Breaking News

MIJIN MARAINIYA PART 2

MIJIN MARAINIYA PART 2
.
Itako safna bata fahimci me goggo ke nufe ba dan bata da
wannan labarin , haka tai ta zaman jiran goggo har ta gaji
tun tana ganin wucewan mutane daidai har ta daina gani
dan haka tsoro ya shige ta, mikiwa tayi tabi hanyar da
goggo tabi , tana tafiya tana dubawa ko Allah zai sa su hadu
da goggo. wata mota ce ta shigo layin tun daga nesa motar
ke hasko ta, dan haka ta tsora ta , motar na zuwa kusa da
ita ta tsaya, wani dake cikin motar yace yace ke ina zaki da
daddaren nan, kisan ko karfe nawa kuwa? cikin kuka me
ban tau sayi ta girgiza kai wanda ke mazauni direba yace
kabir ina ruwan ka da ita ne kasani ko aljana ce yanzun
12:15 pm fah ,yace yarinyar ar zikice za aganta a waje
awannan lokaci, kabir yace kuma fah haka ne aboki na,
motar su kaja suka mike layin.
.
Safna ko babu abin da take ban da kuka, gaba tayi kadan ta
samu wani dan dutse ta zauna sautin kukan ta kawai kake ji
awajan wasu samari ne suka zo wucewa su uku irin yan
shaye shayen nanne sun sha sun bugu daya daga cikin su
yace kai kunga wata baby danya, da sauri suka isa wajen ta
suka fara ja mata dan karamin hijjabin dake jikin ta safna
ko kuka take tana kokarin guduwa amman Ina sun riga sun
rike ta dukkan su ukun har sun yaga mata riga dama
bawani kwari ke gare suba suna kokawan kwance mata
zani . wan,nan motar ta dazun ce ta sake dawo ,mutun
daya ne acikin ta sabani dazun da suke su biyu jin uhun
yariyar yasa shi tsayawa ya haska su da fitalan motar yaga
abinda ke faruwa da sauri ya fito yafara takawa zuwa
wajen yana musu tsawa cikin fada ya daga murya sosai .
daya daga cikin su yace kai kuzo mu gudu yaya abduljalal
ne da gudu suka kwasa abduljalal ya matso kusa da ita ya
tsoguna ya dauko hajjabin ta ya mika mata ta karba ta saka
kuka kawai take abduljalal yace yanzun ina zaki? tace
goggo nace tabar agun wata bishiya tace na jirata kuma
naga ta dade bata dawo ba, sheni na biyo hanya ko zan
ganta. cikin mama jalal yace kina nufin mahaifiyar ki kece
abarki a titi. a,a kishiyar mama tace. yace to ke ina mamar
ki? cikin kuka tace suyi hatsari har baba na sun rasu. Jalal
ya tausaya mata sai dai har yanzun be gama yar da, da
yarinyar ba yana ganin kamar dai ta fito yawo ne, ya juya
yace Ina yan uwan ku suke, tace nibasan kowa daga cikin
dangin muba kakata kawai na sani itama ta rasu jiya akayi
bakwai, shine akace ma goggona takaini gun dangin kakata,
shine ta barni tace najira ta tadawo. hankalin jalal ya tashi
ya rasa yan zun ya zai yi da yariyar nan gashi dare na
dadayi , zuwa yayi yabude motar sa ya shiga da gudu safna
ta biyo shi tana fadin dan Allah karkabar ni anan. ai bazan
barki a nan ba ya bude dayan gefen yace shiga mutafi ,
bayan tashiga ta zauna jalal yace ya sunan ki? tace sunana
safna. Jalal ya sake maimaita sunan safna da sauri yafara
neman fitilan motar haske ya baiyana yace safna bake bace
shekarun baya na saya rake wajen ki, dama ke ma
rainiyace. cikin kuka tace eh. Yace to kibar kuka safna
insha Allahu zakiji dadin rayuwan ki , jan mutan yayi ya fara
tafiya yana tunani yadda zasu kwashe da ummin sa.
lokacin da ya isa gida me gadi yabude mai ya shiga yarasa
yadda zaiyi da safna dan yasan yanzun ummi batayi bacci
ba saitaga dawowan shi , kilama yanzun tana kallon shi,
dan haka dibara tafado mai yace safna inazuwa bari naje
nadawo. cikin sauri safna ta rokoshi tace dan Allah karka
gudu ka barni kaima. cikin kwatar da murya yace bazan
guduba safna yanzun zan dawo ai nan gidan mune da
guduwa zanyi ai bazan shigo dake cikin gidan muba, ban so
ne ummi na ta ganki daddaren nan saboda kartayi wani
tunani daban kuma nasan tananan tana jiran shigowa ta,
sabo da haka kijirani yanzun nan zan dawo. Gyada mishi
kai kawai tayi amman bata son ya bar ta anan. yana shiga
ya samu ummi sai zagaye falon take da sauri shi yaje ya
rungume ta, hannu ta tasa ta tukude shi.
.
abinda kuma zaka fara kenan yawon dare Ina ka tsaya har
1:30 shiyasa babanka yake cewa ninake sangarta ka.
tsugunawa yayi ya kama kafar ta yace immi kiyi hakuri
kabir ne be fito da motar saba sai da nakaishi gida kuma
ummi kisan gidan su da nisa amman ummi dan Allah kiyi
hakuri bazan kara ba. hannun ta tasa ta dago shi ta
rungume tace jalal dole hankali na ya tashi kaikadai nake
kallo naji farin ciki ya lulubeni nazaci kai kadai ne kwaina a
duniya sai daga baya Allah ya kawo mana Kairat alokacin
dana cire tsanmani kuma har yanzun baji sonka ya ragu
azuciya taba, jalal nakosa naga matarka zataga gatan da
babu wacce ta taba samu a gurin sirikar ta, balle kuma
naga yaran ka. dukar dakai yayi yana murmushi , ummi
tasake cewa jalal baka fara tunanin aure bane har yanzun.
da da durkusar dakanshi kasa yayi yana sosa keya. ummi
tace yau kuma kunya ta kakeji , hmmm jalal mayan kasan,
abin da nake so dakai in katashi nemu mata kasamo mana
yar manyan mutane kar ka sake kawo mana yar matsiya
ta.
.
jalal ya dago ya kalli ummi yace ba komai ummi karki
damu, ummi bari naje na kwanta tace to ba damuwa Allah
ya tashi mu lfy,mikewa yayi yanufi hanyar dakin shi ummi
ta bishi da kallo tana murmushi har ya Kule. shiko jalal ko
dakin shi be shiga ba yabi ta kofar baya ya fita, ya bude
murfin mutan yaga safna tayi zuru zuru roko mata hannu
yayi suka shiga ciki ya bude dakin shi suka shi , yace kinaji
yunwa ne? tace a,a . to ga bayi nan kishiga kiyi wanka inki
fito kisaka wannan rigar yanuna mata wata karamar rigar
shi. in kin gama ki hau gado ki kwanta da safe zan shigo
karki sake ki fito. futowa yayi falo ya kwanta washe gari
jalal najin kiran sallah subahi ya mike ya shiga dakin ya
tashi safna dake bacci akan makeken gadon shi, sannan ya
wuce masallaci. bayan safna ta idar da sallah tana zaune
kan darduma, taji anturo kofar da karfi , wata yar yarinya ta
gani ba zata wuce shekara biyar ba , tana fadi yaya jalal
jiya inata jiranka har nayi bacci baka dawo ba ,waige waige
ta fara da safna su kai ido hudu dan haka ta saka kuka ta
juya aguje tafita adakin, tana fita sukaci Karo da jalal ,
yarike ta yana fadin me ya sa meki ?
.
dakin ka naji neman ka ban gan kaba sai wata aljana
nagani . Jalal dariya yayi sosai sannan yace ba aljana bace
anty ki ce na kawo miki amman karki gayawa ummi. da
sauri tace sabo da me baka son ummi ta sani. saboda bana
son ummi ta koreta koke kina son ta kore ta. a,a to yaya
matar kace. a,a kairat itama kanwa tace kamar yadda kike
kanwata , janta yayi suka shiga cikin dakin. lokacin safna
na zaune abakin gado tayi tagumi. ya dade tsaye akanta
bata masan ya shigo ba. sai da safna ta kwana uku ummi
bata san da zuwan ta ba. ummi ko na lura da jalal baya
kwana dakin shi kuma yanzu baya cin abinci sai dai yakai
dakin shi , sabanin da yana ci yana sha gwaba, dan haka
tace azuciyar ta koma me yake baye mata yau zata gain.
yauma kamar kullum jalal ya dauke abincin shi ya nufi
dakin sa ummi na kallon shi, tana nan zaune har ya fito,
binshi da kallo kawai take, ya dade zaune ya mike yace
ummi sai da safe, to kawai tace dashi. Yashiga kenan ya
zauna yaji anturo kofar , razana yayi ya mike yana fadi
ummi lafiya, ummi bata bi ta kansa ba zuwa tayi ta dago
safna dake kwance akan gadon jalal tayi wurgi da ita.
.
jalal ya mike da sauri ya daga ta yasa ta ajikin shi yana
rarashin ta dan har ta fita hai yacin ta. ummi ce ta kara
matsowa cike da mamaki tace yaro Ina kasamo yarinya har
ka ajeta adakin ka ban sani ba. kallon shi tayi taga yasa ta a
kirjin sa , sai faman rarrashin ta yake, cikin daga murya
tace jalal kaine ka kawo min karuwa har cikin gida kasata a
kirjin ka agabana dan ka nunamin kai tantirin dan iska ne
ko? cikin sauri ya sake safna yace ba haka bane ummi wlh
ummi ban taba zinaba kuma wlh safna ba karuwa bace
marainiya ce bata da uwa bata da uba kuma abin da yasa
na kasa gayamiki nasan bazaki fahimce ni ba ne. ummi
tace shi yasa ka muna fun ce ni , to maza maza ka tarkata
ta ka fitar min da ita agidan nan, dan kaga na kwalfa rai
akanka shine zaka neme ka watsa min kasa a ido , kasani
sarai bana hada guri da talaka. abduljalal yace to naji zata
fita ummi amman nima bazan xauna ba zan je na nemar
mata gurin da zata zauna tunda mu arzikin mu talaka bazai
amfana da shiba. cikin taga murya tace ni kake mayarwa
da magana akan wata banzan yarinya, to katafi din in baka
tafi ba karai na Allah kuka tasa harda kururuwa yau ga dan
ta na cikin ta yana mayar mata da magana, tace indai ko
kabi yarinyar nan Allah ya isa nono na ?da kasha. Jalal ya
zaro ido yace ummi abin har yakai haka, to shi kenan ummi
na hakura ke safna tashi ki tafi , safna tana kuka ta mike ta
fita daga dakin. Jalal ma tsugunawa yayi ya soma kuka
yana fadin ummi,ba ta san kowa ba fa , kuma bata da inda
zata ummi marainiya ce fa , ummi ko gezau bayi ba. suna
cikin haka suka ga alhaji mustafa rike ta safna ya shigo har
dakin abduljalal, ummi da sauri tace alhaji shine bayi waya
kana hanya yau ba sai dai kawai muganka. jalal mikewa
yayi yakoma jikin dady ya kwanta alhaji yace wanan
wacece na ganta Waje tana kuka . cikin sauri ummi tace
bamu santa ba. alhaji yace karya kike yi zaliha duk naji abin
da ya faru wai kece kike kin talaka dau la yasa kin manta
asalin ki, to tun da kin manta bari na tuna miki