Breaking News

RABO NA CE PART 8

RABO NA CE PART 8
.
Ummey ce da Anti Najma suka shigo gidan, sun dawo daga
gurin salon ko me za'a ma salon ohon, gashi kamar bindin
akuya, itadai Anti Najma da yake ita kam akwai gashi har
gadon baya, kyau ne kawai batada sai ido kamar na mujiya,
dan Ummey ta kereta nesa ba kusa ba gurin kyau, suna
tafee suna hira, a palo tayi karo da Muhammad ya dawo
daga makaranta, yana chin abinci ta kalleshi, tace "yaron
Mumy sannu da aiki" ya kuwa cika bakinsa da abinci yana
ya mutsa baki, chakwal- chakwal, ta yatsina fuska,"kai
wallhy ban san lokacin da zaka iya chin abinci ba, kalli
bakinka dan Allah,? kalli gaban ka ma, haka zaka yiwa
Shaheed idan yazo ganinka,?" sabida jin an kira Shaheed,
nan da nan ya kware ya fara tari, sai da yayi tari sosai,
sannan ya dawo hayyacinsa, idonsa sun wani firfito, a haka
kums yanada bakin magana yace " sister Uncle Shaheed
zaizo ne?" dariya aka saka dukansu ya kwabe fuska,
shikam bayason yayi magana a masa dariya sai kace wani
babban mutum ta matso ta dafa kanshi, " sorry yaron
Mumy, shaheed yace zaizo gurinka on 25/5, sai ka shirya
tarbonsa," ihu ya saka yayi wani tsalle, garin tsalle ya fad'i,
amma ko a jikinsa, mik'e wa yayi yaci gaba da jin dad'in sa,
sai da ya k'are sannan yace " sister yaushe ne 25/5 saura
kwana nawa daga yanzu?" ya tashi ya janyo kujera ya taka
ya d'auko agogon bango, " sister sai yakai k'arshe sau
nawa, zai zama 25/5 d'in? " yaba kowa dariya a palon har
nafee anka 'yar aiki da take lek'ensu, dan haka halinta yake
tana aiki tana lek'en mutanen gida dan gulma, itama sai da
ta dara, ya k'ara k'ule wa, Ammar yace "kai kyalesu zo na
nuna maka," da sauri ya rungume agogon yaje gun Ammar,
Ammar ya karba ijiye agogon " kaga shi kwanan wata ba
irin agogo bane," nan dai Ammar yayi ta masa bayani har
saida ya tabbatar da ya gane, sannan ya barshi, nan fa
Muhammad ya fara lissafi, daga yau zuwa ranar saura
kwana goma kenan daga yau, aiki ya sami maza, haka ya
matsa saida aka kira masa Dady ya masa albishir, bayan ya
k'are yace a kira Ummul-khairi itama saida ya gaya mata,
haka ya nace sai da aka kira sauran yayyen sa aka musu
albishir suma, yana ta jin dad'i, ranar duk motsi zancen sa
d'aya...
.
********
Shaheed ne ya dawo gida daga wani wasa da suka buga
duk ya gaji, yana zuwa ya cire kayan jikinsa, sai wasu na
ciki, ya d'ora d'an towel a kafad'arsa ya kwankwad'i juice,
ya d'ago kansa ya hura iska "Huuuuuuuuwww" idonsa suka
fad'a akan hoton sa dana Muhammad daya kafa a palon,
da sauran wasu fans d'in sa da yakeji dasu, ya kalli
Muhammad, wannan yaron akwai rigima yayi d'an
murmushi, shikam Allah ya d'aura masa son Muhammad,
ko dai yayar Muhammad, matsowa yayi d'an kusa da hoton,
ya kalleta yasan bashi da matsala, kamarshi a Nigeria ba
macen da zai ce yana so ta k'ishi, musamman idan yaga
yanda yan mata suke masa zarya, saboda haka yasan ma
Ummey rabonsa ce, so bazai nuna mata maitar sa a fili ba,
tunda fans dinsa ce dole ma ta amince dashi, ya matsa daf
da hoton ya shafa fuskar su, da yake tad'an fito kad'an a
hoton, yace " basai nasha wuya gun gabatar da kaina ba,
nasan Ummey ke RABON NA CE" ya fad'a cikin gadara da
shauk'i da gani kasan yana son abinda ya fad'a, dan fuskar
nan tashi cike take da annuri, yana k'are fad'ar haka ya
haura sama, ya sami kansa yanason jin muryar Ummey, ya
d'auko wayar sa ya kirata ba'a jima ba ta d'auka da muryan
nan tata garo-garo, a ranshi yace "tsarki ya tabbata ga uban
gijin wannan yarinya, maganar ta ma sanyi take da,"
maganin wani gubar wani inji bahaushe, shiko muryar ta
take masa dad'i, da taji shirun yayi yawa, sai ta sake cewa
"hello," sannan ya dawo hayyacin sa daga duniyar tunanin
da ya tafi, ya amsa mata cikin natsuwa, bayan sun gaisa
take cewa" gashi kuwa Muhammad d'in yana islamiyah, sai
dai idan ya dawo sai mu sake kiranka," yayi murmushi "ba
komai Muhammad's sister idan ya dawo ku kirani, hope
kuna lafiya?" Ta amsa da "muna lafiya mungode da
k'aunarka garemu," Sukayi sallama, Ya wani lashe bakinsa,
anya bazan tafi gobeba, I really Miss u Ummey!! Ya juya
yana murmushi har bacci ya d'aukeshi cike da tabbacin
bazai sha wuya gurin Ummey ba.
.
Sannu-Sannu kwana nesa, yau saura kwana biyu Shaheed
yazo gun Muhammad d'insa, ko nace gun sister d'in
Muhammad, suna zaune a palo ana hira kamar an tsokari
Muhammad ya juyo da sauri ya kalli baban nasu "Dady
gaskiya a ma gidannan fenti, a zana hoton basketball ball a
gate d'in gidan, kuma kowa a dinka masa sabbin tufafi," da
ka kalli fuskar Muhammad zaka gane da gaske yake
zancen sa, haba nanfa aka shiga dariya, sam baya fushi
akan shaheed d'in sa, da ace akan wani issue ne, da yanzu
yayi fushi ya fara kunbure-kunbure kowa dai jinsa yake, ana
binsa da to, dan bana jin wayannan abubuwan da yake
lissafo za'a aikata ko kwatar su, haka dai ya kare zubar sa
har bacci yayi awon gaba dashi. Bayan wannan
Muhammad gaba ki d'aya class mate d'insa ya gayyace su
har na islamiyya dana boko, kuma bai gayawa kowa cewa
yayi gayya ba, ya sakawa yaran sharad'in cewa duk wanda
zaizo dole ya saka riga mai sunan Shaheed Al- Qaseem,
Muhammad kenan.
.
**************
Ranar 25/5 baiyi bacci ba Sam, bayan ya k'are borinsa
akan ank'i a ma gida fenti kuma ank'i yin d'inki sabo, amma
yace dole a saka kayan sallah, a gun Muhammad sune
kayan da suka fi ko wane daraja, ya k'are jarabarsa da
yake bacci barawo ne tuni ya sace shi, bai farka ba sai
bayan asuba, shima motsin mutane ya tayar dashi, nan fa
ya d'ora daga inda ya tsaya, har gari ya waye, haka ya saka
mutane gaba, ya matsa musu akan sai kowa yayi wanka,
kai ranar kowa da dabara ya samu ya gudu masu
makaranta suka tafi, masu zuwa aiki suka wuce, koda ya
duba ba kowa a gidan bai damu ba, Mumy ya hango a
kitchen tana ma nafee anka fad'a da wa'azi, sabida satar
abincin da take tana kaiwa gidan su, yana shiga yace
"Mumy waina zaki masa, da miya," haka kuwa ya hana ayi
ko wane girki a gidan dan ya iya jaraba, idan akayi magana
sai yace "gurinna zaizo ba gurin mutum ba," Muhammad na
shaheed, Mumy dai kam da dabara ta k'ara had'a wasu
abincuka na tarbon bak'on kunya, batare da Muhammad
yasan abincin waye ba, shi dama ya shirya tun safee, da
gyar ya bari aka k'ara shiryashi, tun guraren k'arfe biyu
yara suka fara zuwa gidan, kowa yana mamaki miya kawo
yara a gidan, basu san uban gayya ya gayyatosuba, ko
wanne da rigar Shaheed kuwa, har wayanda bai gayyata ba
sunzo, haka ya jibgesu k'ofar gida wai su masa sannu da
zuwa idan yazo.
.
Shaheed ne ya fito gidan sa, shigar kayan hausa yayi, ta
zarce har k'asa, sun masa kyau sun fito da cikar surarsa,
dama ba laifi Shaheed, ga fara'a ga farin jini, d'an gajere
dashi, kamar an bugawa k'usa guduma sai yayi kyau cikin
kayan sosai, ta zarce a gurin gajeren mutum ba k'aramin
kyau yakeyiba, ya kama hanya ya nufi gun Muhammad ko,
ya fito ya tsaya wani mall yayi siyayyah wa Muhammad bai
siya ma Ummey komai ba dan kada ya bada kanshi a
ganeshi lokaci d'aya, a hanya yayi karo da wani yaron sa,
ya kawo masa riguna masu d'auke da sunan sa, har zai ce
ya kaisu gida, sai kawai ya bud'e but yace a zuba masa su
ciki, ya ci gaba da tafiya. Dama ya karb'i address a gurin
Ummey so baisha wuyar gane gidan ba, dama yaso saidai
kawai su ganshi ne, tun daga nesa ya hango kamar yara,
sanye da riguna masu d'auke da number sa da sunan sa,
saida ya kawo ya gaskgata zarginsa, murmushi kawai yayi,
yana fitowa yaran suka zagayeshi suna masa welcome, yaji
dad'i sosai dan yanason yara a rayuwarshi, a lokacin yaji
dad'in rigunan da ya karb'a , ya bud'e bayan mota ya d'auko
ya rarraba musu sunata murna, a lokacin ne Muhammad ya
fito cikin gida sabida ya d'an ji hayaniya, karaf idon sa akan
Shaheed, habawa da gudu yaje gunsa yana murna ya
rungume shi, bakinnan mara hak'ora yak'i rufuwa sai wage
shi yake, shaheed ya samu ya k'are da yaran, Muhammad
yace "an sallami kowa, kowa ya tafi gida," a haka suka
watse, yana rik'e da hannun Muhammad, ya tsuguna, yana
masa murmushi, yama rasa mi zai ce masa, ya sami kansa
da cewa "ina sister Ummey?" "Suna islamiyah sai Ana
Allahu Akbar suke dawowa.....
.
A ranshi yace "kodai ta manta ne? Idan kuwa ta manta to
banida muhimmanci a gurinta! No bazai zama ta manta ba,
inaga dai ta d'auka da yamma ne zanzo tunda ban fad'i ko
k'arfe nawa zanzo ba," Muhammad yace "mu shiga ciki
Mumy ta maka girki, kana chin waina, ko?" Ya fad'a yana
kallon sa, yad'an yi murmushi, " sosai nakeson waina, gashi
kuwa na dad'e banci ba" yana k'ok'arin janyo hannun sa,
yace "no tsaya muyi hoto" ya d'auko camera ya fara d'au
kansu hoto, haka Muhammad yayi ta rufee baki kada aga
ba shida hak'ora, saida ya gaji ya sake bakin dan kanshi,
sai da sukayi hoto sosai sannan ya turashi yace ya gayawa
mutan gidan yazo zasu gaisa, ya ruga da gudu ya gaya
musu an masa iso ciki, ya gaisa da kowa cikin mutunci yaji
dad'in yanda aka girmama shi, sabida haka ya k'ara
tabbatar da cewa bashida matsala a wannan gidan, yaci
yasha, yasha labarai a gun Muhammad har wanda ba'a
tambayeshi, sabida hatta fenti da yace ayi aka k'i yi saida
ya fad'a, ya bashi tarihin duk gidan iya abinda ya sani,
shikam Shaheed hankalin sa na gun Ummey da har yanzu
bata dawo ba, har Dady ya dawo sun gaisa, shima ya
gaidashi cikin girmamawa Dady yaji dad'in ganinsa, mutum
fitacce irinsa yazo gidan sa sabida d'an sa ai da dad'i, sai
chan Ummey ta dawo, Muhammad ya jiyo maganar ta palo,
ya dafa kafad'arsa "Uncle bari na kira Anti na" ya wuce da
gudu yana zuwa ya janyo hannun ta "uncle Shaheed yazo
Ina kika tafi tun d'azu nake neman ki" ta shafa kansa, suka
wuce d'akin, tana shigowa ya mik'e tsaye, ya gaidata, " laa
miye haka Uncle Shaheed" ta fad'a tana murmushi, a ransa
ya maimata sunan "Uncle Shaheed" shikam muryan ta na
masa dad'i yanda take magama dad'd'aya duk da cewa
muryanta garo-garo ne, sun gaisa suka d'an tab'a hira
dukan su, duk da ba wani zancen soyayyah sukayiba amma
yaji dad'in kasan cewa tare da ita, har yayi sallama ya wuce
gida, Muhammad kamar ya bishi yakeji, hadda d'an kukan
shi, sai lokacin Shaheed ya tuna ya masa siyayyah sannan
ya d'auko ya bashi, sai kuma yayi shiru. Shaheed kam ranar
cike da nishad'i har ya koma gida, waswasin da yake
akanta duk ya gudu, shi kam Ummey ta masa, yanayin
maganar ta yana masa dad'i, gata da murya garo-garo
amma kuma ta iya magana, Ummey insha Allah RABO NA
CE ke, sai na Aure ki duk tsanani, haka ya k'are surutun sa
har bacci yayi awon gaba dashi... Muhammad kuwa ba'a
cewa komai sai kuri yake yana wani jin dad'i, hirar dai d'aya
uncle Shaheed, saida kowa ya gaji.
.
**********
Su Ummey an sami nasarar shiga jami'a har zata 200lvl
Yanzu, kada kuyi tunanin Shaheed ko jaheed cikin su ya
bayyana abinda ke ransa, ko alama har yanzu, Shaheed
gani yake ita fans d'insa ce to komai ya nema a gurinta zai
samu, sannan gashi ya samu shiga gidan su, yanda yake
fitaccen nan daya fad'i yana sonta dole ta amince,
musamman yanda take girmamashi sai yake ganin kamar
sonshin da takeyi yafi Wanda yake mata yawa. shi kuma
jaheed gani yake komai yana samuwa da sauk'i, yake ganin
kamar yarinya ce so yana fad'a zata amince tunda ba tada
wani tsayayye. Sai kaka.
.
*****
Yauma Dady yazo musu da labari mara dad'i, an k'ara
masa transfer zuwa sokoto birnin Shehu, koda yaji dad'in
haka musamman idan ya dubi cewa sokoto chan ne
asalinsa, kowa baiji dad'i ba har ma dai su Ummey da suka
fara karatu yanzu, har sunce a barsu garin su koma hostel
amma Mumy tak'i yarda, haka suka hak'ura suka tattara
suka koma sokoto birnin mujaddadi Shehu. Basu sha
wahala ba gun shiga dan fodiyyo, sabida sunada hanya, nan
da nan taci gaba daga inda ta tsaya, anan suka had'u da
wata yarinya course mate d'in su ce mai bala'en shishigi, ga
gulma da surutu, duk abinda ya faru a makarantar tasan
dashi, koma da ita aka had'a shi, SADYDY ake ce mata,
wasu suna ce mata gul -gul uwar gulma amma batasan da
sunan ba, mugun halinta yasa Ummey bata bata fuska sam
duk da tayi shishigi daidai kwarkwado Amma ba nasara sai
ta dawo tanajin haushin Ummey.
.
***
Sun fito lecture, ta tsaya jiran Najma su dawo gida tare, ta
fito take bata labarin jibi zasu je dam d'in garin shagari,
gurin wani show, da yake agricultural take karantawa, suna
tafe suna hira har suka isa gida. Ranar da zasu tafi, tun
safee takejin kamar batada lafiya, amma dan jaraba da son
yawo saida ta tafi, sun isa gurin bayan an nuna musu
abubuwan da sukazo yi, tadan zauna tana sauraren wata
wak'a ta soyayyah, a ranta takejin zata tsayar da saurayi
dan tana buk'atar soyayyah, soyayyah akwai dad'i a cewar
ta.!
.
Tana tsaye Sadydy tazo tana mata iyayi, bata tsaya kulata
ba dan bata bata fuska ko kadan, "Laaa Ummey kalli Dr
Mahbuob," Ummey ta d'aga kai takai duban ta zuwa ga
wanda aka cewa Dr. Mahbuob kyakyawa ne ajin k'arshe,
dan gaskiya duk yafi su shahed da Mujaheed had'u wa ta ko
wane fanni, k'ananan kayana a jikinsa, ya saka wata hulan
sanyi a kansa had'e da wani shol a wutansa, hannun rik'e
yake da wata sanda irin wacce hadaddun gayu suke rik'e
wa yasha wani shade a fuskarsa dayan hannu kuma
camera ce shigar turawa yayi, yana ta selfie yana wani
karye karyen jiki kamar benazir zata d'auki hoto, shine turo
baki, shine lankwashewa, murmushi kawai Ummey tayi,
Sadydy gul-gul ta washe watsatsun hak'oranta tace, "wallhy
duk dan fodiyyo ba wanda yakai guy dinn nan iya wanka,
kumafa lecture ne," ta wani had'e yawu, ta kalli Ummey
"Allah inason guy d'innan inama zai soni" Ummey ta kalleta
wata mummuna da ita, ko hak'oranta abin kallo ne dan a
hargitse suke, gata wata mummuna da ita, gata ita ba
tsawoba kamar doya a dunk'ule take, ga k'ananan ido
kamar na yan china, Ummey a ranta tace kyanki abarki nan
kiyi ta noma kawai dan kin fi kama da manoma,murmushi
Ummey tayi ta k'ara kallonshi ta juyo ta kalli Sadydy ta
tintsire da dariya aranta tace inake Ina wannan flowers d'in,
itama Sadydy dariya tayi tana jin dad'i yau Ummey ta
kulata, Ummey kawar da kai tayi , chan Sadydy tace "
Ummey kalli shi kalleshi," ta fad'a tana jijjiga Ummey, wato
wani hoto ne ya d'auka wanda nima Jabo saida ya burgeni,
tsam Ummey ta mik'e tabar gurin Sadydy, ta bita da kallo,
tsaki tayi ta murguda bakinta da yaji hargitsatstun hagora,
Ummey chan ta matsa chan gab da ruwa tana tsaye sai
itama taji bari tayi hoton tarihi ta more, wato ruwa akwai
dad'in kallo, kuma suna cirewa mutum kadaici, ta dauko
wayar ta fara nata hotunan, ashe Dr. ya hango ta, kuma ta
burgeshi musamman yanda yaga cewa yar department d'in
su ce, daga chan nesa da mutane taje, tana ta d'aukar
kanta hoto, yana kalle da ita dan shima mayen hotone na
k'arshe ji yake kamar ya bita su dauka tare, wanine ya
kirashi ya tashi koda ya dawo bai ganta ba, yayita dube-
dube bata, da yake mafi yawan cin student suna cikin tent
d'in da aka kafa suna hutawa wasu kuma sun shiga lambu,
sai yad'an lek'a tent d'in mata a hankali cikin taku na
kwararren d'an boko, amma duka bata, ya matsa gurin da
ya ganta cikin taku na isa da nuna irin aikin gabana nakefa,
koda yaje gurin, ga jakarta a k'asa ga wayanta amma bata,
kuma ko wanne kamar anyi wurgi dasu ne, d'aga idon da
zaiyi ya hangota tana butsul- butsul cikin ruwa, wani ihu
yayi Wanda ya janyo hankali duka mutanen gurin, mutane
suka yo gunsu da gudu kamin suzo tuni ya fad'a ruwan,
ashe gurin wani mahaukacin zurfi yake dashi, dagyar ya isa
gurinta Amma yasha ruwa dan zurfin wurin ya wuce
hankali, gashi ya d'auko ka amma sai ya kasa fitowa da ita,
sai kokowa yake da ruwa, ya d'auketa yanda ba zata sha
ruwaba, amma shi sai shan ruwan yake, har k'arfinsa ya
kusa k'arewa, a wajen kuwa masu kuka na kuka masu
d'aukar hoto na d'auka aka rasa Wanda zai shiga ya
taimakosu, sabida malaman sun ce masu kula da gurin su
bar student su sake,hakan yasa k'auyawan dake gurin duk
suka tafi gida, Dr Mahbuob a ruwa duk ya galabaita, dai-dai
nan ya saketa yayi k'asan ruwan....