HAUSA NOBLE'S
7.GANGAR JIKINSA NA AURA P7 NA (JUT)
Ya ce "Eh
Baba, ai a rubuce ajikin takardar aka rubuta
za'a dinka mata kayanmakaranta har kala
hudu, wanda zata sa idan zasuaji da wanda
zata saka a dakunansu, dana wasanni (sport)
duk an rubuta kuma lallai-lallai sai da
kayanmakaranta za'a karbeta ba zata ta saka
kayan gidaba, sannan daga karshe aka
rubuta zata zo dakudin makaranta (school
fees) shi kuma dakesabuwar zuwace sai kun
biya sama da dubu.....Malam Habu ya katse shi
da sauri ya ce "Tsaya yaro karma ka
kirawomin wadannan dubunnai. Ta faruta
kare wai anyiwa mai dami daya sata, yaro
nagode madallah, sai anjima. Malam Habu ya
juya batare da ya jira amsa daga bakin
saurayin nan ba yadoshi inda Hanne ke zaune
da saurinsa kamar zaikifa cikin gaggawa, ya
ce "*Yar Baba tashi maza mu tafi ga magariba
ta kawo kai. Cikin sauri ta mike yaciccibi
akwati ya dora mata akai ya sungumi
bokitida katifa suka kama hanyar get din fita.
Sunyi takudaya biyu sai sai suka ji magana
kamar daga samaance "A'a Baba ina zaku
kuma? Su duka suka juyadan ganin mai
maganar sai suka ga wannan kyakkyawan
saurayin ne ya taso yazo wajensu.Malam
Habu ya ce "To yaro me zamu yi in ba
tafiyaba, dubunnan kudi fa naji kana kira,
kuma ka tsayacak ka kalleni dani da dubu
daya ma waye ya ajiyewani? Daman kansilan
garinmu ne da maigari sukasani dole na
kawo *yar nan makaranta, suka ce za'a aiko
da kudin, na tabbata har ga Allah basusan
kudin yakai dubunnai ba da suma basu
tankaba. Kuma kudin gwamnati ba'a bashi
babu yaddaza'ayi nazo na ajiye yarinya a
makaranta babukudin makaranta babu kayan
makaranta na ce abimu bashi zamu kawo ba.
"Wannan ba zai yiwuba, inji saurayin. Malam
Habu ya ce "To ka gani cewasuka yi na zo na
kawo ta za'a aiko da kudin kumayadda naji
kalamansa shi kansilan a tunaninsakudin
makarantar bai wuce dari uku ba, bai
sandubunnai bane kuma koda shine yazo ya
kawotaaka kira dubunnan nan cewa zaiyi ta
fasa karatun. Don karamar hukuma baza ta
biya wadannanmakudan kudin ba.Saurayin
nan yayi murmushi ya girgiza kaiya ce "Amma
Baba bai kamata daga kirandubunnan nan ka
kwasheta haka da sauri kacezaku tafi ba.
Malam Habu ya fara jin haushinsaurayin nan,
ya ce a ransa "Wai shin wannan dukzancen
nan da ake bai gane ba ne? Makaranta sai da
kudi kuma babu kudin jiran me zanyi, ko shi
baisan babu ba ne? Saurayin nan yaci gaba
da cewa"Baba kuzo ku ajiye kayan nan bai
kamata ka juyada yarinyar nan ba, ai bai
kamata ba. Ta cimakaranta har kun shigo
cikin makarantar sannanku kwasa ku tafi ka
ce ka fasa, babu fa abin da Uba zai yiwa
*yarsa a duniya in ba ya bata ilimi ba,yarinya
kamar wannan ai kamata yayi tanamakaranta
tunda bata isa aure ba, me zata yi agidan?
Malam Habu ya sake jin haushin saurayinnan
kamar ya doke bakin da yake masa
wadannankalamai ya ajiye bokiti dake
hannunsa ya ce "Yaro, wai shin a harshen
Hausa idan akace babu me akenufi? Yayi
murmushi ya ce "Baba kenan, na gameduk
dalilan da kake nuna min yanzu, ni kuma
abinda nake so na rokeka shine ka fasa tafiya
da itatunda ka kawota har cikin makarantar
ka kyaletatayi karatu. Abun da ya kamata ka
tambayeni shine tayaya zata yi karatu tunda
babu kayan makarantababu kudin
makaranta? Malam Habu ya ce "toyanzu
nasan ka gane babu,ta yaya zata yi
karatubabu kudin makaranta babu kayan
makaranta?Kyakkyawan saurayin nan ya ce
"Yauwa Baba kayitambaya mai kyau, amsar
tambayar ita ce in Allah Yaso Ya yarda Hanne
zata yi karatu in har kaamince ka yarda zaka
ringa turo ta makaranta dazarar hutu ya kare
ba sai ta fara ba kace baza tadawo ba ka cire
ta.Idan kayimin alkawarin haka kuzo ku
ajiyekayan nan ka tafi ka barta. Malam Habu
yayi jigumyana tunani, a ransa ya ce "Wannan
yaron me yakenufi? Hanya zaiyi mana a dauki
Hanne babu kudinmakaranta babu kayan
makaranta ko kuma yayaza'ayi? Bana tunanin
dai shi zai biya mata kudin makaranta harda
dubunnan da ko karamarhukumar mu baza
ta iya biya mata ba yaddazamanin nan ya
canja masu kudi basa taimako,babu yadda
za'ayi yaron nan ya zare makudankudi ya
baiwa yarinyar da bai santa ba bai tabaganin
ta ba bazan bar *yar Baba a makarantar nan
ba in tafi ta wulakanta ba, wacce bata san
hanyarda zata bi ta koma gida ba idan an
korota. Yanzuakan Naira goma masu mota
suke kokarin sudanneni su dauka ina ga
dubunnan kudade gakayan makaranta har
kala hudu waye zai dinkomata? Saurayin nan
ya katse Malam Habu daga tunanin da yake yi
ya ce "Baba tunanin me kake yine? Karka yi
kokonto ba zaka yi dana sanin barinHanne a
makarantar nan ba in Allah Ya yarda
babuabin da zai sami Hanne sai alheri da
kwanciyarhankali ka tsarkake zuciyarka ka
danka Hanne gaAllah wanda a koda yaushe
Yana kallon halin da bayinsa suke ciki na
kunci kona farin ciki, sannanka danka Hanne
amana ce a wajena.
Banso ace sai dai kawai a karanta a kara gaba ko?
Comments naku neh yake karamin karfin guiwa har nake
bata lokaci Ina rubuta maku labari duk tsayinsa.