MIJIN MARAINIYA PART 6
MIJIN MARAINIYA PART 6
.
Ummi kwana tayi kuka ta shiga damuwa mutuka atake
tunanin iyayan ta ya fado mata haka iyaye sukeji idan suga
dan su zai shiga cikin wani hali, to yanzun wani hali iyayan
ta suke ciki na rashin ta da sukayi, yau she rabon ta da
ganin su, tun kusan shekara goma shatara da suka wuce
lokacin jalal yana karami, bazata manta ba tun lokacin da
sukazo kawayen ta na gidan tace musu suyi sauri su koma
gida kar kawayan ta sugan su tanan zuwa, suka tafi cikin
bacin rai, suna fadin tunda baki son agan mu a matsayin
iyayenki karki kara zuwa inda muke, taso washe gari tabisu
tabasu hakuri amman tana cikin shirin tafiya saiga yayarta
rabi tazo cikin kuka tana gaya mata cewa jiya dasu baffa
suka zo gurinki sun taho da saudatu ba aganta ba taba ce,
sanadi haka baffa yana cen ba lfy mama ma ba lfy ta cika
ba, yan zon nazone kizo muje nemanta ko Allah zai sa
adace, ummi kin binta tayi ta dauko kudi ta mika mata tace
kije ki duba ta nima ba lfyr gareni ba, in nashiga rana
ciwona zai iya tashi kije duk halin da ake ciki kizo kisanar
dani.
.
yaya rabi batayi musu ba ta wuce , haka yaya rabi tayi ta
zaga gari har tsawon kwana uku tasake dawowa gurin
ummi akarshe dai ummi koran kare ta mata tun daga ranar
babu wanda ya sake zuwa gidan ayanzun haka ummi bata
saniba ko anga saudatu ko ba,agan ta ba, amman ita tana
ganin angan ta, haka ummi taita tunanin baya, tare da ganin
wautan ta da ta bari har haka ya faru, yanzun ya zatayi ta
shawo kan iyayen ta kilama alhakin iyayen tane gashi
yanzun har ansa ranar auren jalal dan cikinta amman ba,ayi
shawara da itaba, dan ba,a dauketa abakin komai ba alhj
yanuna mata iyayen sa suna da mahim manci yaje yayi
shawara dasu hakadai ummi taita tunani kafin gari ya waye
idon ta yayi ja sunkun bura. koda alhaji ya shiga dakin
ummi da safe yasame ta cikin wannan hali yayi tunanin kin
auren ne ya dame ta, bece komi akaiba yayi mata sallama
ya fito. alhj da jalal ne tafe amota alhji yace jalal kasan ina
zamu ,jalal yace a,a zan kaikane kaga wani abokin ka,
tafiya sikayi sosai sannan suka isa wani gida dan madai
daici mai kyau, suka shiga da sallama, wata tsohowa ya
gani tana shara tana ganin alhaji ta sake tsin tsiyar cikin
Fara,a , ta dauko tabarma ta fara kokarin shinfidawa sannu
da zuwa alhaji bari na fadawa baban Ku, bayan wasu yan
mituna baffa ya fito yana fadin sanu da zuwa kai dawa
kake tafe yau kuma, yace baffa jalal ne. cikin bacin rai
baffa yace ba munyi dakai daga mahaifiyar shi har shi
bazaka nuna wa kowa nan ba. alhaji yace baffa kayi hakuri
ganinayi bayi da lefi kuma be dace muyi ta tafiya ahaka ba,
yanzun gashi jalal har zaiyi aure, haka alhaji yayi ta jan
hankalin baffa sannan ya kalli jalal yakama hannun shi yace
kodan maihaifin ka ,bana kika ba, abduljalal maifinka yamin
abinda 'yata da haifa ta kasa yi min, mahaifiyar ka kunya
ma takeji ace mune muka haifeta saboda tayi kudi baffa
kasa magana yayi ya fashe da kuka mama ma tana daga
gefe tana share hawaye. jalal da be gane suba dan rabon
shi dasu tun yana karami sai a magan ganun sune ya
fahimci kakannin shine iyayan ummi, tausayin su ya kama
shi daman ba wuyar kuka gareshi ba, tuni hawaye suka fara
ambaliya afuskar shi ya kama hannun tsohon ya shiga
bashi hakuri sai da yaga hankalin su ya kwanta sannan
yace yauwa baffa ina anty saudatu yanzu? nan danan suka
kara barkewa da sabon kuka suna bawa jalal lbrn batan
saudatu haka sukai ta kuka har jalal , jalal ji yayi ya tsani
ummin sa kwata kwata ya dade yana tambayan ta su sai
tace yabar maganar bata so. haka sukawa su baffa wuni
sai yamma suka taho bayan sun cika su da tsara ba, saidai
sunce su ba wanda zaizo biki daga barayin su, saidai wata
rana yakawo musu amarya su gani jalal yanata basu hakuri,
amman suka ki.
.
****** shirye sheryen biki nata tafiya gidan hajiya kamar
cenne gidan bikin acan ake shirya komai .
.
ummi bata kara tada zancen auren ba illah hankalinta ba
akwance yake ba, kulum cikin kuka take, tarasa yaya zatayi
ta dakatar da wannan auran. Jalal kuwa ayanzun gani yake
mahaifin shi beyi dacen mata ba yakamata daddy ya kara
aure dan koshi da ana cenza uwa da ya cenza ummi dan ko
ganinta bayasan yi. ana jibi daurin aure kanwar alhaji anty
nusaiba da matar kanin alhaji hajiya fatima da wasu mata
su hudu yan uwan hajiya, suka faka faka jibge giyar motan
su a haraban gidan alhaji, rabon su da zuwa gidan sun
dade, wata motar na biye da nasu, direban motocin suka
fara fito da akwatuna masu kyau daga cikin motar sukuwa
matan tuni suka shiga gidan. sunata sallama a falon har
suka gaji ba,a amsa musuba suka nemi guri suka zauna ,
bayan anshigo da akwatunan ne , aka fara shigo da kayan
abinci, anty nusaiba ce take nuna inda za,a ajiye komai,
ummi dake kwance tana kuka taji mutsi yayi yawa ta share
hawayen ta tafito, mutane ta gani cike da falon, nusaiba
kawai ta shaida. nusaiba ta fara mata bayani anty
munshigo munata sallama gidan shiru. eh wlh kaina ke
cewo nadan kwanta. nusaiba tace gakayan safna nan mun
kawo ki duba ki gani. ummi ta zauna suka fara budewa
lallai alhaji ya kashe kudi wannan uban kayan duk na safna
ne , aikowa safna bazata sasu ita daya ba, bayan sun
maida akwatin sun rufe, anty nusaiba tace mufa munzo
kenan sai bayan baki.
.
ummi tayi yake tace ai yakamata tunda kune kirjin biki.
hajiya fatima tace ina amaryar tamu ko taje kunshi ne? sai
alokacin ummi ta tuna da wata safna, tace anya kuwa inajin
tana daki. anty nusaiba tamike tashiga dakin ta hango
safna makure agado ta xata bacci take sai da ta taba ta
taga ashe kuka takeyi. itako safna ta zata ummi ce dan
haka ta mike afirgece, da sauri anty nusaiba ta riketa suka
kalli juna, nusaiba tace safna me yasame ki kike kuka, ko
baki son auren ne? girgiza kai tayi. to me yake damunki?
koda safna bata san anty nusaiba saita tsinci kanta da
cewa tunanin iyayena nakeyi da kakata, nusaiba ta tausaya
mata tace safna ardua zakiyi musu ba kuka ba, tana buye
hawayen ta sake cewa me yasa bakiyi kunshi ba, zo naga
kan ki, ta bude kan taga tsohon kitsone, ta kwatar da safna
akan cinyar ta tafara warware mata kitson , haye na zuba
afuskar ta
.
Anty nusaiba na tsefe wa safna kai tana tunanin ga yarinya
me kyau amma gwanin ban tau sayi, bayan ta gama tsefe
mata kai taji muryar jalal suna gaisawa da mutane afalo
dan haka ta kwala mai kira, ya amsa ya mike ya nufi dakin
safna ummi ce ta dakatar dashi yadawo tace ba alhaji ya
hanaka shiga dakin safna ba? eh amman yanzun bakiji anty
na kira na bane.
.
rasa abin cewa tayi dan haka jalal ya juya ya shiga dakin
lokacin da jalal ya shigo dakin safna tana bayi tana wanka.
Jalal yace dama ke kadai ce adakin? anty tace nida safna
ne yanzun ta shiga wanka, kai kuma haka ake yi baza ka
ba amarya kudin lalleba ko haka kake son akai maka ita.
toh ni anty babu wadda yace na bada kudin lalle agidan nan
nifah da daddy kawai muke shirye shiyen mu agidan nan
kinga mu bamu san yadda akeyi ba, anty kinsa ma wani
abu kuwa rabon da naga safna na man ta in na,aika kairat
ta kirata sai tace ta cemin tayi bacci, ko kiranta nayi awaya
bata dauka, ni ina tunanin ma babu wanda ta gaiyata katin
ma dana aiki kairat takai mata dawo min dashi tayi wai
bata da wanda zata bawa, dan haka na barta . anty nusaiba
ta nisa tace ai irin wannan da sai ka gayawa ummin ka ta
mata fada. wace ummi, ai ummi bason auren nan take ba,
ni ina tunanin kamar ma itace take firgita, ta haka sukai ta
tattanawa tsakani su, anty nusaiba tace wai safna har
yanzun baki gama wanka bane? safna dake tsaye abayi
duk firan da suke tana jinsu tace nagama anty, namanta ne
ban shigo da hajjab ba.
.
anty tace au haka ne cikin dariya tace jalal tashi ka fita inta
gama shirya wa sai kadawo. jalal yace a,a anty ta fito
kawai ni babu ruwana da ita ba kallonta zanyi ba. anty tayi
tayi jalal ya fita yaki fita, tashi da kanta ta dauko hijjab kato
ta mikawa safna, tasa sannan ta fito kanta akasa dan
yanzun wani irin kunyar jalal takeji, tashige cen longu ta
zauna ta fara shafa mai, acikin hijjab take shafawa jalal
Nata kallon ta, cen yace bazaki gaishe ni bane, kafin ya rufe
baki tace ina wuni, shiru yayi sai cen yace bazan amsa ba,
saida naroka, safna tace ina fa shirin gaisheka kayi
magana. toh nidai bazan amsa gaisuwa daga nesa ba,
saikin matso kusa dani. safna tana kokarin ajiye man
shafawa tace inazuwa bari nasa kaya. a,a kizo ahaka. anty
tana gefe ta jin su tace ke dauki kayanki kishiga bayi ki
saka, wai dama jalal ashe baka da kunya haka, agaba na .
jalal yace to menayi kuma daga nace ta matso kusa dani.
safna bata saurari me suke cewaba tashiga bayi tasaka
kaya dogowar riga tasaka na atamfa tayi kyau duk da
bawani kwalliya tayi sosai ba, ta dora karami hijjab akai
sannan ta fito, gurin jalal ta nufa tace ina wuni, mamayan
ta yayi ya rike hunnuwan ta, yace tsorona kikeji kuma.
tsugunawa tayi tana boye fuskar ta cikin cinyoyinta shiko
jalal yana rike da hannuwan ta yana kokarin daka kanta,
ciki ciki suke sosai safna da jalal waishi dole sai yaga
fuskarta itakuma taki bari , safna taga jalal yafi karfinta dan
haka ta fara kiran anty kin ganshi ko? anty dake gefe tana
kallon ikon Allah tace wlh jalal zan bata maka rai, ko
kunyata bakaji nazama babba banza kenan . dasauri ya
sake ta yana fadin na bari Anty na mance ne, ya mike yace
bari naje anty , yaza ayi maganar kunshin ? karka damu
yanzun zankai ta amman inaga acen zan barta ta kwana
dan naga bawani gyara da aka mata. jalal yaja ya tsaya
anty kuma harda kwana toh abar kunshin mana ai badole
bane kallon jalal tayi tace ai yan zon baka da ikon hanata
fita saika bari sai an daura auran.
**********
haka anty nusaiba tadauki safna ta kaita gidan kawar ta
hajiya asata me ygara amare, hajiya asata tana ta yiwa
anty ko rafin me yasa ba,akawo ta da wuriba sai ana jibi
biki. bayan anty ta dawo gida tasamu alhaji awaje ranshi
abace saboda ummi ta kitsa mashi magan ganu iri iri. tun
daga nesa alhaji ya farawa anty nusaiba fada, nusaiba ina
kukaje har dare yayi haka? wlh yaya nakai safna kunshi ne.
shine kuka kai dare haka, to yanzun ina safna. yaya tana
cen sai gobe zan koma nadauko ta. alhaji ya fara fada ta
inda yake shiga battanan yake fita ba. lokacin da nusaiba
ta shiga ciki ta samo ummi da kawayen ta sai shewa suke
suna ganin nusaiba suka fara yadda habaici. Madina ta kalli
dayar dake kusa da ita to amara kirjin biki komai shishige
wanki dai, dan nan namu ne, kuma duk inda akaje dole
adawo.