HAUSA NOBLE'S
6.GANGAR JIKINSA NA AURA P6 NA JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
Cikin sauri Hanne tasa hannu a cikin
bokiti dakegabanta tadauko takarda tazo ta
mikawa Babanta da hannubiyu ta dukahar
kasa. Babu abinda wannan saurayi yake
saikallon Hanne sama da kasa kayan jikinta
yake kallo da takalmindakekafarta wanda ta
daure da leda saboda ya tsinkekudin
naninma aiki ne, wata uwar danmara kai
kace dambentsiya za'a kwasa, wuyan, hannu
da kafa tsakiyoyi. Saurayinnan ya kulada lallai
Hanne ita kanta tana jin kunyar shigar
nantata ganinkallon da yake yi mata, sai yayi
sauri ya fara dubatakardar da Malam Habu ya
mika masa. Ya karance tsaf, sannanya dagoya
ce "Hanne Habu Imamu ko? Tace "Eh, ya ce
"ToBaba saikun dan jira don nima nan
Malamin nake jira gashitakamaimai ma ni
bansani ba ko yana makarantar kobayanan
don nima shigowata kenan. Malam
HabuyayiHamma gami da yin dan siririn tsaki
ya ce "Yaroyanzu bayadda za'ayi ka karbi
yarinyar nan, dole sai waccan din ya zo?
Saurayin ya ce "Ni Malami ne amma kuma
bapermanentteacher ba bautar kasa (service)
nazo yi, a ka'idarwannanmakarantar kuma
senior master ne ya kamata ya
karbetamusamman ma kasancewarta
sabuwar daliba ce.Gashi yau lahadi, dama
litinin ce ko sauranranakun aiki lokacin
principal tana nan, da sauranpamanent
teachers duk sai su karbeta koda
seniormaster baya nan, amma yanzu ku jira
kadan idannan da minti talatin bai dawo ba,
zan tashi nima nashiga staff quaters din na
gani ko yana ma cikin makarantar dan nima
shi nake so na gani zan karbimukullan
gidana. Malam Habu ya ce "To Allah
Yakawoshi lafiya bari nayi sallar la'asar, nasan
biyartayi ko sallar la'asar bamu yi ba. Yaro ina
buta? Yanuna masa wani fanfo can kusa
dashi kuma dazagayeyyen waje nan ne
Masallaci. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya
kalli Hanne wacce ke tsaye agefe har yanzu ya
ce "*Yar Baba koma kanakwatinki ki zauna
zanje nayi sallah kinji. Cikinsanyin murya ta ce
"To, ta juya ta doshi wajenakwatin. Malam
Habu ya bita da kallo zuciyarta cikeda
tausayinta ganin yininsu guda babu abun da
suka ci tun dan kokon safe da suka dan
kukkurbaa tsattsaye bala'in Iya Abu ya
hanasu su zauna susha sosai. Malam Habu ya
girgiza kai alamartausayawa kansu da kansu
ya ce "Allah Sarki *yarBaba hakuri dai za ki yi,
ki kuma ci gaba dayi.Sannan ya juya ya nufi
wajen fanfo. Kyakkyawan saurayin nan na
zaune yana kallonsu zuciyarsacike da
alamomin tambaya da tsananin tausayi. Canya
nisa yayi ajiyar zuciya ya zaro gilashin
dakealjihunsa ya saka a idonsa gami da cusa
hular dakehannunsa a cikin aljihunsa na
wando yasahannunsa ya dafe habarsa yaci
gaba da kallon Hanne dake zaune kan
akwatinta tayi lamo tanatunani ba tare da
tasan wani na nan gefenta ta cikingilas yana
kallonta ba. Ya ce a ransa "Wadannandaga
wanne kauye suke?Sun kuwa karanta
takardar dake hannunsusunsan me ya
kamata su tanada suzo dashi? Kaibasu san
dokar da aka rubuta ba a jikin
joininginstruction din nan ba. Lallai kuwa da
sun san meaka rubuta da baza taci uwar
danmarar nan ba tashigo makarantar nan
haka ba. Bayan kamar tafiyar Malam Habu da
minti ashirin sai gashi yadawo. Ya zo ya wuce
ta gaban saurayin ya ce"Sannun ka da
hutawa, ya katse tunanin da yakeya ce
"Yauwa Baba. Malam Habu ya kara da
cewa"Har yanzu dai kaga shiru baizo ba ga
rana nan nashirin faduwa yau kuwa anya mai
karbar yaran nan zai dawo? Yayi murmushi
ya ce "Ina ganin kakawo duk abubuwan da
aka ce ta siya da kudinmakaranta zan yi
kasada na karbeta yanzu in yasoranar litinin
wato gobe idan mutum yazo ya rubutarisitai
yanzu sai nayi magana da masu gadin get
dinHostel su kirawo prefect din.... Malam Habu
ya matso kusa dashi ya ce "Yaro fadamin da
Hausasosai na gane me kake cewa?