MIJIN MARAINIYA PART 9
MIJIN MARAINIYA PART 9
.
Alhaji ya kalli jalal yace duba nan jalal tashi ka zauna ,
kasan yazun yaya za,a ,tashi zakayi kaje ka lallashi matar
ka, koma me ka mata kaje ka bata hakuri zata saurare ka.
shiru yayi ya ya mutsa fuska ni dai daddy ka tai makeni ka
bata hakuri. alhaji juyawa yayi ya kalli ummi gace zaliha ke
kika lalata garon nan shagwaba tama sa yawa kuma
yanzun ke kin zame kinbar ni dashi. dariya tayi wani irin na
zame nima fah yana min. alhaji ya juya ya kalli jalal ya
kwashi da dariya yace zaliha maza Kira min safna naga
abin babba ne . ummi waya ta daga ta kira safna daure wa
kawai take tana yashe baki dan bin shawarar kawar ta
madina. safna tashigo tare da sallah ma dasauri ummi tace
zonan 'yata safna ta karasa kusa da ummi, ummi tasa
hannuta ta jawota ta daurata akan cinyar ta , tace safna me
jalal yayi miki da zafi haka ne ? ummi ni baiyin min komai
ba. jalal yace a,a safna namiki laifi kedai kawai bazaki fada
bane. alhaji yace zonan safna ,sauka tayi ta koma gaban
alhaji kusa da jalal ta zauna. yace koma me jalal yayi miki
kiyi hakuri ki yafe mishi kinji yasan cewa yayi laifi kiji ko?
daga kai tayi ,alhaji yace yauwa safna haka akeso jalal
kuwa bin safna kawai yake da kallo alhaji yace to jalal tashi
ka dauki matar ku kutafi shi besan cewa ummi ta raba
musu daki ba. bayan sun fita ummi nata sauri tabi bayan su
alhaji ya dakatar da ita. zaliha ina da magana dake , ta
koma ta zauna . yace kina zuwa gurin su baffa kuwa? a,a
kwana ki naje akace sun tashi alhaji wani abune ya faru?
a,a ba abinda ya faru, amman me yasa baki neme inda suke
ba . mike wa tayi zata bar wajan. alhaji yace saboda basu
da kudi ko. komawa tayi ta zauna tace aini dama tunda
naga yan uwan ka sunzu bikin nan nasan sai su kulla min
wani sharrin. alhaji yace basu suka fada ba baffa da kanshi
ya fada haka. mikewa tayi alhaji aina kaga baffa? aini tunni
nasan inda suke tun bayan koran ron su da kikayi kokaci
bananan baya sati biyu na dawo tun kafin nashigo gida jalal
ya gaya min baffa yazo kin kore su, abin ya bani mamaki
amman bayi miki magana ba na nufi gidan nasa me su cikin
ma wuyacin hali bafffa ba lfy mama haka , sai yaya rabi ce
akan su itama kuka take.anan take gaya min saudatu ta
bata wanda har yau ba,a ganta ba. bayan nakai su asibiti
kwan su uku aka sallame su. tunda ranar nakai su wani
gida na dana saya baffa kin shiga gidan yayi, wai bai son
abinda zai sake hadaki dashi da ke dan haka namai
alkawarin bazan gaya miki inda suke ba, san nan ya yarda.
duk wata nake zuwa ina kai musu kayan abin ci, in takaice
miki har daurin auran jalal baffa yazo, inata jira inga ranar
da hakalin ki zai karka gare su amman sai naji shiru kamar
an shuka dusa dan haka naga innabar ki ahaka banyi miki
adalci ba, amfanin zaman tare kenan in kaga wanda yake
kusa dakai zai bata kasa shi ahanya dan haka idai bakibi
iyayen ki ba toh matakin da zan dauka bazai yi miki dadi
ba.
********
kafin ya gama magana hawaye ya wanke wa ummi fusku
yanzun dama tuntuni ba,aga saudatu ba, amman basu
nemi ni ba lalai su bafffa suyi matukar fushi dani. tsuguna
wa tayi ta fara wa alhaji magiyar ya rakata ta nemi gafarar
su. alhaji yace indai nine bazan taba kaiki ba kije ki nema
da kan ki. shiko jalal bayan sun fita dakin sa ya nufa da
safna ya kara kwasan gara bayan tayi wanka jalal ya shiga
, kamar jira take tana ganin ya shiga wanka tamike ta leko
bataga kowa ba ahanyar ta fito saf saf ta shige dakin su.
jalal ya fito bega safna ba dan haka yana saka kaya ya fito,
daidai lokacin ummi ta leka dakin dakin safna tagani ko
jalal ya wuce da da ita dakin sa. tana ganin safna hankalin
ta ya kwanta juyawa tayi dai lokacin suka ci karo da ummi.
ganin ummi yayi abirkice yace ummi lfy kuwa?
.
wucewa tayi zuwa dakin ta ta fada gado tasaki kuka, jalal
ya shigo dakin yace ummi me ya faru ne. mikiwa tayi cikin
kuka ta kwashe duk abinda yake faruwa ta gaya mishi. dadi
ya kama jalal Allah ya karbi Andu,ar shi ummi ta fara
tunanin iyayen ta. yace ummi ki kwatar da hankalin ki ,ni
nasan gidan zan rakaki. ummi cikin sauri ta dauki gyale
tace muje jalal. jalal yace ummi ki bari sai gobe mana. eh ai
kana tare da uwarka da ubanka dole kace na bari sai gobe.
Jalal yace Allah ya baki hakuri ummi muje, sun fito kenan
saiga safna da kairat zasu fita jalal yace ina zaku ? kairat
tace waje zamu muga gari safna ko shiru tayi jalal yace
koma gida. kairat kuka ta fara toh ni ummi zanbi. ummi
tace zo muje yar auta ta. safna na kallo suka shiga mota
sai daga musu hannu take. bayan sun isa jalal ne ya fara
shiga gidan sunata murna baffa har yana tam bayan jalal
ya baka taho da amaryar ba, ko kana tsoron karta ganin
tace ni take so. jalal dariya yayi yace baffa ni da baki ne
fah, nabar su a mota. a,a banda abinka ya zaka baro so
akofar gida jekace su shugo. waya ya dauka yace shi go.
shigowa tayi da sallama rike da hannun kairat idon ta
hawaye ne kawai ke zuba. baffa ya mike ya nuna ummi
yace zaliha mama dake tsugune tana zubawa jalal abinci ta
sake kwanan ta dau ko itacen dake cikin murhun ta fito tana
fadin ina zalihar take. baffa ya nuna zaliha yace kinzo ki
koremu ne daga gidan da mijinki ya bamu? tsugu nawa tayi
ta fashe da kuka tana fadin baffa nazo neman gafarar kune
dan Allah ku yafe min. bata rufe baki ba ta fara jin saukan
itace ajikin ta. jalal saifaman ba baffa hakuri ya keyi, yaju
ya yaga anata jabgar ummi mikewa yayi yazo ya karbi icen
yana bawa mama hakuyi. baffa yace ta fita karta kara nufo
inda muke, shi ya dade da cireta acikin 'ya'yan shi. wani
makocin baffa ne yaji hayaniya tayi yawa ya zagayo. me
yake faruwa ne? baffa ne ya fara gayawa makocin shi,
malam buba yace kinyi kuskure yarinya, nan ya shiga bawa
baffa hakuri amman baffa ya kekashe kasa yaki hakura
ummi sai man share hawaye take, ahankali mutane sai
taruwa suke anyi anyi su hakura suki.
.
jalal ya tsuguna ya rike kafar bafffa yana rokon shi. baffa
yace mike abduljalal idan ina kallon ka gani nake kamar
mahaifin ka ne zan yafewa mahaifiyar ka amman da
sharadi. sharadin kuwa shine karta kara zuwa inda nake har
sai ta nemo min 'yata saudatu. ummi saka hannu tayi aka,
yanzun a ina zata nemo wadda tayi wajen shekara 20 da
bata bayan sun dawo gida ummi da gudu ta shige dakin ta
ban da kuka ba abinda take. jalal ma dakin shi ya shiga ya
fara zubar da hawayen bakin ciki, amman koma meye
ummi ita tajawa kanta. haka ya kwanta yayi ta kuka. kairat
ma duk da yake tana da karancin shekaru sai da tashiga da
muwan ganin abin da akawa ummin ta. da daddare safna
ta fito falo ta zauna yau abin mamaki jalal ko awaya be ne
meta ba , taita zama ita kadai har ta gaji ta wuce dakin su.
kasa barci tayi bata san tana matukar son jalal ba sai yau,
sai juyi take agado gaskiya tana son ganin mijin ta, daukan
waya tayi ta kira jalal har sau 4 be dauka ba, gani tayi
bazata jura ba, ta mike. zuwa tayi ta taba kairat dake
kwance akan gado , dasauri ta zabura. safna tace dama
bakiyi bacci ba, wai yau me ya same ki tunda kuka dawo
sai faman fashi kike.
.
duk da karancin shekarun kairat sai taji bata son ta fadawa
safna abin da ya faru dan haka tashiga tunanin me zata
fadawa safna, cen tuna yaya jalal idan bai son ya fadi
gaskiya sai yace kansa ke ciwo, dan haka da sauri ta ce
anty kaina ne yake min ciwo, amman yamin sauki. safna
tace sannu da kuwa aiken ki zanyi gashi kince kanki na
ciwo. ai yayi sauki, tashi tayi tace ina zaki aikeni gun yaya
jalal? eh kije dakin sa ki gani lfyr sa kalau san nan kuma
kice mai nace ina gaida shi. da gudu ta nufi dakin jalal .
ummi na kawance tana ta faman aikin kuka taji takun tafiya
tace azuciyar ta wannan ba yafiyar jalal bane da sauri ta
mike ta fito . hango kairat tayi ta taba kofar jalal tace ke
kuma ina zuwa? ummi anty safna ce ta aike ni gun yaya.
toh naji jeki karki dade, tura kofar tayi tashiga ta same shi
yana zaune ya hada kai da gwaiwa. zuwa tayi daf dashi ta
zauna ta kira sunan shi yaya baka da lfy ne ? dagowa yayi
cikin fada yace ke fita ki bani guri. kairat tace yaya fah anty
ce ta aiko ni. me tace?
.
tace wai tana gaishe ka. dadi yaji har ransa wannan ne karo
na farko da safna ta nuna ta damu dashi amman saidai yau
baya cikin farin ciki. yace kairat kice mata ina amsawa .
juyawa tayi da gudu , jalal yasake tsayar da ita yace kice
mata nace tabar wayar ta a kun ne zan kira ta. ummi na
zaune afalo kairat ta fito ta wuce ta tashiga nasu dakin. da
sauri safna tace me yace mike kairat ta gaya mata abin da
yace. tunani ta shiga yi gaskiya akwai abin da yake damun
jalal, haka taita jiran jalal yakira ta taji shiru har gari ya
waye. 8:30 ummi ta shiga dakin jalal tasa meshi yagama
shiryawa tace yauwa jalal dama so nake ka rakani gidan
yaya rabi. ummi da yau ina son na koma office ne kinga tun
biki ban koma ba kar daddy yayi fada. jalal ina cikin
wannan halin har kake maganar office har ina tunanin kana
tausaya min. jalal yace ummi bawai bana tausa sayin ki
bane dama tsoro nake ji kar ran daddy ya baci, amm ba
komai zo muje. suna fitowa falo yace ummi bari naje na
danga safna. daurewa tayi tace to karka dade
***********
yana shiga yace kairat jeki falo da gudu ta fita, shi kuwa
jalal zuwa yayi ya hau kan gadon ya daga safna dake
kwance ta rufa da bargo, fuskar ta duk hawaye, yace safna
me ya faru? da sauri tace bakai bane kaki daukan waya na
kuma kace zaka kirani amman kaki Kira. daukan ta yayi ya
daura ta ajikin sa kiyi hakuri safna bansa kinkira niba kuma
jiya bana jin dadi ne shi yasa baki ganin ba, safna dama
zaki shiga da muwa idan baki ganni ba? tura kanta tayi cikin
kirjin shi tana dariya. Shima kara matseta yayi yana dariya
suna cikin haka saiga kairat ta shigo. da sauri jalal ya ajiye
safna yace ke bacewa nayi kije gurin ummi ba. a tsora ce
tace ummi ce tace na dawo na zauna. sai alokacin jalal ya
tuna ummi na jiran shi, sau kowa yayi yaje kunne safna ya
rada mata wasu magana ya fita yana dariya ita kuma tasa
hannu ta rufe ido. yana fitowa yace ummi muje kallon jalal
tayi ta daure fuska ahaka zaka tafi kayan ka a yamutse.