Breaking News

RABO NA CE PART 7

RABO NA CE PART 7
.
Ta shigo gida wani ira da ita, " malama daga ina?" Ta
kalleta da fuskar tausayi, "Allah sarki Anti Najma!! Wallahi
jaheed ne yazo kd bai gayamin ba, wai zaiyi surprising d'ina
ne, baisan mun bar Kd mun dawo nan ba," cike da mamaki
Anti Najma tace "au dama baki gaya masa mun bar kd ba?"
"tab wallhy ni sam na manta sai da yace yazo na tuna,"
jinjina kai kawai tayi, har zata watso mata bak'ar magana
sai kawai ta wuce kitchen gun 'yar aikin su nafee anka dan
tanason ta had'a mata kunun gyad'a, dukda Ummey tace
girkin Nafee anka kamar an wanke kai yake, "wa kunbo wa
kayan ta"... Kai tsaye gun TV ta nufa, taje neman magana
gun Muhammad, dan chanza tasha zata yi, tana d'aukar
remote yayi cikinta da sauri, "kai!! Allah saidai kowa kada ya
kalla," kamin ya k'ara so gunta har ta chanza tasha d'in, ya
juyo yaga ina taje, kamin su fara rigima, dan Muhammad
k'aramin aikinsa ne yace zaiyi kokuwa da ita, "Oh My God.!!
Sister please don't change it," ya fad'a, da sauri yaje gaban
TV ya had'e k'afafuwansa yana kallo, hira ake da fitaccen
d'an wasan basketball d'innan Shaheed Al- Qaseem, "wayyo
sister kalli yanda yake magana" ya juyo ya kalleta, "ya had'u
ko, sister,? " eh kawai tace masa, dan har ga Allah ba
abinda takeson ta kalla ba kenan, amma sai taji kunya ta
chanza masa, " wayyo Allah sister kina gane English d'inda
yakeyi kuwa?
.
American English ne, shi yasa bakya ganewa sosai," tsaki
tayi "wa ya gaya maka ba na ganewa? " "To ai naga bakya
cewa komai ne," tsaki tayi dan ya isheta da surutu, har ta
mik'e zata bar gurin ya rik'e ta, "dan Allah ki d'aukar mini
muryar sa, haka yayi ta damunta sai ta masa recoding d'in
voice d'in Shaheed, bada son ranta ta d'au kar masa ba, a
k'arshen hirar shi, ya baiwa masoyan sa dama, da suzo zai
gana dasu ranar assabar mai zuwa, wani ihu yayi, ya tashi
yana rawa, dai-dai shigowar Dady yayi kan sa da gudu
yana murna, ko hutawa bai bari yayi ba, ya shiga bashi
labarin abin da shaheed ya fad'a, baya ko missing point,
saida ya fad'i komai cikin hirar duk yabi ya dami mutane da
zance d'aya, " Dady ranar Saturday dawa zamu tafi
gurinsa?" Dady ya kalli Al Ameen da yaci glss d'insa na
makafi, yana danna waya " sai Ku tafi da Al Ameen, "
Muhammad da gudu ya tafi gun Al Ameen, " kaji Dady yace
ka kaini naga shaheed on Saturday, to kaima riga mai
sunansa zaka saka, dan shima yasan muna sonsa, sai dai
kash! Rigana bata maka, saidai ka siyo sabo nima ka siyo
min sabo dan bai dace muje masa da old one ba, kaga
sai......." " please Muhammad naji ka bari sai ranar ko!
Haba?" Al Ameen ya kasteshi, sabida surutun nashi yayi
yawa, nima dai Jabo nace " wannan shine ainihin talkative
d'in ba kowa ba, dan nasan yafi chuchun gaye surutu," gaba
daya ranar gidan hirar shaheed aka yi mutum ko baya so
sai Muhammad ya masa hirar shaheed....
.
After each second sai ki ganshi yayi kamar wani bawan
Allah ya lallab'a, "Anti Ummey dan Allah ki kunna min
muryar sa naji" haka zata kunna masa voice d'in shaheed,
ya saurara, gashi da naci, k'arshe kawai ta tura a iPad
d'inta ta mik'a masa iPad d'in, sannan ta sami zaman
lafiya, kullan cikin lissafin rana yake, har Allah ya kawo mu
assabar, Ranar tun bayan asuba Muhammad bai koma
bacci ba, sabida d"aukin ganin shaheed, tun asuba yaje gun
'yar aikin gidan su, Nafee Anka ta masa wanka ta shirya
shi, ita kam tasha surutu, koda itama ba baya ba fuska ne
kawai bata samu ba tunda aikatawau take, da sai tayi
bala'en shishigi da surutu tsiya, tun asuba ya shirya, wanda
zasu tafi da la'asar amma tin asuba ya shirya, da gudu taje
d'akin Al Ameen, " Yaya Al Ameen, ka tashi ka shirya kada
mu makara?"
.
Al Ameen ya juya ya bude idonsa, ya kalli agogo, yaga
k'arfe shida lokacin, shine zai wani tasheshi, tsawa ya daka
masa ya koresa a d'akin, ya fito yana kuka, ya nufi d'akin
Mumy ya kai k'ara, ta bashi hakuri, akan zata tada Al
Ameen an jima, haka ya sakata gaba sai da ta tayar da Al
Ameen d'in, da ta gaji da nacin sa, taje ta tayar dashi, dama
Al Ameen akwai fushi, yaji haushi an hanashi bacci, yace
bama zai kaishi ba, ya bar gidan gaba d'aya tofa.! nan
Muhammad ya shiga watsa kuka, ya hargitsa gida da ihu,
duk wanda aka tuntuba sai yace bazai jeba yana da aiki,
daga k'arshe Dady yace zai kaishi da kanshi, sannan fa aka
sami zaman lafiya yayi shiru," Dady ka tashi mu tafi yanzu
kada mu makara, tunda sai munje kasuwa ka siyo shrt mai
sunan Shaheed wacce zan saka kaima ka saka," kowa
saida yayi dariya a parlour en, Dady yaga ta kansa, ya
kallesa yace "Muhammad kasan agogo kuwa??," yace
"aah," tashi Dady yayi ya d'auko agogon bango, ya zo yace
"kaga sai wannan gajeren k'arfe ya dawo nan, sannan za'a
ganshi, kuma kaga yanzu gajeren saman goma yake, sai ka
bari sai ya gangaro k'asa gurin wannan sai mu tafi, an sami
damar sa, anan aka had'a shi da agogo, ajima- ajima ya
dubi agogo, "Dady shi wannan k'aramin baya tafiya ne, tun
d'azu yake chan gurin" nan ma saida sukayi dariya, har
nafee anka da take kitchen tana aikinta na wanke-wanke
saida tayi dariya, yasa agogo gaba, ji yake kamar ya k'ara
masa gudu, an dad'e ana koya masa agogo yak'i maida
hankali, amma ranar saida ya iya agogo tsab, Guraren uku
da rabi, Dady yayi bak'i, bak'in da ba hanyar guje musu,
Muhammad kam kuka ya saka sabida gajeren k'arfen har
yakai gun hud'u harda kwata, amma ba zancen tafiya,
kukansa ya tsanan ta, Mumy ta kira duk yaran ta kowa
yana da aiki mai mihimmanci, har hudu da rabi, ya baiwa
Ummey tausayi, sabida har ya rame lokaci d'aya, "kanaso
na rakaka?" Cikin kuka yace " ai ke mace ne bazaki iya saka
riga mai sunan saba, kuma ko kin saka bazai ganiba tunda
hijabi kike sakawa zai dauka bakya sonsaaaaas," ya
k'arasa yana kuka, Ummey kam dariya tayi ta wucewar ta,
da yaga kukan bazai fitar dashi ba, sai ya bita d"aki yace ta
rakashi gun Shaheed Al- Qaseem..
.
Ummey a gurguje ta shirya, duk inda ta soka k'afarta
Muhammad yana biye da ita, lokacin har biyar ta kusa,
bayan ta shirya ta d'auko hijabinta ta saka, nanfa
Muhammad yace lallai bazata saka hijabi ba, tace saidai a
fasa tafiyar, dayaga tafishi naci ya hak'ura y yace su tafi,
amma fa baya mata magana, sai biyar suka isa, sun isa
gurin a cike, suma suka bi layi, da ka kalli fuskar
Muhammad sai kaga yana murmushi, dan har ya saki
fuskarsa, suna tsaye, lokaci d'aya taji kamshin da take
yawan ji gurare da dama, har hospital da ta kwanta taji
wannan k'amshin, amma har yau bata ga mai saka turaren
ba, akwai lokacin da taje kasuwa, duk wani turare saida ta
shinshinashi amma bata had'u da wannan turaren ba, ta
k'are waige- waigen ta ta hak'ura, idan da sabo, ta saba da
jin wannan k'amshin, sunanan tsaye, an kusa kaiwa garesu,
wani guy ya fito da turanci yayi sanarwa akan mutane suyi
hakuri sai next time, shaheed yana godiya da ziyarar su,
Muhammad ya tabo Ummey " sister ni bana jin English, mi
wannan mutum yace" ta kyalkale da dariya kamar cikinta
zai kulle, wato yaune bayajin English da yake bad
announcement ne, ranar hadda ce mata da tanajin turanci
da ta gane abinda Shaheed yake fad'a, ta dafa kanshi,
"cewa sukayi bazamu sami damar ganin shaheed ba sabida
munyi letti," wata k'ara ya saki wacce saida duk mutanen
gurin sukayo kansa, tun farko ya gane abinda aka fad'a
kawai gani yayi kamar kunnen sa ne ya masa k'arya, ya
fara birgima yana kuka, tayi rarrashi har ta gaji, haka ta
d'aukeshi ya wani sank'are mata kamar k'arfe, ta rasa
yanda zatayi, sai wani tara mata mutane da yayi, kowa
kallon su yake, da taga idon mutane ya mata yawa sai ta
chanza hanya, tabi wata hanya wacce take tunanin zata fito
da ita daga baya ne, dan Muhammad yak'i daina kuka, suna
fitowa waje dai-dai shigar Shaheed mota ana k'ok'arin
tayar da motar, da sauri ta sauke Muhammad, taje tasha
gaban motar ta, kalli Muhammad "je gashi nan cikin mota
ka gaidashi" Muhammad da gudu yayo gun motar, guard
d'insa suka tareshi Ummey ta matso tace " please ku bari ya
ganshi mana," amma suka hana, Shaheed ne ya fito motar
idonsa gyar akan Ummey, wacce tunda tasha gaban motar
yake kallonta, har ta matso kusa da motar, bai ma kula da
Muhammad ba, Muhammad da gudu ya rungume shi, sai
lokacin shaheed ya kula dashi, Muhammad yace"I love you
uncle Shaheed am bigs fan of you" shaheed yace "wawooo"
ya shafa kan Muhammad ya tsuguna, yace " I love you too
ya sunan ka?" Muhammad bai maji tambayar da aka masa
ba, yace "sister Ummey, zo ki ji yana cemin I love you,
kema zo ki gaya masa you love him," ya d'aga kai ya kalli
wacce aka kira da Ummey, shima yace "sister Ummey
come & tell me how much u love me" murmushi kawai tayi
ta matso, suka d'an gaisa, ta gaya mishi d'an kad'an daga
cikin Son da K"anin ta ke mishi, da abinda ya faru yau, yaji
dad'i sosai duk da yana da fans kala kala amma nayau
daban ne, "sister d'an d'auke mu hoto mana," ta d'aukesu
hoto, ya baiwa mai kula dashi camera ya d'auke su hoto,
yana rik'e da hannun sa, yace "Muhammad sai yaushe zan
k'ara ganinka," jikin Muhammad har rawa yake, "ka ga
yamin gidan ka kullam zanzo gurin ka" yayi dariya, saidai ka
bani number na rik'a kiran ka, "to number Dady ko Mumy ko
yy Mahmoud ko ta ya Aleey ko anti Ummulkhairi kota alAnti
Ummey kota ya Al Ameen,? Sai ya tsaya, Allah bazan baka
ta Al Ameen ba sabida yak'i kawoni gurinka" har zaici gaba
ya dakatar dashi, "bani ta Anti Ummey, " tuni ya karanto
masa number ta a ka, dan ya haddace number kowa a
gidan, sukayi sallama ya sa aka baiwa Muhammad riga
d'aya da ball daya, wayyo kuzo kuga murna gun
Muhammad sukayi sallama suka wuce, Har suka isa gida
magana d'aya yakeyi ta Shaheed,kowa yasha labarin sa,
harda su Yar aikin su Nafee anka tasha labarin, ya min kaza
yace kaza, hatta Al Ameen da yak'i kaishi ba'a barshi a
baya ba, dan shima yasha labari, ya d'auki wayar Momy ya
kira Antinsa Ummul-khairi dukda ba tada lafiya kamar tana
d'an laulayin sabon ciki, sai da ya bata labari, bayan ya
k'are yace a baiwa Uncle Abdallah shima ya bashi labarin
Shaheed, har Mudhahhar da ya saka rigima sai an bashi
Uncl Muhammad, saida aka bashi shima ya zuba masa,
ajima-ajima yazo ya tambaya sister bai kirani ba? Tace
masa bai kiraba...
.
******
Mujaheed zaune a palon su yana chin lasagna da
k'anwarsa Siyarmerh ta had'a, "Allah sarki Yaya yanzu sai
k'arshen shekara zamu ganka," ta karashe maganar kamar
za tayi kuka, yana chin lasagna dinsa yana kora drink, "sai
yanzu kike marmarina, da kuwa kullan cikin yi mini tsiwa da
fitsara kike," Ammi ce ta shigo "Alhaji fa yace kayi sauri
kasan 12 zaku tashi, kuma yanzu har goma tayi, haka suka
k'are suka dunguma rakashi airport, saida ya shiga jirgi ya
zauna kamin a tashi, ya d'auko wayarsa ya turawa Ummey
SMS, " yanzu zamu tashi, insha Allah duk ranar dana dawo
akwai magana mai matuk'ar mihimmanci da zamu tattauna
akai, please keep promise Ummey, Bye & Miss u" bayan ta
karanta a ranta tace wane promise kuma,? " haka dai ta
masa reply da in sha Allah, da kuma fatan alkhairi da fatan
nasara a karatunsu, haka jirgin su ya tashi yana cike da
shauk'i da kuma missing d'in abar k'aunarshi, wacce yace
k'aramace har yanzu...
.
*******
Calling ne ya shigo wayarta da new number, bata kusa da
wayar kuma da ta dawo bata kiraba. Da yamma suna
zaune ana kallon TV ana hira da Shaheed, a tsakiyar hirar
sukaga an nuno hoton Shaheed da Muhammad, ya kira
Muhammad a matsayin babban masoyinsa, wanda yake
alfakhari dashi, hoton Ummey ma ya fito kad'an, dan tana
gefe da akayi hoton, Muhammad kamar ya had'iye TVn
yake ji, sai ihu yake yana jin dad'i, bai bukaci kowa ya
fassara masa turancin ba, sabida kamar duk duniya
turancin Shaheed kawai yake ganewa, a program d'in ne
aka baiwa masoya dama su kirashi suyi tambaya, amma
yace sai ya kira babban masoyinsa Muhammad,
Muhammad najin haka, sai ya juyo da gudu, "sister zai
kirani," aka mik'a masa wayar, bayan minti biyar nan
Muhammad yayi ta zuba zance kamar wani radio, a cikin
masu masa tambaya, wata mace ta kira ta masa tambaya
tace yana da aure kuwa yace bashida Aure amma
Muhammad d'insa zai samo masa mata, tace ita kam tana
sonsa da zatasan inda Muhammad yake da zatazo gunsa
ya kaita a matsayin matarsa yace sai ta bada himma ta
nemo Muhammad.! Har aka k'are program d'in. Bayan
kowa ya tashi anje an kwanta anan Shaheed ya k'ara kira,
bayan ya gabatar da kansa, tace ta gane ai, bari ta kaiwa
Muhammad wayan, "No na kirane kawai na gaida
Muhammad's sister," taji dad'i, yake gaya mata tama
Muhammad Albishir da cewa 20/5 zai kawo ma
Muhammad ziyara....
.