Breaking News

*****MUGUN MIJI PART 1*****

MUGUN MIJI PART (1) . ___________NA_______ ZAHARA'U
BABA YAKASAI . A hankali take tukin motar ta end of
discussion green kala ta fito daga number one city da ke
titin IBB way,kyakkyawar mace ce wacce ta amsa sunan
haduwa,hajiya Kareema gefen, ta yar matashiyar budurwa
ce sanye da doguwar riga da Hijab dinta, Deena ta juyo ta
kalli hajiya tace, "Anti ki aje ni a koki ko?'' Hajiya Kareema
ta bata ranta, tayi kicin-kicin tace, "ba zan aje ki ba,ni ban
ga dalilin da kike fifita duk wanda ya danganci ubanki a
kaina ba'' Deena ta sunkuyar ta kanta tana kallon
yatsunta,tana mamakin mahaifiyarta da irin halinta. Ta
gyada kai ta fito da furucin mahaifinta da yake yawan
fadawa mahaifiyar tata, ''duniya zata koya miki
hankali,domin na kula ke ba ki san komai ba a babin
rayuwa ba''. Tabbas ita ma Deena kallon da take yiwa
mahaifiyar tata kenan,ko yaushe ne duniyar zata koyar da
Anti darasi? oho! Haka sukayi shiru babu wanda ya tankawa
wani sai can wayar kareema ta soma kida,ta sanya hannu
ta dauka yadda take kashe murya ya sanya Deena kwanciya
jikin kujerar tana jin wani azababben takaicin mahaifiyar ta.
''Baby na ka iso?'' ta fada tana kashe murya.can
tace,''ganinan zuwa, ka bani minti goma zan iso''. Ta kashe
wayar, Deena ta kasa hadiye takaicinta, ta ce Anty waye
yazo,bako kika yi?'' ta kada kai tace , Bilal ne'' fuskar Deena
ta daure tam, ta ce Anty Bilal fa karamin yaro ne,nifa ina
gaya miki yayi miki kankanta ki aure shi kin girme shi fa''.Ta
dakawa Deena tsawa tace ''so kike na auri tsoho? An gaya
miki ni din wata babba ce banda kaddarar haihuwarku ai
kin san ban isa na haife ku ba,kuma da kike cewa na girme
shi, ai nana khadija ta girmewa manzon Allah S.A.W .
saboda haka kinga ai nayi sunna ko? Deena tace,''tafsirai
da yawa sun nuna nana khadija bata girmi manzo Allah
S.A.W ba, sai dai ana ganin yana shekaru ashirin da biyar
ita ma tana da ashirin da biyar suka yi aure.mafiya yawan
malamai sun yarda da hakan. Ta daka mata tsawa, ''rufe
min baki, zan haife ki a cikina a ce kin fini sanin duniya
ne,ko kin fini hankali. Bilal shine mutumin da naga ya dace
da ni,shi ne wanda zan aura,kuma ke baki isa ki hana ni jin
dadin rayuwata ba, Ita kam Deena tayi shiru bata ce komai
ba,tana mamakin budurwan zuciya irin ta mahaifiyar ta.
Haka suka isa gida,wani makeken gida ne wanda samun
irinsa da haduwarsa na da wuya.cikin G.R.A gidan yake ko
a can din ma gidan yana daga jerin gidajen da samunsu a
gurin ba karamin abin alfahari bane.Mai gadi ya bude kofa
tayi fakin Bilal cikin wasu kananan kaya ya fito, yaro ne
kyakkyawa ajin karshe a kyau.ya hadu matuka fari ne
sol,gashin kansa a kwance yake tamkar gashin mutanen
hindu.Gashi ya dauki gyara na zamani,ya iya daukar
kwalliya domin komai hassadarka Bilal yayi. A hankali ya
ringa taku ya bude mata kofa yana wani irin murmushin
burgewa yana kallonta tsakiyar ido irin kallon da maza 'yan
duniya ke yiwa wayayyun mata. "My Dear kin shanyani fa,"
Tace, "haba Baby na muna hanya ne amma yanzu gani na
iso, ai bansan zaka zo ba dama ban fita ba." Yace, "ina gida
kawai naji inaso in ganki, ni kuma idan ban ganki ba bazanji
dadin rayuwata ba, ".