RABONA CE PART 3
RABONA CE PART 3
.
Yana fita Dady biyo shi ya rakashi har mota, ya k'ara masa
godiya, yana tajin dad'i, sabida shi ya ceto rayuwar y'arsa
da yanzu bata, tunda an manta da ita a dajin, da anan jinin
ta zai tsiyaye har ta mutu, amma da taimakon Mujaheed
komai ya zo da sauk'i. "Ke hatta mutumin da ya ceci
rayuwarki sai kinma yanga, da wani tsirka tsirkan gashi naki
kamar anci goruba da wuk'a" ta bata fuska, "Mumy kinga
anti Najma ko!?" "Ai gaskiya ta fad'a, nima banji dad'in
yanda kika masa ba, mutumin da ya ceci rayuwarka a ya
wuce komai a gurin ka," kawar da kanta kawai tayi, Najma
tace, " tana masa yanga kai kace yace yana sonta, to in
gaya miki wannan ya wuce ajinki yarinya, wannan da
ganinsa d'an hutu ne, ke ni Wallhy har naji miki kunya da
yaga wannan gashin kan naki!"
.
Ta tintsire da dariya, tsaki tayi tace"shi d'an hutu ni kuma
'yar wahala ba, waima ina ma ruwanki dani" Dady ne ya
shigo daga rakiyar da yayiwa Mujaheed tuni Najma tayi
tseet, amma ya d'an ji zancen su, "kada fa a dameta da
hayaniya ku burta ta huta, ya matso kusa da ita, sannu
Ummey na" " yauwa Dady " tana murmushi, nan dai akayi ta
tad'i ana dariya. Muhammad ne yazo d'an autan su, ya fara
surutu, "sister wai ya bullet yake ne? da aka harbeki ya
kikaji? Zafi sosai ko?" kowa saida ya dara da irin tashi
tambayar, " kaga ko, ana harbina ina rik'e jakata, sai kawai
naji jakar ta fad'i, nayi k'ok'arin d'auka da hannun sai naji
na kasa, koda na duba sai naga jini, a hankali sai kawai na
fad'i a gurin" " kina nufin sister bakiji zafi ba lokacin da
kikaji shuuuut.?" Ya fad'a yana zare ido, tayi dariya, "wai
shuuuut! Muhammad waya gaya maka bullet yanada zafi,
lokacin da aka harbeka ba lallai bane kama sani, saidai idan
jinin ka ya zube sai ka fara ganin jiri sai ka fad'i amma wani
bullet ana harbin ka zaka fad'i musamman a k'afa ko ciki,
ko...." Bai bari ta k'are ba ya katseta, " kai anti ba haka
bane fa, a film fa da an har besu suke fad'uwa su mutu
kedai baki sani ba" tayi dariya, zata ci gaba da magana
sukayi bak'i yan dubiya sai tayi shiru.. kwanan ta tara a
asibiti aka sallamesu, sai dai still hannun ta a d'aure yake.
Tun lokacin kullum sai Mujaheed ya kira Dady yaji lafiyar ta,
a rashin sa'a kullum ya kira Dady baya asibiti bare ya bata
su gaisa, shi kuma bai taba cewa a bata ba, ko ina take ba,
ko a bashi number ta, amma lallai ta masa kuma yana jinta
har cikin ransa, saidai gani yake yarinya ce sai ta dad'a
girma zai bayyana mata abinda ke ranshi.
.
************
Kamar kullum, Mujaheed ne saman dokin sa yana gudu
kamar yanda ya saba, yayi abinda zaiyi ya dawo gida, a
palo ya had'u da k'anwarshi siyermah manne da waya ta
wani makure guri d'aya kamar ta shige cikin garun, tanata
murmushi, da gani soyayyah takeyi, tsaki yaja, ta kallo shi,
ta gyara zamanta da sauri, ya wuce ta bishi da murgud'a
baki, aranta tace ba zaka takuran ba bakasan soyayyah
bane, ya wuce d'akin sa yayi wanka ya fito koda ya zo ya
tarar da miss call biyu, da SMS daya, SMS ya fara bud'ewa
ya karanta " Sorry na kira ba tare da na gabatar da kaina ba
Ummey Ibraheem ce " yayi shiru yana maimaita sunan
"Ummey Ibraheem" shi baisan wata mai wannan sunan ba,
yad'an ninke bakin sa ya turo leben sa, anya ba wrong
number bane, sai dai ya daure yayi calling back, Ringin biyu
ta d'auka, garo garon muryanta yaji ta daki kunnensa "
Hello Jaheed" ya amsa nan take sabida ya ganeta, sabida a
rayuwarsa ita kadai ta taba kiransa da Jaheed " dama Dady
ne yace na kira na maka godiya na gode sosai, Allah ya
saka da alkhairi ya bar zumunci," sun gaisa sosai sannan
sukayi sallama,! Uhummm. Su Jaheed fa tun lokacin an
kamu, sai dai yana ganin tayi k'arama sai ta dad'a girma,
dan Dady yace mishi kwanannan ta k'are zana neco, zai
bari sai ta k'ara sai ya gaya mata, ita kam Ummey ko a
jikinta .....
.
Haka Kullum idan yayi free sai ya kirata sun gaisa, garo-
garon muryan ta na masa dad'i a hankali sun shak'u amma
ya kasa bayyana mata ra'ayinsa, suna mutuncin su cikin
natsuwa da girmama juna, amma shi jaheed gani yake
kamar ta gane manufarsa, tana masa na matane, kawai dai
yasan cewa insha Allah Ummey rabonsa ce, ita ko Ummey
bata taba kawo hakan a ranta ba.
.
**********
Waige waige takeyi, " Wai lafiya kike waige- waige haka?"
Najma ta tambayi ummey " mtwsss, wallhy k'amshin wani
turare nakeji mai sanyi, ke bakijishi ba?" " ni banji komai ba,
kece hancinki da jiye jiye" " Allah tun ina asibiti wani lokaci
sai naji k'amshin yana fitowa ta window, ko kuma na tashi
bacci naji d'akin na ta k'amshin," Anti Najma tab'e baki tayi,
"sai kije kasuwa ki nemoshi ai" Ummey ta kalleta, " Allah ya
miki sauk'in bak'ar magana ana zancen arziki kina bak'ar
magana, " banza tayi da ita, sukaci gaba da tafiya, wayar ta
tayi k'ara a screen d'in wayar sunan Jaheed ne ya bayyana
b'aro b'aro, tayi murmushi, ta d'auka " Hello Jaheed" bayan
sun gaisa yace "Ummey gani a Kd fa idan kina gida zan zo
na gaida su Dady" "laaa shine saida ka iso zaka gaya min" "
ooh sorry sister na" suka k'are magana ta juyo " Najma, wai
Jaheeh ne yazo KD, kuma fa bai gaya min zaizo ba, sai
yanzu" "ai ba matsala sai muje mu gyara d'aki a masa d'an
girki " " kinga fa kamin muje kila ya iso, kima Mumy magana
kawai ta had'a masa girki" ta zaro ido," Mumy ce zata mana
girki, " ta fad'a tana girgiza kai.......