Breaking News

*** *BARIKI IYAWA PART 8* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 8* ***
.
Tai murmushi kan ta tashi tai kitchen tana kiran Qanwar ta..
Ya kallo Aminu"Dan Allah kaban naka details din da ka Sani
a kanta,,ni kaina bazan ce ga abinda yasa na damu da ita
ba a yau kadai ba,,Aminu yai dariya"Ba yau kadai ka damu
da ita ba,.ina kula da kai,,har Allah Allah kake Ku hadu da
Sa'a I know u fa..Ya kada kai,, duk abinda Ummi ta sanar
mishi haka Shima Aminu ya sanar mishi,,"tun zuwan su
Sa'a unguwar mu na Santa,, a lokacin bata fi yar 7 to 8 yrs
ba,,tun a wancan lokacin ina ganin ta a islamiyar unguwar
mu har yau din nan Hafeez,, en u know what?? Ya girgiza
mishi kai,, a shekara 6 ta gama tai sauka,,sannan ta
haddace littafai da dama da kake ganin ta haka,,sosai tasan
abinda take yi,,yanxu haka ta gama amma bata daina zuwa
hadda ba da daura wa wasu duk ran weekend, shine yau
lahadi ka ganta,toh chan ta nufa,,nayi imani Hafeez ba
haka ka dau Sa'a ba,,shi yasa yana da kyau ka kyautata
niyar ka akan mutum,, Ya kada kai,, tare da rintse ido,, bai
son a daina bashi lbrn Sa'a, Dan yana sashi nishadi,,take
yaji wani abu na yawo a kwakwalwar shi zuwa jikin shi.. Ya
bude ido ya kalli Aminu da wani yanayi,, "yaushe take tashi
a makarantar? Ya kallo shi ya kyalkyale da dariya,tuni ya
kule,, "kaifa dan iska ne wlh,, ni ka fadan nai gaba
malam,.ya tsagaita dariyar kan ya fada mishi lokaci,, tuni
ya kalli agogon hannun shi ya mike,," sai mun hadu,,ya
kwalawa Ummi kira"na wuce,,,ta fito tana dariya,"sai ina?ya
hararo Aminu,kan Yace mata"inda kuka aike ni,,ya dau key
din shi ya fita,,suka sheke da dariya,,sun San wataran za'a
Rina haka,.
.
Tana woo wa kwanar ta dage nikaf din ta,,sauri take dan
wata irin yunwa take ji,,daga kan da zatai ta hango shi yana
fito a mota yana tahowa wajen ta, da sauri ta sauke Nikaf
din ta juya bayan ta tana salati da faduwar gaba..ta shiga 3
indai ta bari Hafeez ya ritsata a gun nan sai dai wata ba
Sa'a ba,, gashi a ka'idar ta in zata islamiya ba mai Binta a
baya a masu take mata baya,,ta waiga taga gidan su Tj a
bude da sauri ta kule tare da turo kofa,,d sauri ya bita yana
kira,, "Sa'a ki bude dan Allah,, magana zamu yi,,cikin tsiwa
tace" ba a bude ba,,kasan dai ramako nai ai,,wlh kama
kauce kan na Tara maka yaran unguwa suma Atule,, yai
murmushi,, toh na tafi bude,,wlh ba abunda zan
miki,,tace"waxaka maida Yarinya,,na San ka ai,,ka tafi
kawai,ba maganar da zanyi da kai,,taji shiru,,sai da ta kusa
minti 10 taji shiru kan a hankali ta zare sakata a hankali
zata leka ya turo kai ciki da sauri,,taja baya tare da kwala
ihu,,zatai cikin gidan da sauri ya ruko hijab dinta,,ganin
hijab din zai matse mata wuya yasa ta tsaya,. "Cikan
hijab,yai murmushi tare da sa dayan hannun ya cire nikaf
din da sauri,,ido ta zaro kanta nuno shi da hannu" wani
salon wulakancin ne wannan komai? ya girgiza kai, "ka
cikan hijab toh,ban son iskanci,, ta warce nikaf din ta,.jin
ihu yasa Tj da kanin shi suka leko,," su waye?,,ta dallah
musu harara,,"Jisu a gun,,toh Aljanu ne,,kallon bakin ta
kawai yake,,akwai Iya fadan gan gan ga tsoro,, Tj ya
murguda baki, itama ta murguda mishi,,Yace"Kuje ba
komai,,suka kada kai,, ya juyo kan ta da take hararar shi,,
yai murmushi, duk da haka yaki sake mata hijab,, bata nufa
kawai sai ganin shi tai ya zube mata a kasa yai kalar
tausayi,, da sauri taja baya tare da zaro ido cikin mamaki,,.
Da sauri tace "meye haka?ya kada mata kai,," I am really
sorry Sa'a,,wlh Sa'adatu believe me,, ban taba daukar
hannu na taba wata da sunan duka ba,,koda kwa Qanwata
ta ce,,but thank God, ba wanda ya gani,daga ni sai ke,sai
Ummi da Hafeez,, tuni ta fara hawaye,,dan tuno yadda taji a
jiyan,,tare da rintse ido,, take wani karfi yazo mata ta kwace
hijab din ta da karfi,, cikin kuka tace"how could you?
.
Ko kasan ko iyayen da suka haifo ni basu taba mari na ba a
rayuwa,,ta goge hawayen ta,,"no bama haka ba,, Hafeez,
duk da ba wanda Ya gani, amma zubar mutunci nawa
ne,,da sauri Yace,"I know,, but pls I am so sorry,,nasan na
miki ba dai dai ba, amma in kin duba duk mun ma juna
pls,,ta girgiza kai, "ka Sani kuka,ka Sani a bakin ciki,ka
dauran tsanar da ban San lefi na ba,. Ta goge idon ta tare
da nuno shi da masifa,."Ban waje na wuce kawai,,fashio
yai,dan yasan ba kula shi zatai ba yanxun., yana kauce wa
ta fita tana daura Nikaf.. Ya bita da kallo har ta sha kwanar
gidan su.
.
Tana zuwa kofa taga mota a kofar gidan wata mai kyau,, da
mamaki yau kuma wata samu haka??ta shiga,suna tsakar
gida an shimfida taburma a inuwa,,harda Baba da a ka'ida
iyanxu baya gida,,ta cire Nikaf din tare da sallama,,baban
Yace"Kaga yar halak, walaikum salam,ta kalli bakon, tuni ta
hade rai,, baba Yace"kin dawo mama ta?ta daga kai,"Baba
lfy? yau nagan ka a gida?da fara'a Yace"a, baki gane bakon
namu bane?ta kallo shi, dan jaraba kuwa kirrr ya kafe ta da
ido,."Ban gane shi ba Baba,, bakon yai murmushi,, "lalle
Sa'a,, Duniya da alkawari kuwa?ta harare shi a takaice,, ta
basar,, baban yai murmushi," shekara 3 kam baici ki manta
Ali ba,,dan wajen mai gida na da ya tafi kasar waje
karatu,,naga har gidan nan yana zuwa kan ya tafi?tace"au,
na gane,.bari na shiga ciki,,baban Yace dama fita zamuyi
yazo gaida su Maman ki ne,,ta kada kai, Baban yai
waje,,zata shiga Ali ya bita da kallo,,lalle Sa'a ta sake girma
da kyau, wlh karan nan bazai bi ta kanta ba,,baisan dame
ya ragu da Sa'a take kinshi ba? ya girgiza kai lokacin da ya
tuno rabuwar su ta karshe da ta furta mishi ba aure a
gaban ta yanxu,..yai murmushi, yanxu kam yasan
akwai,,shi a yanxu gani yake irin su Sa'a ne kadai ajin auren
shi a garin,,gashi Wai dan tsabar takaice Wai bata ma gane
shi ba..yai kwafa,yasan ta inda zai bullo mata ai,, inta San
wata,bata San wata ba. Shi kwa Hafeez tunda dare yai ya
nemi nutsuwar shi ya rasa,, jin wannan abun da ke yawo a
jikin shi sai karuwa yake,,ya kasa sukuni sai tunanin Sa'a,,.
Duk da bata yafe ba,but at least ta gano yai nadama,, ya
hasko lokacin da ya cire mata Nikaf dinta,, Ya salam,Ashe
Sa'an karshe ce,amma mey yasa da bai kula da kyan
nutsuwar ta,,ga ba karamin kyau hijab din ya mata ba,, yai
murmushi, "Hafeez mey ke kanka ne yau 4d first time??
,
Sa'adatu.. Kamar an tsikare shi ya tashi tare da lalumar
wayan shi,, ya kalli agogo 9 ma batai ba,, Aminu ya
kira,,bugun farko ya dauka,,"Nifa tsiyata da gauron mutum
baiya sanin dare yayi masa,. Dan tsaki yai" commot ni
temako zaka min,,ka nemi gauro kuma,dan nima na kusa
aure,.ya kyalkyale mishi da wannan dariyar da take kulal da
Hafeez,, kan ya tsagaita, "kai shegen kaya,har an dai daita
da Zahra ne?? Hafeez yai tsaki, "wace haka?dan Allah be
serious, numbern Sa'a nake so kaban..yace"eyeee?mey
kace?ya kara tsaki,"kai fa dan wulakanci ne,zakace bakaji
mey nace bane? Aminu ya ci mur kamar yana kallon shi,
"meye dan na tambaya, nasan mey zaka karta mata,haka
kawai kasa gobe tazo ta sauken kwandon bala'i a gida..toh
da sake,.ji yai kamar ya bishi ta wayar ya rufe shi da
duka..sai dai yasan halin Aminu,sai ya hana shi tsaf,,tuni ya
dawo lallami,," no wlh ba abinda kake tsammani bane pls,
gaisawa kawai zamuyi,,pls,.ya kara kecewa da dariya,, "lalle
Sa'a tai zarra,a takaice dai tai wining kenan?da sauri yace
"eh,duk ya matso ya bashi,amma dan wulakancin sai ja
mishi rai yake,." Ni in zaka ban kaban malam,,Yace"kai,wlh
kai ladabi,tam,,lalle Mutumi na da magana a kasa.,bani
2mints yazo zan turo,,tuni ya sauke wata ajiyar zuciya,.kan
ya kashe. "Toh in na kira ma mey zan fara ce mata??ya
salam,,Wai mey hakan ke nufi ne dashi da ya kasa sukuni?
kadai wannan fa shi ake kira da so?dan ya San ance so a
zuciya yake,gashi shima tashi zuciyar sai tsanan ta bugawa
take,,tun a ganin shi na farko da Sa'a Saida yaji haka..yai
murmushi,, da ya tuno yadda in sun gamu suke rabuwa,,in
tana zazzaga fada bakin ta kawai yake tuna wa, komai da
gaske take yin shi,,..
.
shigo war text ne ya katse shi, da sauri ya duba,,editing
kawai yai ya danna calling,ya sata a kunne tare da komawa
da baya ya kwanta rigin gine,,caller tune ya fara ji na sheikh
sudeis na Allahumma Aslihlana Duniyall....take ya lumshe
ido,,a hankali ya furta" Sa'a "bai tsammani ba yaji ance "
Yes,who's this? Ido ya lumshe,dan baima San ta dauka
ba,,ita kwa ta bangaren ta tuni ta fara kulewa,,a tunanin ta
ko yan iskan samarin tane yan naci,,tuni ta fara
sababi"Malam in baka da tace wa bacci nake ji,,yai
murmushi kan Yace" am sorry,, Hafeez din ki ne..tuni taji
abun wani bankwara kwai,Wai Hafeez din ki,,"Hafeez dina?
tace"Toh daga wace jahar?yai murmushi mai sautin da ya
ratsa ranta,duk da ta gane wake magana kuwa..ya katse ta
"Sa'a,tace" umm,,"nasan kin gane mai magana,,kiyi hakuri
again,na nemi afuwa pls,,,ta lumshe ido,, ya cigaba"Sa'a,,
da baki juyar da Marin nan kaina ba da bazan taba yafe wa
kaina ba,, amma ki tsimaye ni gobe,zanzo in tsaya a titi ki
Tara kema jama'a ki rama Marin ki,,Kila in munyi 1-0 nima
nawa mutuncin ya zuba sai ki yafen.. Pls,,ta ja numfashi,"ni
bance ba,,Yace"meye baki ce ba?tai shiru, Yace"Ok,yanxu
kin yafe ni ba sai kin rama ba??cikin kaguwa tace"eh..yai
murmushi, "Ok,tnks, bari na barki,. Sweet dreams,,.. Kit ya
kashe,,tabi wayar da kallo,,har kwakwalwar ta taji Kalmar"
sweet dreams din nan..samun kanta tai da murmushi,,
kome ta tuno take ta keme fuska kamar yana ganin ta.
,
Yau kwana 2 da faruwar haka,Ummi ta kira ta harda fadan
su,, dan wulakanci batazo an kawo ta da ita ba,sannan har
yanxu taki ta leko ta,,toh wlh zata fadawa mama,, tana jin
tace mama ta hau bata hakuri,,zata zo yau,,"uwar jaraba, ta
ce"na kai ki?saura ki min lattin zuwa..sukai sallama, ita
kanta tasan bata kyauta ba,,. Da yamma misalin karfe 4
kwa ta dau wanka cikin wani dakakken Orange din les da
blue, yai bala'in mata kyau,tai ado da blue sarka ta
fashion,,batai wata kwalliya ba,amma sai kyalli take na
dilka,ga kunshin biki kamar yau akai mata..Mama ta kalle
ta,,"ah gaskiya baki kauta ba,amma kunfi kusa,,tai
murmushi, "mama zan wuce,ba sako?dan gidan fadeela
zan fara zuwa,,tai murmushi," babu,Ki gaida ta kawai.,ta
gyada kai kan ta fita,,.
.
Tuki take tamkar bata so,,duk da tana dan gudu,,bata San
meya sa haka kawai take jin nishadin yamma cin,, dake gari
ne na damuna,, ko ina gwanin ban sha'awa,, minti 7 ya kaita
gidan fadeela,, a waje ta parker motar ta,, kan ta fito tai
bakin gate,,ta tura karamar kofar ta shiga,,ba laifi,gida ne
madai dai ci mai kyau, rabon ta da gidan kusan sati
2,,tunda ta fuskanci kishiyar fadeelan yar rainin hankali
ce,,.a parlour kwa ta tarar ta ta hakimce,,ba kowa sai ita
kadai,tana shiga ta hade rai,, take ta kalle ta ta watsar, ba
tasan dalili ba ta tsani yarinyar nan fiye da yayar tata da
take kishiyar ta,,gata da dan banzan kwarjini bare ta tanka
ma Sa'an,, ko kallo bata ishe ta ba daga sallama tai ciki., ta
hada hannu da kumatu tai tagumi halamar tunani,,ta cire
gyalen ta ta ajiye kamin ta tabe baki,, "fadeela,, da sauri ta
kalle ta tare da goge hawaye,,dan bakin ciki Sa'a baki ta
sake tana kallon ta,,kan tace" lalle kin gamu da aiki
kuwa,,wlh kinyi asarar kudin Tara fadeela,, tai murmushi,
"sannu da zuwa,,mey nai kuma daga zuwan ki,,Sa'a ta tabe
baki kan ta zauna ta daura kafa daya kan daya,,"
.
Fadeela ba karamin haushi kike bani a rayuwa ba,,dama
Saida nace wa mana karki auri mai mata,dan nasan babu
abunda zaki Iya dauka a gidan sai dolanci,,take fadeelan ta
hade rai "ke ban San wulakanci fa,,abun harda zagi?ta
hararo ta,"jiki fa,,dan Allah kina kallon mudubi kuwa?kinga
ramar da kikai a abinda baifi wata guda ba??tai wani
murmushi,kan ta mike tsaye tana gyara Riga,," wlh na gode
da ban tsamu guntu a abunda kika sha na karba ba,da tuni
nima na rako mata duniyar nan,,ki dube ni da kyau,, "wlh
nafi karfin gujewa kishiya,,nafi karfin kishiya ta juyani wlh
ko ita wace ce,,da sauri fadeelan ta taso tana sa hannu a
baki halamar tai shiru kar taji,,taja tsaki kan ta suri jakar
ta,," ki same ni a parlour,solomiyo kawai,,duk abinda ake
kishiyar tana ji,,tana fitowa direct kujerar dake facing din
kishiyar ta zauna,,ta ajiye jakar ta a dayar tare da daura
kafa daya kan daya,,kishiyar taja tsaki,dai fadeela ta fito,sai
wani rakabe wa take,,Sa'a ta kallo ta,, "meye hakan?a gidan
mijin ki kike sanda?ta kallo kishiyar ta ta,.ta dallah mata
harara kan taja wani uban tsaki,," dama dan talaka haka
yake ai,bai oya samun guri ba,,anzo an hau kujera da babu
ita a gidan uba,..ta kara makowa fadeelan harara..a rakabe
tazo zata zauna tuni Sa'a ta amshe,,"dadin ta mun San
uwale mun San ubale,,sannan tsinke ubale bai kawo gidan
ba,tsiya kuma ai duk mun ganta har ke,, gwara mu da rufin
asirin Allah,, sannan auran So da kauna aka kula
damu,bawai tushe ba..ta nuno ta da hannu,,"mun San kom
ai,,so babu wata rufa rufa..ta dawo kan fadeela.. "Gidan
mijin ki ne nan,,yadda uban ki bai kawo kujera ba haka
nata,,so kowa yai zagi a Kasuwa yasan da wanda yake..tuni
ta hazuko ta mike,,"ni zaki gwada wa BARIKIN da ake fadi,,
wlh kije shan kiyi karuwancin ki ba a gida na ba,.yar BARIKI
kawai,,Sa'a ta kallo ta, sai wani huci take kamar tayi gudun
fallako,,tai wani shegen murmushi,, tare da rausayar da
kai.." Fadi da ihu ki kara da wayyo Allah,,. Ta tashi
tsaye"BARIKI ba IYAWA ake fada miki,ta na wani yauki tare
da jujjuya wa a hankali..horn suka jiyo,halamar mai gidan
ya dawo..ta nuno ta key din motar ta.."kuma kisha
kallo,yau zakiga karuwanci ganin idon ki,,BARIKI ba?yau
zan baki darasi.