HAUSA NOBLE'S
5.GANGAR JIKINSA NA AURA P5 NA JAMILA UMAR TANKO
(JUT).Hanne ta hau kan akwatinta ta zauna
Malam Habu ya ce "To fawannanshine ko in
kula, yanzu kuma ina zamu dosa kokuma
wazamu tambaya? Ni wallahi abun nan na
makarantarbokon nan ya ishe ni daga nan sai
can ana tsattsare ka datambayakamar a lahira
mun gama da masu gadi yanzukuma Allah
nekadai Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah
Yakyauta, wannan shine ake cewa ba shiga
ba fita wai anbawamahaukaci gadin kofa.
Shigowar wata dalleliyarmota ce Jeeplaunin
koriya (dark green) wacce ta tunkaro
indasuke, ita ta katsewa Malam Habu surutun
da yake yi. Ta zo dafda su tatsaya babu
abinda yake tashi a cikinta sai sautinkida
dasanyin A.C maza ne samari guda biyu suka
fitodaga gani wa ne da kaninsa, kanin yana
sanye da kayan bautarkasa ajikinsa wato
(N.Y.S.C) Yayan kuwa wata tsadaddiyarshadda
cefara sol a jikinsa sai kamshin wani
tsadadden turarene yake tashi. Abunka da
kauyawa sai kallo suke dukkauba da
*yar,kanin ya bude but din baya ya dauko
wata Jakarkaya, yamayar ya rufe ya ce da
wansa "Yaya Habib, na godesai dai nace
maka Allah Ya kiyaye hanya. Yaya Habib
yayimurmushiya ce "To madalla. Allah Ya bada
sa'a sai yaushekuma zaka zomana weekend?
Ina fatan dai wannan karan zakayi kamar
wata baka zo ba ko?Su duka biyun suka
tuntsire da dariya, kanin yace "Ai Yayaranar
juma'ar nan zaka ganni a gida ko
ba'azodaukana ba mazanzo Kano, haba ai sai
jini na ya hau zama a kauyein ba dole ba wa
zai iya? Yayan yana dariya ya mikawakanin
hannusuka gaisa ya ce "To Allah Ya taimaka,
ina ganinranar juma'arda zaka zo may be
baza mu hadu ba saboda dasassafe zan tashi
zuwa america kai kuma nasan sai da
yammazaka tahosai an tashi *yan makaranta
ko? Kanin ya ce "Ehkuwa bazamu hadu ba
Allah Ya kiyaye hanya Ya dawomana da kai
lafiya, Yaya akwatinan auren da nawa da
naka yazamo iridaya. Yaya Habib ya ce "Insha
Allahu, Yaya Habibya shigamota har zai ja
kofar motar ya rufe sai ya juyo yakalli Hanne
da Babanta ya ce "Salamu alaikum" Malam
Habu yaamsagami da daga hannu, Yaya Habib
yaja motarsa yajuya ya nufikofar fita kanin na
tsaye yana daga masa hannu.ayan da motar
Yaya Habib ta kure, idanuwansuduka na
kantasannan hankalin kowa ya dawo jikinsa.
TunaninHanne yakoma ga kallon kyakkyawan
ginin makarantarginin bulo da bulo,yaune
rana ta farko da take tunanin take saran
zatakwanta a dakin ginin bulo ba gidan kasa
ba rufinazara. Ta cea ranta "Cafdijan yau
kuwa zan iya bacci? Anyabazan ringa jin
sanyi ba a wannan dogayen gininnikan. Bata
sansanda tayimurmushi ba har hakoranta
suka fito, sai tawayence ta kifakanta akan
cinyarta kada Babanta ya ganemurmushin
dadi take. Kyakkyawan saurayin nan ya
tunkaro indasuke yanarataye da jakarsa a
kafadarsa, ya yiwa Malam Habusallamagami
da dan dukawa kadan, kana ya wuce su
yajegindin wata bishiyar dake kusa da tasu
ya daga wani benci yazauna yaajiye jakar
kayansa a kusa dashi yaci gaba dakallon
Hanne daMahaifinta. Can Malam Habu yaje ya
same shi a indayake zaune ya ce "Dan Allah
*yan samari kai maka'aikacine ananko kaima
bako ne? Yayi murmushi ya ce "Yaya akayi
Baba?Malam Habu ya ce "Yarinya na kawo
makaranta tundazu banga kowa ba balle in
tambayeshi hannun wa yakamata indankata?
Saurayin nan ya gyara zama gami da cirehular
dakekansa ya ce "Daliba, daliba ce wannan?
Malam Habuya ce "Eh nan aka ce na kawota
kuma gama takardar canbari ta mikogama
korarmu akayi dazu da babu takardar,
yakwalla kira yace "Hanne kawo takardar nan
ta dazu.