*** *BARIKI IYAWA PART 14* ***
*** *BARIKI IYAWA PART 14* ***
.
Bacci suka koma,cikin daddadan sanyin safiyar,, Sai 10
suka tashi,Shima ji tai ba mutum a kusa da ita,,sanye yake
cikin Farar shadda, an mata aiki da brown din zare,,ya
daura hulal shi yar zanna brown da milky ajiki,,sai kamshi
yake tashi a jikin shi,, ta lumshe ido a hankali ta kara
budewa,,yai mata kyau ainun,,Ta mika mishi hannu da
Shagwaba,, bai wata wata ba ya kamo,,Tun jiya yake shan
shagwaba, gashi Aminu sai waya suke mishi zasu gaisuwar
sirikai,,ya sumbaci hannun ta,, "Ga abinci Hajiya ta aiko,,En
Aminu suna ta kira..Ta rausayar da ido,," Ai da ka tashe
ni,,yai murmushi,, cikin 10 mints tai dan wanka,ta shirya
cikin Brown less, da ratsin milk,,Batai wata kwalliya ba,dan
sauri suke,,Ya sauka ya tarar da Zahra har ta gama cin
nata,,ta hakimce a kan kujera tana kallo,,doguwar Riga tasa
ta Attamfa, tai kyau itama,,sai dai a hakika ba kallon ne a
ranta ba,dan tun da ya kwankwasa mata kofa tai sallah ta
kasa koma wa bacci,,hatta hawan shi sama ta gani bayan
ya bude an kawo abinci,,. Rike suke da hannun juna suna
murmushi, sai wani langwabe kai take a kafadar shi cikin
salon ta,,Tuni Zahra ta fara cika tana batsewa,,taja dan
karamin tsaki ta cigaba da kallon ta,, Hafeez ya kalle ta,,"A
Zahra,,kin tashi ne??Tai mai banza,, Yace"Magana nake
fa??kan ta daga kai,.Ko gaisuwa babu,, Wai ita a dole sun
bata haushi jiya,,Sa'a tai murmushi, Lalle yarinyar nan batta
da wayo,,dan tsabar ta kara bata haushi tace"Sister in
kwanan mu?Zahran ta kallo ta fuska a tamke, Lalle Za'a
gwada mata BARIKI,, sai ta dauke kai ba tare da ta amsa
ba,, Hafeez ranshi ya baci,cikin fada Yace"Ke baki Iya gaida
mutane ba sai mu zamu gaida ki??Ta kallo shi, ganin ya
fara kumfar baki ta gaida shi yai mata banza yaja Sa'a kan
dining,,Tashi tai ta tafi daki,tana"kar ka amsa,a ranta.. Sun
ciyar da juna cikin kulawa da kware wa a so,,yana fita ta
rufe sauran tai sama tare da tsantsara hadaddiyar
kwalliya,taja dauri,,. Da akwai wuta ta sanya turaren wuta
tare da kullo glass din saman dan kar ya fice,,ta shiga ta
hau gyara har ta gama ta kira mama da tsabar kewar
su..tana in Fadeela tazo a bata sakon.
.
Tana sama taji hayaniyar baki,,Ta fito tare da daga labilen
jikin glass din kadan,,su Aunty Maryam ne da wasu dangin
su Hafeez din baki da sauran cousins din su,suna gaisawa
da Zahra da tai zirif ta fito parlour kar a bata mata
daki,,Tana ganin dangin su ne ta fara yake baki suna
fillanci,,Dan autan Aunty Maryam Habeeb mai koyan
tafiya,yaron mai kiriniya ne sosai,,Yana sauka yai wajen TV
stand din ta,,ba kunya ta debe remote din ta tana nifa kar
kamin ta'asa,,Sa'a duk tana kallon ta,, duk da batajin abinda
take fada,ta kalli yanayin Aunty Maryam,Duk da yake take
amma in ka kula zakaga ta sauya,,ita kam Tasleem dama
binta kawai take da ido,,sai ta kashe kallon ma duka,,tana
cigaba da musu tadi,,ita mai yan uwa harda fada musu
abunda ya faru bayan tafiyar su,,kowa kallon mamaki yake
Binta dashi,,mamaki suke Zahra tamkar ba yar gidan Aunty
Sadiya ba,,wannan Ai abun kunya jiya ta tafka,,Sa'a taga
tana dai ta kumfar baki,sai ta sauke labulen ta ta fesa Air
weak,,ta hakimce a parlour,, komai take kallo cikin tsari an
jera mata,,Tai murmushi da ta tuna da Hafeez din ta,,Yace
"Komai Unique kamar kin tambaye ni tsari na...kwankwasa
glass din ne ya dawo da ita,ta kara kallon kanta jikin glass
din kan ta bude,,Da fara'ar ta ta tare su,," A Aunty,,Sannun
Ku da zuwa,,Qanwata,,Tasleem ta wage baki,,Habeeb yana
ganin ta ya bangale baki,,ta mika hannu tare da karban shi
tana"Oyoyo Habeebe nah,, Missed you,, Tuni kwa Aunty
Maryam din suma suka hau murmushi,, da fuska duk ba
fara'a,, tun zuwan ta take son yaron lokacin da taje gaida
ta,,. "Bissmillah., Ku zauna,, harda yan tsofi 2,da jiya basu
zo kawo amare ba yan uwan Baban su Baffa
Modibo,,saboda haka Tuni tai kasa su kuma suka zauna a
kujera suna yaba tarbar data musu,,da girma mawa ta
gaida su,, Saboda haka fuska sake suka amsa,,barin ma
Aunty Maryam,, ganan Habib sai tsayuwa yake a kanta
yana tabo daurin dankwalin ta,,chakulkuli ta fara mishi a
wasa,sai ta dau hankalin sauran yaran,,data tashi sai suka
biyo ta,, Lalle,Shimfidar fuska,tafi ta Taburma,,Ta kwala
kiran Tasleem a hankali,. Takwara cire gyale ta ajiye a
kujera ta bita kitchen,, Aunty Maryam ta kalli yan uwan
nasu da cousins din ta,," Allah yarinyar nan yar mutunci
ce,,ga Waccan uwar fitsararrun tarbar da ta muku,,ko ruwa
babu sai shegen mita ya Taga courtu,,..
.
tai shiru ganin su Tasleem,,Tasleem dauke da Cups na
glass, Yayin da yaran ta basu flates guda 4 cike da
hadadden Doughnuts da cake,ta bawa Habib exotic babba
daya ya rike,ta debo wasu Drinks din da ruwa a flats,,"Aunty
kuyi hakuri mun barku,, Tana murmushi tana tsiyaya
musu,,kamin ta mika musu,,Tashi tai ta kunna kallo,,Ta
kallo su Inna Balki,," Inna Wanne kuke so,,Inna tai
murmushin jin dadi,,tace"Muda zamu tafi,Ta kallo Maryam,
"Mairamu kishiya ta na son mu jima hala,,tai murmushi,
Kan ta kallo Sa'a," sa musu na Dan ibro,dan she really enjoy
his Movie show,,Sa'a ta kada kai da murmushi, itama tana
son Film din ibro,shi yasa ma ta siyo wani film da ya jima
amma tana son shi,,NA MAMAJO...Ta kallo Habbeb daya
kin kumo kwali ya kawo mata,,Wai ta bude mishi,,ta dau cup
din Tasleem ta zuba mishi,,Tasleem tace,"Ganan su innan
mu,jiya basu samu zuwa ba,,Da fara'a ta kalle
su,,"Aiya,,Sannun Ku inna,,ya taro??suka ce Alhamdulillah,
chan aka fara show na ibro Abin dariya,,Ta yafico Tasleem,
tana tashi Habeeb ma ya tashi,sai glass cup din hannun
yaron ya subuce,Tuni ya fashe,,Ta juyo da sauri
tana"Subhanallah,Habeebe,,hope bakaji ciwo ba??Shima
yaron duk yai kamar zai kuka,.
.
Hanun yaron take duba wa,,Wai koya yanke,,Aunty Maryam
ta taso,"Dama ban so ki bashi glass cup ba,,gashi ya
fasa,Habib da kiriniya,,ta kallo ta,"Kai Aunty,ni tsoro na ma
kar ya yanke,,ta Kar kade mishi jiki,"Aunty rike min shi na
kwashe,ya make kafada,,Tace"Sorry yanxu zan dawo,,ta
shafi kumatun shi lufulufu,,"That's my Boy,,Aunty tai ma
Tasleem da ka kan ta karbo tsintsiyar,fir ta hana ta,ta share
tai moping wajen,,Sai mamakin kirkin Sa'a suke,. 12 nayi ta
bar su sukai kitchen ita da Tasleem, guntun kajin jiya tasa
Tasleem ta sauka kasa ta dakko miyar cikin flasks din da
aka kawo da safe,ta gyara ta ta juye kajin,,Tuni kamshi ya
gauraye saman,,tai cous cous mai sauki,,ta taho da sobo ta
daura a wuta ganin tana da kankara da cucumber data zo
da ita,kan 1 da wani abu ta gama komai,,Ta dawo parlour
sun gama kallo suna ta tadin su da fulanci, duk na yabon
ta,,duk da bata ji,amma 4 sure tasan yabon ta suke,ganin
yadda suke kus kus suna dariya,,Tace"Aunty su Inna kwa
sun shiga ciki?? Ta kallo ta da murmushi,"No,mai daki na
kitchen Ai basa shiga ba,,ta waro ido,, "La,Ai ba komai,Inna
Ku shiga Ku ga,,ta Jere musu abinci a flasks,sai ga su
Fadeela da Ummi,,ana fara kiran sallah ta ta shimfida musu
Darduma,,wasu suka shiga bandakin parlour, Tace wasu su
shiga ciki,Ba kyama haka ta dinga tafiyar da su,,nan wajen
ta suka kai sallah suka ci abinci hade da jin dadi,basu bar
gidan ba sai da ta tabbatar da kowa ya tafi da kirkin ta a
bakin shi,,.
.
Ita kam Zahra qawaye na zuwa suka kule daki,,Inna ta
leko,"toh mu zamu wuce,Fatuu ba dan karar kuzo kuga
dakina ma koh?Tace" Au,Ku shiga,kudai tsofin nan sai
ganin gulma,,Ita kam Aunty Maryam tai gaba da danta da
sauran yara,tai ma Hafeez waya cewa sun fito ya dakko su
inna,yaran sai murna suke ta basu chocolate,..A mota sai
yabon Sa'a su Inna suke,"Kai Hafeezu kai dacen mace mai
son Jama'a, sai son barka,Sa'a tai kaza,Sa'a tai
kaza,,shikam Murmushi kawai yake,Tuni yaji Sa'a ta kara
samun martaba a idon shi,Tuni ya kara share mata waje a
cikin Birnin zuciyar shi,, tuki yake yana murmushi,, Sa'a,
Sa'a, a ranshi fadi yake"She's d Best,,.Duk da sun ma
manta da iskancin da Zahra ta musu. Suna dira,suka fara
bawa Hajiya labari,,a ranta tana mamaki,da Wai suka kasa
gano wace ce YAR BARIKI?.. Sai dai ta bisu da murmushi,
amma ita kam Zahra ce ta ta,duk tsiya,,. In banda waya,ba
abinda suke,ta kira,ya kira,Su Ummi sun tasa ta gaba suna
ganin fi'ili iri iri a wajen Sa'a,,.
.
A yanxu ma waya take,su da suke kusa da itama dakyar
suke jin zancen,magana take tana wani kashe ido,kai kace
Hafeez din yana gaban ta,, Ta ajiye ta kalle su,,"Ya akai ne
Guys,irin wannan kallo??ta tashi daga kishingi den da
take,,Ummi tai Murmushi, "Wallahi Ade tausayin Kishiyar
nan taki nake,,Wai kishi da Ade BARIKI?? Woo, amma fa a
dan mata sassauci pls,,suka tuntsire da dariya harda
shewa, " Ke,in taso zan zame mata tamkar yar uwa,buh ta
sake tace zata ja Sa'ada,, woo woo,sunan ta sorry,,dan
Wallahi yadda nake jin Hafeez yanxu a kokan raina...Hmm
kedai abar tone tone,but he's d best, ta lumshe ido,, Fadeela
tace"Ai itama da ganin ta yar yi ce,kiga fa yadda take amsa
mana gaisuwa tana wani yatsina fuska,nidai dan Allah kisa
da hakuri kar ki biye mata.. Ta dallah mata harara,,"An fada
miki kowa ma irin ki ne,,hakuri?? Ai ban ganshi ba,indai
akan kishi ce,tana Dana min,wallahi zan Dana mata
nawa,in ta rissina sai mu sai saita,,but bafa fada
ba,No,BARIKI kawai,ya ishe ta,, Ummi tace "Toh Allah ka
bawa Zahra hakuri,dan zamuyi kuli da ita,,tai wani
murmushi," Ummi kenan,,ni Ai bana fatan haduwa da
kishiya Lumbu lumbu,hmm wutar k'ai k'ai ce,,Bana son
ajiye makaman yaki na da wuri,gwara wacce zamu dama a
fagen yakin Ni ko Ke??..Kuma Allah ya bani,don Haka nake
so,,ban son munafukar kishiya,Wai Ita mai hakuri,,. Ta kallo
Fadeela,"Toh ke ya batun sanjan gida??
.
Tai murmushi, "Kai Sa'a,Wallahi u r too much,, duk da kin
sa Matar nan ta rissina,kinsan da bakin ta ta fada mishi Wai
sai ya sauya mana gida,indai zaman lafiya yake nema,ba ko
musu ya yarda," Tun kuwa da ta kalla taga cikin nan ta kara
haukacewa,Ai sauri a sauya gidan nan,,,Tai kasa da
kai,"Wallahi har tausayi ta fara bani,,Sa'a tai tsaki,,"Ai sai
kiyi ta jin tausayin nata,,ke ta Tausa ki Ai,,Taje itama Allah
ya bata rabon ta Albarka cin ki,Ai adalci ma na mata,dan
kazantar da baka gani ba tsafta ce,kina ga in ta cigaba da
ganin rawar kan da Alhaji yake akan cikin nan bazata
hadayi zuciya ba??,,.Suka tafa "Baki kyau,,tace" Ko nai
wanka,,Yanzu Ai ban fara komai ba Wallahi, zan daga mata
kafa na fake da kunya ta sati guda,daga nan zan fara bude
koli na a gidan nan, Suka tuntsire da dariya,tace "Kudai Ku
rike dangin Miji,dan tamkar shi kuka rike,dan duk abinda
kika musu zasu fada yaji,en tanan, wani sirrin rike wuyan
Miji ne tamau in fada muku,,. Sai da suka Taya ta ta gyare
gidan ta tsaf, sukai magriba kamin Suka tafi,direct wanka ta
shiga,banda kamshin turaren wanka,babu abinda ke
tashi,,Ta fito daure da Towel,ta cire hular wankan,Zara
zaran kitson nan sun zubo mata kafada,ta gyara na gaban
kan tahau kyali,tamkar wacce zata Dinner,,Ta dame cikin
Riga da skirt din wata Holland blue da ratsin purple ajiki,,Tai
kyau ainun,sai kamshi ke tashi na Amarya,,ta kullo Kofar
glass din dan taji har yanxu Qawayen Zahra na nan,,tasau
turaren wuta, Tuni yahau kamshin dadi,,ta feshe Air
weak,tare da yarfa turaren Carpet da kujera,Tuni wani irin
gamsashen kamshi ya kewaye saman,har yana dan ratso
kasa,,. Kai Zahra sai fa kin dage,ji wannan hadadden
kamshi,Tai murmushi," Lokacin ta ne,daga yau Ai sai ni,nayi
imani in ya dani kunamar nan,sai wata ba ita ba,,Jumai
tace"Toh tashi kiban kudi na,dan nasha wahala kan nasamu
kayan nan,,.nan Ita tafi karfi,gani take tunda ba ita keda
Hafeez din ba,Ai ba sai ta gyara ba,ita dai ta gyara chan..
Da zumudi ya shigo gidan,dan tun fitar shi yake mar Marin
zuwa gidan,duk Sa'a ta gama kar kato da hankalin shi gare
ta da daddan muryar ta a waya..Sai dai mey,yana shiga
gidan Zahra na fitowa ta bata mishi budget,,.
.
Wai sai ya kai Qawayen ta gida,,A ranshi yana toh mey suke
har yanzu da basu tafi ba??8 fa saura,,.
.
Amma haka ya Nada,tana ta murna Wai ita ta fara danawa
Sa'a Bom,dan tasan in har zai kai kowa gidan ta zai bata
lokaci,,wannan plan din jummai ne,,Har dan tsalle ta buga
tai daki,Sa'a ta kada kai, tare da sauke labule,dan tunda taji
horn din motar shi ta leko,duk tana ganin abinda Zahra
tai,,ta kada kai tare da murmushin mugun ta,,. 8:30 ya
shigo,da mamakin Zahra sai ganin shi tai,,Ko ta kanta bai bi
ba yai sama,,yaja glass din,,yana tunanin ya zai tarar da
Sa'a, dan tunda zai shigo ya fada mata,,amma da mamakin
shi da fara'ar yaga ta taho,,ta dan lafe a jikin shi, Tuni ya
sau ajiyar zuciya, ta zaunar shi kamar mai rada tana mishi
sannu da isowa,ta zame takalmin shi,ta cire socks
din,Murmushi kawai yake mata,,taje ta kai kayan kitchen ta
dawo,, hau,Kusa dashi ta zauna tana hura mishi iskar bakin
ta, "Sannu,.hannun ta ya kamo," Kinyi kyau,tai murmushi,
"Muje kai wanka,zaka ware,Allah sa ka ci abinci baka bar
min kan ka da yunwa ba,ta wani marai rai ce, Jawo ta
yai,da halamar jin dadin kulawar da take nuna mishi tun
fitar shi zuwa yanzun,,. Bayan yai wanka,Ta zuba mishi
abincin da Fadeela ta taho musu dashi,,bashi ya sakko ba
sai Kusan 11,da mamakin shi Zahra na parlour, Yai turus,,"
A,ke bakiyi bacci bane har yanzun?? A kai kaice ta kalle shi,
Ta watsar,"Bana bacci da wuri ni,,Ya kada kai, kan ya kulo
kofa,ya mata sai da safe,,Da sauri ta sha gaban shi,,"Nifa
yunwa nake ji,,Ya kalle ta da mamaki,,"Yunwa kuma??..Ta
daga kai,,"Ince Sa'a ta aiko miki abinci da yamman nan??Ta
daga kai, "Ba na ci ne,dan bansan mey aka bar bada min ba
wallahi, yai murmushi, A ledar da na baki babu abin ci??..Ta
fara marai rai ta,ita a dole so take ta bawa Sa'a haushi in ta
rike shi,,"Kayan zakin zanci na kwanta?..Tab..A hasale
yace" Toh ki kwana da yunwa..Ya haura sama ya barta
nan,,Tai kwafa,"Ba dan kai nai ba,,.
.
Washegari sukuku Suka tashi,barin shi da yake ga yau ba
Sa'a gare shi ba,dan kwana 2 nan,sun musu wuyar fassara,
babi guda Suka ware musu a Rayuwar su,,. Zahra ba
zama,dan jummai tace kar tai sanya,,sai dai gaba daya
lamari haka ya tafi sukuku,dan barta da kyallin chan,
bangaren tarairaya an baro ta a baya,. Da yazo ma Sa'a
sallama harda kukan ta,, Dakyar yai ta lallashi,, dan ji tai
wani mugun kishi ya tokare ta a makoshi,sai da tai ta
Inalillahi tukun ta samu sa'ida,Ashe haka kishi yake??Ashe
mugun ciwo ne??..Lalle dole in ka kasa control da shi yai
maka illah,Ranar bacci sai barawo ga Sa'a,,. Ita kam yana
shigo wa dakin yasha freshener,sai dai sirrin kamshin Sa'an
shi daban ne,,Shi ko hade ran da Zahra take bai kula
ba,,fatan shi Allah bashi ikon adalci...
.
Gashi dai Yayi Iya yinshi ganin yayi Adalci, amma abin yaci
tura,,Sa'a kadai ya mallakawa kanshi da zuciyar shi,, duk
itama Zahra ya yaba da yadda ya riske ta,sai dai d"ai da'i
da sallah ta gagara tashi,, Har ya dawo tana yadda ya
barta,bata da niya ma bare ya taimaka mata,,Yai murmushi,
ya tuno da Sa'a, Zai latti a masallaci tace yaje zata
Iya,sannan ya dawo ya tarar ta a kan sallaya,,baya yai
kawai ya koma parlour,, Bangaren Sa'a kawai ya sawa
ido,,Yana murmushi, yaje tashin ta yaji tana karatun
Qur'ani, Tuni yaji tausayin ta, Allah dai yasa tai bacci
yau,,.Sai da yaji zubar ruwa a bayan gida ya koma
dakin,zanin gadon ya yaye ya sanya wani,,kan ya dan
kishin g'ida,,Bacci ya sure shi,,Farka wa yai ya ganta a
kwance itama,,kare mata kallo yake,Tana da kyau na nuna
wa Sa'a, a dabi'a tana da ita mai kyau,ya rasa meye dalilin
da yasa karfi da yaji Zahra ta chanja hali??..Yanzu yar
gatse gatse ce,,Tashi yai ya shiga bandaki ya watsa
ruwa,ya fito ya shirya,9:20.,yasan yau kam bamai kawo
musu abinci, dan jiya ma Hajiya bata kawo ba,duk da yai
wa kowa cefanen ta da yamma.