HAUSA NOBLE'S
11.GANGAR JIKINSA NA AURA P11 NA JAMILA UMAR
TANKO(JUT)
Haisam yayi musu rantsuwa da allah acikin su ukun nan
duk wanda ta fadi jarabawartasai yayi mata bulala kuma
daga ranar data fadi jarabawa babu ruwansa da ita ya
cireta a cikinkannansa gaban hanna ya fadi rasa dajin
bayaninyaya haisam tace a ranta tace idan yaya haisa
yacebabu ruwansa dani aina shiga uku tunda babu
maiyimun siyayyar makaranta karshenta ma
karshenkaratuna yazo. Ta kudiri aniyar daga yau babu ita
babu cikakken bacci zata dage da karatu don tacijarabawa
kada haisam yayi fushi da ita. a sati dayasu hannah suka
gama jarabawarsu,jarabawabibiyu suke a rana daya. Don
haka babu hutu badare ba rana kowacce ta dukufa da
karatu,musamman hannah sallah ce da cin abinci tashinta
daga kan littafin karatunta, haka kuma ta zanajarabawar
cikin sauki ma'ana da an bata questionpaper sai taga tasan
amsoshin gaba daya, hakatake amsasu cikin sauki saboda
tsaban ta gamakarance litattafanta, hannah tasan yaya
haisamzayyi murna da sakamakon jarabawarta tunda tayi
karatu yadda ya kamata. Hutu kuma sai juma.a donhaka
dukka wadannan ranakun babu abinda sukeyi sai wasanni
da raye raye da wasanninkwaikwayo na kungiyoyi (club)din
makarantarkasancewar akwai kungiyoyi daban daban
amakarantar kaar english club, hausa club, jet club.
Che,ical club, geography club. Yoroba da igbo dadai
sauransu, kuma kowacce daliba daga yar ajidaya zuwa
shida tana da damar da zata shigakowanne club a
makarantar. Su kuwa malamaicikin satin nan suka dukufa
da aikin makinjarabawar dalibai, don ganin kafin ranar hutu
sun bawa kowacce daliba sakamakon jarabawarta tatafi
dashi gida iyayenta su gani. Ranar alhamis anagobe hutu
haisam ya tara 'yan ajinsa a bakinbabban dakin taron dake
makaranatar wato halldon ya bawa kowacce sakamakon
jarabawarta(report card) 'yan ajin malam haisam suna da
dimbun yawa don dalibai saba'in da shida ne a ajinhausawa
da yarbawa,igbo,musulmai da kiristocisma da talatin ba
hausawa bane kuma ba kiristocibane, wata ko zo bata sani
ba da hausa, tundadaga kudu suke babu abunda suka sa a
gaba saikaratun littafinsu don shine abunda ya kawosu tun
daga uwa duniya zuwa nan arewa. Don haka babukoma
baya a ciki kowacce tayi iya kokarintamatuka a wannan
jarabawa. haisam ya kallifuskokinsu daya bayan daya
sannan ya kyalkyaleda dariya. Abun mamaki babu wacce ta
taya shidariya kamar yadda suke wasa da dariya a aji yau
kowacce fargaban jin sakamakonta takemasamman ma
hanna. Tunanin maganar da yayahaisam ya fada yayi musu
ranstuwa yace dukwacce ta fadi jarabawa sai yayi mata
bulala kumababu ruwansa da ita. Hakika bata fargabar
bulalarsosai tafi fargabar babu ruwansa da ita din daya
fada, idan haisam ya cire hannunsa akan hannahwaye
kuma ya tsaya mata a duniya yadda takekaunar makarantar
nan aiko hutu bata so ayi. Watohannah na daya daga cikin
yan kwaleji tafi gidadadi, ga uwa uba kwanciyar hankali
wasa dadariya da kawayenta sabanin a gidansu sai bauta.
Anan makaranta akan sasu aiki ko aike ammabamai wahala
ba kasancewarsu kanana 'yan ajidaya dole seniors zasu
aikesu. Haisam yace ''oh''yau babu dariya duk kunyi cirko
cirko kuna jiransakamako to da yawa daga cikinku kunyi
kokariamma wasu basu yi kokari ba don haka wadanda
basuyi kokari ba sai sun dage idan ba haka bakarshen
shekara za'ayi musu repeating kowa yawuce aji biyu a
barku a aji daya ku sake maimaitashekara,. Gaban hannah
ya sake fadi ras sai addu'atake sannan taji dan saukin
dukan da zuciyartatake yi mata. Haisam yace'' yanxu zan
fara kiran sunan wadanda suka yi na daya zuwa uku sai
atafa musu zan basu kuma kyaututtuka sannan nakirawo
na hudu zuwa goma zuma zasu fito a tafamusu sune suka
fi yin kokari sauran kuma sai kudage nan gaba ''hadiyar
yawu yake ji mukut mukutdakiban nayi don faduwar gaba
dariya ta sake kecewa malam haisam ya girgiza kai.