Breaking News

*** *BARIKI IYAWA PART 20* *** ****** *KARSHE ******

*** *BARIKI IYAWA PART 20* ***
****** *KARSHE ******
.
Baba mai gadi ta sanar wa abinda ake ciki,.Tana kokarin
fita da mota sai ga nan Jummai, rike da Jaka 2 a hannun
ta,. Fitowa tai a motar Ganin kanta tsaye tai cikin gida,Binta
tai taga Iya gudun ruwan ta,. Kofa take ta ja taki bude
wa.."Hala da gadon Ubale a gidan nan ne Jummai??. Ta
juyo baki sake tana kallon ta,. Harde take da hannu a girji,
ta hade girar sama da kasa., Sai tai mata bala'in k'warjini,.
Dan Tunda suke zuwa gidan Sa'a basu ishe kallo ba bare tai
musayar yawu dasu,. Kai ta girgiza mata,. "Wajen Zahra
nazo.. Rai hade tace"Uhmm, daga nan fa??.Duk rashin
mutuncin Jummai sai ta zama kamar wata doluwa a gaban
Sa'a,. " Jakar ta na kawo mata,. Baba mai gadi ta kwalawa
kira,cewar ya kulle mata gate ya zo kuma, Tace ta bata
jakar,.Ba musu ta miko mata,. Maimakon ta karbi ta
Zahran, sai ta warce ta Jumman,. Yayi dai-dai da zuwan
Mai gadi,. Matsowa tai da zummar kwace jakar ta taja
baya.. Hannu ta nuno mata,.tare da kada mata su,. "A'a.,ta
kada mata hannu halamar gargadi," (Don't even think about
it),.Tai mata wani kallo.." Dan Kinsan Allah? kika yarda kika
matso sai kin yaba wa A'ya zakin ta a gidan nan,.. Chak ta
tsaya,baki sake ta kasa magana,. Ta kallo Baba
maigadi,wanda ya dakko katuwar gorar shi,. Jira yake Tace
"Ass,ya sau aiki.. " Baba in tai k'wak'waran motsi Ka bigen
yar iska,.Ya kada kai "An gama Hajiya,. Tuni ya Matsa
gaban Jummai yai (ready)da sandar shi,. Zazzage jakar
tayi,kudi Suka zubo da tarikicen magun gunan ta,.
.
Ta zuge munafukin zip din cikin, sai ga sarkar Zahra ta fito,.
Wanda akallah zatai 250,haka Abban su Hafeez ya sa
musu,.Ta makawa Jummai harara,."Macuciyar Allah ta'ala
kawai,.. Jummai ta hadiyi yawu,.. Tace" Da kika boye
sarkar,ce mata zakiyi dan wannan chanjin ne kudin
sarkar??.Ta girgiza mata kai.., Sa'a tai kwafa,."Allah ya so
ki baki siyar ba,da wallahi na Lahira sai ya fiki kwanciyar
Hankali,."Ashawo kawai,.Ta warce jakar Zahran tana kara
hararar ta,. Gyalen Zahran ne aciki da wayar ta, ta dago
tana zare mata ido..,"Ina kudin da ke jakar ta'ta kan kije
Saida sarkar??..Da tsananin mamaki Jummai take kallon ta,
a zuciyar ta tana "Wai ina Sa'a tasan duk wannan
abun?.."Tambayar ki nake?..A yatsine tace. " wane
kudi??.."Au tambaya ta ma kike?.."Eyee??.. Ni zaki gwada
wa BARIKI??.. Tai kwafa,. Kudin jakar jumman ta tattara ta
mikawa mai gadi,."Baba kirga min su da sauri..,Da sauri ya
lissafa,."Dubu Asirin ne da Bakwai da Dari uku,.Ta kada
kai,. "(Good),.Baba ware min Ashirin da biyar aciki,.Ya kada
kai, tuni Jummai ta zaburo,,."Wallahi baki isa ba,Dubu
ashirin ne nata,.Toh Wai ma ina ruwan ki da harkar
mu??..Sa'a tai wani murmushin mugun ta,. Tace" Karamar
Yar iska kawai,.
.
Ba kince babu ba??..Nasan Na Zahra dubu Ashirin ne,.Biyar
din cikon na Taxi ne,.Sannan,daga rana irin ta yau, Baba
idan Ka kara Ganin kafar ta a gidan nan na baka izinin Ka
karya shegiya,. Yace"An gama Hajiya.,Jummai tai mata
kallon Banza,. "Ai ba wajen ki nake zuwa ba Malama,.
Wajen k'awata nake zuwa,.Kai ta girgiza mata, tana
murmushi, Da key din motar ta ta nuno ta " Idan Jummai ta
fito a cikin Uwale da halaliya,toh ki kara sako kafar ki a
layin nan ma kadai inda kiga??.. Ta dawo kan Baba,"Ka
ajiye min wannan jakar,Ka bata sauran chanjin Ta,. Sannan
kan na kirga (10),Ta bace min da gani anan,.Tace"D'aya,..
Ya duk'ar da kai "An gama Hajiya,.. Kan Jummai yai.,"
Maza tattara kan wa'adin ki ya cika,. Sa'a tace"Biyu,.Kallon
banza ta tsaya yi mata,."Uku,.Ba tsammani taji Baba ya
rafka mata Gora a gadon baya,Ai ba shiri ta hau tattare
kaya tana Kunkuni,.Sa'a Tace "Hudu,.. Baba ya sake sakar
mata wata,.Ba shiri tai magana" Toh Ka dakata man na
hada,.Da mugun ta Sa'a tace"Biyar,. Ai kwa ya kara dagawa
zai muka mata,datai wani uban tsalle sai tai gefe,."Allah ya
isa wallahi,. Sa'a tace"Shida,.Sai kwa Baban yai kanta da
gora,.Haba wa.,Jummai K'afa mai naci ban baki ba,.Sai ta
runtuma Gate a guje tana kiciniyar bude wa,. Sa'a tana
dariyar mugunta Ta kwala da karfi,."Takwas,.Ai baba ya
samu moriya, tuni ya kara sau mata aka,.Ihu ta kwala,
"Wayyo,Toh Ka bude na fita man,.Harda yar kwallar
ta,.Baban yace " Ba kin tsaya taurin kai ba??..Ni dan Tauri
ne,.Sa'a ta kara kwalo wa"Tara..,Dai dai baba ya bude
mata,amma da yake Shima chali-chalin kansa ne sai da ya
muka mata,.Sa'a mey zatai inba dariya ba,. Har kasa..Fadi
take "Ki tsaya man,Yar Kot'ar nan..Sai abi wani sarki
kuma,.. Da Allah ya isa ta shiga Taxin da ya kawo ta,dama
tace ya tsaya,..Har ta bar unguwar tana Allah ya isa,. Sa'a
ta zo gun Baban, Shima sai Dariyar keta yake bayan fitar
jumman,. Kudin ya bata,." Kaji Min Y'a da taurin kai
Hajiya..,Sa'a tai dariya,"Ai nasan bazata dawo ba,. Dubu
(2)ta ware,"Ungo Baba, kaima Allah ya sha dakai,.Bani
kayan ma kawai nakai ciki,. Ya duka baki har kunne,."Wai
Wai Wai,.Hajjaju Harda mu??..Tai murmushi,. "Toh Allah ja
da kwana,.Allah ya sauki Yar uwar ki lafiya.. Tace"
Amin,.Sai Lokacin ta tuna da asibiti, da sauri ta sa kayan
aciki,ta boye sarkar ta kullo tai asibiti..
.
Tana zuwa duk yan uwan Zahran sun zo,.Su Aunty
Maryam,. Suka tare ta suna mata sannu,.Tasleem da
Auntyn su Zahran Suka Taya ta debo kaya..Tambaya suke
an shiga??.Suka ce"Wai sai(9),.(In charge)din ne sai yanzu
yazo,. Ta duba agogo,(8:43)..Tai ajiyar zuciya,. "Toh Allah
yasa Ai a Sa'a,. Suka ce " Amin,. (8:55)Suka garo ta daga
labour Room,. Tayi lamau,kamar mai bacci,.Cewa tai a
tsaya tukun,.Duk Suka iyo kanta,."Sannu Zahra,.Ta daga
musu kai,.Sa'a take kallo,.Kan ta ce ta duko kanta
kadan,kamar mai rada tace"Sis ya Tambaye ni koh??..Ta
girgiza mata kai,. Hawaye ta fara,"Nidai kira min shi dan
Allah,Nace ya yafe ni. Sa'a ta dago,."Kiyi hakuri sis,.kinga
Doctors na jira a theater room,. Amma nayi alkawarin zan
nema miki(Right now)..Ta goge hawayen ta, "Nagode,. Allah
ya kaddara haduwar mu,..Sai ta karyar mata zuciya ta fara
itama kuka,. Kowa Kallon su yake, musamman Aunty
Maryam da tasan Sa'an Basa shiri da Zahra,. Ta rike Sa'an
aka gara Zahran,. Sai fatan a fito lafiya. Hafeez din ta
kira,.duk da wayan shi biyu tun zuwan ta,. Ta Isar da sakon
Zahran,. Suna nan zaune har kusan (11)Kamin aka garo
ta,.Ba inda ke motsi a jikin ta,. Suka basu Babyn girl din
data samu,. Zahra taje wajen Nurses din,." Ya naga bata
motsi toh??.. Sukai murmushi,. "Ai an mata (Anesthesia),
..
Za ta Iya tashi " (any moment) …Kar ki damu,.Ta sauke
ajiyar zuciya..Tace wa su Aunty Maryam zata zauna taga
tashin ta,. Su kace taje gida.,Ga masu kwana da yawa,.
Sannan gidan su ba kowa.. Aunty Ladi aka bari ta kwana da
ita,.Dakyar da taimakon wayar Hafeez ta Iya bacci,. Dan
ma ta taho da Tasleem,. Washegari sassafe ta gama
komai,.Su Bahon wankan baby,ruwan zafi,.Abinci, Tun
asubar fari data tashi bata koma ba,.Bacci ne tun yana
diban ta har ta daina ji,.Akai Assalatu ta tashi Tasleem, da
mamakin ta taga sai kiciniyar soye- soye take,.Tace Ai da ta
tashe ta,. (7)Suna asibiti,.Ta tashi Alhamdulillah,Sai dai
Rashin karfin jiki,. Sukai mata sannu,,ta dau
baby,mashaAllah, Babyn Mai kyau da ita jinin su Hafeez,
kamar su guda,. Tace"Umm,su Zahra, An samu abin
nema,.Ganan Zankadediyar Budurwa mun samu,.Tai
Murmushi tare da kokarin a gyara ta,. Aunty Ladi tace zata
gida Tunda Sun zo,dan bata shirya ba,.Tasleem ta tafi karbo
wani result,. Ta kallo Sa'a,. "Sis kema Allah ya baki
Baby,.Tai Murmushi,. "Sis sai dai fatan sauka lafiya,.Ido ta
waro,." Kai haba??..Ta kada kai tana murmushi,. Sai yanzu
ta kula da farin Sa'an, tai wani fresh da ita,. Ga cikin duk
yabi jikin ta, musamman kasa.. Tai murna kwarai har
ranta,.Tai mata fatan Rabuwa lafiya,. Kan (11),yan uwa sun
zo da daman su,.Kowa yana tai wa Sa'a son barka,dan
kwarai ta burge su,.Ga nan mai kula zai ga cikin ya dan
tasa,.Aunty Maryam data kula da cikin Sa'an taji dadi
kwarai,.Tana son Sa'a, don mai son naka Ai Ka so shi.
Hafeez ya kira su ta bawa Zahran Suka basu waje,.Amma
sai ta rike Sa'a,.
.
Azahar Hafeez ya danno Asibiti, ko gida bai je ba,.Sa'a ta
mika mishi baby tare da manne mishi suna Kallon ta
tare,.Zahra tuni ta fara adu'a,.Dan jin chanji a ranta,.kai
gaskiya kishi jaraba ne,.Ita Sa'a bata dauki abun wani abu
bama,. Kwanan su 3 aka sallame su Suka tarkata gida,.Dan
fa Zahra tsaf take manne kayar ta ba ko kara,. In za'ai
wanka,ta dinga"Ai hankali da idon ta,. Koda Hafeez ya nemi
ba'asin waya,Sa'a ce tace"Ai ita ta bari a despensry,.Ya
chake mata kudin ta na asibiti,.Fir tace Gudun mawar
tane,.Baba ya kira yai mishi godiya.
.
Sa'an shi ta daban ce. Zahra ko ta Jummai bata yi,burin ta
ta tsallake fadan Hafeez, tasan yanzu K'afa ya daga mata.
Batun suna da ya tambayi Zahra ta bashi mamaki da tace
Sa'a,. Kuma yaji dadi sosai. Amma tace ya rufe Kar ya fada
mata sai ran suna. Dake garau take,suna ba fashi sati
nayi,. Da safe taci Ado na kece raini da Wani less Din su da
Sa'a ta din Ka musu na fitar suna,. Kiran wayar ta Sa'an
tayi kan ta same ta a stairs,. Ta kalli mudubi, komai
yaji,.Taso sarkar ta na nan yau ta Kar kwalliya,."Fash
ion"tasa ta fesa turare,.Mai zama mata tace"Kayan nan sun
amshe ki Zahra,. Tai murmushi tare da fadin ta gode,.
Saman ta haura, dan amsa kiran Sa'a,. Tana zuwa ta tarar
ta taci Ado itama da Less din nasu,.Color ne kawai ya
banban ta..Ganan sarkar ta irin ta ta a dambare a wuyan
ta,.Ga zobuna manya guda biyu,.Bangles na Awarwaro
manya kamar Gold,. Tasha Adon Gold, sai shining take,.Sai
ta gane kyaun les din a jikin Sa'an.. Tai murmushi, "Sis
kinyi kyau fa,. Itama tai murmushin,. Kan ta zaunar ta kan
kujera,. Ta kamo hannun Zahran,,. "(Guess what)?.Ta bude
ido da Neman Sani,."(what)??..Tai murmushi,. "Kawo
hannun ki,amma ki rufe ido,.Ta kada kai da murmushi,..
Sarkar Sa'an ta zaro a inda ta boye,,.Ta daura mata a
hannu tare da fadin,"Tan taran.., Ido Zahran ta bude,.Aikwa
Tana Ganin sarkar ta ta rukunkume Sa'an da
murna..Hafeez da Tunda ya shigo yai tsaye yana kallon su
a bakin kofar,.Murmushi yake,.Komai Sa'a tai burge shi
take,.Yaji dadin ganin su kwarai a haka.. Karaso wa yai
yana. " Kun dai manta dani a rayuwa Matan nan koh,.Suka
cika juna suna dariya,. Ko Break ba wacce ta kula nayi."Ai
angon karni baya yunwa,.bari (1)minutes,. Zahra rike ta
tai,."No yi zaman ki Maman twins na zubo mishi..Ta kada
kai tana kallon hafeez,. Yana Ganin ta fita ya ruko hannun
ta,."Ya Zahra tasan ke Maman twins ce?.Tai Murmushi,
kawai (Guessing )ne..kai ya kada "Kai kunyi kyau fa Allah,.
.
Tai murmushi tare da Ruko kumatun shi kamar Wani yaro"
Mun gode,.Sunan wa aka sa ne ni?? Yace"sistern naki naki
bata baki Bayani ba??..girgiza kai,. Dai dai shigo war Zahra
da faranti a hannun ta shake da papee chicken,.Zahra ta
taro ta tare da karbar Abincin,. "Wannan fa ya miki nauyi..
Tai Murmushi,. Hafeez yace"Baki sanar ta mai sunan Babyn
ba?..Tace "Da zumudin Dana zo kenan,so nake na fada a
gaban ka,Da fatan baka rigani ba?. Sa'a sai Kallon su
take.,amma su sai ja mata rai suke., Tace"Hajiya aka sa Ai
na Sani Tunda baza Ku fadan ba,. Sukai Murmushi,. Zahra
tace" Baki chan Ka ba,.Ta rike hannun ta,. "Sunan Babyn
mu, SA'ADATU Hafeez Takwarar Momyn ta..Sa'a ta waro
ido,."Ni Sa'an?. Ta nuno kanta,.Kai ta kada mata,.Basui
aune ba takwa kwala kara,tare da Doka tsalle,." Wayyo dadi
Barni da raina,. Da sauri Hafeez ya nuno ta,. "A'a,kinyi na
kudin ki Unique,.Kar ki mini illah.. Tace" Sorry..
Sorry,.Murna fal ranta ta rukun kumo shi,. Ta hado Zahran
ma duka tana kwarara musu Godiya..
Dariya suke tayi,farin ciki fal ran su,.Cika su tai ta ban kada
cushion din ta dakko kudi ta mika wa Zahra,."Ga nan ajiyar
ki,.Ta karba,tana kallon ta da rashin fahimta,.
.
Ganin Hafeez a wajen yasa tai mata gwari gwari,."Cikon
Sarkar Jummai,. Zakui waya dai,.Ta Ciro 5k,"wannan kuma
Tukwici ne,kan Babban yazo,.Zahra tama rasa mey zata ce
mata,.Ganan sarka ta amso mata,.Ashe harda Kudin Boka
sai da ta lale su wajen Jummai? Har ga Allah ta fidda rai da
samun su,dan tun daga ranar Jummai har yanzu bata kira
ta ba,.Tai murmushi, Lalle maganin shege,akace sai Dan
Iska,.Jummai ta gamu da gamon ta,. Kawai sai ta Rungumo
ta tana zuba godiya ba adadi,.A ranta tana rokon Allah Kar
ya kara kawo ranar da zata sabawa Sa'a, dan ta mata
Hallaccin da zata Iya kiran ta da YAR UWA CE kadai mai
mata ba kishiya ba,. Haka Suka tafiyar da sunan su gwanin
sha'awa, komai Sister, komai Sa'a,. Har aka watse lafiya..,
Tabbas Zahra tasan Sa'a ta daban ce,ba yadda za ai ta
hada kai da ita,.Don Bazata Iya ba,Hakan yasa ta dau
damarar janyo hakurin ta na Da,ta yarfa wa ranta,..Takan
gujewa duk wani cikas na zaman su da Sa'an, Duk da ta
fara mata karar abubuwa da dama,.Sai dai babu ta inda ta
rage wa Hafeez.. Tabbas kowanne bawa da irin baiwar da
Allah yake haifar sa,.Musamman mata,kowa da irin tata
salon Iya kissar,. Tanan kam,ko ita ta sarawa Sa'a,. A
hankali ta siye su da yan uwan su Cikin hikima da
Dabara,.Sai dai Abu d'aya ta Kudirta a ranta,,shine duk
yaran da zata Haifa mata,toh fa zata damkawa Sa'a su,dan
ta karantar su Darasi,Musamman na gidan Miji,.
.
LAIFIN DADI???..
Naufal,da Nailah ne ke ta kai kawo Cikin Sittern su a
parlourn,. Twins din Sa'a kenan,. Yaran gwanin
sha'awa,bulo bul dasu,.Watan su (6).Amma in ka gansu ka
dauka yan wata (8)ne,.Danna Button din sittern Naufal ke yi
yana wakar "Twinkle Twinkle Little star,.Yayin da Nailah ke
ta bangala mishi baki tana dariya tana bubbuga tata,.
.
Da sallama ya shigo,.Daga chan kitchen aka amsa
mishi,.Tuni ya karaso da sararrafa wajen yaran,wanda tun
sallamar shi Suka fara murna,." Ina Matan gidan aka bar
mun 2 little Angels na su kadai??..Ya cire Nailah "My little
Princess,. Papa's home,.Sama ya hulla ta ya chafe,.sai
dariya take bangala wa..Ya sauke ta ya dau Naufal,Shima
ya masa,.Fitowa sukai a kitchen din zahra inda suke hada
kwanikan lunch,. Da fara'ar su Suka fito,.Zahra dauke da
karamin Cikin ta data kara Nad'a,. Jikin shi Sa'an tai kamar
yadda ta saba,. Da sauri Zahra ta kau da kai,.Gudun zigin
shedan,.Irin haka yasa take mar Marin yin nesa dasu,dan
tasan zuciya batta kashi,kuma zo mu zauna,Tabbas
wataran zo mu saba ne,gwara kazantar da bata ga ba a
wajen ta tsafta ce,. Sai dai tana tunanin rayuwar gidan da
bata tare da su Naufal,Ga Naina ta saba dasu,. Tai
murmushi, dan tuna wa da Naina da aka kai yaye..Da tasan
ta na nan da Tuni tana makale dasu Naihan.. Ta kallo Sa'a,
Yadda ta maida hankali kan Mijin ta,. In Hafeez na gaban
ta, toh hatta yaran ta gefe suke.,bare ita,.Tai murmushi,.
Bazata kara da Sa'a ba,dan ko ta bangaren kula da Miji ta
daga mata tuta,Burin su Allah ya kara hade Kansu.
.
Alhamdulillah... Nan muka kawo karshen BARIKI
IYAWA...Muna rokon Allah kuskuren da mukai ya yafe
mana.

Saimunji ra'ayinku da bukatunku akan wasu littattan kudai kusance da mu