MIJIN MARAINIYA PART 11
MIJIN MARAINIYA PART 11
.
Da sauri ummi tace toh ku tai maka ku kaini gurin matar
tasa. suna fitowa ummi ta nufi mota mutumin da me
unguwa ya hada su dashi yace hajiya ai mota bata shiga
unguwar. nan suka bar motar suka yanka a kafa tafiya suke
tafiya taki karewa ummi ta gaji jalal yace ummi ko zaki
zauna ki huta ne? a,a jalal mu tafi kawai kafin su isa ummi
taci bakar wuya takalmin ta har ya bare zufa ke yanko mata
ta ko ina kafar nan futo futo kamar ba itaba, suna zuwa ya
nuna musu gidan. ummi ce ta shiga jalal yana waje sallama
tayi acikin gidan ,goggo ta taho da sauri tana fadin hajiya
batan kai kikayi ne ummi tace a,a baki ne mu , munzo gurin
mijinki sai muka same lbrn rasuwar sa. goggo tace ayya
malam ai ya dade da rasuwa, shigo ki zauna dauko
tabarma tayi ta shin fida. ummi ta zauna tana fadi ba zama
ma zamuyi ba muna sauri ne. goggo tace ai ban shai da
kiba hajiya kin dai yimin kama da wata wadda na sani.
.
cikin murna ummi ta gayawa goggo abinda yake tafe da ita.
goggo tace ikon Allah ni ko na san saudatu kishiya ta ce
tunda malam ya tsunto ta shekarar ta uku babu wanda yazo
neman ta dan haka malam ya aure ta amman Allah yayi
mata rasuwa tare da malam sukayi hatsarin mota su rasu.
da karfi ummi tasa ka kuka , jalal dake waje yaji kukan
ummi ya shigo aguje. yana shigowa ummi ta fara cewa
abduljalal saudatu ta rasu. jalal yayi tabawa ummi hakuyi,
yace tashi mutafi sun mike zasu tafi goggo tabi ummi da
kallo matar nan ta bata tausayi tana son ta kaya mata
saudatu tana da yarinya amman tanajin tsoro dan bata san
inda safna take ba. sun mata sallama zasu fita kenan sai
ga wata kawar goggo ta shigo gidan. tace baki kikayi ne?
goggo tace wlh yayar saudatu ce sai yanzun Allah ya bai
yana yan uwanta matar tace Allah sarki Allah ya kara muku
hakuri saukin ta ma tanada yarinya. dasauri ummi ta sake
hannun jalal tace dama saudatu tabar yarinya shine baki
fada mana ba. tuni goggo ta fara rawar baki em dama
mantawa nayi dayake yarinyar ba a gurin na take ba tana
cen gurin dangin kakar su shi yasa bari ma kika hotunan
saudatu shiga daki tayi da fito da hoton saudatu da malam
da yar karamar yarinyar su dayan kuwa saudatu ce kadai
ummi ta dauki wadda suke harda yarinyar ta kurawa
yarinyar ido gani tayi kamar ta taba ganin yarinyar tuni
tafara share hawaye tana fadin jalal yariyar nan kyakyawa
ce tafi saudatu kyau tace jalal yarinya nan saina nemota
saina mantar da ita rashin mahaifiyar ta da tayi. jalal yayi
murmushi yace ummi nima naji ina matsanan cin son
yariyar. bayan goggo ta musu kwatan cen garin su iya a
zaria jalal yace yasan unguwar suna zuwa da alhaji. haka
suka ma goggo sallama bayan sun bata gudi masu yawa
suka baro ta. jalal ya cire takalman kafar sa ya mikawa
ummi taki karba , dan haka ya tanbaya a ina ake saida ta
kalmi aka nuna masa yaje ya sayo ma ummi silifas ne
yama mata yawa ta karba tasa. bayan sun isa gurin me
unguwa sukayi godiya sannan abduljalal ya dauki kudi
masu yawa yace akai baba asibiti. haka suka isa gida ga
farin ciki ga bakin ciki.
.
suna fitowa a mota suka hango safna da kairat suna zaune
agurin da jalal yake zama , kairat ce ta fara mikewa ta nufu
gurin su ummi, dan haka safna babu damar guduwa itama
gurin su ta nufu da miyar daddawan ta ahannu tana sha da
cukali. kairat tana hango ummi ta fara sheka dariya tace
yaya kalli takalmin ummi daga kan ta tayi takalli jalal taga
fararan kayan shi sunyi jawur idon nan zuro zuro takara
fashewa da dariya tana cewa anty safna kalle su. safna
dariya ke neman kwace mata Amman tsoran ummi ya
hanata yi. ummi tariko kairat tana fadi almura dan bamuje
dake bane dasai kin fimu datti, ummi ta juya zata shiga
gida jalal ya ruko safna kairat dake rike ahannun ummi tace
anty safna wlh ki gudu zai shafa mike datti. ummi ta yaigo
tace jalal meye haka. sakin safna yayi ya fara tam bayanta
meye wannan kike sha, ko faten daddawan ne? banza tayi
dashi yace wai har yanzun baki huce bane? nan ma babu
amsa da haka suka isa falon, lokacin da suka shiga sun
samu ummi tana nunawa kairat hoton saudatu da yar ta .
kairat ta nuna karamar tace wannan wacece? ummi tace
antyn ki ce kinga mamarta kanwata ce kairat tace ummi
yaya sunan ta? ummi tace na manta ban tamyi sunta ba,
dai dai nan jalal ya shigo shi da safna. ummi tace jalal
yama sunan yariyar nan. jalal yace au ummi baki tambayi
sun ta bane? ummi kasa magana tayi ta dafa kai. Jalal
yace ba komai ummi karki damu suna ba matsala bane
kwanan zamu gano ta.
.
nisawa tayi tace Allah yasa haka jalal, Allah yayi maka
albarka. jalal yaji dadi sosai yace ameen ummi , juyawa
yayi ya kalli safna sai fama shan abu take yace ummi kalli
abinda yariyar nan take sha. ummi tace menene shi? jalal
yace wani abune baki wai faten daddawa? ummi tace faten
daddawa ko dai miyar daddawa, safna kawo nagani. safna
ta mike ta nufi gurin ummi ummi ta kalla tace miyar
daddawa ce bar ta taita sha kila ta saba sha akauyen su.
Safna takalli ummi ta sunkuyar da kai tunda take da ummi
bata taba mata rai kamar na yau ba, ta karbi miyar ta juya
zata tafi jalal ya mike ya karbi miyar yana fadin bazaki sha
ba. safna tace kabani miyata ina ruwan ka. jalal yace akwai
ruwana wlh bazaki shaba. safna na ja jalal naja safna ta
juya taga ummi tana kallon su da sauri ta sakar mishi ta
wuce daki tana kuka. jalal zuwa yayi zubar da miyar yabi
bayan safna yana shiga yasa meta ta fito bayi, yace wlh
karna kuma ganin kinsha wanna abin kinji ko, inkuma kinki
zan gayawa daddy, barima nagayawa anty nusaiba, dauko
waya yayi aljihun sa yana dannawa. safna ta mike da gudu
saboda wani amai da taji yana taso Mata . jalal na kokarin
neman anty nusaiba yafara jiyo kakarin aman safna .
.
Da sauri jalal yabi bayan safna ya kamata haka taita amai
jalal na mata sannu, bayan ta gama da kansa ya wanke
mata ya kamo ta suna kokarin fita kairat ta shigo tace yaya
ummi na kiran ka . to yace da ita ya wuce da safna kan
gado ya kwatar da ita , sannan yace toh yanzun me zakici
nasan kina jin yinwa. da saurinta tace miyata zaka bani. au
bazaki bar zancen miyar bako baya gashinan ya lalata miki
ciki, amma bazaki bar shan taba. wlh ni ita kawai nake son
sha dan Allah ka dauko min. jalal yace ai nagaya miki baza
ki sha shiba ni nama zubar da shi. safna najin ya zubar
mata da miya ta fara kuka. jalal mikewa yayi yana fadi abin
naki babba ne , yasa kai ya fita. yana zuwa falo ya samu
ummi har tayi wanka ta fito tace jalal memakon kaje kayi
wanka ka hota . ummi safna ce wannan abun da take sha
ya lalata mata ciki sai faman amai take. wuce kaje kayi
wanka karabu da ita ita tasa ni. cikin mamaki jalal ya wuce
dakin sa yana mamakin wanne irin tsana ummi tayiwa
safna yana cikin wanka ya jiyo kairat tana yiwa daddy
oyoyo sauri ya kara dan dama ya kosa dady ya dawo . yana
gamawa kuwa yafito kananan kaya ne ajikin sa, kayan sun
amshe shi yayi kyau matuka. yana shiga ya nufi daddy, tun
daga nesa daddy yace jalal karka karaso nan dan bazaka
haumin jiki ba mutun sai girma yake amman shi be saniba
jalal be tsaya ba dariya ya fara yana fadin daddy nafa dade
ban ganka ba, yana isa ya zauna daf da daddy ya daura
kashi akafadar daddy yace ina wuni daddy. lfy lau jalal, ya
safna? ai daddy mun kusa batawa da safna, bata jin
magana ta.
.
meya faro kuma kaida safnar taka? daddy wai daddawa
take dafawa tana ci, nayi nayi ta bari taki bari. murmushi
daddy yayi sannan yace jalal karka kara hanata ka bar ta
taci, wata kila Sha,awa take. daddy yau fa ya lalata mata
ciki amai tai tayi fah dazun, yanzun ma tana cen kwance,
bayan sun fito safna har lokacin bacci take, gidan hajiya
suka wuce suna isa alhaji ya shiga yana fadi , jalal tashi
yariyar nan ta kwanta sosai. jalal na taba safna ta mike ta
fito amman jiri sai dibanta yake, jalal ya riketa, ahaka suka
shiga ciki, wannan shine zuwan humaira na farko gidan
hajiya, saidai kuma jikinta babu kwari. folo suka same su
har anty nusaiba suna shiga hajiya tace kawo ta nan kusa
dani ta kwanta, anti nusaiba ce ta dafa safna tace safna
meya sameki, duk kinbi kin lalace sai kace ba amarya ba.
sai alokaci safna ta sake kuka, anty ni yunwa nakeji , kuma
nasha wahala nayi miyata yaya ya zubar min wai bazan
shaba. da sauri anty ta juya barayi jalal tace me yasa ka
zubar mata, kana hauka ne? jalal yace anty kisan abinda ta
mayar abincin ta, daddawa fa take tafawa taita faman sha ,
kamar wata mahaukaciya. daddy na daga gefe yana jinsu.
hajiya tace wata kila kaine mahaukacin banda abinka jalal
dacen tana ci ne, tunda kaga tana ci ai saika tuhume ta,
amman ba laifin ka bane, zaliha ce babban me lefi. jalal har
yanzun bai gane me suke nufiba. hajiya ta sake cewa safna
sai ki fada wani abun da kike so adafa miki . safna kasa
tayi da murya tace ni irin miyata nake so. da sauri anty
tashi ta shiga kitchen. jalal matsawa yayi kusa da safna
yace wai ke lafiyar ki kuwa. be gama rufe bakiba yaji ta
kwaro mai amai ajiki, jalal be damu da aman dake jikin shi
ba yaje ya rike safna.
.
hajiya ta mike tarike safna tace jalal jeka ka gyara jikinka,
jalal fita yayi arude alhaji ya bishi da kallo. jalal na fita
aman ya tsaya toilet ta wuce da ita tahada mata ruwan
wanka, fitowa tayi ta wanke kayan safna ta shanya, safna
nafitowa anty nusaiba tayi daki da ita, zanin hajiya ta bata
ta daura ta hada mata da karamar riga, tace to muje ga
miyar cen na gama. suna fitowa suka samu hajiya suna ta
fira da alhaji, jalal kuwa ya kwanta akan kujera, babu riga
ajikin sa sai faman danna waya yake. safna ko tana
shigowa ta toshe hancinta. anty nusaiba ta kalli safna tace
meye kuma? daurewa kawai tayi tace babu komai anty ni
daki zan zauna. anty tace a,a ki zauna cikin mutane zakifi
jin dadin jikin ki. haka safna ta zauna badan ranta ya soba
dan ita kusa da jalal ne bata son zama saboda wani irin
wari yake mata. karban miyar tayi ta fara sha, dadi sosai ya
mata domin anty har hanta ta zuba aciki, daddy kuwa kalon
safna kawai yake yana murmushi, shikuwa jalal gani yake
be kamata su biye mata taita shaba. zuwa cen safna tace
anty kicewa yaya jalal yaje waje. anty tace akan me zai
fita? Jalal ma tashi yayi ya zauna yana jira yaji me zata ce.
safna tace anty wlh wani irin wari yake min, zai sani amai.
da sauri jalal ya nufo safna Ina wasa dake ne , dan kin
rainani zakice ina wari.
.
Alhaji ne ya da katar da jalal kar ka taba yariyar nan kabar
ta taji da abin da yake damun ta. daddy bakajin abin da
take cewa ne wai nine nake wari. eh naji zo muje gida gobe
kazo ka duba ta. daddy to safna fa anan zamu bar ta? alhaji
yace eh, ke nusaiba gobe ki tam yi mijinki in yabar ki kizo ki
kaita asibiti, nusaiba ta amsa, alhaji ya juya yana fadin jalal
zomu tafi. jalal kuwa ya kulu iya kuluwa yana gani daddy ya
fita yace wlh zaki sani bakin ga suna goyan bayanki ba har
kike cewa ina wari ko, yana gama fadan haka ya fita da
sauri. ahan yar su ta zuwa gida ne alhaji yace meye naka
na damuwa dan ance kana wari, kasani ko ciki gareta. jalal
yayi shiro cen yace daddy cikin haihuwa? eh mana ko baka
sone? sai alokacin kunya ta kama jalal ya dukar da kai.
alhaji yasa ke cewa dakai fa nake magana. jalal yayi kasa
da murya yace ina so. kana so amman kake ta mata fada?
jalal ya sake cewa daddy ai ni ban kawo tuna nin haka ba,
nadauka kawai kwadayi ne. alhaji yayi dariya yace wa yaga
jalal da d'a jalal ma dariya yayi, ya shiga tunanin yanzo in
ummi ta sani yaya zata yi, gaskiya be so ciki yanzon ba
yaso sai sun tare agidan su. sun kusa gida gaban jalal sai
faduwa yake kar fa daddy ya fadawa ummi dan yaga daddy
marna yake sosai bakin shi yaki rufowa. jalal ya fara sosa
kai, alhaji yace jalal akwai magana kenan, gaya min me
yake damun ka. daddy dama zan ce ne karka gayawa
ummi.
.
tuni murmushin dake kan fuskar sa ya gushe yace saboda
me? rasa abun da zaice yayi sai cen yace ina ganin kamar
bazata so bane. fada alhaji ya fara kada Allah yasa taso,
abon kunya kayi, ko cikin shege ne? da sauri jalal yace a,a
bayan sun shiga gida ummi ta tare su da murna jalal ya
wuce dakin sa. bayan wucewan jalal ummi duk ta kwashe
yadda akayi zuwan su gidan goggota gaya mai, alhaji
nisawa yayi sannan yace ya kamata agayawa baffa domin
su tabbatar ta mutu hankalin su ya kwanta kuma suyi mata
ardu,a. ummi tace alhaji bazan iya tunkaran su da wannan
maganar ba, da dai ace na samo yariyar ne sai naje. alhaji
yace kibani hotan na tafi dashi sai nayi musu bayani. bayan
subar wannan zancen alhaji yace zaliha wai yaya kike ganin
yaran nan jalal da matar sa suna dai zaune lafiya ko? ummi
ta tabe baki tace nidai alhaji a inda nake ganin su kamar
basa zaune lfy, shima da yake rawar kai naga ba kamar da
ba. alhaji yace nikuma sai naga kamar yarinyar ciki ne da
ita. haba dai alhaji wani irin ciki kuma. alhaji yace ban gane
haba dai ba, sai kace wadda bata da miji. da sauri ummi
tasha kwana a,a alhaji ai dama ba cewa nayi bata da miji
ba, nidai banga alamun ciki bane, atare da ita. ai dama
bazaki gani ba saboda ba kula kike da itaba, da jalal ne bayi
da lfy har yake amai bazaki ce baki sani ba. eh alhaji jalal
ya gayamin safna tana amai amman alhaji ai ba lallai sai
ciki ba ne ake amai. alhaji yace toh yariya dai tana ce babu
lfy. mikewa tayi bari na gan ta. alhaji yace ai gidan hajiya
muka baro ta, ummi ji tayi babu dadi.
.
washe gari jalal ya fito da safe zai tafi gidan hajiya. ummi
tana ganin shi tace ina zakaje da sasafen nan bayan yau
babu aiki. ummi zanje gidan hajiya ne, in duba safna. zonan
ka zauna babu inda zakaje. ummi bata fah da lafiya ne. eh
naji zoka zauna bayan jalal ya sauna ummi tace wai me
yake damun safna? jalal yace nima ban sani ba. ummi ta
sake cewa toh waye yace wa alhaji safna tana da ciki?
gaban jalal ya fadi da saurin sa yace ummi ban sani ba.
ummi ta sake cewa jalal ina fatan dai babu abinda ya shiga
tsakanin ka da safna? shiro yayi kan shi akasa, gaban shi
kuwa sai faman faduwa yake dan gaskiya yana matukar jin
kunyar ummi sa, kartaga yaki jin magarta. cikin fada ummi
tace dan ubanka bada kai nake magana ba. sai alokacin
jalal yace ummi babu komai kasa ka rasawa yayi dai dai
lokacin alhaji ya fito. alhaji yana fitowa yace jalal kana
nufin cikin da safna take dauke dashi ba na ka bane?? jalal
mikewa yayi yace nawa ne daddy. mikewa ummi tayi tace
wlh alhaji karya yake zai dai rufa mata asiri ne , amman
bata taba kwana dakin sa ba. alhaji ya juya yace haka ne
jalal, ka fada min gaskiya? jalal ji yayi kamar ya tsaga kasa
ya shige ayau zai kar yata mahaifiyar shi kuma in yayi shiru
beyiwa safna adalci ba. alhaji ya sake cewa jalal dakai
nake magana, dama baka taba kwana daki daya da safna
ba?? dukar da kai yayi hawaye na zuba afuskar shi yace
mun taba daddy sau biyu.