RABO NA CE 13
RABO NA CE 13
.
Haka Shaheed ya k'are tunane-tunanen sa har bacci ya
d'aukeshi. Ita kam Ummey batayi bacci ba a daren yanda
taga rana haka taga dare. Da safe Dady ya Shigo d'akin
Ummey, yana kallon ta tausayin ta ya kama shi ya daure
yayi na maza. "Ummey nasha gaya miki cewa duk abinda
ya sami bawa to k'addara ce daga Allah, kuma haka Allah
ya rubuta zai sameshi saidai kawai bawa yayi addu'a duk
jarabawar da zata zo masa Allah ya bashi imanin cinye
wannan jarabawa, kiyi tawakkali ki mik'awa Allah lamuran
ki zai miki sakakkaya......"
.
Bata bari Dady ya k'arasa fad'ar abinda yakeson fad'a ba ta
katseshi cikin kuka. " Dady miyasa ni kadai ake jarabta a
gidannan ? Miyasa banga Ana jarabtar Yaya Ali ba, anti
Najma Anti Ummul-khairi, miyasa saini Dady? Nice
HEPATITIS,( ciwon hanta) kuma yanzu ga abinda ya faru
dani Miyasa ni?? miyasa Dady....!!!" Ta k'ara she zancen
tana fadawa jikin Dady nata had'i da wani kuka mai ban
tausayi, Dady yayi shiru a hankali yana rarrashinta,
"Ummey kada ki sabawa Allah fa.! Zafin abinda ya sameki
kada yasa ki fad'i maganar da bata dace ba, bakisan cewa
babbar daraja tana tare da babbar jarabawa? haba Ummey
na! Ke ba jahila bace, Kiyi tawakkali ga mahaliccin ki shine
ya tsara miki rayuwar ki haka, so ki gode masa, sai ya k'ara
miki baiwa Amma wannan zancen da kike bai kamacekiba"
Haka Dady yayi ta rarrashin ta har ya samu ta saki jikin ta
tayi istigfarin abinda ta fad'a. "Ki shirya gobe zamu koma
asibiti dama Kinsan bayan wata shida ne likita yace mu
dawo a k'ara dubaki, kuma akwai buk'atar ki koma a miki
wani test d'in jinin, Allah ya 'kara tsarewa" Ta amsa masa
da "To" Ya wuce office d'in sa, zuciyar sa a cunkushe da
bak'in ciki yana tunane-tunanen, Ashe haka iyaye suke
kwasar bakin ciki idan aka ma yaransu haka? Sai yanzu
yake tuna wani abokinsa sa da yazo yana kuka sabida
anma yarsa fyade, sai yau yake d'an d'ana abinda yakeji,
yanzu fyade ya zama ruwan dare a duniyar nan, manya da
yara duk Ana musu. Babban abin bak'in ciki yanda ba wani
mataki da aka d'auka akan masu aikata haka kuma an san
dasu, yanda ba wani mataki da ake d'auka akan masu
aikata haka. Har ya isa office yana tunani yanda k'asar nan
ta lalace kuma hukuma tana kallon abubuwan da yake
faruwa amman ta kasa daukar mataki a kai yajaa wani
dogon tsaki. Wayar umme ce tayi k'ara kallon wayar kawai
tayi ta kawar da kanta Amma bata d'aga ba, ta k'ara yin
k'ara tana kallon sunan mujaheed baro-baro wani tsaki taja
ta yamutsa fuska, ta tashi daga gurin ta koma palo. fitarta
ke da wuya kamar an wurgo Muhammad a d'akin ko me
yazo nema ohoooo! yana kallon wayar tana ringing yaga
mujaheed ne har ya k'ara tsinkewa ba'a samu d'auka ba,
shi kuma Mujaheed da naci ya k'ara kira sai Muhammad ya
d'aga. " Hello Uncle Mujaheed Aunty Ummey bata nan,
kuma ko tana nan bazata d'aga ba, kasan fa bata da
lafiyyah, jiya ma kowa yayi kuka a Gidan ni kadai ne banyi
kuka ba" Cikin mamaki mujaheed yace "Subhanallahi...!!
Muhammad ne?? Meya ke damunta meyasa kowa yake
kuka.??" "Nima ban san abin da yake damunta ba, amman
dai ranar da mukaje asibiti kasan da ni akaje, to likita yace
tana da ciwon hy patatos k'ila ciwon dankali yake nufi ko??
Kuma jiya naji ance wai anyi mata fade shine naga kowa
yana kuka Aunty Najma naji tana fadawa Aunty Ummul-
khairi a waya wai an mata fade kuma ka..."
.
Mujaheed ya katse shi cikin k'araji. "Don't tell me Ummey
she's HEPATITIS, and also she's rpd what kind of nonsense
is dat? garin ya za'ayi mata fade??" Muhammad yace.
"Yace ohooon musu! kai ka gane ciwon ne hala? ni fa
bansan meye ciwon dankalin ba kuma ai naga ana dafa
mata dankali ana bata tana ci kuma ance ciwon Dankali"
Mujaheed yaja wani dogon tsaki yace "Shirme kawai, Ba
yanda za'ayi ama babban mutum fyade, wallhy sai da son
ranshi, sabida haka da son ranta ta aikata, & thanks God
ban aure mace mara lafiya ba da sai lik'a min a banza,
ciwon ma HEPATITIS, waiiii. thanks God wooooo"
Muhammad yace "Look at this Uncle, ai a islamiya malamin
mu yace mana idan mutun baya da lafiyyah addu'a zamuyi
masa, har yaji sauk'i yace kar mu kyamace shi even
yanada HIV, sabida basu suka d'aura wa kan su ba Allah ne
ya d'aura musu Amman kai kana babba..." Mujaheed ya
katse shi cikin wani irin tsawa sai da muhammad ya firgita
yace mishi. " Ai gara HIV da cutar yayar ka sabida....." sai
muhammad ya katse wayar ya fito pala, duk haushi ya
kamashi, had'uwa yayi da Mumy ta fito daga d'akin ta. "
yawwa Mumy kinga wannan uncle mujaheed d'in, kawai
dan na fada mishi anyi wa Aunty Ummey fade, and also
bata da lfy yake..." Mumy cikin hanzari ka kifa masa wani
wawan mari sai da ya kife a K'asa, bakinsa ya bugu har sai
da bakinsa ya fashe da jini, nan da nan hak'orinsa, ya fita
tasa kafa tayi ball dashi, har sai da yakai gurin da Ummey
take zaune, da gudu ya mik'e ya k'ara sa gurin Ummey "
Wayyo Aunty Ummey wayyo jinina...! Wayyo hak'orana...!
Kinga Mumy zata kashe ni" Mumy ne tayi kansa kamar
mayunwacin zakin da ya hango barewa a dawa, Ummey
duk da batajin jikin ta dai-dai sai ta mik'e ta boye shi tace,
"Mumy Dan Allah kiyi hak'uri ki yafe masa, waima meya
miki haka??" Muhammad da yake bayan ta a b'oye
hak'urinsa d'aya da ya fita ya rik'e sa gam a hannunsa
yana wani irin kuka. " Yace kawai dan na fad'a ma Uncle
Mujaheed kina da...." Yayi ajiyar zuciya yajaa majina a
hancinsa. "Kina da hy patatos...... kuma anyi miki fade. .....
.
Wai shine kawai take duka na" Mumy cikin bacin rai ta
finciko shi ta kwada masa wani mari sai da ya kai k'asa ya
fasa wani wawan ihu Ummey tayi kansa da gudu Mumyn ta
ture ta dukda bata da karfi a jikin ta amman tayi nasaran
janyo shi Mumy tace "Wallahi yau Muhammad sai ka fad'a
min uban wa yace maka tana da HEPATITIS! kuma wa ya
gaya maka an yi mata fyade," "Wayyo Aunty Ummey zata
kashe ni, ki gaya mata ranar da mukaje asibiti ne likita ya
fad'a naji....... kuma ai naji Anti Najma na gayawa Anti
Ummul-khairi....." "Ummey tace Mumy ki bar shi ai ba
k'arya ya fad'a ba, ina da HEPATITIS, kuma anyi min fyade"
Ta k'arasa maganar tana wani irin matsanacin kuka Wanda
yasa jikin Mumy yayi la'asar.
.
Wasu hawaye new suka gangaro a idon ta cikin rashin
kuzari tabar gurin, Ummey ta rungume Muhammad tana
kuka yana kuka, gwanin ban tausayi haka sukayi ta kuka.
.
Ya Ali ne ya shigo ya gansu a hakan suna ta kuka
Muhammad yayi jikinsa da gudu ya fara bashi labarin dukan
da Mumy ta mishi, yake tambayarsa miyayi ta dakeshi,
lbarin abin da ya faru ya baiwa Ya Ali, Ya Ali ya daka mishi
mishi wani tsawa, Wanda gara na Mumy sau d'ubu akan
shi, Muhammad yana ganin yayi wannan tsawar ya gudu
bayan Ummey, sabida har yana k'ok'arin kai masa duka..
Ummey cikin kuka tace "Meyasa kuke haka ne?? ba gaskiya
ya fad'a ba? k'arya ne bani da HEPATITIS?? k'arya ne
ba'ayi min fyade ba, ku barshi nana!!" yaya Ali yayi mata
wani kallo me cike da ban tausayi yama rasa abin da zai
fad'a sai kawai ya wuce ya bar su. Haka ranar suka wuni a
gidan, Muhammad bashi ba mafaka sai gurin Ummey,
sabida ya fahimci kowa idan yaji abinda ya aikata neman
dukan sa yakeyi, har Dady ya dawo gida, Muhammad baiyi
gigin gaya masa ba, sabida yasan zaiyi masa dukan da yafi
nasu Mumy.. Mumy ce tayi wa Dady bayanin abin da ya
faru Dady yace "Kai Hajiya meya sa zaki dake shi?? Ai yaro
ne, yanda Muhammad yake son Ummey da yasan cewa
fadan wannan abun illa ne wallahi ina da yak'inin bazai
fad'a ba, sabida shi kanshi yasa cin zarafi ne ga Yar uwar
sa amma da yake baisan illar haka ba kinga ya fad'a."
Muhammad ya kwalawa kira, Amman Muhammad yanaji ko
motsi baiyi ba, da Dady ya gaji da kira sai ya fito waje yace
" Yaron Dady bakaji Dady yana kiranka ba??
.
To kazo na siyo maka PSP kuma akwai game din uncle
Shaheed d'inka a ciki" Muhammad ya turo baki, "Bayan yau
an jij jibgeni kamar jaki a gidan nan, kowa sai hararana
yakeyi, kawai dan na fad'awa Uncle Mujaheed cewa Aunty
Ummey tana hy patatos, wannan dai ciwon na dankali,
kuma an mata fade" Dady yayi dariya sosai, wai ciwon
dankali, wato HEPATITIS d'in da yaji ana fad'aya d'auka hy
patatos ake cewa, yaro yarone Dady cikin hikima ya
tambaye Muhammad yanda sukayi da Mujaheed
Muhammad ya fada masa daga farko har karshe, Dady
cikin dabara yace " Amman kaga Muhammad kar ka k'ara
fadawa kowa Auntyn ka tana da ciwon dankali ko anyi mata
fade kaji? tunda yanzu kaji abin da Mujaheed yace akanta,
kada ka k'ara fadawa kowa kaji yaron Dady" Muhammad ya
kad'a kanshi alamar yaji kuma ba zai k'ara fad'a wa kowa
ba, bakin shi ya kumbura sum tum Mumy ne ta fito daga
daki ta Harare shi. Shima ya Harare ta yaje dai dai kunnan
Dady yace "Dady daga kai sai Aunty Ummey nake so, sai
uncle Shaheed dina".
.
Haka dai Dady ya samu ya hana Muhammad zancen cikin
hikima irin tasu ta manya, bayan nan ya ma Ummey
bayanin abinda Mujaheed ya fad'a ma Muhammad tayi
mamaki matuk'ar gaya, waima dan shirme zai zauna yana
zancen da Muhammad, miye laifi idan ya gaya mata da
bakinsa, tayi matuk'ar mamakin sa sabida yanda take kallon
Mujaheed wani bawan Allah dashi, gashi duk gidan kowa ya
yaba da hankalin sa, kuma ya samu shiga ba kad'an ba,
sau da dama takance idan kowa ya k'ita tasan Mujaheed
zai sota, Amma lokaci d'aya ya barta ba tare da yaji ta
bakin ta ba, tana tsaka da tunani wayarta tayi k'ara ta kalla
Shaheed ne a ranta tace "Bama zan d'auka ba nasan bazai
wuce kace ka barni ba" har wayar ta tsinke SMS ya mata, "
miyasa kike azabtar da zuciyar da take k'aunar ki." Ta
karanta ta k'ara karantawa ya k'ara kira nan ma tak'i
d'auka, ya k'ara mata SMS, "Please pick my call Ummey
na!!" Sai kawai ta bushe fitilarta ta d'auki wayar, wani ajiyar
zuciya yayi, "Haba Ummey yau kwana biyu kin daina
d'aukar wayata ko nayi laifi ne?" Shiru tayi wata zuciya na
raya mata ki gaya masa kawai ki huta idan zai iya to, idan
ma zai barki ya barki da hujja, "Kinyi shiru Ummey" Ta
had'iye wasu busassun yawu tace "Uncle Shaheed Ina ganin
zamu hak'ura da juna ne sabida kaga ni am ........ "
.
"Sheeeeeeeeeeeeee!!!" Ya katseta da sauri "Don't tell me
anything Ummey, am already knew everything, so ki
kwantar da hankalin ki Ina sonki ne, kuma zan zauna dake,
a da nayi tunanin ke kike sona shi yasa na tsaya bata lokaci
tun farko Amma Ummey na dad'e da sanin ke RABO NA
CE ! Kuma zuciyata da gabban jikina sun aminta dake, zan
aurenki da dukkan sharuddan ki, zan aureki da zuciya d'aya
Ummey! Ina sonki kuma nasan duk abinda ya sameki
k'addara ce daga Allah, sannan bakeba koni, ko k'anwata
ko wani wana Allah zai iya jarabtar d'aya daga cikin mu,
idan ya jarabcemu sai na gudu ??" Hawaye ne suka gangaro
a idonta, "Kina jina kuwa? " Tayi ajiyar zuciya, "Ina jinka
Uncle" Haka yayi ta mata zantuka masu sanyaya zuciya har
saida taji natsuwa a zuciyarta kuma bai gaya mata ya iso
sokoto ba, sabida yayi Alk'awari sai ya d'aukar mata fansar
abinda prof Dan jumma ya mata, sabida duk ya tuna abin
da aka gaya mishi, na cewa wani ya mishi shigar sauri, sai
yaji kamar ya had'iye zuciya dan bak'in ciki. Ranar Ummey
tayi baccin farin ciki, Allah ya bamu masu sonmu da
gaskiya.
.
Da safee ta shirya zuwa asibiti ba'a dad'e ba sai ga Dady ya
fito Muhammad suka gani yayi zuru- zuru yana kallon su da
kunburarren bakin sa, nan dai suka gane mi yake nufi, Dady
yace yaje gun Nafeesa ta shirya su tafi, Mumy ce ta fito
d'aki da taji ance a shirya Shi, ta watsawa Muhammad
harara. "Kai wuce d'aki ko na k'arasa ka yanzu nan, ba inda
za'a tafi dakai mai surutun tsiya kawai" Dady baiko kalleta
ba yace " Nafee Anka ki wuce dashi ki shirya shi yanzu
muna jira," Ya juyo ya kalli Mummy cikin bacin rai yace
"Miyasa kike masa haka ne eh? A tunanin ki da hakan zai
daina ko fandarewa zaiyi? yaro d'an rarrashine ban sanki da
haka ba wannan ba halin ki bane" Batace masa komai ba ta
wuce d'akin ta Nafee anka ta shirya Muhammad suka wuce
asibiti a mota yace "Daddy kalleni cikin madubi duk na cire
kyau na dawo mummuna, kalli bakina Dady" Dariya sukayi
Dady yace, "Kananan kyakyawan ka yaron Dady, bakayi
muni ba" haka har suka isa asibiti sun sami ganin likita inda
suka bashi duka takardun ta da komai nata, Dama tun
zuwan su na farko an rubuta musu hoton da za'a mata a
k'irjin ta, kuma anyi hoton an kawo ma likita, ya k'are dube
duben sa ya d'ago ya kalli Ummey, "Kina samun sauk'i, kina
Chan maganin da na rubuta miki ko??" Ta gyada kai alamar
Eh, "Yauwa yanzu zan rubuta miki wani test d'in sabida
muga tasirin da maganin yayi a jikinki, idan an samu chi
gaba sai na rubuta miki allurar da zakiyi shima zai taimka
sosai, kilama ki warke gaba daya," Zaro ido tayi "Dr Ana
warkewa a CHRONIC Dama? Kaifa kace ba'a warkewa
please kada kayi hoping d'ina akan abinda bazai yiwuba!!"
Likita ya gyara glass d'in sa yace, "No Ummey ba haka
bane, shi kanshi CHRONIC d'in( mai tsanin Wanda baya
warkewa) akwai adadin da yake kaiwa bazai warke ba,
akwai kuma Wanda da taimakon allurar PEGYLAYTED
INTERFERON INJECTION ko kuma wannan maganin dana
baki zai iya warkewa dukda cewa CHRONIC ne, don't
confuse please" Gyada kai tayi almar ta gane, Dady yace
"kenan ACUTE ne ko Dr." No CHRONIC ne Amma still idan
baiyi k'arfi sosai sosai ba, zai warke shima" duk sun
fahimta.
.
Likita yace "Yanzu Amma kamin ayi allurar sai Munga chi
gaban da aka samu, sabida ba ko wane irin HEPATITIS B
bane ake yiwa allurar kaman yanda na fad'a muku, dole sai
Munga ci gaban da aka samu a jikinki, shiyasa farko ban
rubuta miki allurar ba na fara baku wannan LAMUVIDINE
d'in, sabida maganin yana taimakawa sosai musamman
gurin taimakon LIVER (hanta) daga kamuwa da CANCER" Ya
kalli Dady "Alaji hope kunyi allurar riga kafin da akace duk
family kuyi ko?" Dady ya sosa kai, "Ai allurar ce ta cika
tsada, munyi magana da ita mahaifiyar yarinyar akan zasu
kiyaye, Amma an yiwa k'aramin kanin ta sabida shi bayajin
magana," Dariya likta yayi "Haba alaji ka daure kuma kuyi,
sabida Ana tsoron k'addara by mistake zaku iya kamuwa da
ciwon kuma, kuma kasan riga kafi yafi magani," Dady yace .
"In sha Allah zamuyi" Likita yace "Good, yanzu zan rubuta
muku wani drink ta zata rik'a sha zai taimaka mata sosai,
sannan akwai buk'atar kada ta k'ara k'iba daga haka, Zan
baku wani magani shima for diet ne in sha Allah she will be
better" Ya d'auko takarda ya rubuta mata EVIRON HEALTH
DRINK no Alcohol No caffiene No preservative No rifined
sugar, made in Korea, sannan ya rubuta mata ULTRA
NOURISH, shi kuma zai taimaka mata ta yanda zata dai-dai
ta kibarta sabida ba'a buk'atar mai HEPATITIS yayi k'iba
sosai tanada illa matuk'a a jikin mutum, 64 Ya d'ago ya kalli
Dady "Ina fatar Alaji kuna kula da abin cin ta, kada ta rik'a
chin abinci sosai, kamar yanda na fad'a muku tun farko,
zata ci sau hud'u a rana, zaku iya mata abinci mai ruwa
ruwa sabida bashida nauyi a ciki maimakon lokaci daya sai
ta rik'a ci rabi- rabi kuma kada taci abinci lokacin da take
kallon TV, haka kada taci awa biyar before bacci, please a
kiyaye time d'in chin abincin ta yanada matuk'ar
mihimmanci, kuma ta rik'a motsa jiki kada ta zauna guri
d'aya," Haka dai likita ya maimata musu bayanan da ya
musu zuwan farko, sannan k'arshen sati zasu zo su karbi
result na gwajin jinin da zatayi, idan tana buk'atar allurar
sai ya mata, idan kuma bata buk'ata sai asan yanda zasuyi.
Bayan sun fita Dady yaje gurin wani likita abokin sa ya
masa bayanin aika aikar da wani Prof ya mata a makaran
ta, likita cikin jimami da tausayawa had'i da tsinewa Prof
d'in ya had'a ta da wata likita aka dubata ba wani illa da
aka mata a gaban ta, saidai ta rubuta mata takardar kwajin
HIV da HBsAG da dai sauran cutukan da ake d'auka. Direct
d'akin awon jini suka wuce a ka d'ibi jinin ta, za'a mata
gwaji da Wanda likitan ta ya bata da na gurin Matar, Suka
dawo gida.. Shaheed ne cikin wata shiga ta alfarma da
ganin sa zakaga yanaji da kanshi, direct Dan fodiyyo ya
wuce, ya shiga yana bud'e mota sai wani ya ganshi kallo
d'aya ya gane shi da sauri yaje ya kai gaisuwa, kan kace
me fans d'in sa sun zagayeshi dagyar ya samu ya kubuce
musu, Gurin director ya wuce, da yake yanada fans sosai a
gun baisha wahala ba gurin ganinsa bayan sun gaisa cikin
d'aure fuska Shaheed yace masa Ya San abin da ke faruwa
a makarantar sa, Nan danan ya masa bayani sannan yace
an yiwa kanwarsa fyade a makarantar ne shine yazo a
d'aukar masa fansa ko kuma shi ya d'auka da kanshi.....
.
Director shiru yayi, yana nazari tabbas an gaya mishi cewa
Prof d'an jumma yayi ma wata fyade Amma baisan ko
waye ba, kuma baibi ta kan zancen ba sabida yayi busy.
Cikin rashin sanin mafita da matakin d'auka yace "In sha
Allah zamu d'auki matakin da ya dace, kuma zamu
tuntubeka" Shaheed na kallon idon sa ya fahimci ba abinda
zaiyi. Murmushin mugunta yayi idan dai ni dan Nigeria ne
sai na maka Nigerian ci kamar yanda ka mini Prof d'an
jumma.. Saina take hakkin ka kamar yanda ka take nawa
kuma nothing will happen, yana fitowa fans d'in sa masu
jiran sa suka biyoshi ya samu duk ya musu signing sannan
ya wuce, ya sami mai gadi ya sallameshi ya karb'i details
d'in prof d'an jumma gaba d'aya, daga d'an fodiyyo yayi
waya da yaron ministan ilimi na K'asa Dama fans d'in sa
ne, kuma d'an sokoto ne ya gaya masa abinda ya kawoshi
sokoto, da abinda yake buk'ata. yaron mai suna Abdul
Hakam yace an gama. Sukaje gurin baban sa "Dady favor
d'aya nake buk'ata a gurin ka please, munason a lallata duk
wani document na Prof d'an jumma ta yanda duk inda yaje
bazai sami aiki ba har k'arshen rayuwar sa da wannan
takardun please Abbah....." Minstr ya d'ago kai ya kalleshi
ba tare da damuwa ba yace "OK I will do that my son"