Breaking News

*** *BARIKI IYAWA PART 17* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 17* ***
.
Da murnar ta ta Dane Maman,lokacin Baba ya dawo,,Ta
dawo kan Baba,Sai dariya suke mata da Hafeez, Tuni
shagwaba ta dawo,,kan ta tashi ta dakko ma su Zahra ruwa
bayan sun gaisa,,. Basu Suka je gida ba sai 10,,a jabe
Zahra ta zube a parlourn,, Sa'a tai musu sai da safe,ta haye
sama,,banta yai da kallo,kan ya shiga dakin Zahran, itama
binshi tai,yai wanka,dan lokacin zafi ne duk ya takura,yana
fitowa itama ta shiga,, yai murmushi, Sa'a, Sa'an shi, da
itace toh da tare zasu shiga,,Saman yai,lokacin tana
parlourn, daga ita sai towel halamar daga wanka ta
fito,chargy take jona wa ganin NEPA,,yai murmushi, tana
ganin shi Ta sau mishi murmushi,, kamar jira yake ya
karasa,.ajiyar zuciya ya saukar,idon shi lumshe,, Sa'a itace
nutsuwar ruhin sa,,idan tana kusa yakan manta komai,sai
yai da gaske ko ta nusar shi yake Iya kaman ta adalci,,
yanzun ma ji tai kidan na Neman sauya wa,,da sauri ta mai
chakulkuli ya sau ta,, Ta Matsa baya,,"Good Night,. Kai ya
kada mata, sai ya bata tausayi,,Ta matso tare da riko
hannun shi, har wajen glass din ta rako shi,.Tamkar wani
marayu haka Suka rabu,.Ko kadan bata son shiga hakkin
Zahra. "Amma ya Hafeez kana sane da rashin adalcin da
kake mun ina hakuri koh??Ya kallo," Da nai mey kuma??
sarauniyar yan complain? Naga randa girkin ki zai tsaya,ba
tare da kin kawo Suka ba,Tuni ta kara kuluwa harda
hawaye,,"Ni in girkin ta ne a sharp sharp kai min sai da safe
ka fice,amma in nawa ne,toh fa in ka hau sama sai na
ganka,,.Ya girgiza kai., kan ya gyara pillow,, kwanciyar shi
yai,ta kara kuluwa kuwa,''Dama nasan ni Matar tushe
ce,kullum ni ke laifi,yar goal din taka bata yi,,Ya
juyo,,"Yanzu toh mey kike so ayi??Tai mishi banza tana ci
gaba da kukan ta,,.
.
"Na Sani,Allah ne ya dauran son ka,amma at least ka nunan
ko kan kani kana yi dani ma da dadi,,yai shiru, ," Zahra
problem, yaga ranar da zai zo dakin ta bata bashi sukar
Sa'a ba,,dole Sa'a tana birge shi,dan fin wata kenan,amma
bata taba kawo mishi sukar Zahra ko kara ba,asali ma sai
dai ta tunasar shi adalci a tsakani,,sannan yasan indai so
ne!toh Sa'a tafi Zahra son shi, don tana komai dan faran ta
mishi,matukar bai saba wa shari'a ba.. Ya sauke ajiyar
zuciya, jawo ta yai,,"Toh shikenan, yanzu ki bar
kukan,.Nima ina son mata na duka Sweet Zahra,. Tuni ta
fara murmushi,, a hankali da dan guntun salon ta ta tafiyar
dashi,Sai dai shi abinda ke daure mishi kai, duk tsiwar nan
ta Zahra a fagen nan kunya take,komai a kunya ce,ita ba'a
sabo da ita,duk da bata da makusa,,amma Sa'a ta daban
ce,,.Yau kam tashin farin ciki akai,tun asuba ta gaida shi,ita
a dole ta samo kan Hafeez,, tai break, tare da taimakon
shi,.Bayan sun gama yai sama kiran Sa'a, nan fa ta fara
cika tana batse wa,,ita kam mey zatai wa Hafeez ya dau
lokaci ba tare da ya tuna hawa saman Sa'a ba??,koda Suka
sakko tare da Sa'an yai mamakin sauya war Zahran, dan
ana wasa ya barta ya hau saman,ya girgiza kai, Zahra? Sai
a barta,,. Kamar kullum, yauma Sa'a ta gaida ta, a dakile ta
amsa,Kan ta hau hada ma Hafeez tea,,Yau da matukar farin
ciki ya tashi,,dan yau kam,yasan sai kwanan saman Sa'a,
tana kula dashi,,kujerar shi na facing ta Sa'an, yayin da
Zahran ta zauna gefen shi,,Cokali take juya wa a tea in data
hada,lokaci lokaci takan dan kalle shi,, kamar mai jin kunyar
shi kuma sai ta dukar da kai tana Murmushi, Sa'a mai
dubun salo,yau kuma da salon kunya ta motsa da rashin
son magana,,.Ta kai Cup bakin ta taji yana mata tafiyar
tsutsa a K'afa,,ta kalle shi tai Murmushi tare da dukar da
kai,,Kafar shi ya matsar gefe,da zummar in ta kawo tata ta
rasa,dan yasan zata rama,,Ai kwa kamar ya Sani,,Kurbar
tea Zahra take,,taji wani salo ana mata a kafar data mike
ta,Tuni ta kware lokacin da ta gane mai mata,Dan taga
lokacin da ta kanne mishi ido,,a zabure ta mike cike da
masifa,"Nifa ban son karuwan ci!ehee,in banda jaraba ki
bari yau Ai zai dawo gare ki,sai ki cinye shi danye ma.Da
sauri Sa'a ta gintse dariyar ta, "Kai sis.,ban fa kula ba,,ta
wani marai rai ce mata harda langwabe kai gefe,,",mtsww..
Taja dogon tsaki" kyaji dashi dai,,.Ta ture kujerar ta basu
waje..Tana shiga daki Suka fasa dariya...Da sauri ya taso
ya dawo kan plate din ta,,Sai da sukai mai Isar su tukun
Tace "Amma fa baka kyauta ba,,Yanzu da ta rufe ni da
duka fa???Ya kara tuntsura dariya," Allah bansan ta kawo
kafar ta ba...Ta dan harare shi, "wataran ina ga sai kasa
Zahra tamin lilis a gidan nan,I swear na tsorata,.kuma kai
kaja, da akan ka zan rama.. Yai Murmushi tare da ruko
hannun ta,," Ada!.Ta zuba mishi ido..ido cikin ido suke
kallon juna,sai dai takan dan lumshe nata,sun kai a kala
5mints,kan daga bisani ta kalle shi, kamar hadin baki su
furta wa juna "I Love you,,..Suka sake kallon juna,Sai kuma
abin ya basu dariya.,Ta kan kamo shi," Love you too
sweetheart... Ya sauke ajiyar zuciya,,. Zahra da ta fito ta
sake komawa, gado ta fada,ta fara rera kuka,,"Mai Sa'a ta
fita ne a rayuwa??.. Kyau??Tasan bazata gwada mata shi
ba,,..diri fa?? Sai dai ta fita kauri da cikar muzauna,,Gashi
tana da dai dai gwargwado,, tana kitso duk bayan
sati,sabanin Sa'a, da sai dai tai wash and set,,.tana kokari
sosai ganin itama tana kwalliya,,.Ance mata yan BARIKI
akwai su da gyara kodan su kwace maka Miji,Toh tasan a
bayan auran su kadai kudin data kashe dan ta gyara kanta
ba kadan bane,kuma ko yau Jummai tazo da sabon da zata
kawo mata,,Amma Sa'a fa,tun zuwan su in banda Ummi da
tai zuwa 2,toh bata taba ganin wata Qawa tazo mata
ba,,..Toh meye sirrin da Sa'a take da wanda ita batta
dashi???Tai tunanin har ta kare bata Gano da mey ta Gaza
ba..Zahra kenan...Duba da kyau dai,am sure akwai su...
Bude loca taji,ta juya,Hafeez ne tsaye,tashi tai tare da goge
idon ta,, amma a ranta tana wallahi Sa'a zata biya bashin
nan na yau..
.
Zama yai rarrashi, murmushi kawai take mai,wanda na
mugun ta ne,,abin yi zuciya ta raya mata,,Kallon ta yake
shikam da mamaki,dan yasan da a da ne,da Tuni Zahra ta
fara complain, amma yau Murmushi take mai,,Shima sai yai
murmushi, "Zan tafi office, 9 tayi,Ta kada mishi kai,," A
dawo lafiya,,.Shima ya kada kai, Ya tashi,.ganin batta niyar
tashi yasa ya girgiza kai,, Allah sarki Sa'an shi, da yanzu
itace tana manne dashi da yar shagwabar na Kar ya
jima,,sannan ya kula mata da kanshi kamar tana gani,,..Yai
Murmushi har hakwaran shi Suka fito,kan yai waje.. Yana
mai daukin dare yayi yakai ga Unique din shi.. Washegari
Bayan ta sallame shi ta koma sama dan ramakon baccin
ta..Zahra najin shiru,ta shiga kitchen ta hada miyar
Tankwar ta,attarugu zallah,tana yi tana dariyar mugun
ta,tana gamawa ta zauna a parlour tare da daura K'afa
d'aya kan d'aya, jira take Sa'a kawai ta sakko da abinci,,ita
kuma ta sau mata Bom din ta ciki,.Da mamakin ta har 12
bata ji motsin Sa'an ba,.Tashi tai ta hau saman da zummar
tada ta.. Mafarki take Wai Hafeez na sabe da ita a baya
suna kewaye parlour suna dariya,.
.
Murmushin take dirka wa a baiyyane,taji ana buga mata
glass,,. A firgice ta tashi tare da kallon agogo,,
"Subhanallah,,past 12??..Da sauri tai kofar,,Zahra ce,da
mamakin ta tana Murmushi,," Sis,naji shiru ne,shine nace ko
bacci ya dauke ki hala,,tai Murmushi,. "Wallahi
kuwa,nagode kwarai sis..Ta juya kasa tana murmushi,,
Sa'an ta bita da kallo,,kawai sai taji bata yadda da
murmushin nan na Zahra ba,dan tsawan zaman su sai dai
tai wa mijin ta, ita kwa sai dai ta bita da harara,,ta dai kada
kai,ta shiga kitchen a gurguje, Allah ya sota ta dafa
markade,. Tasan Gogan ta bai fiya son k'yali a abinci
ba,shidai basshi a shinkafa, saboda haka cikin gaggawa ta
daura,ta hau soya miya,duk ta manta da wayan ta dake a
kashe da zata kwanta,.Yi take tana kallon agogo,,1pm yake
dawo wa gida,ga indai ya kwaso yunwa,toh fa tanan ake
fada dashi,dan shi Sam baya jimirin yunwa da yaji a
abinci,yanzu za'a ji kanku dashi,dake ita tasan abinta Shi
yasa take karewa,, a kalla in tai latti bata gama abincin rana
ba takai 1,Shima kan Ya koma bakin aiki ne,. 1 da 20 ta
sakko ta ajiye flasks dinta,har Zahra na mata sannu,,.
Komawa tai ta fara yanka cabbage da zata hada cous
low,da mamakin ta shiru Hafeez bai zo ba,har 2 na Neman
yi,,kan ta gurza karas tai wajen wayan ta, kai ta dafe,kan tai
saurin kunna wayan,.Tamkar wanda ake jira sai ga kira ya
shigo,tai kitchen tana receiving,,. "Am sorry,aiki ya
kachamen,kasan kana raina,,.Yai ajiyar zuciya," na aza kin
manta ni ne?? Tai murmushi, "Da kuwa na manta kaina ma
Baby,,.u know u r special.. Yai Murmushi n jin dadi,,kan ya
fara sanar ta Ya kai sako ne,sai Fodio ya kira shi,amma
Gashi nan,dan duk yunwa ta rarake mishi ciki.. Bayan sunyi
sallama da gaggawa ta tattare komai,tabar cous lown takai
daga baya,,Wanka ta shiga,dan sai zufa take tai komai cikin
sauri.
.
Zahra na ganin hawar ta tai saurin shiga kitchen,, leke
take,tamkar wata muna fuka, ta juye kusan Rabin Miyar
Tankwar a miyar Sa'a, ta juya,Tuni ta hade kamar ba'a
zuba ba,da gudu ta koma kitchen har tana tun tube,, Ta
dawo Taji kamshin miyar data bude ta cika parlourn, da
sauri ta dakko freshener ta hau fesa wa,.Kallon Dining din
take tana wata shu'umar dariya,,ta kalli agogo,2:09,tasan
duk inda Hafeez yake iyanzun yunwa ta ciwo shi,. Ta tuna
randa ya fara fita office datai lattin abinci ya yai
mata,tamkar ya rufe ta da duka,dan Hajiya tasha fada mata
Hafeez baya jimirin yunwa,,akwai lokacin da yaji ya zarce
mata a miya,da bai ci abincin nan ba,kwana 2 yai basu dai
dai ta ba...Tai murmushin mugun ta..." Sa'adatu Yau sai
Buzun ki a gidan nan,,. Zan ga karyar BARIKIN yau.,Kai Kila
ma ya kifa mata mari yadda yai lattin nan,tadan doka
tsallen murna,,Daki ta koma,tai alwala Ta hau make up..sai
kuma jiran zuwan Hafeez.
.
Da Sallama ya shigo,duk din su suna parlour, Kallo suke,sai
dai duk hankalin su ba'a Kallon yake ba,kowacce da abun
da ke ranta,,duk da kowacce murmushi ke kwance a fuskar
ta,,. Ba karamin dadin ganin su yai a haka ba,,da dan gudu
gudu Sa'a ta taro shi,,.Zahra ma ta tashi,.da yar dariyar da
take kunshe wa,"Sannu da zuwa,,Ya daga mata kai,"yauwa,
ya gida,.tai daki,dariya take dillikawa,nan da yan mintina
zata ji kan su,,. Ba'ai 10mints ba Suka sakko,,Manne take a
kafadar shi, tana jin su ta fito,sabanin D'a da sai a an kira
ta tana yanga,,. Kujerar Sa'a ta ja mishi,ganin yau suna
dasawa da Zahran yasa ta barshi yaci da kanshi,,Tai
serving kowa ta tura ma Zahra,,ta bashi nashi tana
Murmushi, ja yai,zai fara aka kira wayan shi,Zahra ta danne
cokali,, da jin haushin wanda yai kiran,,. Sa'an ta zuba
mishi ido,, a fada fada yake wayan,ta kuma San yunwa ne,,
sai da taga ya ajiye wayan Kan ta dau cokali d'aya bakin
ta..
.
Da sauri ta rintse ido, dan jin wani azababben yaji da ya
ziyar ci kwakwalwar ta..da sauri ta bude ido, dan tunawa
da yanxu Hafeez zai kai tashi lomar shi,ta kuma San halin
shi akan "Y'aji," baya son Y'aji a abin,,,.Sai dai ina ta
makaro,dan har Ya kaita,Furzar da abincin yai,yama rasa
ina zai sa bakin shi yaji dadi,.. batai wata wata ba tai wajen
shi tare da saurin tallafar kanshi ta hau kan dining table din
ta zauna,,shishitu ya fara,idon nan Tuni har sun kada dan
azabar attarugu,,in banda kunshe dariya babu abinda Zahra
take,,yau daya,tasan sai buzun Sa'a,, dan tasan sarai bai
son Y'aji,sannan gwani ne wajen Iya masifa akan yunwa
inta ciwo shi,sai dai da mamakin ta, sai ganin Sa'a tai itama
tana shshitu cikin marai rai ce fuska,,fadi take"Am so sorry
Baby tana hura mishi bakin halamar yajin ya huce,,.Zumbur
Zahra ta mike,sakamakon ganin Sa'a ta hada bakin Hafeez
da nata,,Saida ta tabbatar ta kauda duk wani yaji kan ta
dago,shikwa gogan abin nema ya samu,tuni ya manta da
wani yaji yahau mata murmushi,, abincin ta jawo,sai ta dan
matsar da miyar,ta kara cous lown,da plantain din ta cigaba
da bashi,,duk loma daya saita manna mishi kiss,,Ina,Zahra
har ta fara zufa dan ganin Ajab,, bashi take yana
murmushi,, ita kwa sai aikin ta take,,cokalin hannun ta ta
buga akan flate din nata,,da gudu tai daki tana kunshe
kuka,,duk Sa'a na kula da ita,,.
.
Sassayan ajiyar zuciya ta sauke,ganin ta tsallake rijiya da
baya da kyar..Sauka tai zata tafi ya ruko hannun ta yana
langwabe kai gefe,sai kace irin qananan yaran nan"Ban
koshi ba?,,Tai ajiyar zuciya kan ta kakalo murmushi,,shikwa
yadda take mishi ne bai son ta daina,,.Saida ta tabbatar ya
koshi,kan ta sauka ta je fridge tana mai gode wa Allah,,
tabbas tasan wannan aikin Zahra ne,,amma tasan ko giyar
wake tasha gaba bazata kara mata haka ba..Ta dakko
mishi fresh milk,Allah ya sota akwai,Ta tsiyaya mishi dan
shashe baki,,.a ranta tunani take,wani irin attarugu Zahra ta
afka mata a miya haka??..Oho,wato wannan ne dalilin
Murmushin ta na tun dazun? Ta girgiza kai, "wannan Ai
dabarar yan Da ce in banda Zahra,,tai Murmushi kan ta
koma tana tsiyaya mishi,,.. Kuka take,tana da ma bata
aikata hakan ba, dan Gashi a karshe ita ce da kuka,ranar
dan bakin ciki bata fito ba sai taran dare,.
.
Washegari ta fito zata kitchen ta tarar da Sa'a ta daura
K'afa d'aya kan d'aya a kan kujerar ta,, murmushi
take,wanda yasa Zahran saurin kawar da kai,,ta tako a
hankali tana rausaya, "Sis ina kwana?. Da sauri ta dago
kai,dan batai tunanin haka zata barta ba,. Murmushin dole
ta kwakulo,,tare da amsawa,,.tace" Tun jiya shiru,hope dai
lafiya naga baki fito ba??. Ta dan harare ta, "Lafiya,,.ta
kada kai" Ok,.Ga nan abincin ki,,.ta juya tai sama tana mata
sai ta sakko anjima.. Da kallo ta bita,da mamakin maganar
da bata mata ba ta jiya,,. "Baby,ya juyo yana kallon ta,,. Ta
tashi tare da kwanto wa cinyar shi,,.ta dan shafo fuskar
shi,," Ya roko na please, gobe date line da suka bani
please,,. Tuni ya sanja fuska,,tare da matsar da system din
gaban shi,,. "Na zata na gama da nan wannan shafin
Unique??.. Bana sha'awar mata ta da aiki,bare na gidan
TV,,. Da marai rai ta ta dukar da kai da dan murmushin
Neman kuka,,. Allah yaga Babban burin ta ne ta ganta tana
News,amma Gashi mutumin nan yana son kwafsa mata,,.
Bata San guntun hawaye ya zubo a,,sai ji tai ya bar sababin
ya janyo ta,,." Am sorry,,.Ta dukar da kai kasa,,."Zan kare
komai Dear,,wallahi buri na ne hakan,please,. Ya furzar da
iska,,a times Sa'a tana sashi abinda bai niya ba,,.Yai ajiyar
zuciya, "Da sharadi, Cikin zumudi ta mike dan jin sharadin,,.
Yace " Na farko,babu zuwa da gyale,,na biyu,Babu magana
da kowanne abokin aiki sai dole,,. Na karshe,aikin ki bazai
shafi kula dani ba,,. Ta rukun kumo shi,"Duk na yarda Allah,,
wannan Ai masu sauki ne,,. Washegari girkin Zahra, Yau da
zumudi Sa'an ta tashi,,ta Riga kowa,kan kwa 7:30 ta
shirya,. Jira take su gaisa da ogan kawai ta wuce,..Zahra ta
kallo ta da mamaki,"Wai da gaske aiki zaki fara?. Ta daga
mata kai"ya fice Wai,.Ta kada kai, "Yayi,.Tai kitchen,,. Lalle
Hafeez bai ya adalci a lamarin shi,. Toh wallahi ko sama da
kasa zasu hade sai ya nemo mata itama aiki.. A wajen aiki
ana ta nuna mata tsarin wajen,,Murna fal ranta, yau gata a
office,,. Bilkisu ta zo wajen ta,. " Suna na Bilkisu, kefa??.
Sa'a tai Murmushi, "Sa'adatu,,. Da fara'ar ta tai mata barka
da zuwa office din su,,. Tana tashi gida ta wuce,dan yau
chan zata wuni,. Tana tuki ta dau waya," Ranka ya
dade,,Yanzun kake raina sai ga kiran ka,,. Yai Murmushi,
"Ya aikin toh? Naga first NeWS naki,very interesting, sai dai
fa da matsala.. Tai karamin dariya," Nasan matsalar, sai an
daure,,.Suna ta tadi har ta isa gida,. Yau auren su wata (6)
kenan, Matsalar da ta fara fuskan ta bai wuce samun cikin
Zahra ba, Gar da gar zata na Goran ta mata haihuwa.. Ko
in sun zauna ta tsiri ko dai Sa'a tana planning ne??.. Tun
abin baya tasiri a wajen Hafeez ya fara,sai ya fara zargin ko
dan aiki Sa'a take planning,,. Duk randa Zahra tace haka
takan yi Murmushi,. Dan tasan da gaiyya take fada mata
haka a gaban Hafeez kullum,. Yau suna kwance ya riko
hannun ta,,. "Unique,, ta kallo shi tare da shafo fuskar shi,,."
Please in da gaske kina planing ki taimake ni ki daina,,ina
matukar son yara,musamman su fito ta tsatson ki,,Aiki
baya hana haihuwa please,.. Da mamaki take kallon shi,dan
ko kadan batai tunanin maganar Zahra zatai tasiri a ranshi
ba,,.Kallon shi take ta ma kasa cewa komai, shi kuma sai ya
zata bata yarda bane,,. Dan haushi ma ta kasa mai
maganar,. Tashi yai yana mai gaskata zancen shi, lalle Sa'a
planning take tunda bata Musa ba,indai kuwa hakane dole
ya sa mata ido,. Tun ranar Sa'a ta kasa sukuni,yau ta kudiri
niyar ganin likita in ta tashi a aiki,,.File yasa ta bude tare da
bata appointment ran Friday,,.
.
Allah Allah take Friday tai ta gano meye matsalar ta. Dr ya
kalle ta bayan an kawo result din ta,sannan ya fidda result
na scan,."Madam (you are absolutely fine,,. The uterus is
normal in size,,.But abinda ban gane ba shine,cervix naki
naga halamun rufe wa,Sannan akwai kince dan ruwa na
linking kadan,,so bazan tantance yanzu ba since kin ce this
month kinyi period, right??. Ta daga mishi kai,,. Ya kada
kai,"OK, yanzu let see,PMC nakin yazo ending, if ba wani
Sign then sai muyi tackling next month,,. Don't
worry,everything will be fine,,.Kin ma yi dabara da kika zo
da wuri,. Tai Murmushi,. Ya bata result da magun guna ko
da da infection ya baje,,. A gajiye taje gida,dan ma Ta sanar
shi zata biya anguwa,,Yana zaune a parlour shida
Zahra,,cikin ta har ya tasa,fi'ili ake mishi kala kala,.Sa'a tai
murmushi,, "Sannun Ku da hutawa,.Yai Murmushi,," Yauwa
Unique,, kin dawo??. Ta daga kai tana Murmushi,,. Kallon
Zahra take yadda tai d'ai d'ai a cinyar shi da duk Rabin jikin
ta,,. Wani malolon kishi ya tokare mata makoshi,,. Ciki tai
tana musu bari ta huta,.. Ta fara fuskan tar chanji a Hafeez
kwarai tana kula,da a da ne da yanzu ya biyo bayan ta,.
.
Ta cire kayan ta tare da Ciro maganin ta sa a side bed,.Ta
fito a wanka sai Gashi,,. Kallon ta yake,Fatar nan a mur
mure,, sai shining take,,ta dan kara kiba kadan,,.Ya riko cikin
ta tabaya,,. Kallon su yake a mudubi tare da ajiyar zuciya,,.
Shi indai bai dangana da jikin Unique din shi ba bai samun
nutsuwa, Gashi Zahra ta dakko mishi wani sanabe,Wai
kamshin jikin shi take so,,Haka zai na bata lokaci agun
ta,yasan kwarai Unique din shi mai hakuri ce,,dan bata taba
complain ba a kan hakan,,duk da Gashi yau girkin ta ne,.
"Missed you Janeeman,. Tai Murmushi tare da juyo wa,,.Ta
shafo fuskar shi" Missed you too Pyaree,,.Yai Murmushi
tare da riko kugun ta,, Na matso naga kin fara min rakin
masu ciki kema,,kokarin kunce mata towel yake,amma sai
ta rike Kam,,Ta fara gazawa da mitar Hafeez,, Ai ba sai ita
zata Haifa mishi yara ba,ganan Zahra ta wadatar,,Kallon ta
yake ganin yadda ta sauya,, ya fuskanci a yan kwanakin
nan in yai mata irin maganar nan sai ta sauya fuska,,it
means bata son zancen haihuwa ko mey??.Cika ta yai ya
zauna kan gado,ba tare da ta tanka shi ba ta fara Shafa
mai,, shedan ya fara hura mata zuciya,,sanar ta yake
Hafeez fa gori yake miki a fakaice,,. Tuni ta kara cika da
masifa,.kiris take jira ya kara tofa wa,,ganin tana Neman
fita hanyar da ba ta ta yasa ta fara karanto adu'ar Neman
tsari daga shedan,,.
.
Ta rintse ido, a hankali taji nutsuwar ta na dawo wa,.Da
yanzu ta tafka kuskure babba, wato masifa wa
Miji..,Drawern ta ta bude tana son daukar kaya taji ya kara
rukun kumo ta,,. "Fushi kikai Ada??.Da sauri ta kada mishi
kai da murmushi, Ya juyo da ita,Kallon shi take cikin
ido,Shima haka,,." Ina son yara ne musamman daga gare ki,
ba laifi bane dan na fada,,Tai murmushi, tare da sadda kai
kasa,ta Sani bai fita son yara ba a yanzun,kodan ta tsallake
gurin Zahra, sannan ta wanke kanta daga zargin tana
planning,,. Dago habarta yai,tare da manna mata salon shi
dake mantar ta bacin rai,,.Tuni suka Lula Duniyar su tasu
kadai. Yau ta tashi da murnar haihuwar Fadeela, Direct
chan ta nufa,,an sake mata gida kamar yadda Hajiya Rabi
ta nema,duk tayi laushi tunda taga yadda Alhaji ke rawar kai
da Fadeela,,. Ita kwa har a labour sai da ta Roka mata Allah
ya bata itama..