"Sannan yana haifar da CANCER a cikin hanta, wanda daga
k'arshe saidai a cire wannan hantar ayi dashen wata
( transplantation) idan anyi nasara shikenan idan ba'ayi ba
kuma to mutum zai iya rasa ransa," Ya d'ago ya kalli
Ummey da take ta zubar da hawaye, cikin harshen turan ci
yace. " ki kwantar da hankalin ki, akwai abubuwan da zaki
kiyaye Wanda insha Allah zaki ma warke gaba d'aya ma da
yardar Allah, idan ma baki warke ba to zaki kasan ce cikin
lafiya kamar ma bakida ciwon, sabida zaman ciwon a gurin
hanta ne yakeda illa sosai, idan ba haka ba ba abin
damuwa bane. Yanzu Ina muku bayanin ciwon ne dan
kusan hadarin sa ta yanda zaki kula da kanki sosai wajen
kiyaye abubuwan da zan zayyano miki, so please kiyi shiru
ki saurareni." Ummey ta goge hawayen ta ta natsu tana
kallon likitan "kunga ana d'aukar wannan ciwon ta hanyar
abubuwa uku zuwa hud'u * Ta hanyar saduwa da mai cutar
* Ta hanyar haihuwa, uwa mai cutar idan ta haifi yaro, to
dolene a dubasa.
.
*Ta hanyar amfani da abubuwa masu kaifi na mai cutar
kamar reza, nail clippers (abin cire kunba) ko brush ko duk
wani Abu mai tsini da zai iya sa jinnin mutum dana mai
ciwon ya had'u, Ana d'aukar ciwon hadda gun yan kunne.
Amma BA'ADAUKAR CIWON ta hanyar Cin abinci da mai
cutar, ko kissing d'in sa, ko yin sallama dashi, ko shan ruwa
haka, ko tari atishawa, ko zama bayin daya zauna, duk wani
CASUAL CONTACT ba adaukar ciwon da gurin." Ya kalli
Dady, yace "Amma Ku family d'in ta dole ne Ku kiyaye,
kuma dolene dukan su a muku VACCINE (Riga kafi)dan kada
kuma Ku kwashi cutar" Ummey duk'ar da kanta tayi, Dady
ne yayi tambaya, " Likita kace virus kuma kace ana masa
riga kafi? Ya hakan yake,?" Ya daga kai ya gyara zama, " Eh
virus ce, kuma itace farkon anti cancer virus da akayi a
Duniya, sanna tanada kyau sosai, zata kareku daga daga
kwasar cutar koda kuwa baku daina sharing d'in abubuwan
dana lissafa ba, kusan 80% zata kare Ku daga cutar hanta,
kuma duk likitocin duniya sun yarda da riga kafin nata,
sabida haka Ku kwantar da hankalin Ku." Daddy wani
gwauron numfashi ya sauke, had'i da tambayar liktan mi
yake kawo ciwon? " Eh to da yawan likitoci sun tafi akan
cewa shan giya yana kawo cutar, haka cin magani mai daci
irin su dogon yaro, wasu masana ma sun kawo wayannan
abubuwan a matsayin abuwan da suke kawo ciwon hnta
HEPATITIS, kamar su dadewa ba'ayi bacci ba, rashin yin
fitsari da safee, chin abinci ba K'aidi, rashin cin breakfast,
shan magunguna barkatai chin kayan gwan gwani na
company, Amfani da mayukan da ba natural ba, chin
danyen abinci Wanda bai dahu ba, duk masana sunce suna
saka ciwon hanta, Amma ba lallai su zama HEPATITIS ba.
Mafi abinda yake kawo cutar shine shan giya, Amma anfi
d'aukar cutar ne ta hanyar saduwa, ko kuma amfani da
kayan kaifi ko tsini Wanda zaisa jinin ka dana mai cutar ya
had'u.
.
So yanzu zan gaya miki abuwan da zaki kiyaye , da yake
akwai kashe kashen HEPATITIS d'in sabida daga A ne zuwa
E, Amma B da kuma C sunfi illa, A da E su bama komai
bane suna warkewa, kuma ba'a daukar su a gurin mutum
Ina nnfin su ba virus bane, Sorry akwai magani
LAMUVIDINE, yana taimakawa cutar sosai bawai zai warke
bane, no zai dai taimaka gurin hana kamuwa da LIVER
CANCER," Likita ya kalli Ummey, cikin surar tausayi yace,
"My sister ba kuka zakiyi ba kiyeye wayannan abubuwan
zakiyi sai komai yazo miki da sauk'i. a daina chin abincin da
proteins ya masa yawa, bawai kada aci bane gaba daya no,
aci Amma not much, A kiye su soyayen dankali, zata iya
dafa dankali kawai ba komai cikin sa sa taci, yanada amfani
a jiki, su sandwich, su pizza, dadai kayan gwangwani haka,
sannan ta rik'a shan rakee tanada mihimmanci sosai a
jikinta." Ya juyo ya kalli Dady, dole a kula da yanayin abincin
ta kaga zai zama tana chi hudu a yini, Dan ba'ason ta rik'a
ci lokaci d'aya ta koshi, zaifi kyau ta raba cin abincin nata
kashi hud'u kuma kada ta rik'a cin abinci mai nauyi, sorry
sir idan kunzo VIRAL LORD insha Allah zan k'ara muku
bayani wasu abubuwan," Ya kalli Ummey da take ta zubar
da hawaye, "Oh my God sister! Why Are crying? Please, kayi
shiru!" Dady yayi murmushi suka yiwa likata godiya suka
fito Muhammad da yake zaune ba abinda ya gane shima ya
taso ya biyosu, A hanya Dady ya tsaya ya siyo mata
LAMIVUDINE d'in ( sunan maganin kenan.) Sannan suka
wuce gida....