Breaking News

*** *BARIKI IYAWA PART 18* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 18* ***
.
Takarda yake dube,Gashi Sa'an ta na gidan Fadeela,ya kira
wayan ta ya shiga bata kusa,,. Turus ya tsaya tare da
kwaso su ya zube a kan gado,,Plygyl ya gani da sauran
tarikicen mugun gunan da likita ya rubuto ma Sa'a,, Gasu
nan har ta kusa shan rabi,,budewa yai ya fara karanta
wa,,Duk da bai fahimci komai ba, amma ya ga an rubuta
mai ciki Kar ta sha in yana first trimiser,.Tuni wata zuciyar
ta fara fada mishi na hana daukar ciki ne,,deba yai Ya
sakko kasa,sai huci yake,Tana gado tana waya da Jummai
ya shigo,da sauri ta katse ta,. Dake tayi science, sannan
bangaren ta karan ta a Deploma a pharmacy,, Ya zube mata
magungunan,. "Na meye wannan Zahra?Ki waren wanda
yake hana shigar ciki,.Tuni ta harbo jirgin shi,.Tai
murmushin mugun ta,, kan ta daga flygyl,,. "Wannan flygyl
ne,400g,Yana Iya zubar da ciki koda na kwana d'aya ne,.Ta
daga dayan,sarai tasan na dan infection ake rubuta shi tace
pills ne,,dayan kuma na infection,,. Huci yake kamar wanda
zaici babu,,ya kwashe su har yana warta,,.Da gwalo ta
bishi,," Jeka dai,,kai ba mai yar goal ba,ba'a taba jin kan Ku
ba,yau maji ma gani Ai.. Missed call taga nashi,da azama
ta hau kira,. Dafe yake da kai a hannu,"mey yasa Sa'a zata
mishi haka??.wato dan ya barta aiki shine ta samu damar
raina mishi hankali.., Wayan ta katse shi, yasan ita ce,dan
ringing tune nata daban ne,,yai tsaki,da kamar bazai dauka
ba,,. "Am sorry Habeebe,muna chan hidimar aiki,Ya kake...
"Ki dawo ina son ganin ki yanzu,A tsorace ta waro ido,dan
jin yadda yake magana fada fada,,sannan ba ita gare shi
ba,,.Da marai rai ta tace" Ok,. Ta kalli Ummi da. Fadeela,
"Zan je na dawo,,suka daga mata kai,dan duk sunga sauya
war ta,kuma sun San da wa take waya,. Ta dau mukullin
motar ta ta fice. A saman ta same shi a daki,yai kicin
kicin,Zahra najin sallamar ta ta labe a gefe dan jin mey zai
wakana,,.Yadda ta tarar shi ya bata tsoro, ganan mugun
gunan ta a watse kan gado,. A rabe ta zauna a bakin gado,,"
Baby hope dai lafiya kake?,,. Cikin daga murya ya fara
fada,ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba,,.Kai tai
kasa,dan tsabar al'ajabi,Bai taba mata haka ba sai
yau,,Tuni hawaye ya fara zirya a fuskar ta,.
.
"Mey zakice game da wannan??. Ya nuno mata magani,,sai
ta zata dan taje asibiti bata fada mishi bane yasa hakan,,."
Kai hakuri,naso fada maka,Sai..."Kimin shiru,tambayar ki
nake na meye??.Baki sake take kallon shi,,. Sai dai yai
nisa,,ta girgiza kai "Na infection ne,.Yai Murmushin cin rai
ganin ta ma raina mishi hankali,. Kai ya kada," Daga yau na
soke aikin ki a gidan nan toh..Da sauri ta tashi tana waro
ido,. "Hafeez mey nai haka da zafi ne??." Au tambaya ta
ma kike??. Ta girgiza kai tan hawaye,"Kai hakuri,wallahi
ban San zuwa asibiti na zai bata ma ba,.Yai Murmushin
takaici,."na dai sanar ki na soke aiki,kinga sai ki zauna
zaman Tara yaran yanzu,.Amma Sa'a ban San lokacin da
kika daina so na ba,,ta dago da sauri,.
.
Waje yayi dan ganin kukan nata na k'aruwa,.zahra dake
labe a kasa da sauri ta zauna a kujera..waje yayi ta bishi da
dariyar keta.. A gado ta zube tana mai kuka mai tsuma
rai,.Wato maganin ne ma na planing??. Ta kuma sanar shi
na meye yaki yarda,,. Tai mai Isar ta har magriba kan ta
tashi ta goge ta shiga wanka,,.Tana fito wa ta tsantsara
uwar kwalliya kamar mai zuwa party,,kai in ka ganta baka
ce ita tasha kuka ba,. Riga da skirt ta dakko,skirt din ya
wuce cinya mai yalwa Green da ratsin baki baki,,.Sai top din
shi Mai yankekken hannu,.Ta tufke gashin ta sai kamshi
take tai kasa,.Lokacin Zahra na kitchen, sai fitowa tai taga
mace ta daura d'aya kan d'aya tana waya,."Eh sai dai
goben,,InshaAllah da wuri zan zo,.. Suna hada ido ta sau
mata Murmushi,. Zahran itama tai yake,.kitchen ta koma
tana cije lebe,. Wace irin jarababbiya Allah ya hadata da
ita??. Ji kamar ba da ita akai dazu ba??.
.
Tai kwafa,ta gani Ai.. 8:pm ya shigo,.Kallon Sa'an yake,ta
bala'in mishi kyau,,.Ta kallo shi,. Da sauri ya dauke kai,.
Zahra ta kulu Iya wuya,.sannu da zuwa ta mishi fuskar ta
sake,.ya amsa yana kallon ta,,. Da yaga zata kallo shi sai
ya dauke kai,.. Suna cin abinci sai dan tsakura take,,yana
kula da ita,,.sai dai bai son mata magana ta ga ko ya
sakko,.Amma duk tausayin ta yake,. Yasa Unique din shi
kuka,. Suna gama cin abinci tai musu sai da safe.. Da kallo
ya bita har ta kule,,.Ya sauke ajiyar zuciya,,Zahra ta buga
plate kan wani tana tattara wa,."Anya Sa'a haka ta bar
Hafeez kuwa??.Anya baza tabi shawarar Jummai ba na
iyaka tsakanin shi da sa'a ba??.. Tai kwafa,.. Washegari
sunan Fadeela, da wuri ta tafi,.Yaro yaci sunan Baban
shi,,harda Hajiya Rabi a wajen hidima,in ka ganta gwanin
tausayi duk tai laushi,,tunda taga ba sarki sai Allah ta
fauwala wa Allah komai,.Dan Fadeelan bata da bace,. Anyi
suna an tashi lafiya,.Ta dawo gida da jin haushin Zahra,
dan sai da tai Dama bata je mata ba,. A gaban su Aunty
Maryam take mata feleken ita bata son kaza da kaza,an
kawo abinci ma bata son warin curry..
.
Hmm sai ita halin ta. Ita ke gare shi, duk tayi kicin kicin,kiris
take jira ya kula ta tasau mishi kuka,dan kwarai ya bata
mamaki jiya,. Shima dake Namijin Duniya ne haka ya daure
yaki lallashi, sai dai da aka zo kwanciya kamar kullum ta
lafe jikin shi, anan komai ya sai tu.. Dan baya Iya hakurin
Iya jure rashin ta kusa.. Washegari warai aka koma kamar
ba Ai ba,.sai ma wani nan nan da yake da ita,.Batun aiki ta
share shi,.Wai aka ce fadan masoya ba fada bane,. Sabe ya
sakko da ita tana bayan shi,. Dariya suke yi tamkar basu
bane jiya da shekaran jiya,. Da azama Zahra ta koma
daki,.Tabbas zargin ta ya zama gaskiya,.Dan ita sun sha
fada daga baya sai an kai ruwa rana ashirya., Dan ita in tai
fada da Miji toh fa kowa sai ya Sani,.Dan zata hau fishi ne
har a shimfida,. Yayin da shi kuma sai ya basar ta.. Amma
sa'a Duniya,cikin ruwan sanyi ta mantar shi komai. Yana
Office tace mishi zata unguwa,. Yace sai ta dawo,.So take
ta kai ga likita,dan sanar mishi changing da take ji kamar
yadda yace,.Ta koyi nawa kwana biyu,ba ita ta bar gidan ba
sai dab da yana dawo wa,. Dai dai zata bi junction Shima ya
taho,.yana ta mata horn ina,bata kula ba,.sai ya samu
kanshi da bin ta ganin tayi hanyar asibiti.. Tai
parking.,Shima yai a dan nesa da ita,.Binta yake ba tare da
ta kula ba,,.gaban shi sai faduwa yake,.a tunanin shi Sa'a ta
hakura tunda ya barta aiki,.Ashe ta daura daga inda ta
tsaya,. Toh zai ga likitan mai planing din,zaiji uban mey
yasa zaiwa Matar shi planning ba tare da yardar shi ba...
Anti Nital tabi, yaga a sama an rubuta /Family Planing,.
Kwanar yaga tayi,.da azama ya bita dan ganin inda ta dosa.
.
Ita Hakima ce,bata bin layi,,dan da shigar ta ma sai ka
dauka Matar wani Babban mutum din ce,Direct ta shige
data tabbatar ba kowa,,Shima da fara'a ya kallo ta, dan
gwanin Kallon News ne,kuma yasan Sa'a,.Ta fara mishi
bayani kenan sukaji an banko kofa,.Da azama ta mike
lokacin da tai arba da Hafeez,,. Shi kam bai wata wata ba
ya chakumo Dr,. "Da sa hannun wa kake wa mata ta
planing??. Dr ya zaro ido,," Hala baka hankali??..kaga an
rubuta planing a office dina??..Ya rike hannun shi tare da
kokarin ban bare wa,,.Amma ina,Hafeez ya rike shi tamau,.
Sa'a ta fara Hawayen takaici,,. "Hafeez yaushe ka fara min
Titsiye a rayuwa??..Ya juyo yana hararar ta.." Ki bari,zan zo
kanki kema Ai,.Zanji dalilin zuwan ki nan?.Allah ya bawa Dr
Sa'a ya ban bare da kyar..,"Ya kamata kana bincike kan ka
hau zargi,,.Ya daga mishi hannu,"A kaga malam,kayi na
kudin ka,dan duk randa zan kara ganin ka da mata ta court
ce zata raba mu..Dr Dariya ma ya fara,Ganin sai wani dage
wa yake,,.Tabbas yana son mutum mai kishin Matar shi,.
Yace"Toh madam din ka tana dauke Da ciki yanzu
haka..,Ya maka mishi harara,"Kar ka layan ce min
malam,ba shi zai hana na yarda da kai ba,.Yai murmushi
tare da dafa kafadar shi,."Abokina ka nutsu,,.Kaga kasa
Matar ka kuka,.Mu fidda zancen wasa,.Tabbas likitan Mata
ne ni,bari in ma gwari gwari,kuma ina planing, amma ba ga
Matar ka ba,,.Ita nata planing din Samun ciki muke,Kuma
da dukkan Alamu mun dace,,.Ya kallo Sa'a, "Madam,inda
muje ki kwanta,,.
.
Ya dafa Hafeez," Calm down,. Ka zauna please,. Ya zauna
da niyar Ganin gudun ruwan shi,,.cewa yai Sa'a ta dan daga
rigar ta ta mike sosai,.Hafeez ta kallo da shi kuma yake
Kallon Dr,,yai Murmushi, "Scanning zan yi,so ka rintse ido,
Tashi yai ya tsaya a kan machine din,.Likita ya girgiza kai
yana masa Dariya,.Da kamar minti 5 ya dago kai,,." You
see,,Ganan Babies din ku a cikin madam,,.Matsowa ya
karayi baki sake,,Likita ya sake daura abin a kan marar
Sa'a., Tuni hawaye ya silalo mata,.Da sauri Hafeez yakai
hannu zai goge mata ta gantsara mishi cizo da harara,ba
shiri ya sau kara,.Likita sai Dariya yake sha,,.Nuna mishi
har Heartbeats na Babies din ya fara harbawa,,. Hannun ta
ya ruko,"Am Sorry my chocolate,,. Tuni ta sau dariya ita da
likita,.Ta kan kame hannun shi suna Kallon yaran yan yiri
yiri a alon Machine din,.Dr ya juyo bayan sun gama.."Toh
yanzu zamu shiga court da dalili,,.Yai Murmushi,
"afuwan,Yanzu Unique ma Courtn kanta ce.,Toh amma
Dr.,pills din Dana gani kwanaki ka bata fa kuma na planing?
Ya kallo Sa'a,." Madam,wane pills kuma??.Ta kada kai, kan
ta mishi bayani,.Yace "Abokina Ai wannan Antibiotics ne na
bata,koda in akwai infection, ba mai flygyl ba??Ya kada
kai,,." Kuma ance Shima yana zubda ciki..Yai dariya"kai
madam sai kin dage,, Mutumin ki Ba dama ne,,.Yanzu dai
wancan sun wuce,,Ganan wannan,,.Yanzu zata fara sha
dan inganta lafiyar yaran,.cikin zumudi tace"Dr Watan su
nawa??..Ya kallo Hafeez, "Madam fa ta fika dauki,kaji wata
nawa take tambaya,. Yai Murmushi,tare da kallo Sa'an,"
nidai nasan basufi 2 month ba,,.Ya gyada kai, "Suna cikin
week6 ne,,. Sukai Murmushi, sai kuma ta dukar da kai,ita
kunya. Suna fita a asibiti ya bita a baya har suka je gida,.
.
Tana fitowa ya dauke ta chilak,.Da dariya suka shigo,Zahra
ta sau baki tana kallon su,.Ganan ciki ya mata ham a
gaba,,dan ya doshi 7month,,.Kiciniyar sauka take amma
yaki sauke ta,Ganin Girkin Zahran ne,,.Har sama ya kaita a
haka,Wai baison ta wahala hawa stairs.. Tai murmushi,
itama kenan ta shiga sahun su Ummi..Sakalo wuyan shi
tai..tana yai alkawarin babu mai jin cikin ta ko twins take
dauke dasu,in sunzo a bazata yafi.. Yai Jim" anya zan
Iya??.ko Aminu sai Y'aji,,Tai Murmushi, "BBC
kenan??..kace Duniya taji kawai..Yai Dariya, za su sha
mamaki,ba mai ji toh Mom twins,.. Tasa hannu ta rufe
fuska, Wai ita kunyar karya..Ya dungure mata kai yai waje..
Dan yasan Zahra an hau 90.. "Kiyi da jikin ki mana
Zahra,tun kan su dawo,.ta daga K'afa da kyar,,Duk da
gaban ta sai faduwa yake amma bazai hana ta zuwa inda
zata samo yancin ta ba,,EDDn ta cikin satin nan zai
tsaya,.Amma tunda Ta kyalla taga yadda abin Hafeez yake
gaba akan Sa'a tace Ba taga ta zama ba,,.Dan tun kan ta
haifi D'a, ya daina daukin shi sosai,.a Ganin ta Sa'a farraku
tai mata da Hafeez da cikin tun kan yazo Duniya,,.Zuwan ta
na biyu kenan wajen malamai,da taimakon Jummai.
.
Sanye yake da Babbar malun malun,Yaci uban
rawani,,.Ganan wasu manyan charbi da maka makan
littafai, kai ka dauka Qur'ani., Da Ganin fuskar shi yafi kama
da irin yan Duniyar nan,amma in baka kula ba sai ka mishi
Kallon Malami,,.Ya washe baki yana kallon Jummai,. Dama
yana ganin Zahra ya karanci matsalar ta,,. Yace"Kishiya
koh?.Da sauri ta kalli Jummai tana hadiyar yawu,,. Kai ta
kada mishi,,. Ya gyara zama a wayan ce yana kare wa
Zahran kallo,.Wai,chakwala dadi,. Yana son harka da
Matan aure,bare kuma mai juna biyu,. Yasan akan
kishiya,mata sukan yarda da wannan Halin nashi,.Bare
Zahra,da gani ta k'agu.. Sai dai yau,yana da Mai debe
mishi,.Bayan ta gama kwararo mishi bayani ya kallo
Zahran,. "Kuna sake da taimako alhalin kuna da
kishiyoyi,,.Ki duba ki.,duk ta miki dabaibayi da mijin
Ku,zakiga baya rawar kai akan ki,Toh da baki zo da wuri
ba,D'an ma da zaki Haifa bashi ba uban sa,.Tuni ta yarda
har ta fara zufa,.Fadi take,." Yanzu malam ya za ai?,,. Ya
hadiye yawu lokacin da ya kalli bakin Zahran,. Sai wani
marai rai ce wa take mishi,.Ya kallo Jummai,. Yace Zahran
ta jira su a waje,.Dakyar ta tashi,tai waje,.Ya kallo
Jummai,. "Ina kika samo wannan yar dakwala dakwalan?,.
Tai murmushi,." Nidai na sanka da cika aiki malam,.A
taimaki Qawata,.Ya shashe baki,.tare da Shafa gemu,."Kin
tabbata bata da gardama??.Ta kada kai, "indai akan kishiya
ne toh batta gardama,,.Tana kashe ko nawa ne,.Yai
murmushi.." Kizo min gobe da ita.,Zakiga aiki da cikawa..
Tana fita ta kora mata bayani,."Gaskiya Jummai zan so yau
ayi ta ta kare,dan Kinga yadda nake,Gashi dakyar gobe ya
kuma bari na fita,kuma weekend yana gida,.
.
Tace"wannan mai sauki ne,.kedai Allah ya kaimu.,ta kada
kai badan taso ba,.Gidan su ta wuce,.Kamar kullum su
Mamy suna zaune da Auntyn su suna Fira,.Agajiye ta zauna
tana haki,. Mamy ta kallo ta. "Yanzu Zahra baza ki sallama
wa yawo ba haka??..ko tausayin kanki bakya ji??..Ta kallo
ta,. Ruwa Auntyn nasu ta bata,haka ta daga ta
kwankwade,.. Sai da ta samu nutsuwa tukun ta Iya gaida
su,.Mamy ita dai sai fada take akan ta hakura da fita haka,
indai ba Wai haihuwar Titi take nema ba,. Bayan sun shiga
daki take sanar da mamy Wai Sa'a tai mata farraku
tsakanin ta da Hafeez, kuma wallahi itama bazata barta
ba..Hannu tasa a haba Mamyn tana kallon yar tata,." Zahra
ina fata Baki bi hanyar bata ba koh??..Ta kallo ta da rashin
fahimta,. Ta cigaba "A kullum ina fada miki ki kara
hakuri,.Ki fawwala wa Allah lamarin ki,.sannan kisa a ranki
babu mai miki abu sai da ikon Allah.
.
Kishiyar ki mai saukin kai ce,a gani na inkin bita zakiji dadin
zama da ita,.Ki fidda zargi cikin lamarin ki,, Sannan ina
rabaki da Qawayen banza Zahra, wallahi su suke kai mutum
su baro,..Nasiha take mata mai ratsa jiki,kan ta guji bin
malaman Tsibbun nan,Ta kuma kuji sharrin Qawaye Marasa
kan gado,.Duk nasihar ta ratsata,amma banda ta Sa'a, dan
ita ganau ce ba jiyau ba..Tabbas Sa'a ba haka tabar
Hafeez ba,.A haka a ta jogana ta shiga gidan Meenat
Qawar ta,. Duk da ta zubar ta da.,tunda ta samu Jummai,.
Basa shiri da meenat, dan takan tsage mata gaskiya duk
daccin ta, sai dai ba taje gidan ta ba,.takan gaya mata Sa'a
Yar siyasar Duniya ce,zama da ita sai Ka koyi hakuri da Iya
kaima siyasa,sannan a yadda ta kula da ta yi a hankali
zasuyi zaman lafiya da Sa'an, toh fa anan sukai Baran
Baran,. Ita Wai data hada kai da kishiya.toh gwara ta
sallama mata mijin..
.
Da fara'ar ta meenat din ta karbe ta, duk da karshen
rabuwar su da fada suka rabu,.Amma tasan Zahra tasan
Value nata,.Dole gaba zata neme ta,. " Ya kamata ki ajiye
fita Zahra haka,.kinga kafar ki kuwa??,.Tai dan tsaki,."Ke
barni.,fitar ta dole ce,. Nan ta koro mata bayani duk da
tasan ba yarda zatai ba,. Murmushi tai tare da girgiza kai,.
"Zahra,a kullum bazan Gaji da baki shawara ta Gaskiya
ba,koda kuwa zamu b'abe…Sa'a ta fiki Tattalin Hafeez,.a
kan ido na ina gani,kefa?Gani kike Wai duk abinda take Wai
a Ganin ki karuwa ce,.Dole kiga Tasku Zahra, dan Namiji na
tarai rayar mai Taryar shine Zahra,.In yayi rawar kai a
kanta,itama tana yi akan shi,.Ki duba abinda idon Basira,.
Wallahi ki gujewa muguwar Qawa,zata kai ki kawai ta baro
ne,.Shiru tai,a duk zance tana dauka,amma mudin an sako
Sa'a, toh fa sai taji tana mai jin haushin maganar ma..
Karshe sai shiru meenat ta mata.. Duk ta mata gargadi
akan Kar ta koma wajen Bokan nan,dan duk malamin da zai
fada maka haka wallahi Boka ne..Toh taji wannan. Sai dare
Hafeez ya dauke ta sukai gida,.A daran yake fada mata
gobe zai tafiya kwana d'aya.. Washegari gida ita kadai,Sa'a
taje barkar Ummi data haihu da asuba,.Tana zaune,tun jiya
take jin dan milmil,amma taki nuna wa kowa,.Duk Sa'an har
daki ta mata sallamar ta fita.. Tariyo zaman su da Sa'a
take,. Bata taba takallar sunyi fada ba,.Bata taba rama
sharri da sharri ba,.sai dai tai abinda zataji haushi,.matsala
r ta d'aya??.. Data mallake Hafeez ita kadai... Sallamar
Jummai ce ta katse mata tunani,.