Breaking News

*** *BARIKI IYAWA PART 19* ***

*** *BARIKI IYAWA PART 19* ***
.
Ta kallo ta, "Tunanin mey kike haka ina ta kwankwasa kofa
da sallama?? Tai ajiyar zuciya," Kin Sani Ai Jumee.,Ta tabe
baki., "Keda kike da maganin tunani,sai kinje kin kashe
kanki a banza ita kwa tana Shana war ta,.Yanzu ki
tashi.,dan ina da wajen zuwa,.Ta kalli Jummai.. .
.
Ba wata kyakyawa bace,fuskar nan taci bleaching, kan nan
Dan kare da attachment din gashin kanti,.kai da ka ganta
Kaga yar Duniya,,kuma ita Zahra ta zaba a matsayin
Qawa,. Farkon haduwar su a saloon ne tun ana saura 3
month bikin su,a time din taje Shampoo na sallah., Baje
kaya tai tana wa Matan wajen Talla da bayani,Wannan duk
iskancin kishiya kikai amfani dashi sunan ta sorry,,ita tasan
makamar kishiya,tai ta zurma su..anan Zahra ta
zurmu,bata aure,auren ta 3 duk ya mutu,dan da zancen
hakane,toh yaci ta zauna gidan Miji.. Taja gauran numfashi,
tare da kada kai,"Jummai anya zani kuwa?.Dan yau banjin
dadi kadan, sannan wallahi gani nake ma kamar mutumin
nan fa Boka ne,.Jummai tai tsaki.,a zuciyar ta tana tunanin
Kar Zahra ta kwafsa mata,dan har sun shafci kudin da za'a
fadawa Zahran,na kan ya zama nata.. Da sauri ta dawo
wajen ta, " Waya fada miki Boka ne??.Malama inma zaki
ware ki ware,ita ina take??..kika San ita wajen wane bokan
taje??..Nan tai ta zugo ta tare da zugar shedan,suka hadu
suka sha tunanin ta har ta amince,. Tana cije ciwo har suka
je kwalta suka tsaida keke Napep sai wajen Boka..
"Yauwa,Jummai kice ta shigo,.ta kallo Zahra," ki kula,kiyi
yarda Yace,dan wannan ce kadai damar mu da abinda ke
jikin ta..Yanzu ki kawo sarkar naje bakin asibiti na sayar,
dan dole mu cika mishi kudin shi,,.Tai Jim,dan sarkar auren
su ce.,Abban su Hafeez ya sai musu,amma tanaji tana gani
ta cire,sai zugata take.
.
Ai Wai biyan bukata yafi dogon buri,,. Ta shiga ciki,da sauri
ta fito,dan Ganin dakin baki kirin dashi,.sai da ya kara mata
magana tukun ta shiga da sallama,. Ya amsa.,a rabe ta
zauna tana karanto ayatul kursiyu,, Ta zauna,,.Ya taso yazo
kusa da ita,.Zaki tashi ki cire gyalen ki,sai ki kwanta akan
gadon Nan, ya nuna mata wani gu tare da haska mata da
waya,,gaban ta ya fara dukan uku uku,"Gyale
malam??.Yace "eh.,saboda komai ya ratsa Ku keda
yaron,,.Ta kada kai tana Dari Dari,.tun kan ta zauna ya
matso,.Da sauri ta tashi,." Malam mey za ai ne??."Kinga,
ba'a magana a dakin nan,yana kokarin kamo ta ta Matsa da
sauri tana,"Amma Allah ya isa,.Ashe wajen dan iska ta kawo
ni??..Da sauri ya biyo ta,ina Ai ko nauyin cikin ta bataji da
gudu tai waje,.ba gyale bare takalmi,jakar ma ta manto ta
dakin,.Allah yasa doguwar Riga baka ce a jikin ta, ta kunce
dan kwalin,.Tafiya take bata ma San ina zata ba.,Ga wani
azababben ciwo da yafi na tun jiya yana ratso ta,.Wani mai
Taxi ne ya shigo layin da fasinja,.Dakyar take daga kafar ta,
ta zauna a baya tare da sanar shi inda zai kaita,..Tun tana
cije wa har ta bara gantsare wa tana yarfe yatsu,.Mai Taxi
ya kula da ita,.Da sauri ya tsaida mota yana masifa,."Dama
nakuda kike kika shigo min mota salon ki haihu mun
aciki??.
.
Toh wallahi fito,Fito maza.,Dakyar take motsa baki,."Dan
Allah ka karasa ni gida,.Yace"aa..fito.na yafe kudin
ma,.Gashi dai tsakanin su da gidan baifi kwana 2 ba, ga
unguwa sabuwar unguwa ba kowa,.Haka tana ji tana gani
ya dire ta nan,. Ta sawo kan motar ta kenan ta hangi wata a
chan nesa rike da kugu a durkushe,,. Daga gani Matar na jin
jiki,,Sauri take ta koma dan 5 har ta kusa,.Gashi ta bar
Zahra a gida da tsohon ciki,.Ummi tayi tayi ta kai dare
taki,duk da ko ta zo kusa da ita banda habaici bata abin
mata,amma Hakki ne a kanta zama da ita tsakani da Allah
da tausaya wa. Birki taja,kan ta fitotaiy wajen Matar da
kanta ke durkushe,. "Ya salam,Baiwar Allah Daga ina
haka??..Da sauri ta dago kanta dan jin muryar mai
magana,.
.
Ido ta waro dan Ganin mai murkususun...ido fal hawaye sai
cije lebe take. "Sis Zahra mey ya kawo ki nan??..Inalillahi,.C
iccibar ta ta fara,."Kiyi hakuri.,yanzu ma saurin da nake na
dawo gida na barki ke kadai,.Ita dai Cije lebe kawai
take,.Dakyar take fadin"Sa'a ki taimaken zan mutu,.Da
sauri ta bude baya tana fadin"ba zaki mutu ba,kiyi hakuri
muje asibiti,. "Ga waya na ba chargy,na mota yaki min,ban
San wa zan kira ba,,Ya salam,sannu,,.Reverse tai a hankali,
tana hawa kwalta ta fara gudu,.Ganin yadda take zufa yasa
ta kure mata A.C,duk da bata son kamshin dake fita
aciki,.Ajima kadan ta juyo,kan ta kalli titi..Ta mata sannu
yafi a kirga,.Ta kara dabarar sa chargy fir wayan taki
karba,. Suna zuwa ta kira Nurse da attaindance suka
ciccibe ta,.Nurses Yi suke amma ina,fir cervix yaki
budewa,,Ga tazo har 8Cm..Sa'a ta sai kai kawo take,har 6
shiru,sai lokacin ta tuna da Drn dake duba ta,,Tana zuwa
yana kokarin tashi,.Dake yana da kirki sai ya biyo ta..Har
ciki suka shiga,,Yai yan dube duben shi,,.Sai lokacin ta tuna
da ta kira Hafeez ko a wayan wani ne,.Dr ya ara mata
waya,,.Zatai waje Kam ta rike Sa'a Wai Kar ta tafi ta
barta,.Ta zauna a gefen gadon,." Zahra kiyi hakuri,zan kira
Hafeez,yasan halin da muke ciki,InshaAllah zaki sauka
lafiya,.Dakyar ta cika ta,,sai dai tana fita ta cije cije ta fara
mai yawa,.Matsalar protein,Sa'a ta shigo,.Likita yace ta
samu,ta girgiza kai.. "Wallahi matsalar network,yace" Gashi
Preeclampcia ya fara,dan akwai protein a urine din
ta,.sannan ga major problem din,Bpn ta,.Tana ma zuwa
awu kuwa??.Ta daga kai,.."Eclampcia, Dr ya za ai toh??
Subhanallah,. Babu numbern wanda ta rike a Familyn
Hafeez, duk suna waya tana mota,"Baba,.Baban ta ne ya
fado mata,.da sauri ta karbi Wayan,"Dr bari na sanar da
Baban mu sai yazo,.Ya kada mata kai,."Zai fi,.dan a yanzu
(there is no cure for Pre-eclampcia beside delivering of the
baby,.),.And wannan yaki samu wa,cox cervix nata yaki
buduwa,.Ina tunanin. Cs,.shine best solution indai muna
gudun Kamuwar mai duka,.
.
Yanzu zan fita,in kin kira abinda kuka yanke zan nemi
sauran Doctors sai mu shiga emergency... Ta daga mishi
kai,.Juyo wa tai Ta kallo Zahra da hawaye,.Itama mai d'aya
kenan, toh ina ita ma biyu,.Har ranta ta tausaya
mata,.Zama tai a kan gadon tare da ruko hannun ta., Tunda
taji Cs ta tsaida kukan ta,. "Sa'a, Amini dan Allah,. Ta kallo
ta,," Toh Zahra,yanzu ba numbern da zamu kira sai ta Baba
kawai,,.Ga wayan ki kema yana gida,.Tana jin ta ambaci
waya ta tuna inda ta baro jakar tata duka.,Baba ne ya
dauka take sanar shi abinda ke faruwa, Yace "ina shi
Hafeez din,. Tana kuka tace" Baba baya gari,Gashi layin shi
yaki tafiya,.Baba Gashi Ba wanda ya Sani ko a gidan su
Zahran,.Zan sa hannu kawai gudun Kar abinda ake gudu ya
faru,..Yace"Gashi nan zuwa,.. Tunda ta fara wayar zahra
take kallon ta tana hawaye,.Sa'a wace iri ce??..Mai saka
alkairi akan sharri??.. Tun samun cikin nan kullum sai ta
mata gori akan shi,.Ta wa Sa'a abu dayawa a zaman
su,.Duk da zata rama,. Ga niyar ta ta zuwa wajen
malam.,amma Sai gashi yanzu ita ke dawainiya da ita
harda hawaye,..Wani irin kuka ta saka mai cin rai,. Kila ma
Allah ne ya kamata da hakin Sa'a, ga fitar da tai ba tare da
izinin Hafeez ba,Gashi ta kuma tsallake iyakar Allah,. Duk
da ta gude Allah da ta gudo da Kila achan ma zata mutu a
gadon Boka.. Kuka take Sa'an na aikin lallashi,ita a zaton ta
Zafin ciwo ne,.it a ranta tama manta da Zahra kishiyar ta
ce,gani take tamkar Fadeela ce a gaban ta a haka,ga ciki
yai sama ba halamun zai sakko kasa...Hawaye take tana
lallashin ta,."Zahra kiyi hakuri kiyi shiru,InshaAllah yanzu
za'a shiga dake,.Ina tsoron sa hannu ne alhalin babu wani
Babba a kusa..
.
Amma bari na fado wa Dr sai su fara shiri.,kai ta kada
mata, ta bita da kallo har ta fita,.Ba'a jima ba sai gata ta
dawo,tace "Ga nan Baba a waje,.ki daure ki samin numbern
ko mutum d'aya ne a gida,Ta mika mata wayan,.Iyanzu
tama daina jin ciwo,sai Sai abinda ba za'a rasa
ba,.Numbern Mamy ta bata,.Ta tashi,Kamin tai dailing ta
ruko hannun ta,." Sa'adatu, juyo wa tai kan ta amsa,,.ta
kallo Nurses din,"Dan Allah sisters Ku dan bamu waje,.Suka
kada kai sukai waje,.Zama tai tana kallon ta,. Hawaye
take,."SA'ADATU dan Allah ki yafe min duk abinda na
miki,.Ashe da gaske yar uwa kika dauke ni,.Nasan hakin ki
Dana Hafeez ne yake tambaya ta yanzun,.Nasha binki da
sharri kina tsallake wa,.Gashi yau har ta kaini da aikata
Babban aiki,.Wanda nasan yau inna mutu wallahi wuta zani
Sa'adatu... Kuka ta kara fashe wa dashi,Da sauri Sa'an ta
ruko ta,. "Zahra ni baki min komai ba,. Inma kinyi wallahi na
yafe miki,.Amma ki Sani.,Ba'a yanke rabo da Rahmar Allah,
Kar ki kara ambatawa kan ki wuta Zahra,.. Murmushi tai
wanda yafi kuka ciwo,." Sa'a meye hukuncin wanda yaje
wajen Boka a wajen Allah??
.
Ta kallo ta,. "Boka Zahra,.Allah yai mana tsari dasu,. Tace"
Amin,.Sa'a jiya da yau naje gun Boka, tare da taimakon
shaidan da Muguwar Qawa,.Sa'a nayi shirka wa Allah
Alhalin nasan hukunci,. Sa'a Bani da sallah ta kwanaki
Arba'in,. Ga tsinuwar mala'ikun Allah dake bina har na
dawo dan ban tambayi Hafeez ba,.Taya in na mutu yau,zan
ce ina Aljanna??,.Taya ya Sa'a.. Nan ta hau bata labarin
yadda sukai da Shi.,da tafiyar Jummai da gudowar ta har
zuwa Ganin da ta mata,."Allah kadai ya cece ni a yau,da
Tuni na tafka kuskuren da har na mutu bazan Iya goge wa
ba.,.Kuka take kamar ba ita ke labor ba,.Da tsananin
tausayi Sa'a ke kallon ta,. "Ki gode Allah Tunda baki yarda
dashi ba,.Sannan ki gode Allah Tunda kin tuba kin kyautata
niya,.Allahu Gafurur Raheem ne Zahra,. Tabbas kin Tafka
kuskure, Amma baki idda ba... Shigo war Dr ne ya katse
su,." Ga nan Baban ya sa hannu,.sannan ya kira Baban Mai
gidan,.Kar Ku damu,Lafiya za a fito da ita.., Yace Sa'a ta
fita zasu kimtsa Zahran dan wuce wa Operation Room,. Da
kuka Suka rabu da Zahra,ita fa gani take in ta shiga bazata
fito ba,.Burin ta tace wa Hafeez ya yafe mata.. Tana fita
Abba Yace"yanzu na kira shi Alhajn su Hafeez din, Sai Ku
kimtsa,Ganan na basu advance kan a fito da ita,dan 10k
kawai gare ni a gida.., Ta kada kai "Baba mun gode,.Bari
naje gida,dan dakko kayan ta da abin bukata.. Ya kada
kai,.. A hanya Suka hadu da Mama,ta fada mata inda
Baban yake., Tana bude gida waya ta fara sawa a chargy
Allah ya so ta da wuta, Dakin Zahran a bude,ta shiga,kaya
ta debo set uku,karaf kaf ba zani sai skirt sai doguwar
Riga,. In ba shadda ba,duk dinki ita kan batta a skirt, ganan
ranar zani tazo,..Tana bude Dayan Side din ganan kayan
baby duk na mata sai unisex,. Sa'a tai murmushi,. wato
itama mace take so kamar ta?..Allah basu Nagari shine
fata..
.
Allah dai yasa Zahra ba tai tarun Banza ba..,Ta fito ta haura
sama,.Kayan ta masu Riga da zani ta dakko guda 2,ta dau
pillow da sauran abin nema,.Abincin da tai kan ta fita ta
juyo duka,,.Ta Bude ma'ajiyar kudin ta ta dakko kudi,Na
Adashen da suke a office ne,jiyan nan ta dauka,tana burin
rabawa 2.,ta kaiwa su Baba,d'aya tai wa Zahra
siyayya,.30k ta dauka,ta maida sauran,.Ta kulle gidan ta
fito Chargern mota ta sauya,ta kunna wayan,.Kamar mai
jira aka kira,.Hafeez ne,duk hankalin shi a tashe,. " Unique
yau ina kuka shiga ne haka??.. Na kira Zahra wani yana
dauka Wai a gidan shi ta bari!.Bata gidan ne??.Damm taji
gaban ta ya fadi,. Wato dan iskan bokan ne ya
dauka??,.wace karya zata mishi dan wanke Zahra ita kuwa
a yanzu???..katse ta yayi,."Hello,.Da inda inda ta
amsa,."Amm..Dama,.Am,Tun dazu nake kiran Ka yaki
shiga,.Zahran ce dama..Da sauri ya katse ta cikin
fada.."Wajen wani katon ta bar wayar tayi??..Kenan bata
gidan??.."Aa,,Dear Ka saurare ni,.ina ai ta inda yake shiga
ba tanan yake fita ba,."Dan taga bana gari ta sirki wani
iskanci koh.. "Hafeez tana Theater Room..Sit yai dan jin ta
ambaci sunan shi da kuma Theater Room..Sai kuma ya
dawo ya rikice..," Mey ya same ta??..Haihuwar
ce??."Eh.Amma yanzu za'a fito ma InshaAllah,. Ka mata
adu'a.., Ce mata yai ta kashe ga Abba yana kiran
shi...Katse wa tayi,,Tai ajiyar zuciya,. Hafeez akwai
kishi,Tuni idon sa zai rufe..,Tana tsoron yasan abin
nan,Allah yasa Bokan nan Kar ya tona wa Zahra asiri,Tunda
ga Jaka,Takalmi,Gyalen ta duk suna gidan shi.