*** *BARIKI IYAWA PART 13* ***
*** *BARIKI IYAWA PART 13* ***
.
Ta dan kalli Zahra a takaice,sanye take da Baki da Arsh na
net itama,tai mata kyau,kamanin ta na fulanin usul ya
fito,kai inba kallon tsoro ta mata ba sai tace suna yanayin
kama da Hafeez, Ta sau mata murmushi cikin kissar ta,,A
Yatsine ta jutar da kai,dan bazata juri ganin Sa'an ba,,.Kai
ita sai yanxu ma take da na sanin zuwan ta Dinner... A
Bangaren Sa'a, tun daga kallon da Zahra tai mata tasan
zasu dama.. Wannan shine karo na farko da taga
Zahra,,dan koda sukaje gidan su kin fitowa tai su gaisa,,.
Har aka tashi Dinner Zahra bata cikin walwala,har Aunty
maryam yayar Hafeez ta fara mata nuni da hannu kan ta
saki fuska,sai dai ina,ji take kamar ta sau ihu,dan tadin su
suke tamkar rada rada,,ga wani munafikin murmushi da
suke sakar wa juna,,koya juyo kan tasa baki sai dai ta tabe
baki,, Tuni ta kara jin haushin Sa'an a ranta..
.
Yai yin Duniya dakyar ta shiga mota Wai shi zai kaisu da
Sa'a, ganin Sa'an ta hakimce a gaba,yasa ta ja Tasleem
suka shiga baya tana turo baki,,Zahra ya fara sauke
wa,wanda dama Allah Allah take ya sauke ta,,Sa'a ta dago
mata hannu halamar bye bye,,"Sister good nyt,,Tai mata
banza tare da doko kofar,,Duk yana kula dasu,,Sai dai ganin
Sa'an ta cigaba da fara'ar ta yasa bai ce komai ba,,
Tasleem ta kallo su,,"Kai Matar yaya kin ganki kuwa??Ta
kallo Hafeez ya kashe mata ido 1,,da sauri ta dauke ta
dawo da kallon ta Tasleem,,Tace "Na kai Yayan ki
kuwa??..Tai dariya,," Kai Aunty na kin fishi,,Wallahi u look
so Gorgeous..Kunyi keda aunty Zahra...kai Bros kai
samuwa,..Suka kyalkyale mata da dariya,,.Sai santin Sa'a
suke ita da Yayan nata,har abun ya fara bawa Sa'an
mamaki,ganin basuyi wa Zahra haka ba,kuma Bilhakki tai
kyau itama.,Kai badan Tasleem ba,yau da sai 12 zai
tafi,dan bai Gaji da kallon sahibar ba.. Suna tafiya ta
makawa Aminu kira,yana dauka ya hau mata tsiyan
nashi,,chan tace" Abu daya zaka min Aminu, yace "ina jin ki
amaryar mu,,tai murmushi, kan tace,,"so nake kai duk
yadda zakai na rigata zuwa gidan Hafeez.. In kamin
wannan kamin komai a rayuwa.. Yai murmushi.,Dan tuna
wa da Hafeez da yai,Shima dazun ya gama mai mitar su
fara dakko Sa'an shi, dan ita yake so ta zama uwar gida..Da
karfe ya furta "Done.., Kaga uwar gida sarautar mata..ta
kada idanu tace" Dadina da kai Aminu akwai saurin gane
karatu..suka kyalkyala dariya..Ummi ta karba. Washegari
da misalin 10am aka daura auren Zahra da Hafeez,kan
suka rankayo Gidan su Sa'a,, Murna a cikin Hafeez sai an
tona,,Wai yau shine mallakin mata 2?musamman Sa'an
shi??,,.Wayyo dadi,banda godiya wa Allah babu abunda ya
ke. Da yamma kwa Aminu ya cika alkawari, sai da suka jera
motocin daukar amarya kan suka cewa su aunty Maryam
Wai suzo su kai su za'a karbo amanar Sa'a, duk da Hajiyan
taso ranfo su,dan a dole ita fa Zahra za'a fara kaiwa,yadda
aka fara daura auren ta.
.
Kwarai su Aunty Maryam sunji dadin karramawar da dangin
Sa'a suka musu,,kayan gara nasu turum haka aka yi musu
tsaraba,zo kaga kukan tausayi wajen zahra da mama da
Baba,kai ko tafiyar Fadeela basuyi haka ba,,musamman
Baba,,haka ya kankame Sa'an shi suna kuka yana mata
fadan ta zauna da abokiyar zaman ta da mijin ta
lafiya,,Aunty Maryam sai murmushi take musu,Gaskiya
familyn Sa'a ita kam sun mata,dan ta fuskan ta akwai
Tarbiya...Da kyar Aunty Maryam din ta banbare Sa'a ita da
Fadeela,, suka kai amarya Gidan ta,, Dan gin su Zahra basu
kara barke wa da lamarin ba Saida suka ga Wai anyi sama
da amarya,,wato sama ya bata ya ajiye tasu a kasa,,Dan su
basu zo Jere ba,dangin Baban su ne,suma maza
kawai,,Aunty Maryam ce kadai bata tabe baki cikin su,kowa
da abinda yake tofa wa,,basu gama mamaki ba sai da suka
dira bangaren Sa'an,, a haka suna musu kallon talakawa zo
kaga uwar dukiyar da aka narka mata,,dan mai gidan Baba
ne ya dau nauyin Gado,wani dan uban su Chinese bed milky
brown,,komai na bedroom din milk n brown,tsarin ra'ayin
Hafeez kenan,,yana son daki haka ko Blue.. Parlourn ta
kwa an zuba wasu uban su kujeru ledar, green ne da ratsin
dan milky kadan,sai grass carpet Shima green da
milk,center table da wani dan tray an sa mishi Apple na
roba masu kyau greens,sai Set na kayan kallon ta na
plasma screen TV katuwa,flowers ne masu design din Royal
tree,,sun kawata parloun sosai,,ya sanar ta bai son tarkace
a parlour,shi yasa ta sanar da yan Jere fridge a kai mata
kitchen,, show glass asa ta a daki,,.. Su Kansu dangin Zahra
baki suka saka dan ganin komai yaji cikin tsari da wayewa..
Sai dare aka kawo Zahra,,abinda ya kara burge Sa'a ta
kuma kara tabbatar da Lalle ita ne uwar gida shine, ana
zuwa Saida aka hauro da Zahra saman ta,aka musu fada su
zauna lafiya,tunda itace Babba,,Tuni Zahra ta kulaci su
Aunty Maryam,,ya zasu ce Wai itace Babba, bayan ita aka
fara daura aure da ita?? .
.
Kowa ya watse sai tsiraran Qawayen amare da Tasleem
data makale a dakin Sa'a, dan tun Ran sakun Lalle take
hararar ta, Wai dan taje Sa'a tasa an mata Lalle..Fanfo
kawai Qawayen Zahra suke mata,Wai sai ta tashi tsaye,dan
kishiyar nan tata Lalle da gani kam yar BARIKIN Asali ce.
Ango yazo bayan yan rakiya sun rako shi,suka wuce da
Qawayen Amarya,Ya kira Zahra sama,Da kamar baza ta zo
ba,sai dai ganin yana jiran ta,, Komai na Kayanta Ja take
da muradi,,Sunyi kyau sosai,dan auren Gata aka
mata,musamman da take yar fari,,Sai dai duk da ken nata
tana zuwa saman na Sa'a ta sau baki,,amma Lalle an mata
ba zata,,Saima taga kamar sunfi nata haskuwa,,Ya kalle ta,,
"ki zauna bari na kira Sa'adan,,ta tabe baki kan ta
zauna.,yai ciki yana ta zumudin arbawa da sahibar shi,,
Akan sallaya ya tarar ta, ta daga hannu sama tana mai
kwararo mishi godiya daya nuna mata itama ranar ta,tana
mai fatan Allah kawo na yan baya. Murmushi yake yana
mai kara yaba halin Sa'a, tabbas yasan yai dace,Sa'an shi
da ya kira da "Unique,,Ta juyo tana mai murmushin kunya
tare da dukar da kai,,ya kare wa dakin kallo,komai yayi
kamar an tambaye shi,,takowa yai tare da tsuguna waa
gaba ta..Hannun ta ya kamo ganin taki tashi,Karo na farko
da ya fara gigin taba hannun ta,,Wani irin abu yaji yana
tsirga mishi,,yayin da ita ma taji makaman cin haka...ya
sauke ajiyar zuciya,a hankali ya tada ta tsaye "Muje parlour
ina son magana daku,,Ta kada kai. Bayan ya bude taro da
adu'a ya fara musu bayanin abinda yasa ya Tara su,sannan
da fadan kowa ta zauna da kowa cikin Aminci.. Ya kallo
Zahra.." Sa'a uwar gidan ki ce,so duk wani girma natane a
gidan nan,,kiyi respecting nata..ya juyo gun Sa'a,, "Amm
Unique, ta kallo shi da murmushi, Shima ya maida mata,,"
Ganan Zahra,duk da nasan kin dauke ta a matsayin yar
uwa,pls ki kara akan Nada..Ta daga mishi kai,,Ya kallo
Zahra,"Da mai magana??.. KAMAR jira take kuwa tai
zaraf.."Nifa ban gane ba da naji ana kiran ta uwar gida
na??
.
Ina ce ni aka fara aura kamin ita?Ya kallo Sa'an, ita kuma
tana kallon zone tare da kokarin cire wa..ya dawo kan
Zahra.. "A ka'ida,wacce aka fara kawo wa ita ce uwar gida,
bawai wacce aka fara aure ba,,Am I clear?Ta kara tabe baki
tare da hararar Sa'a ta gefe,,ya cigaba," So tunda kin
fahimta,My Unique, ta dago kai,"Kwana nawa kike ganin za
ana yi? Ta kalli Zahra, "Sis, nawa nawa yake tambaya?Da
sauri Yace" Ok, sorry,,Nawa kuke ganin za ai?? Sa'a tace 2
sai Zahra ta rigata da sauri.."Uku yayi,,Ya kallo Sa'a,
"Unique 2 naji kince ba,,ta kada kai tana wani yauki,,yai
murmushi kan ya kallo Zahra data kule,"biyu it's Ok,dan zai
fi min nima,,ya kamo hannun Sa'a," Yayi ba?Ta jijjiga kai, ya
dawo kan Zahra, Tuni ta mike,tace"Yadda kuka ce,Yanxu
sai ka taso a fara ta kaina.,Da sauri suka dube ta,har Sa'a
na Neman dariya,,yai murmushi A ranshi yana"Lalle
hasashen Fodio gaske ne,da Yace duk dangi ba mai fitsarar
Zahra.
.
Ya sake kallon Sa'a, ta mike itama tana wani rausaya "Baby
ka raka ta,Kila tsoron sauka take,,yai murmushi ya kallo
Zahra,da zumudi ya mike," Atoh muje na rakaki ki
kwanta,,na ma manta ne,,Baki sake kawai take kallon Sa'a,
wacce tai hanyar daki tana tafiya tamkar hawainiya,,Da
sauri ta juya tai kasa tana hawaye,, Hafeez yana kiran ta ko
oho,,ya tabe baki,, In ta shine dama bai son motsawa yau
ko kadan a wajen Sa'an shi,, da azama ya dau abinda ya
taho dashi nata ya shiga da sallama,, kai duke tana sake
mamakin karfin hali irin na Zahra,,Wai kuma a haka gaba da
bayan ta bafulatana,, wannan Ai bada kai ne ma wallahi, sai
ta Rena mata wayo ma,,. Duk kan wani ala'ada sun gabatar
cikin wayewa,,a yau,yasha mamakin Sa'an shi akan ilimin
addini,,Dukkan wata Amsa gamshasheya ya same ta game
da Sa'a, murmushi kawai yake kara mata,,jin yadda take
fidda harrufa kowanne da hakkin shi,,babu ta bangaren da
Sa'a ta Gaza mishi,.. Kyau Ilimin addini Ilimin Boko
Wayewa Ga Iya zama da mutum, a yau kadai yasan zatai
adalci,. Hmm Bariki ce Hafeez.
.
A gaskiya shi bai taba jin salon kamshin Sa'a ba a
Duniya,,duk inda ta gifta kamshi ke tashi, ga wani shining
da ta kara yi,ansha wankan lalle da madarar shanu,,ita kam
tana girma ma abubuwa Natural,, Yabon kyaun ta yake,har
Saida ta fara jin ko ta zama wata Queen ne,,laushi da
santsin fatar ta ya kara hura wutar da ke ruruwa a sassan
jikin shi,, ko da da yai zaman waje yasan ya tsallake
dokokin Allah, burin shi yai aure kamin ya mallakawa Matar
shi ta Sunnah dukkan kaunar shi da gaskiya,,komai karo da
karo,,sabbin shiga,duk sai ta gigita shi,, dan tabbas tasha
gyara Iya gyara,,Wannan dare a gare su sun ware mishi
shafi daban a rayuwar su,,Duk da tai juriya,amma Hafeez
din ta sai Da yasa ta data sanin gyaran datai mai
yawa..Waras ta samu yabo da kirari wanda har yanzun da
take kan sallaya murmushi take in ta tuno su,,Bazata gushe
ba,tana mai alfahari da kai Budurcin ta gidan Miji,,a ganin
ta, duk wani ji da kai,ko isa a gun Y'a mace,Toh Indai ta
tsallake wannan siradin,toh she's lucky,, In ta tuno da
Daren jiya.,sai taji tana fatan Ina ma ita kadai keda Hafeez?
Ina ma ita kadai ya zama mallakin ta.,Bata zata ba taji
hawaye ya taho zirrr,,Kan ta goge taji hannun mutum,,A
tsorace zatai baya ya ruko ta,, Ta tsinne kai a jikin shi tana
sauke ajiyar zuciya,, dan shaff ya shammace ta bata ji ya
shigo ba,,ya cikata yana murmushi, murmushin da tun jiya
yaki ya kau a fuskar shi,, lalle bai ji kom ba da ya kira Sa'an
shi da "UNIQUE"... Zame wa yai ya kwanto a cinyar ta, Tuni
ta kara sunne fuska cikin kunya,," Ina kwana??...murmu
shin shi ya karu,ba tare da ya amsa ba,shafo fuskar ta
yai,,Yace"Ya kike??
.
Ta kada kai itama da murmushi, tamkar sirikan juna haka
suke ta murmushi, sai dai shi daga Ya shafo fuska, sai
sumbaci hannun ta, lalle ya tsaru a fatar ta,,Sa'an shi Zuma
ce,,ta kuma harba mishi Sonta,,ga ta da wata Ni'imar dumin
jiki da Allah ya hore mata,,shi yasa yanxu kawai burin shi
yaji shi jikin Sa'an shi,, ko hannun ta ya taba Dumi ne,,yaja
doguwar ajiyar zuciya,, ji yake tamkar ya maida ta ciki dan
So,,kokari yake ya kalli fuskar ta su hada ido,amma fir ta
ki,,Yana matukar mutunta mace mai kunya,,shi kyau ma
take mishi yaga mace tana kunya..Indai jiya ke bata kunya
toh,dan ko shi yasan ya kasa Sarrafa kanshi,,amma yasan
akan Sa'a ne,,don abu ne ya kuma hadu Da Tsantsar
so...Hannun ta yakai hanci yana shakar kamshin su,,tai
murmushi,,har kunnen ta ya Gaji da yana kamshin nan. Ita
kwa Zahra tana sauka daki tai tai ta rubzar kukan ta son
rai,,Lalle Hafeez, tun yanxu ya fara rawar jiki akan wata
karuwar Banza,,Da sauri ta tashi ta goge hawayen ta,Zubur
ta mike,Kamar wacce aka tsikara da allura,ta zuge jakar ta,.
"Dani kike zance,,guntun titi kawai,,Ta fara kade kaden
magun guna tana sha,,duk tasan an mata gyara a
gida,,"indai ta nan ne,Ai Sa'adatu Sorry,,dan wallahi sai na
maida ki Mowa,,Hmm Lalle Zahra,Sa'a Ai ta Riga da ta kafa
Govnatin ta.